Citation: Zainab Umar SALEH (2018). Tarihin Samuwar Ilimi Da Makaratun Boko A Ƙasar Hausa Tsakanin (1905-1914). Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 6. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
TARIHIN
SAMUWAR ILIMI DA MAKARATUN BOKO A ƘASAR HAUSA TSAKANIN
(1905-1914)
Zainab Umar SALEH
1.0 Gabatarwa
Idan an
yi maganar samuwar ilimi a ƙasar Hausa, tarihi zai yi ninƙaya ne shekaru masu
yawa da suka gabata. Wannan ya samu ne sakamakon hulɗoɗi tsakanin ƙasar Hausa da ƙasashen Larabawa
kamar yadda za mu ga yawaitar kalmomin Larabci a cikin harshen Hausa, da kuma
samuwar addinin musulunci da samuwar rubutun Ajami, ta haka ilimin karatu da
rubutu a cikin haruffan Larabci ya wadaci al'ummar Hausawa. (Abdullahi, 1997:
shf: 25)
Bayan
cika da batsewar ilimin addinin Musulunci a ƙasar Hausa, kwatsam
Turawa suka gano tarin albarkar ƙasar ta shaƙa, ta hanyar 'yan
yawon buɗe ido da Turawan
Misham da sauransu.Ilimin boko da kafuwar makarantun cikin lallashi da dabaru
suka mamaye yankin ƙasar Hausa.
Kasancewar
waɗannan shekaru ba za a
iya cire su daga cikin tarihin samuwa da buƙatar ilimi da
makarantu a ƙasar Hausa ba (wato 1905-1914)
Duk da
yake Hausawa suna da hanyar koyo da koyarwa kamar tatsuniya, karin magana da
habaici da sauransu, sai dai su wurin karatun a iya cewa kamar ɗakin amare ne ko
tsafaffi ko kuma dandali, yawanci a nan suka fi koyo da koyarwa. Sakamakon cuɗanya da aka samu
tsakanin Larabawa da Hausawa wanda ita ta haifar da masu ilimi da cikin Hausawa
waɗanda suka iya rubutu
da karatu suka ƙirƙiro hanyar rubutu da baƙaƙe da wasulan Larabcin
Hausa. Wannan rubutu shi ake kira da rubutun Ajami. Wannan kuma ya faru ne tun
a ƙarni
na 19-20. Haka kuma ya ci gaba har lokacin da Turawa suka shigo ƙasar Hausa suka haɗu da irin waɗannan Hausawa masu
ilimi. Haka abin ya ƙara faruwa ta yadda Hausawa suka koyi baƙaƙe da wasulan Turawa
wajen rubuta Hausa wanda shi ake kira da rubutun boko.
Takardar
za ta yi duba ne a kan ƙasar Hausa bayan zuwan Turawa da ilimin boko da samuwar
karatun boko a ƙasar Hausa da kuma irin gudunmawar da ilimin boko ya
bayar a ƙasar Hausa.
1.1 Ma'anar
Ilimin Boko
Kalmar
boko dai ta samo asali ne sakamakon haɗuwar Hausawa da Turawa wacce suke mata wani
kallo na kyama ko rashin yadda, ina kyautata zaton cewa kasancewar Hausawa
mutane ne masu raya al’adunsu da kuma ƙin saurin amsar baƙon abu ya sa kalmar
boko yake mata kallon hadarin kaji: Boko ilimin zamani ko rubutun Hausa da
bakaken Romawa” (Ƙamusun Hausa 2006, shf. 50).
(Bunzu:2002)
ya bayyana boko da tsarin rubutu da karatu irin na Turawa. Haka kuma ya ƙunshi tsarin
koyarwarsu da hanyar sanar da ɗalibai koyon karatu, kuma a cikin koyon karatu. Littafi
shi ne lamami wato kalmar boko an samo ta ne daga “book” Haka zalika ya ƙara da cewa Hausawa
mutane ne waɗanda suke ɗaukan duk wani rubutu
da aka yi shi da abin da ya shafi Turawa, ƙarya ce, yaudara ce,
zalunci ne. Misali: idan mutum aka yaudare shi, yakan ce an yi masa book ke
nan. Ya ƙara da cewa “A lokacin da Turawa suka zo ƙasar Hausa sun zo da
salon karantunsu ta hanyar keɓe wuri na musamman kamar ɗaki ko zaure don koyar da ɗalubai kuma a cakuɗa maza da mata,
wannan biri-boko ba gaskiya ba ne.
Shi
ilimin boko hanya ce ta zayyano wasu alamomi a kan takarda ko a kan wani abu
mai bigire don sadar da magana wadda ɗan'adam ya fi faɗinta da fatar baki, a
ji shi da kunne, kamar yadda aka bayyana a baya.
2.0 Ƙasar Hausa Bayan
Zuwan Turawa
Tun
kafin Hausawa su yi mu'amala da Turawa, tuni Turawa sun sarrafa baƙaƙen boko sun yi
rubuce-rubuce cikin Hausa da yawa waɗanda aka buga a cikin mujallu da littattafai
waɗanda ake karantawa a
can a ƙasashen Turai. Su kansu Hausawa ba su san akwai wani irin
rubutu na boko ba sai a cikin ƙarni na ashirin bayan mulkin ƙasar Hausa ya koma
hannun Turawa ne, su Turawan suka ga ya kamata su kafa makarantun koyar da
ilimin boko don horar da 'yan ƙasa waɗanda za su taimaka musu wajen gudanar
da ayyukan mulki a ƙasar. (Yahaya, 1988, shf. 84)
An buɗe makarantun zamani
na farko a Lakwaja da Wusasa ta Zariya a ƙarƙashin ƙungiyar Misham, amma
ba a buɗe ta ba sai da aka yi
'yan gyare-gyare ta yadda zai dace da wannan al'umma. An sami nasarar yin hakan
ne bayan da aka miƙa ragamar jan gorar kafa makarantun gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Sir
Hans Ɓischer bayan ziyarar da ya kai Misira da Sudan da
Gwalkwas (Ghana) domin samo hanyar da za a ɗora jihar Arewa.
A
shekarar 1909 aka buɗe makarantar boko ta
gwamnati ta farko a wurin da ake kira Nasarawa a wajen Birnin Kano. Kamar yadda
tarihi ya nuna cewa tun a karni na 19 Turawa suka aiko da masana domin su
binciki yadda mutanen Afrika suke da kuma yadda al’adunsu ke gudana da yanayin
harsunansu dama addininsu. Sannan kuma su binciko hanyoyin sadarwa da matakan
da suke bita fuskar ciniki da saye da sayarwa. Wannan ƙokari na sanin yanayi
da turawa suka yi, shi ya haifar da kakkafa kungiyoyin turawa masu manufofi
daban-daban(Yahya, 1988, shf. 8). A Ingila an kafa wata kungiya mai suna “Ƙungiyar Afirka” wato
(African Association) a1788, wadda ta ɗauki nauyin aiko da mazaje masu saida rai a
jiragen ruwa da su zo su gano farko da ƙarshen kogin Naija
(Yahya, 1988). Wannnan ƙungiya ita ta turo Mungo Park da Barth da sauransu, waɗanda suka ziyarci
yankunan ƙasar Hausa.
Baya ga
waɗannan ƙungiyoyi na neman
sanin halayen da ƙasashen Afirka suke ciki akwai kuma waɗanda suka zo ƙarkashin kungiyar
Mishan domin yaɗa addinin Kirista a
tsakanin ƙarni na 18-19. Shahararu daga cikin su sune: J.f Schon da
kuma C.H Rabinson da Hans Ɓischer da G.P Bargery da sauransu da
dama. Ta fuskar ‘yan leƙen asiri da sanin labaran ƙasar Hausa kai tsaye
(Malumfashi 2009, shf. 6).
Daga
cikin yan mishan da suka yi tashe kuma suka taimaka wajen gina adabin Hausa da
al’adun Hausawa akwai irin su: G.P Bergery da W.R.S Miller da Hens Ɓischer, waɗanda suna cikin
tawagar mishan ta C.M.S da suka zo Arewacin Nijeriya daga watan Nuwamba ta
shekarar 1900(Yusuf, 2012). Wanda ya fi shahara tun a farko shi ne J.F Schon.
Yawace-yawacen Schon ya sa ya iya harsuna da dama, kuma ta haka ne ya sami
damar yin nazari da rubuce-rubuce kan wasu harsuna, musamman harshen Hausa.
Schon ya wallafa littattafai kan kalmomin Hausa a 1843 da Ƙamusun harshen Hausa
a 1876 da littatafan Karin Magana da labarai da tatsuniyoyin Hausa a 1886 da
kuma littafin Magana Hausa a 1885 da wasu da suka shafi addinin kirista
(Malumfashi, 2009).
Ayyukan
da su Schon suka gabatar sun haska wajen samar da wata kafa ta mayar da adabin
bakan Hausa a rubuce. Don haka tun kafin a kafa mulkin mallaka a ƙasar Hausa a ka mayar
da wasu sassan adabin bakan Hausa a rubuce a cikin harshen Romanci. An tattara
labarai da tatsuniyoyi da karin magana da al’adun Hausawa wuri guda a takarda.
An sami littattafai irin su Specimens of Literature na C.H Rabinson (1896) da
Hausa Sayings da Folklore na R.S (1912) da sauransu.Ta haka ne aka kara faɗaɗa hanyoyin wanzar da ƙagaggun adabin Hausa.
Wani nau’in rubuce-rubuce cikin Hausa na zube na Turawa ‘yan mulkin mallaka.
Turawa irinsu Frank Edger(1911) ya rubuta tatsuniyoyi na Hausa, da su Flec
R.S(1912) da sauransu duk sun yi rubuce-rubuce na zube na Hausa (Malumfashi,
2009).
Bayan Turawan
mulkin mallaka sunyi rubuce-rubuce na zube a cikin Hausa saikuma aka kafa
makarantun boko a Jahar Arewa. Makarantar Ɗan Hausa mai suna Sir
Hans Ɓischer ya buɗe a shekara 1909 a Kano ita ce makarantar
boko ta farko ta gwamnati a Arewa, ko da yake akwai makarantu da ‘yan mishan
suka kafa a Zariya wato a Wusasa Lokwaja tun a shekarar 1900, sannan Manjo
Burdon ya kafa tasa makarantar Elementry a Sokoto a shekarar 1905 (Malumfashi,
2009).
3.0 Karatun
Boko a Ƙasar Hausa
Tafarkin
da Turawa suka ɗauka shine ya wanzar
da abubuwan amfani dangane da al'ummar Hausa. Ta haka aka sami damar zama don
kyautata nazari da kuma rarraba sigogin rubuce-rubucen zuwa azuzuwa mabanbanta.
Shiyasa ko da Turawa suka mallaki ƙasar Hausa, ayyukan
adabi ta fannin tatsuniyoyi da labarai da maganganun azanci sun sami karɓuwa ta hanyar amfani
da harrufan Romawa. Dangane da haka zuwan Turawa ya ƙara taimakawa wajen
kafa makarantu, inda ta haka ne aka ƙara faɗaɗa hanyoyin wanzar da
ayyukan ilimin Hausa. A wannan lokaci ba a yi wani tanadi dangane da tsarin da
za a bi na kyautata ilimin boko ko kuma yadda za a yi dana Musulunci da aka
iske ba. Abin da Turawa suka mayar da hankali a kai shine, tattaunawa kan
batutuwan da suka shafi gudanar da ilimi, sai dai da alama ko da aka fara
wannan tunanin ba a san irin matsayin da za a ba ilimin ba, shin tafiya za a yi
ne da tunanin Mishan waɗanda tuni sun kama ƙasa a wannan fanni ko
kuwa Turawan mullkin mallaka zasu fito da wani sabon tsari ne da ba ruwan shi
da Mishan ko addinin Musulunci? Ko kuwa zasu cigaba da rayar da tsarin da
addinin Musulunci suka riska? Irin wannan tunani shi ne ya shige wa Turawan
mulkin mallaka gaba a dai-dai wannan lokaci. To sai dai wani abin la’akari a nan
shi ne koda yake ta wannan jeka-ka-dawo game da ilmantar da Hausawa ko kuma
musulmin Arewacin Nigeriya wasu daga ciki Razdan-razdan na wannan lokaci sun
nuna irin yadda ya kamata a fito wa wannan harka ba tare da an sami tangarɗa ba, wanda ya fi
damuwa a kan wannan batu shi ne Razdan Manjo Burdon na Sakkwato. Tun farkon
kama aikinsa ya yi watsida tunanin barin Turawa mishan su kafa makarantunsu a
cikin lardunsu da musulmi suka fi yawa. Ganin cewa an fara raja’a zuwa ga
Mishan dama sun ratso ƙasashen musulmi ya sa manjo Burdon ya kafa ta sa
makarantar Elementere a Sakkwato a 1905 Graham (1966-59). Sai dai kamar yadda
nuna damuwa da tsoronsa game da wannan sabon tsari, sarkin Musulmi da hakimai
da dagatai basu ba shi haɗin kai ba, domin kuwa
a shekarar farko ta 1906, ɗaliban ba su wuce huɗu ba. Sai dai daga baya ne sarakunan suka
fahimci ilimin da ake ba yara ba na Kiristanci ba ne, suka fara amincewa da shi
ta yadda ashekarar 1907 akwai dalibai 36 daga masarautar Sakkwato da Gwandu da
Argugun da suke karatu a wannan makaranta ta manjo Burdon.
Saboda
haka tunanin da ake da shi na cewa makarantar gwamnati na farko a Kano ta so ma
zai iya zama tangarɗa idan aka yi
la’akari hoɓɓasar da manjo Burdon
ya yi a Sakkwato ko da yake wasu na iya cewa ba da yawun gwamnatin Ingla aka
soma wannan tsari ba amma tun da har an samar da makarantar, an kuma samar da ɗalibai da malamai har
sun shekara biyu (2) suna koyon darasu da dama, ma iya cewa ɗaliban boko na farko
a ƙasar
Hausa daga Sakkwato suka somo ba daga Kano ba, kamar yadda ya wancin masu
nazari ke nuna a binciken su.
Tun
daga wannan lokaci tattauna batun samar da ilimin boko ga Hausawa bai ragaita
ba domin kuwa batutuwa sun dinga taso wa amma ba a sami ƙarfin da za ayi wani
abu ba a daidai lokacin da Manjo Burdon ke nasa ƙoƙarin a Sakkwato. Tuni
Hans ɓischer ya zama ɗan ƙasa, domin ya sake
dawo wa arewacin Nijeriya a watan Satumba a shekaraa 1903 a matsayin mataimakin
Rasdan a lardin Barno, bayan da ya koma gida daga aikin Mishan da ya yi daga
shekarar 1900 zuwa Fabrairu a 1902 (Graham, 1966, shf. 64).
Da yake
Hans ɓischer ya ƙaro karatu, ya kuma
dawo da digirinsa na biyu, ga shi ya iya Hausa da Larabci sa’annan ya naƙalci arewacin
Nijeriya, domin ya yi aikin mishan na shekara biyu a cikinta, wannan ya sa aka
karɓe shi hannu bibbiyu.
Ya kuma yi aiki tukuru ta yadda aka fara maganar yaya za a yi da batun ilimin
boko? Kowa za a ɗorawa wannan nauyi,
ba wata tababa yawancin Razdan shi suke ga ya dace a ɗorawa wannan nauyi,
musamman kuma da yake mutun ne da ke son Hausawa da aiki tuƙuru domin su, wannan
aminci shi ne ya sa Hausawa suke yi masa laƙabi da Ɗan Hausa.
A
daidai shekarar 1908 ƙimar Hans Ɓischer ta ƙara fitowa fili da
aka fahimci ya naƙalci harshen Kanuri da Fulfulde ba ya ga Hausa da Larabci
da tuni ya ƙware akan su (Graham, 1996, shf. 64). Duk da ba a samar
da ma’aikatar ilimi a arewacin Nijeriya ba a wannan lokacin ba, an sanya Hans Ɓischer ya kasance
shugaban sashen ilmi daga ɗaya ga watan Yuli 1908.
Ganin
cewar bai da ƙwarewa a wannan fanni na ilimi kuma gashi a arewacin
Nijeriya takasance daban dangane da batun ilimin boko a ƙasashen da ke ƙarkashin mulkin
Ingila ya sa aka ba Hans Ɓischer hutun wata shida, aka kuma umar ce shi da kuma ya
ziyarci ƙasashen da Ingila ke mulki da dama, domin ya yi nazarin
tsarin iliminsu, domin yasamu damar gudanar da aikin sa da kyau. An dai tsara
Hans Ɓischer da ya ziyarci ƙasashe kamar su:
Sifros da Masar da Sudan da Gambiya da Saliyo da Gwalkwas da kuma arewacin Nijeriya
(Graham, 1966, shf. 68) daga baya aka kawo Malesiya da kuma Zanzibar cikin
jerin, da aka tace sai aka bar shi da ƙasar Masar da Sudan
da Gwalkwas da kuma Legas a kudancin Nijeriya (Graham, 1966, shf. 68).
Hans Ɓischer ya kai
ziyartar aiki a ƙasar Masar daga ran 1 ga watan Fabrairu na shekarar 1909
inda ya ziyarci makarantun Elemantare guda biyu da Sakandare guda ɗaya, da makarantar
sana’a da makarantar koyon noma da ta masana’antu. A Kartum kuwa zama yayi don ƙaruwar ilimi da
daraktan ilimin ƙasar Sudan James curries, ya koyi yadda aka gudanar da
makarantun boko da suke da na saɓa da Larabci da addinin musulunci. Daga baya
ya leƙa Gwalkwos da Legas (Graham, 1966, shf. 72),ya nazarci
yadda suke gudanar da aikin sun na karantarwa. Daga ƙarshe ya bada
shawarar asamar da tsari mai kama da na Sudan domin shi ne cikakken rahotansa a
watan Satumbar shekarar 1909 (Graham, 1966, shf. 74).
Ba
kamar yadda aka saba ji da gani ba, Hans Ɓischer bai tabbatar
da samuwar boko a daidai lokacin da gwamnati ta tana da ba. Ita dai gwamnati ta
sanya watan Oktoba na shekarar 1910 a matsayin lokaci da za a ƙaddamar da
makarantar, wato shekara da ya da miƙa rahoton Hans ɓischer. Gannin da
sauran lokaci kafin hakan ta faru, dole tasa Hans ɓischer ya ƙera makarantar horan
malamai a watan satumbar 1909, inda ya nemi Rasdan su turo masa yaran da zai
koyar kafin ɗalibai su fara karatu
1910 (Graham, 1966, shf. 79).
Ɗaliban
farko sun zo ne daga lardunan Sakkwato da Kano da Katsina, suma sai da
Razdan-Razdan na yankunan suka matsawa sarakunan yankin su turo da malaman da
za a koyawa aikin malantar. Duk da haka ba a samu haɗin kai ba,domin basu
turo na ƙwarai ba, daga lardin Sakkwato malamai huɗu aka samu harda wani
mai taɓuwar hankali. Duk da
haka Hans Ɓischer bai fasa ba.An buɗe ɗakunan horaswa guda biyu (2) na malamai, Hans
ɓischer shine malami
kuma shugaba, yana koyar da karatu da rubutu da lissafi da labarin ƙasa, ana fara karatu
daga karfe takwas (8) na safe zuwa ƙarfe biyu (2) ko zuwa
huɗu(4). Haka aka dinga
gungurawa har lokacin da sauran sarakuna suka amshi kiran Hans ɓischer sosai ta yadda
daga watan Maris na shekarar 1910 akwai ɗalibai 33 zuwa watan Disamba kuma ɗalibai sun kai
100,(Graham, 1966, shf. 79). Saboda irin wannan cigaba ne da aka samu ya sa
dole aka nemar wa Hans Ɓischer mataimaki, inda aka kawo masa F.Uring Simith daga
Masar, ya kama masa. Ta haka ne aka shiga samar da sauran ma’aikata da malamai,
su kuma sarakuna suna fitar da kuɗi daga bitulmali domin amfanin makarantar,
sai dan taimako da ba a rasa ba daga gwamnatin milkin mallaka.
Kan
nasarar da aka samu daga tsarin da Hans Ɓischer ya kaddanar
aka soma tunanin samar da wasu makarantun a wasu larduna can daban. An fara ne
a Kano, Ƙofar Nasarawa a shekarar 1911. A 1912 kuma aka buɗe wata a Sakkwato da
Katsina, niyyar ita ce ta samar da makaranta ɗaya a kowanne lardi ko babban gari, da
alama kuma komai ya daidaitu domin yawanci malaman sun yawaita, ɗalibai sai tururuwa
suke wannan ya sa aka ƙara ganin ƙimar Hans ɓischer sosai ta yadda
daga 1914 ya zama daraktan ilimi na arewacin Nijeriya na dindindin (Graham,
1966, shf. 96) duk da cewa ba wani sashe da aka buɗe mai kula da harkar
ilimi a wannan lokaci.
Daga
Oktoba na 1912 zuwa Agusta na 1914. Malamai da Turawa masu gudanar da
makarantar sukai ashirin da shida (26). Su kuma ɗaliban da aka yiwa rijista a ranar 31
ga watan Disambar 1913 sunkai 209. Wannan ya jawo ya waitar ƙarancin abubuwan
karantawa, wanda ya sa aka shiga biɗar littattafai da za ayi amfani da su domin
wanda ake da su ba su huce karatun Hausa ba a (1909) da koyan lissafi a(1914)
ba.
An so a
buɗe makarantar horar da
malamai tun a 1914 amma rashin kuɗi ya hana, sai a 1921, inda aka kafa ɗaya a Zariya.
4.0
Kammalawa
Masu
iya magana kan ce, "Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da
farinta", wannan batu ko shakka babu a bisa haka ne aka ɗora akalar binciken.
Hausawa suna da iliminsu tun fil'azal domin sukan yi amfani da shi ne don wayar
wa da mutane kai ko 'ya'yansu ta hanyar tatsuniya da karin magana da habaici da
sauransu.
Maƙalar ta yi nazari ne
musamman a kan abin da ya shafi ilimi da makarantun boko a ƙasar Hausa tsakanin
1905-1914.
An kuma
gano irin ƙoƙarin da Turawa suka yi wajen gano jihar Arewa da samar da
makarantun boko da ire-iren rubutun boko ga 'yan ƙasa. Haka kuma abin
da ya ci gaba har lokacin da Turawa suka shigo ƙasar Hausa suka haɗu da irin waɗannan Hausawa suka haƙiƙance baƙaƙe da wasulan Turawa
wajen rubuta Hausa, da shi ake kira da rubutun boko.
MANAZARTA
Adamu,
A. (2014). Ranar wanka ba a ɓoyen cibi darasi daga tarihi da kuma ƙalubale da ke gaban
harshen Hausa a Yau, Maƙalar da Aka Gabatar a Taron Ƙasa da Ƙasa na Yamai kan
Makomar Harshen Hausa, Wanda Ƙungiyar Marubuta Harsunan Nijar da
Takwararta ta Nijeriya Suka Shirya Daga 192 zuwa Fabarairu 2014, a Emir Sultan Ɓenue, Yamai,
Jumhuriyar Nijar.
Aminu,N.
(2002). Adabin Hausa a zamanin mallaka: Nazari a kan ayyukan Frank Edger,
Kudirin Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jama’ar Usman dan
fodiyo, Sokoto
Bakura
A.R. (2012). Gudunmawar Turawa wajen samuwa da ginuwar adabin Hausa. Kundin
Digiri na Uku, Sakkwato: Jami’ar Usman Ɗan Fodiyo.
Bashir
A.S. da Al”ansar A. I. (2015). Nazarin kwatance adabi na tarihi samuwar
makarantun kwatancen adabi na duniya da matsayinsu a kasar Hausa Maƙalar da aka Gabatar a
Wurin Taron Ƙasa da Ƙasa na Farko kan Tarihin Hausa da
Harshensu a Jami’ar Jihar Kaduna, A ranakun 23-25 (2015).
Bunza
A.M (2002). Tattaunawa a kan littafin ruwan bagaja
Dangambo
A. (1984), Rabe-Raben adabin Hausa da
muhimmancinsa ga rayuwar Hausa. Kano: Madaba’ar Kanfanin “Triumph’’ Gidan
Sa’adu Zungur.
East,
R (1943), Recent actiɓities of the
literature bureau Zaria Northern Nigeria, in Africa Journal of the
International and African Institute, Volume 4 Number 2.
Edger,
F. (1911). Littafi na tatsuniya na Hausa, Belfast W. Erskine mayne, 3 Donegall
West.
Graham,
S. F. (1966). Goɓernment and education
in northern Nigeria 1900-1919 With Special Reference to the Work of Hans ɓischer, Ibadan: University
Press.
Greenberg,
J. H. (1963). The Language of Africa.
Bloomington: Inchana University Press.
International,
I. (1928) Journal of Africa Language and
Culture Vol. 2. London: Oxford University press.
Junaidu
I. da Yar’aduwa, T. M. (2007). Harshe da
adabin Hausa a kammale. Ibadan: Nazareth Press Ltd.
Malumfasshi,
I. (2009). Adabin Abubakar Imam.
Garkuwa Media Services, Limited.
Yahaya,
A.S. (1988). Hausa a rubuce: Tarihin
rubuce rubucen cikin Hausa. Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Yakasai A.S. (1990). Dandalin harshe da al’ada Maƙalar da Aka Gabatar A Bikin Shekara 60 da Fara Rubuta Wasan Kwaikwayon Hausa (1930-1990).

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.