Duk abin da cikin ɗaki ya samu, albarkacin ƙofa ce. Labarin kafuwar makarantun Tsangaya a jihar Kaduna ba zai kammalu ba, in ba a kawo gudummuwar Arc. Muhammadu Namadi Sambo ba. Saboda a shekarar 2009 a ƙarƙashin jagorancinsa ne ya ƙirƙiri shirin kafa makarantar Tsangaya ta kwanan ɗalibai. Makarantar Firamare ta farko da aka kafa ita ce wadda take a Marabar Gwanda a ƙaramar hukumar Sabon gari. Bayan Arc. Namadi Sambo ya zama mataimakin shugaban ƙasa, wanda ya gaje shi marigayi Sir Patrick Ibrahim Yakowa, wanda shi ma mai kishin ilimi ne a jihar Kaduna, ya ba da gagarumar gudummuwa wajen gani tsarin karatun Tsangaya ya tabbata. Wannan a ya sa a ranar 5th Mayu, 2012 ya ƙaddamar da shirin karatun Tsangaya a jihar Kaduna. A yanzu haka makarantar na da yawan ɗalibai 186. A shekarar 2015/2016, ɗalibai 82 suka kammala karatunsu. Makarantar na da malaman koyarwa da marasa koyarwa guda 35.
Muhamman Kalmomi: Karatu; Tsangaya; Jihar Kaduna; Muhammad Namadi Sambo
Sulaiman Salisu Muhammad
Department
of Nigerian Languages and Linguistics
Kaduna State University
08067917740
Gabatarwa
Wannan
aiki, bincike ne wanda ya shafi gano shukar da Arc. Muhammadu Namadi Sambo ya
yi na ƙirƙirƙirar makarantun Tsangaya domin binciko halin da suke ciki a yanzu.
Shin wane ƙoƙari gwamnati
ke yi wajen farfaɗo da rayuwar yara waɗanda aka fi sani da almajirai masu
karatun allo suna bara a gidaje da kasuwanni?
A yunƙurin tsohon
shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan na cim ma shirin muradun ƙarni wajen
ilmantar da dukkan `yan ƙasa, ba tare da wariya ba, gwamnatinsa ta ƙarfafa wani
shiri wanda Gwamnatin Muhammad Namadi Sambo a lokacin yana Gwamnan a Jihar
Kaduna ya ƙirƙira a shekarar 2010. Wannan wani tsari ne da aka fito da shi, na
haɗakar karatun allo tare da na boko.
Tarihin Rayuwar
Arc. Muhammad Namadi Sambo GCON
Shi dai Arc.
Muhammadu Namadi Sambo, an haife shi a ranar 2 ga watan Agusta a shekarar 1954
cikin garin Zariya ta jihar Kaduna. Ya halarci makarantar Firamare ta Baptist
da ke Kakuri Kaduna. Da kuma makarantar Firamare ta Kobi a jihar Bauchi a
shekarar 1959.
Daga shekarar 1967
zuwa 1971 ya zarce zuwa makarantar Sakandare ta Alhudahuda College Zariya.
Alhaji Muhammadu Namadi Sambo ya shiga Jami`ar Ahmadu Bello Zariya daga 1973
zuwa 1978. A wannan Jami`a ya karanci fannin taswirar zanen gine-gine.
Ya yi wa ƙasa
hidima a shekarar 1979 a ma`aikatar ayyuka da gidaje da ke jihar Oyo.
An zaɓe shi a
matsayin gwamnan jihar Kaduna daga shekarar 2007 zuwa 2010. Bayan rasuwar
tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa `Yar aduwa ya rasu, sai Jonathan Ebele Goodluck
ya zame shugaban ƙasa. Daga nan sai ɗauko Arc. Muhammadu Namadi a matsayin
mataimakinsa, a lokacin yana gwamnan jihar Kaduna. Ya yi mataimakin shugaban
ƙasa Goodluck daga 2010 zuwa 2015.
Alhaji Muhammadu
Namadi Sambo yana da mata ɗaya mai suna Amina da `ya`ya shida. Shi ne wanda ya
fara kafa makarantar Tsangaya ta kwana a Marabar Gwanda a ƙaramar hukumar Sabon
Garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Bayani
game da samuwar Almajiri da Allo da Boko
Kafin
tafiya ta yi nisa, bari a yi bayanin yadda bara ta samo asali, har ya kasance
waɗannan yara suna yi. Daga nan kuma sai mu bi diddigin yadda aka yi karatun
boko ya shigo Arewacin ƙasar nan. Amma bari mu fara da bayanin waɗannan kalmomi
uku: (i) almajiri (i) allo (iii) boko. Yin haka zai ƙara mana haske game da
wannan bincike.
Almajiri: Addinin Musulunci,
Annabi Muhammadu (SAW) ne ya zo da shi, daga Allah (SWT). An haife shi a garin
Makka a shekarar 571 AD. Ya taras da iyaye da kakanninsa suna bautar gumaka.
A lokacin da ya
fara yaɗa addinin Musulunci ya sami gagarumar adawa a garin Makka da kewayenta,
daga Sarakuna da masu arziki, da `yan ta`addan gari. Ya yi shekara goma sha uku
yana kira a bauta wa Allah shi kaɗai, amma mafi yawan mutane ba su fahimce shi
ba. Wasu kuma sun fahimta, amma sun kangare. Shi da magoya bayansa sun fuskanci
wulaƙanci iri-iri, ciki har da kora da kisan maza da mata.
Wannan shi ne ya
tilasta wa Manzo (SAW) da mabiyansa yin hijira daga garin Makka zuwa Madina. To
a lokacin nan duk Musulmin da ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, ana kiransa
‘Almuhajir’ wato wanda ya yi hijira.
A lokacin da
Musulmi suka bar garin Makka, sun bar shi ne ba tare da wani cikakken shiri ba.
Sai ya kasance `yan`uwansu Musulmi da ke garin Madina sun riƙa taimaka masu, da
abinci da wurin kwana da wasu abubuwan buƙatar rayuwa.
Sunan ‘Almuhajir’
shi ne a ƙasar Hausa ake amfani da shi ga duk wanda ya bar garinsu ya tafi
neman ilmi, sai ana ce masa Almajiri. Saboda haka duk inda ya je yana buƙatar
taimako. Wannan shi ya sa dukkan yaran da iyayensu suka tura su wasu garuruwa
ake kiransu da sunan Almajirai.
Allo: Da harshen Larabci, itacen da aka sassaƙa
shi ana rubutun Alƙur`ani, ana kiransa da sunan ‘Allauhun’ Wannan kalma ita ce
Bahaushe ya Hausantar da ita ta koma Allo. Saboda haka duk makarantar da ake
amfani da Allo, sai ana kiran ta da sunan makarantar Allo.
Boko: Akwai mabambantan fahimta na masana
dangane da inda aka samo asalin kalmar ‘Boko.’ A fahimta ta farko, wasu na
ganin an samo ta ne daga kalmar ‘Book.’ Wato littafi. Wannan kalmar ce Bahaushe
ya Hausantar da ita ta koma ‘Boko.” Bunza. (2002: 24)
Fahimta ta biyu: A
ƙasar Hausa tun kafin zuwan Turawa, akwai abin da ake kira: “Amaryar Boko.”
Idan an ɗaura aure, bisa al`ada akwai amare iri biyu: Akwai amaryar ƙarya, wata
`yar ƙaramar yarinya ce, wadda za a fara kai ta ɗakin Ango. Bayan Amaryar boko
ta shiga ɗaki, daga bisani, sai Amaryar gaskiya ta bi bayanta. Wannan shi ne
kwatancin karatun boko, da karatun addinin Musulunci. Karatun addini shi ne na
gaskiya, na boko kuma na ƙarya. Abdullah. Hira. (BBC: 2014)
Tsarin Karatun Allo: Shi dai tsarin
karatun allo, a cikin masallaci ko a farfajiyarsa ko kuma a ƙofar gida ko a
Tsangaya ake yin sa. Tsari ne wanda iyaye daga garuruwa ke turo `ya`yansu zuwa
ga wani malami. A irin wannan tsari iyaye ba sa biyan kuɗin makaranta, babu
kuma wani tanadi na abinci da aka yi wa Almajiran. Mafi yawan yaran sun dogara
ne da bara a kullum suna yi domin su sami abin kalaci. (Abdulmalik 2010)
Manufar Bincike
A duk lokacin da mutum ya ɗauki alƙalami domin gudanar da bincike, a
cikin zuciyarsa akwai dalilai day a sa yake son gudanar da wannan binciken. Shi
ma wannan bincike, ba a bar shi a baya ba. Akwai dalilai da dama da suka sa za
a gudanar da wannan bincike: Daga cikin waɗannan dalilai akwai:
i.
Rawar da
Arc. Muhammadu Namadi Sambo ya taka wajen kafuwar makarantun Tsangayu a jihar
Kaduna.
ii.
Shin malam
sun karɓi wannan shiri na tsarin karatun tsangaya a jihar Kaduna?
iii.
Gano wane
tasiri wannan tsarin karatu na tsangaya ya yi a kan malamai da ɗaliban wannan
shiri?
iv.
Binciko
nasarorin da wannan tsari na karatun Tsangaya ya samu a jihar Kaduna.
v.
Binciko
ƙalubalen da ke fuskantar wannan shiri na karatun Tsangaya a yanzu.
Hanyoyin
Gudanar Da Bincike
A yayin gudanar da wannan bincike, ana sa ran za a ziyarci wurare kamar
haka:
i.
Ma`aikatar
ilimi ta jihar Kaduna da ta tarayya, domin samun ƙarin bayani ta yadda suke
gudanar da tsarin koyarwa na Tsangaya a makarantunsu.
ii.
Ziyartar
wasu makarantun Tsangaya a jihar
Kaduna da tattaunawa da malamai da ɗalibai domin jin yadda suke gudanar da
tsarin koyarwa a makarantunsu.
iii.
Sannan za a
yi hirarraki da wasu wasu shugabannin al`umma domin jin ra`ayoyinsu dangane da
wannan tsarin karatu na Tsangaya.
Bitar Ayyukan da Suka Gabata
“Da na gaba ake ganin
zurfin ruwa.” Tsarin karatun Tsangaya ya samo asalin tun da Hausawa suka karɓi
addinin Musulunci. Akwai masana da dama da suka gudanar da bincike game tsarin
tsangaya da almajirci. Daga cikin magabata da suka tofa albarkacin bakinsu game
da almajirci da almajirai akwai:
Bunza (2002) Ya yi
bayanin cewa: Kafin a gabatar da ilimin karatun boko a yankin Arewa, sai da
Gwamna Lugga ya sa aka yi bincike don gano yawan makarantun allo da ake da su,
da kuma yawan almajiransu. A farkon ƙarni na ashirin an gano makarantun allo
fiye da 25,000.00 da yawan ɗalibai fiye da 218, 618.00 a Arewa.
Saboda haka kafin
gwamnati ta fara kafa makarantun boko, sai da ta yi gyare-gyare a fanin bayar
da ilmi, ta yadda zai dace da irin al`ummar da za ta mulka, domin kar a sami
tangarɗa.
Bisa wannan
dalilin a 1909 Gwamna Lugga ya zaɓi wani Bature mai suna Sir Hans Vischer wanda aka fi sani da sunan Ɗan Hausa.
Aka naɗa shi jami`in ilimi a jihar Arewa. Bayan ya kama aiki, sai aka tura shi
domin ya ziyarci Misra, da Sudan, da waɗansu ƙasashen Musulmi. An yi haka ne
domin ya nazarci yadda suke gudanar da tsarin iliminsu, wanda ya haɗa da ilimin
addini da karatun boko, ta yadda zai dace da mutanen Arewa.
Bayan ya dawo daga
ziyarce-ziyarcen da ya yi a wasu ƙashen Afirka, sai aka buɗe makarantar
gwamnati ta farko a Nasarawa Kano a shekarar 1909. Wannan ita ce makaranta ta
farko wadda aka fi sani da sunan makarantar Ɗan Hausa. Kafin a fara koyarwa sai
da Ɗan Hausa ya zaɓi ƙwararrun malaman Arabiyya domin su taimaka masa wajen
koyarwa. Samar da makarantu da aka yi, ya taimaka wajen yaɗuwar karatun boko a
ƙasar Hausa.
Fafunwa (1974) Ya
yi bayanin cewa: Addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun a ƙarni na sha huɗu
(Ƙ.14) A sakamakon ziyarce-ziyarcen kasuwancin shahararren malamin addinin
musuluncin nan daga Afrika ta Arewa Almaghili.
A nasa bayanin,
Yahaya (1988: 90) ya yi tsokaci a kan yadda Turawan mulkin mallaka suka shigo
yankin Arewa har suka yi nasarar kakkafa makarantu a sassa mabambanta a yankin
Arewa.
Yahaya (1988), Ya
ƙara da cwa, Turawa ba kawai karatun boko suka yi yuƙurin kafawa a Arewa ba,
har da makarantun Tsangaya. An yi tsari ta yadda za a haɗa karatun boko da na
addinin musulunci a makarantun da suka kakkafa.
Musa (2008) Shi
kuma ya kalli tsarin karatun Tsangaya ne
jiya da yau. A inda ya danganta
tsarin da karɓar addinin musulunci da Sarakunan Kenam Borno suka yi. Bilkisu
(2013), Ita kuwa ta yi ƙoƙari ne wajen binciko manufofin da suka sa aka kafa
makarantun Tsangaya.
Tahir (2013) Shi
kuwa ya yi tsokaci ne kan yadda ya kamata makarantun Tsangaya su kasance a
yanzu. A bayaninsa ya ga dacewar kafa makarantun Tsangaya iri biyu: Ta farko
ita ce wadda za a kafa a makarantun allo in da ɗalibai ke karatunsu na yau da
kullum. Wato almajirai na zaune tare da malamansu na allo, sai kuma a sami wasu
malamai na boko su riƙa zuwa makarantar suna karantar da su, a wasu ranaku na
musamman.
Tsari na biyu
kuwa, shi ne in da za a gina cikakkiyar makaranta ta zamani, a ɗauki ɗalibai da
malamai masu koyar da karatun boko, da kuma masu koyar da karatun allo.
Tattara
Bayanai
Shigar
Kwamitin Bayar Da Ilimi Na Bai Ɗaya Da Hukumar Tallafa Wa Ilimi ta ƙasa
Jihar Kaduna na ɗaya
daga cikin jihohi goma sha biyar da suka ci gajiyar UBE tun a wajen shekar
2006. Wannan shiri (Integration of Ƙur'anic and Tsangaya education (IƘTE)) an
sanya shi a cikin tsarin nan na ilimi bai ɗaya. (Uniɓersal Besic Education UBE)
Hukumar da ke
gudanar Tsarin Ilimi na bai ɗaya ya umarci Kowace jiha da ta gudanar da abubuwa
kamar haka:
i.
Kafa kwamiti na jiha wanda zai kula da
tsarin gudanar da karatun Tsangaya. Wannan kwamiti zai ƙunshi dukkan wakilan
ma`aikatun ilimi da ƙungiyoyi masu zaman kansu.
ii.
A tattara bayanan farko game da makarantun
Alƙur`ani da ake da su a kowace jiha.
iii.
A tsarin shirin faɗakarwa da neman goyon domin
a sami goyon bayan aiwatar da shirin.
iv.
A gano manyan buƙatun da makarantun ke
buƙata.
Daga
ƙarshe an kafa kwamitin zartarwa na jiha mai ɗauke da membobi kamar haka:
i.
Ƙungiyar Jama`atu Nasirul Islam (JNI)
ii.
Ma`aikatar ilimi
iii.
Hukumar Kula da al`amurran addinin
Musuluci
iv.
Ofishin mai girma gwamna a ƙarƙashin
jagorancin mai ba gwamna shawara a kan harkokin addinin Musulunci.
v.
Ƙungiyar mata Musulmi ta ƙasa (FOMWAN)
vi.
Masu ƙudurin cim ma muradun ƙarni
vii.
Cibiyar ilimi ta ƙasa (ERC)
viii.
Sakatare zai fito daga hukumar ilimi na
bai (UBE)
ix.
Ƙungiyar Alarammomi ta jiha
Kafa kwamitin ke
da wuya, sai ya duƙufa wajen gudanar da ayyukansa. Daga cikin manyan ayyukan
wannan kwamiti akwai:
a.
Yunƙurin binciko dukkan makarantun allo da
ke ƙananan hukumomi 23 na jihar
Kaduna.
b.
Shirya wayar da kai ko faɗakarwa da shirya
tarurruka da ziyartar iyayen ƙasa Sarakuna da shugabannin addini da alarammomi
da ke jihar Kaduna. Daga ƙarshe sai aka kafa makarantun Tsangaya na somin-taɓi
guda 35 a dukkan faɗin jihar Kaduna domin su fara shirin na gwaji a jihar
Kaduna. Waɗannan makarantu da aka kakkafa guda 35 ga su kamar haka:
S/NO |
Ƙananan
Hukumomi |
Sunayen
Makarantu |
Yawan
Ɗalibai |
Mazauninsu
|
|
1 |
Kaduna North |
Makarantar Ƙur`ani ta Alaramma Ahmad |
64 |
No: B5 Sch. Road Ung. Rimi Kad. Ur |
|
2. |
Kaduna
North |
Hidayatul Auladi Muslimina |
64 |
No: KK Biba Cresent Kawo Kd. U/Area |
|
3. |
Kaduna North |
Makarantar Alaramma Ibrahim Abdu |
65 |
No: L4 Kankara Rd. Kawo Kd. U/Area |
|
4.
|
Kaduna
North |
Makarantar Alaramma Rabi`u Ibrahim |
65 |
No: 15 Jama`a Rd. Kwaru Badarwa Kd.
U/Area |
|
5. |
Kaduna
South |
Makarantar Shaikh Ɗahiru Bauchi |
90
|
No: DD 6 Ring road Bye pass Kd (u/Area |
|
6. |
Kaduna
South |
Makarantar Gwani Umar |
70 |
Ibr. Taiwo Soba Strt. T/wada Kd. (U/Area |
|
7.
|
Kaduna
South |
Makarantar Inda Liman Gwani Awwal |
90 |
Ibr. Taiwo Soba Strt. T/wada Kd. (U/Area |
|
8.
|
Giwa
|
Makarantar Malam Lawal |
100 |
Yakawada Giwa (Rural Area |
|
9.
|
Giwa
|
Makarantar Liman M. Lawal |
70 |
Gangara Giwa (Rural Area) |
|
10. |
Sanga |
Ƙur`anic Integration Sch. |
177 |
Gwantu Sanga (Rural Area) |
|
11.
|
Sanga |
Ƙur`anic Integrated Sch. |
177 |
Gwantu Sanga (Rural Area) |
|
12. |
Birnin
Gwari |
Makarantar Ƙur`ani ta Jan Birni |
80 |
Jan Birni Birnin Gwari (R/Area) |
|
13. |
Birnin
Gwari |
Kutemashi Ƙur`ani |
90 |
Kutumeshi B/Gwari(R/Area) |
|
14. |
Zariya |
Makarantar Baba Abubakar |
43 |
Kofar Kuyanbana Zariay (U/Area) |
|
15. |
Zariya |
Makarantar Ahmad Goya |
44 |
T/wada Zariya (U/Area) |
|
16.
|
Zariya |
Makarantar Mal Sa`idu Ibrahim |
43 |
T/wada Zariya (U/Area) |
|
17.
|
Sabon
gari |
Makarantar malam Usman Idris Muchiya |
125 |
Tsugugi S/G Zariya (U/Area) |
|
18.
|
Makarfi |
Ƙur`anic Integrated Sch. Gubuchi |
57 |
Gubuchi Makarfi (R/Area) |
|
19.
|
Kajuru |
SUBEB Pilot Ƙur`anic Sch. |
98 |
Kasuwar Magani Kajuru(R/Area |
|
20.
|
Chikun |
Ƙur`anic Sch. Kujama |
65 |
Keke B Kujama (R/Area) |
|
21. |
Kudan |
Makarantar Malam Abubkar Abdullahi |
63 |
Sabon gari Kuda (R/Area) |
|
22.
|
Kagarko |
Makarantar malam Shehu U/Kara |
40 |
Jere (R/Area) |
|
23. |
Kagarko |
Makarantar Malam Yunusa Kabeji |
35 |
Kagarko (R/Area( |
|
24.
|
Kauru |
Ƙur`anic Sch. Kauru |
35 |
Kauru (R/Area) |
|
25.
|
Lere |
Integrated Ƙur`anic Sch. |
250 |
Lere (R/Area) |
|
26.
|
Igabi |
Makarantar Malam Zangina Habibu |
55 |
Birnin Gwari Rigasa Road(U/Area) |
|
27.
|
Igabi |
Makarantar Malam Abdullahi Balarabe |
55 |
Ifira Ɓillage (R/A) |
|
28.
|
Igabi |
Makarantar Malam Gwani |
55 |
Tudun Nufawa Kd. (U/Area) |
|
29.
|
Zangon
Kataf |
Ƙur`anic Sch. Zonkuwa |
86 |
Kofar gidan Alh. Namadi Zankuwa |
|
30. |
Jema`a |
Mak. Riyadul Ilmi |
198 |
Godogodo (R/Area) |
|
31. |
Jema`a |
Makarantar Isalul Khairat |
197 |
Kafanchan (R/A) |
|
32. |
Ikara |
Mkarantar Tahfizul Ƙur`an |
36 |
Sabon gari Auchan (R/Area) |
|
33. |
Ikara |
Makarantar Malam Ya`u |
30 |
Ikara (R/Area) |
|
34.
|
Soba |
Pilot Integrated Ƙur`anic Sch. Soba |
163 |
Lungu Soba R/Area) |
|
35. |
Kachia |
Integrated Ƙur`anic Sch. |
250 |
Unguwar gabas Kachiya(R/Area) |
|
|
Jimilla |
3043 |
|
||
Waɗannan su ne makarantun
gwaji da aka amince da su waɗanda hukumar SUBEB, za ta tura ƙwararrun malamai
masu karantarwa a Firamare ta gwamnati domin su riƙa karantarwa a waɗannan
makarantu. Duk da yake makarantun za su kasance a ƙarƙashin kulawar alarammomi
wato masu su na ainihi. Waɗannan alarammomi su ne za su riƙa karantar da
karatun Alƙur`ani da sauran fannoni da suka shafi ilimin addinin musulunci. Su
kuma malaman da aka tura, za su riƙa koyar da karatun boko. Kafa harsashin
wannan tsari wanda aka yi shi a shekarar 2008, an gano abubuwa kamar haka:
i.
Makarantun
allo na Alƙur`ani 5,108
ii.
Yawan
ɗalibai 196, 249
iii.
Alarammomi/Malamai
7768
A bisa amincewar
kwamiti na ƙasa mai kulawa da tafiyar da tsare-tsaren gudanar da bayar da
ilimin Tsangaya, ya amince da a tafiyar da shirin makarantun Tsangay nau`i uku
kamar haka:
Tsari
Na 1
Aiwatar da karatun
Tsangaya a ainihin makarantun Tsangayoyi a mazauninsu na asali. Ba tare da ɗalibai
sun je ko`ina ba. A ƙarƙashin wannan shirin, an tanadi abubuwa kamar haka:
i.
Gina farfajiya mai ɗauke da azuzuwa karatu
guda 2 da Ofishi da ɗakin ajiye kaya.
ii.
Babban ɗaki wanda zai iya ɗaukar ɗalibai
50
iii.
Famfon ɗiban ruwa na tuƙa-tuƙa
iv.
Babban falo na karatun Alƙur`ani
v.
Sannan a tanadi makewayi
Tsarin karatun
Tsangaya na II
Shi kuma wannan
tsarin karatun Tsangaya, za a aiwatar da shi ne a makarantun Islamiya wato
Ma`ahad. Za a riƙa koyar da karatun Islamiyya da na boko a tare. A ƙarshin
wannan tsarin za a gyara makarantun da samar masu da duk wasu buƙatun
makarantun.
Tsarin
Karatun Tsangaya na III
A ƙarƙashin wannan
tsari, za a gina cikakkiyar makaranta ce ta zamani mai ɗauke da abubuwa kamar
haka:
i.
Gina ɗakunan karatu guda shida ko bakwai
ko fiye da haka
ii.
Gina ɗakin bincike guda 2 da ɗakin ajiyar
kaya guda 2
iii.
Ofishin malamai da cibiyar na`ura mai ƙwaƙwalwa
iv.
Tsarin sanin makamar aiki da cibiyar koyar
da sana`o`i
v.
Bangajin falo wanda zai ɗauki ɗalibai 200
vi.
Ɗakin cin abinci da ɗakin ajiyar abincin
vii.
Bangajin ɗaki na karatun Al`ƙur`ani
viii.
Gidan shugaban makaranta da sauran malamai
Shirin Tallafa wa ilimi na ƙasa (Support
By Education Sector Support Programme In Nigeria (ESSPIN)
Shirin nan na
tallafa wa ilimi a Nijeriya (Education Sector Support Programm in Nigeria)
(ESSPIN) ya yi tasiri sosai wajen ci gaban tsarin karatun Tsangaya a Tsangaya a
jihar Kaduna. Wato (Integrated Ƙur`anic Tsangaya Education) (IƘTE)
Hanyoyin da yake
bi wajen tallafa wa wannan tsari na karatun Tsangaya akwai:
i.
Tsara
yadda za a tafiyar da yanayin koyarwa a makarantun jiha.
ii.
Agaza
wa shirin karatun Tsangaya a makarantu 192, da ɗalibai 12,470 a ƙananan
hukumomi guda 9. Waɗannan ƙananan hukumomi gas u kamar haka: Kajuru da, Kudan
da, Makarfi da, Kachia da, Jema’a da, Kagarko da, Kaduna North da, Kaduna
South, da Igabi
MAKARFI LGEA
KUDAN LGEA
KAJURU LGEA
IGABI LGEA
AREWACIN KADUNA
KADUNA SOUTH
LGEA
JEMA’A LGA
KACHIA LGEA
KAGARKO LGEA
|
Nasarorin Da
Shirin Karatun Tsangaya Ya Samu
i.
Horar da Malaman Makarantun Tsangaya:
A ƙarƙashin wannan
shiri an horar da malamai guda 200 domin su sami ƙwarewa a kan wannan tsari na
haɗa karatun allo da kuma karatun boko.
ii.
Tsarin
Ciyar da abinci a makarantun:
A makarantun kwana
ne kawai ake ciyar da ɗalibai. Hukuma na kashe wajen Naira Miliyan 4 a kowane
wata domin gudanar da makarantun kwana guda uku a jihar. Wato makarantar
Tsangaya ta Marabar Gwanda a ƙaramar hukumar sabon Gari da ta
Birnin Gwari da kuma ta Huƙuyi a ƙaramar hukumar Kudan. Akwai kulawa sosai
wajen kiwon lafiyar ɗaliban da sauran buƙatunsu na rayuwa.
iii.
Raba
wa ɗalibai suturu da litattafai:
Tun da aka kafa
makarantun Tsangaya a shekarar 2010, ɗalibai ana ba su suturu da litattafai
kyauta ne. Hukumar SUBEB ce ke da alhakin bai wa ɗalibai litattafai da suturu
idan buƙatar haka ta taso.
iv.
Biyan Malamai Alawans na taimakawa:
Alarammomi da ke
koyarwa a makarantun farko guda 35 ɗin nan ana biyan su alawans na dubu #9,000.00
a duk ƙarshen wata huɗu. Wannan ya ƙunshi ɗaukacin malaman da ke koyarwa a ɗaukacin
jihar Kaduna.
v.
Shigar
da karatun boko cikin karatun Tsangaya ba tare da ƙyama ba
vi.
Kafa
makarantar firamare ta Tsangaya ta kwana ta farko a Marabar Gwanda, wanda
gwamnatin jiha ta yi.
vii.
Haɗu
guiwa da cibiyar gudanar da shirin nan na tallafa wa ilimi (ESSPIN) wajen samar
da ilimin farko a makarantun Tsangaya guda 181 a jihar Kaduna. A sakamakon
wannan haɗin guiwa, an samar da abubuwa kamar haka:
a.
Samar
da hanyar gudanar tsarin karatun Tsangaya a jihar Kaduna
b.
Shigo
da malamai `yan sa-kai cikin tsarin, guda 246 da bas u alawans na #4000 a duk
wata. Waɗanda aka tantance su, aka horar da su, sannan aka tura su zuwa
makarantun da suke aiki a yanzu.
c.
Kai
kayayyakin aiki zuwa makarantun kamar litattafan koyar da Ingilishi da Lissafi
da dai duk wasu kayan tallafa wa karatu. Wannan ya haɗa da kayan zuba ruwa.
d.
Shigar
da aikin noma cikin tsarin. Wannan zai taimaka wa Alarammomi wajen samar wa
kansu yadda za su ciyar da kansu, da almajiransu. Wannan zai taimaka wajen hana
su barace-barace. A ƙarƙashin wannan shirin, ana tallafa masu da irin shuka da
takin zamani da maganin ƙwari. Sannan akwai malaman gona suna bas u shawarwari.
Duk da yake
ƙalilan daga cikin Alarammomin sun zaɓi duk wata a ba su #3000, a maimakon yin
noma.
Matsalolin da makarantun Tsangaya ke
fuskanta
i.
Rashin
halartar makarantu da ɗalibai ba sa yi sosai. Wasu kan je jefi-jefi ne.
ii.
Hijirar
da ɗalibai ke yi. Wasu ɗaliban ba zaunannu wuri ɗaya ba ne. Sukan zo ci-rani
ne. Da zarar damuna ta faɗi, sai su koma garuruwansu na asali. Wannan na haifar
da matsaloli.
iii.
Ƙarancin
malamai masu karantar da karatun boko. A wasu makarantun da ke da ɗalibai fiye
da ɗari, sai ka ga malami ɗaya ne ke koyar da su.
iv.
Rashin
isassun kayan aiki. A wasu makarantun kayan aikin da ake kai masu ya yi ƙaranci
saboda yawan ɗaliban.
v.
Rashin
yanayin koyarwa mai kyau a sakamakon rashin isassun makewayi. Sannan akwai
ƙarancin azuzuwa da tebura da kujeru da litattafan karatu.
vi.
Idan
dambu ya yi yawa, ba ya jin mai. Akwai rashin isassun kuɗaɗen gudanar da
makarantun.
Kammalawa
Duk abin da ciki ya samu, albarkacin baki ne. Ta yin la`akari da nasarori
da wannan shiri na karatun Tsangaya ya samu a jihar Kaduna, za mu ce lallai
Arc. Muhammadu Namadi Sambo ya yi dogon tunani da ya ƙirƙiri wannan shiri. Ba
domin tunaninsa ba, ƙila da duk waɗannan nasarori ba a same su ba.
Shawarwari
Gwamnatin jihar Kaduna na yin iyakacin bakin ƙoƙarinta na ganin shirin
nan ya ɗore. Duk da haka ya kamata a sake duba wasu abubuwa kamar haka:
i.
Ƙara buɗe sababbin makarantu, saboda waɗanda ake da
su a yanzu sun yi ƙaranci.
ii.
Samar da kayan aiki ga ɗalibai. A yanzu a wasu
makarantun ba su da isassun kayan rubutu.
iii.
Gina sababbin azuzuwa domin guje wa cunkoso a cikin
aji
iv.
A tabbatar da yaran da ake ɗauka almajiran ne. Wasu
iyaye saboda alaƙarsu da wasu malamai ko ma`aikatan gwamnati, ba almajirai ba
ne, amma sai su kai `ya`yansu makarantun ganin cewa komi kyauta ne.
v.
Ɗaukar sababbin malamai, musamman masu karantar da
karatun boko.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.