Cite this article as: Toki, O. T. & Iwalesin M. J. (2025). Kinin Ma’ana a Wasu Wakokin Ummaru Bagobiri: Nazari Ta Fuskar Muhallin Magana. Zamfara International Journal of Humanities, 4(1). www.doi.org/10.36349/zamijoh.2025.v04i01.008.
KININ MA’ANA A WASU WAƘOƘIN UMMARU BAGOBIRI: NAZARI TA FUSKAR MUHALLIN
MAGANA
Na
Muhammad Zaharaddeen Bello, PhD
Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua University,
Katsina
Da
Sirajo Ibrahim, PhD
Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua University,
Katsina
Tsakure:
Wannan takarda ta yi bayanin yadda Ummaru Bagobiri ke
amfani da kalmomi da suke da bambancin ma’ana a matsayin kalmomi masu kinin
ma’ana wajen gina ɗiyan waƙoƙinsa. Irin waɗannan
kalmomi kan samu bambanci dangane da ma’anonin da suke ɗauke da su, amma
Ummaru Bagobiri na amfani da hikimarsa wajen amfani da su cikin jumla a matsyin
kalmomi masu kinin ma’ana. Hanyoyin da aka bi wajen tattaro bayanai dangane da
wannan takarda kuwa, sun haɗa da sauraren waƙoƙin Ummaru Bagobiri da ganawa da masana da suke
da alaƙa da ɓangaren
ilimin kimiyyar harsuna. An kuma karanta ayyukan da masana suka wallafa dangane
da waɗannan ɓangarori na ilimin kimiyyar harsuna, musamman waɗanda suka
shafi ilimin ma’ana. An kuma yi amfani da hanyar hira da ma’abota saurarren waƙoƙin Ummaru Bagobiri don jin irin ma’anonin da
kalmomin ke ɗauke da su. Don ganin an sami madogara dangane da bayanan da
aka yi cikin wannan takarda, an ɗora wannan bincike ne a kan ra’in Speber
da Wilson, 1995, waɗanda suka samar da ra’in dangane da muhallin magana a
bigeren alaƙa. Binciken ya gano cewa
muhallin magana na taka rawa sosai wajen fayyace ma’anar irin waɗannan jimloli.
Har wa yau, binciken ya gano cewa Ummaru Bagobiri na amfani da hikimarsa wajen
amfani da kalmomi masu mabambanciyar ma’ana a matsayin kalmomi kalmomi masu
kinin ma’ana wajen ginin ɗiyan waƙoƙinsa.
Fitilun Kalmomi: Waƙƙoƙi, Ma’ana, Kalmomi, Kinin Ma’ana, Waƙoƙi
1.0 Gabatarwa
Wannan takarda ta yi bayanin yadda kalmomi ke samun kinin ma’ana a
wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙin Ummaru Bagobiri mai
waƙar dambe a cikin jumla. Kamar yadda za a gani
nan gaba, kalmomi ne ke haɗuwa su tayar da jumla mai ma’ana a cikin harshe. Sai
dai dangane da ma’ana, a iya cewa, aba ce wadda ke iya canzawa a kowane lokaci,
musamman abin da ya shafi isar da saƙon da ke ƙunshe cikin zuciyar mai magana da kuma irin
fahimtar da mai saurare ya yi wa wannan kalma lokacin da take ita kaɗai, ko ta
la’akari da muhallin da ta fito a cikin jumla. Wannan takarda tana ƙunshe da misalai daga waƙoƙin Ummaru Bagobiri mai waƙar dambe.
A taƙaice, Kinin Ma’ana
(synonyms), na nufin wurin da ake samun kalmomi biyu mabanbanta amma kuma suna
da ma’ana iri ɗaya a harshe guda.
Wannan rukuni na kalmomin Hausa suna zuwa da tsarin rubutu
daban-dabban, haka kuma, sautin kalmomin ma ya bambanta. Sai dai kuma kalmomin
kan kasance da ma’ana ɗaya. Amma ya kamata a fahinci cewa danagane da abin
da ya shafi nahawun harshen Hausa, duk da kasancewar irin waɗannan kalmomi na
zuwa da ma’ana guda watau suna wakiltar abu ɗaya dangane da ma’ana, ba
kodayaushe ake iya amfani da duka kalmomin a cikin jumla ba, sai dai kuma ana
iya amfani da su duka a cikin jumla ɗaya kuma sub a da ma’ana cikakka.
Muhallin magana wani ɓangare ne da ya shafi nazari a
kan yadda gurbin da aka yi magana ke ba da gudummawa wajen fito da ma’ana.
Muhallin magana na nuna cewa isar da ma’ana bai tsaya kawai kan kalmomi na mai
magana da mai sauraro kaɗai ba, ya haɗa har da ma yanayin da aka yi magana da kuma
gurin da aka yi maganar.
Stalnaker
(1972:380) ya ce:
“Pragmatics
is the study of the purpose for which sentences are used, of the real world
conditions under which sentence may be appropriately used as an utterance”.
Ma’ana:
“Muhallin
magana nazari ne na manufar da aka gina jimloli ko kuma yanayin rayuwa da
ake ƙoƙarin gina jimla a kai, domin isar da saƙo”.
Yule
(1996:4), ya bayyana muhallin magana da cewa:
“Is the
study of relationship between linguistic forms and the users of these forms”
Ma’ana:
“Muhallin
magana nazari ne a kan dangatakar da ke tsakanin kalmomi ko jimloli da masu
amfani da su”.
Muhallin magana ya shafi ma’anonin da kalmomi
ke ɗauke da shi a cikin keɓaɓɓen zance, da kuma yadda mai magana ke samun
damar zaɓen kalmomin da kuma bas u ma’anonin da ya dace a cikin zance. Sai dai masana da dama sun tofa albarkacin
bakinsu dangane da abin da ake kira muhallin magana
a, kamar yadda za a gani, kalmomi na iya ɗaukar
ma’ana ɗaya, ko su ƙarfafa abu ɗaya dangane da ma’ana a cikin harshe, misali; mage da
kyanwa duka ma’anarsu ɗaya. Haka kuma, wasu kalmomin kan iya ɗaukar
ma’ana fiye da ɗaya ko a yi amfani da su a ƙarfafa abubuwa da yawa dangane da ma’ana a cikin
harshe.Misali, kalmar daƙuwa na iya zama abin ci ko
kuma zagi. Saboda haka, dangane da ma’anar kalmomi, za a ga cewa wasu kalmomi
na da ma’ana mai ‘yanci kamar a kalmar riga, wasu kuwa ma’ana ta nahawu
suke da ita, kamar a ɗafin –r a kalmar rigar. Dangane da jumloli
kuwa, ba a iya cewa ga inda ma’anarsu ta dosa, wannan kuwa na faruwa ne ta
la’akari da ainihin tunani da mai magana ke son isarwa daga harshen zuci zuwa
harshen sarari. Saboda haka, a cikin wannan takarda an kawo bayanai dangane da
ma’anar da kalmar ‘hannu’ ta ke ɗauke da ita, da kuma yadda take
sassauyawa dangane da muhallin maganar da ta fito a ciki ko kuma idan ta sami
wasu canje-canje da suka shafi ƙirar kalma. (Alamajir da
Bello, 2022).
1.1. Ma’anar Waƙar Baka
Muhammad, (1978) ya bayyana bayyana ma'anar
waƙa da cewa "magana ce ta hikima da ake
rairawa ba faɗa kurum ba, wadda ke ɗauke da wani saƙo a cikin zaɓaɓɓun kalmomi wanda ake aunawa ta furucinsu
domin a ga ya yi ba tare da tuntuɓe ba".
Gusau, (2014:3) ya bayyana samuwar waƙar baka da cewa "an jima da fara waƙar baka a duniya tun lokacin da aka sani hanyar
farauta. A ƙasar Hausa, farauta ita
ce daɗaɗɗiyar sana'ar da aka fara yi kuma an sami waƙoƙi da dama game da ita. Daga nan sai farautar
gargajiya suka tsuru a ƙasar Hausa a sakamakon haɗuwar Hausawa ƙungiya-ƙungiya tun zamanin da suka soma zama
wuri ɗaya don su yi noma da aiwatar da wasu sana'o'i Na samun abubuwan
rayuwa. Haka kuma sun tsuru ne don taimaka wa juna da kuma kame kansu daga
namun daji. Wannan ne ya saka ake jin daidai wannan lokacin ne aka fara yi wa
sarki waƙa".
Ma'anar waƙar baka kuwa: Ta kasance
ana ce wadda ake aiwatarwa a cikin harshe mai jan hankali, tare da bayar da
damar yin tunani da lura. Hanya ce ta sadar da tunani zuwa ga maguzawan al'umma
a zanguna daban-daban da rayuwar jama'a ta kan haɗu a kansu. Ana aiwatar da waƙoƙin don tabbatar da haɗa sasanci cikin nasiha da
faɗakarwa da samar da walwala a rayuwar masu sauraronsu. Haka kuma ana aiwatar
da waƙar ta baka cikin hikima
da fusaha wadda ake shirya ta da tsari mai kyau a kuma raira ta tare da kayan
kiɗa na gargajiyar Hausawa, bayan an hardace ta da ka (Gusau, 2012:219)
2.0 Hanyoyin Gudanar da bincike.
An yi amfani da hanyoyi daban daban domin samun bayanan da aka
sarrafa lokacin gunadar da wannan aiki. Irin hanyoyin da aka bi sun haɗa da
1. Tattaunawa ta musamman da wasu masana da manazarta waƙoƙin baka domin samun bayanai da za su taimaka
wajen ganin wannan aiki ya daidaita bisa tsarin da ya dace.
2. Tattaunawa ta musamman da wasu masana da manazarta nahawun
Hausa, musamman ɓangaren ilimin ma’ana, domin samun bayanai da za su
taimaka wajen gudanar da wannan aiki.
3. An yi amfani da hanyar sauran waƙoƙin Ummaru Bagobiri waɗanda aka naɗesu a kaset da
kuma faifan adana waƙoƙi na zamani. Ta haka ne aka yi amfani da damar
wajen mayar da su a rubuce domin nazarin saƙonnin da wasu kalmomi da ɗiyan waƙar ke ɗauke da shi .
4. Haka kuma an yi bitar ayyukan magabata wadanda suka haɗa da
bugaggun littafai, maƙalu da mujallu da
kundayen bincike waɗanda ke da alaƙa da wannan aiki domin ƙara samar wa aikin madogara.
3.0 Ra’in da aka yi Amfani da shi
An
yi ƙoƙarin ɗora wannan takarda a kan ra’in Speber da Wilson (1995) don
fahimtar yanayi da kuma yadda ma‘ana ke duba muhallin magana a yayin da ake
magana ko rubutu. Ra’in yana magana a kan muhallin magana dangane da alaƙa. A ra’in an nuna cewa akwai buƙatar
sanin alaƙa ta magana da yanayin da aka yi ta wajen bayyana jawabi. Ana iya
amfani da wannan ra’i na alaƙa, wajen bayyana ma’ana,
wanda ana ɗaukar cewa ma’anar da ake sa ran a fahimta, na da alaƙa da bayanin da aka yi. A nan ma’anar furuci ta ta’allaƙa ne ba wai ga ma’anar kalmomin da ke ƙunshe a jimla ba, face ta muhalli ko ta fuskar da aka fahimce ta.
Muhallin
magana a nan bai tsaya kawai ga bayani na ainahin wurin da ake magana ko kuma
furucin da aka yi ba, ya haɗa da hasashe na kimiyya ko abubuwan da aka aminta da su na addini
da al’ada da yanayin mai magana dangane da kaifin tunaninsa, waɗanda za su iya taka
muhimmiyar rawa wajen fahimtar abin da aka faɗa. Ma’ana
dai, shi muhallin magana abubuwa ne ƙunshe waɗanda suke sa ma’anar da ake son bayyanawa ta fito sosai.
Irin waɗannan abubuwa kuwa sun
shafi rayuwa ta yau da kullum.
3.1 Taƙaitaccen Tarihin Ummaru Bagobiri
Tarihin Ummaru Amadu Tanko Bagobiri ba zai cika ba face an faro
tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Kasancewar Allah ya yi ma Ummaru
Bagobiri cikawa kafin fara wannan bicike, wannan ya sa samun cikakke kuma
sahihin tarihinsa bai samu ba daga bakinsa sai ta bakin ƙanansa wanda suka gudanar da gwagwarmayar rayuwa
tare kamar yadda muka tattauna da shi a ranar 18/3/2025 a gidansa da ke
Katsina.
An haifi Ummaru Bagobiri a wajajen shekarar (1948). Cikakken sunan
Ummaru Bagobiri shi ne, Ummaru Amadu Tanko Bagobiri, mahaifiyarsa kuma sunanta
Halima, duka iyayensa Gobirawa ne kuma 'yan jihar sakkwato ne a wani gari mai
suna Gabo wanda yake ƙarƙashin garin Illela. An
haifi Ummaru Bagobiri a ƙauyan Gidan Ɗanhillo, wani ƙauye da yake a kan hanyar zuwa Sabon birnin
Gobir. Sai dai mahaifin Ummaru Bagobiri ba mawaƙi ba ne, wato makiyayi ne. Saboda haka, duk
waɗannan kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe da Ummaru Bagobiri ya yi bai gaje su wajen
mahaifinsa ba. Sai dai ya gaji waƙa ne daga ɓangaren mahaifiyarsa, domin
danginsa na wajen mahaifiya makaɗa ne, ke nan Ummaru ta ɓangaren uwa ne ya
gaji kiɗa, ba da rana tsaka ya fara ba.
Ummaru ya yi karatun Allo, cikin ƙauyan Gidan Ɗanhillo, sai dai kamar yadda aka san al’adar
malaman makarantar Allo ta yawo da rashin zama wuri ɗaya, haka shi ma
Ummaru sun yi wannan yawon karatu tun daga Gidan Ɗanhillo har zuwa Ƙauran Namoda. Wannan dalili ya ba Ummaru
Bagobiri damar samun ilimin Alƙur’ani mai tsarki. Sai dai bayan rasuwar mahaifinsa malam Amadu,
daga nan Ummaru ya ci gaba da faɗi tashin rayuwa, kasancewarsa babba a wajen
mahaifinsa. Ummaru ya ci gaba da Noma da kiwo, kamar yadda ya gada wajen
mahaifinsa.
Ummaru ya fara kiɗan yammata a nan cikin garin Gidan Ɗanhillo, inda yake bin kasuwanni da dandali yana
kiɗa, daga nan ne kuma sai sha’awar kiɗan Noma ta fara shiga zuciyarsa, daga
nan ya fara waƙar noma. Ummaru yana ta
yin waƙar noma kuma
ta ɗauke shi ka-in-da-na'in. Daga nan Ummaru ya fara zuwa garin Mada wanda
yake a ƙasar Zamfara idan kaka
ta yi suna yin sana’ar ga-ruwa. Kwatsam sai Ummaru ya yi wa mahaifiyarsa
maganar yin hijira zuwa Mada, sai mahaifiyarsa ta ce ta amince masa da ya bar
gari amma ba Mada zai koma ba, saboda bai da dangi a a Mada, amma ya ta
fi ƙasar Katsina akwai wani
gari da ake kira Sakkwatawa ƙananta na can, sai Ummaru ya yi murna. Bayan sun
gama shiri sai Ummaru da ƙannansa guda biyu Audu da Isuhu da kuma matarsa da matar
Audu ƙanansa da abokinsa Amadu
suka kamo hanya zuwa ƙasar Katsina. Cikin ikon Allah Ummaru da tawagarsa suka iso garin
Sakkwatawa wadda take cikin ƙaranar hukumar Ɗanmusa, abin lura a nan shi ne, kafin Ummaru ya
zo Sakkwatawa bai taɓa yin waƙar dambe ba.
Ana cikin haka wata rana Ummaru sun je cin kasuwar Ɗanmusa, sun kewaya wani lungu sai suka ga ana
dambe, sai Ummaru ya ce wa Buda ku duba nan ma ana irin wannan wasan da na taɓa
cewa za mu riga yin irin waƙoƙinsu. A wannan lokacin
wani mawaƙi aka ɗauko daga
garin Maidabino, bayan an tashi wasa suka koma gida, da sati ya zagayo sai suka
taho da Kalangansu, suka samu shugaban gidan damben Alhaji Shago. Suka gaya
masa daga inda suke, sai yai dariya ya ce ya za ai a yi kiɗan dambe da waɗannan
‘yankalangu, amma ba komi za mu jaraba ku mu gani. Tun daga wannan lokaci duk
lokacin suka zo ana wasan dambe an san su kuma ana ɗan basu dama a bayan
fage. Kwatsam wata rana sai Alhaji Shago ya ce a ba su Ummaru dama su yi wasa
kamar kowa, a wannan rana su Ummaru suka gwada hazaƙarsu kuma mutane suka yaba aka yi ta yi masu liƙo. Wannan ya sa Ummaru ya ji daɗi daga nan suka
zama makaɗan Alhaji Shago na Ɗanmusa, kuma wannan ya sa ya zama ubangidan
Ummaru na farko dangane da abin da ya shafi harkar kiɗan dambe.
Bayan garin Ɗanmusa sai Ummaru ya ci gaba da yawan kiɗa a duk inda ake wasan
dambe. Haka kuma, duk inda ya je ana maraba da zuwansa saboda yana girmama
mutane, kuma ya iya waƙar, cikin yawon kiɗa da
yake zuwa garin Ƙanƙara da ‘yargoje sai Sarkin noman garin ƙanƙara Alhaji Ali ƙanƙara ya ce masa ya kamata ya baro garin
Sakkwatawa ya dawo Ƙanƙara da zama, ganin irin alherin da yake samu a
wannan gari ya sa Ummaru ya kwaso iyalansa ya dawo Ƙanƙara da zama, kuma daga nan ya riƙa fita wasa zuwa Malumfashi inda sarkin fawa
Tsoho na kan Kwana ke sauke shi da Funtua wajen Alhaji Mamman Shata da Dutsinma
wajensu Alhaji Aminu da Charanci wajensu sarkin fawa, sai Katsina da Jibiya da
Daura ƙarƙashin kulawar babban mai gidansa marigayi Amadu
Nafuntua Sa’in Katsina.
Bayan zuwan Ummaru Sakkwatawa ya shahara daga nan aka riƙa nemansa garuruwa don yin wasa wannan ya sa duk
inda ake wasan dambe a arewacin Nijeriya ba inda Ummaru bai je ya yi wasa ba.
Ummaru ya samu nasarori a harkar waƙa inda ya zama sarkin kiɗan marigayi Sa’in
Katsina Alhaji Amadu Nafuntuwa, haka kuma an naɗa shi Sarkin kiɗan Sarkin
Pawwan Katsina hakimin Ƙankara. Ummaru bagobiri ya riƙa wakiltar jihar Katsina a wajen bikin wasannin
gargajiya na ƙasa, kamar wanda aka yi
a Benin, da Bauchi da Kaduna da sauransu.
Allah ya yi wa Ummaru Bagobiri rasuwa a shekarar (2008), ya rasu
ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya uku. Ummaru bagobiri ya rasu a jihar Benin,
kuma a can aka yi masa janaza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
4.0 Nazarin Kinin Ma’an a Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Ummaru Bagobiri
A nan za a warware bayani dangane da ma’anonin da wasu kalmomi da
Ummaru Bagobiri ya riƙa amfani da su a
cikin ɗiyan waƙoƙinsa. Za a yi bayanin ma’anonin kalmomin a
lokacin da suke tsuransu da kuma ma’anonin da suke ɗauke da su a cikin
jumla. Za a riƙa ba da misalai
kai-tsaye daga cikin ɗiyan waƙoƙin Ummaru Bagobiri. Kamar yadda aka sani, waƙoƙin baka na Hausa suna taka rawa wajen saka
nishaɗi da wayar da kai da kuma adana kalmomi. Saboda haka, nazarin ma’anonin
waɗannan kalmomi ta fuskar muhallin magana zai taimaka gaya wajen fahimtar
ainafin saƙon da ɗiyan waƙar ke ɗauke da shi.
Kinin Ma’ana (synonyms): Kinin ma’ana na nufin wurin da ake samun kalmomi biyu
mabanbanta amma suna da ma’ana iri ɗaya a harshe guda.
Wannan rukuni na kalmomin Hausa suna zuwa da tsarin rubutu
daban-dabban, haka kuma, sautin kalmomin ma ya bambanta, sai dai kalmomin kan
kasance da ma’ana ɗaya. Amma ya kamata a fahinci cewa danagane da abin da
ya shafi nahawun harshen Hausa, duk da kasancewar irin waɗannan kalmomi na zuwa
da ma’ana guda, watau suna wakiltar abu ɗaya dangane da ma’ana, ba
koyaushe ake iya amfani da duka kalmomin a cikin jumla ba. Sai dai kuma ana iya
amfani da su a cikin jumla ɗaya, kuma su ba da ma’ana daban.
Ma’anar kalma ko kalmomi ita ce irin ma’anar da kalma ke samu
lokacin da take tsuranta. Kamar yadda za a gani nan gaba, kalmomi a cikin
harshe dangane da ma’anoninsu. Wato, irin ma’anonin da kalmomi ke samu dangane
da abin da ya shafi nahawu da kuma matsayin kalmomi a cikin nahawun harshe.
Misali
Ummaru Bagobiri ya riƙa amfani da waɗannan kalmomi da ke tafe a wurare
daban-daban cikin ɗiyan waƙarsa a matsayin abu ɗaya (damben gargajiya).
Kalma Ma’ana
Yaƙi: Farma wasu mutane da
faɗa domin a mulkesu
Hwaɗa: Rigima da tashin hankali tsakanin mutum biyu ko fiye
Rigima: Tashin hanka ko kutsawa cikin rikici.
Wasa: Abun da ake yi ba da gaske ba.
Ummaru bagobiri ya riƙa amfani da waɗannan kalmomi a mabambantan
wurare a matsayin kalmomi masu kinin ma’ana. Sai dai, idan aka kalli kalmomin
za a ga cewa suna ɗaukar ma’anoni daban daban a lokacin da suke tsuransu.
Saboda haka, za a fara nazarin saƙonnin da kalmomin ke ɗauke da su a cikin
wasu ɗiyan waƙar Ummaru Bagobiri.
1a.Waƙar Tica.
Jagora. : Ya Allahu la'ilaha'ilallah.
‘Yan anshi. Allah la'ilaha'ilallah,
Sani ƙaddara ta ɗaukai,
bai san ana sallah ba,
bai san kiran sallah ba,
Tica bai san gudun yaƙi ba.
b. Waƙar Jafaru Kura
jagora: A bar maka yaƙi Jahwaru.
Kura maganin kare.
‘Yan anshi: A sakar maka yaƙi Jahwaru,
na Ummaru yaƙi yaz zaka.
Jagora: Kowar jaka yaƙi.
Y/amshi: Eh kowaj jaka yaƙi ya sani,
kai aka shakka Jahwaru,
na Ummaru yaƙi yas sani
c. Shagon na Mai’ango
Jagora: Wai me kaka shawarar yaƙi,
horu maza da hannunka.
‘Yan anshi: Eh horu maza da hannunka,
ga shagon Na-mai-ango.
2. Waƙar Ali Zuma.
Jagora : Mai halin Ali, mai halin Ali.
‘Yan anshi: kowaj jaka hwaɗa ya so a raba,
ci da maza hannunka guba,
Ali zuma tsoronka a kai.
3a. Jagora: Ga wani ya rigima ja ya so a raba.
Yan Anshi. Ci da maza hannunka dahi
Ali Zuma tsoronka a kai.
4a. Jagora: Kamar Ali mai maciji, In dai za shi wasa
‘Yan anshi. roƙon Allah muke yi
in ka tahi lahiya lau,
ka dawo lahiya lau.
Dangane
da waɗannan ɗiyan waƙa da aka kawo a sama za a ga cewa an ba wasu kalmomi muhimmanci
inda aka rubuta su da rubutu mai duhu. A nazarin ainafin ma’anar waɗannan kalmomin lokacin da
suke tsuransu yana da wuya a fahinci ma’anar kalmomi. Wannan ya sa aka kalli
muhallin da kalmomin suka fito domin a fahinci saƙon
da ɗiyan waƙar ke ɗauke da shi. A misali na 1a-d Ummaru Bagobiri ya riƙa amfani da kalmar yaƙi inda yake nufin wasan damben gargajiya. Bambanci tsakanin kalmar
yaƙi da danben gargajiya dangane da ma’ana shi ne. Yaƙi ana amfani da makami, kamar bindiga, wuƙa, da sauransu. Amma a cikin dokokin damben gargajiya haramun ne
yin amfani da kowane irin makami, kuma idan mutum ya faɗi ƙasa shi ke nan ba a ƙara bugunsa, da sauran
dokoki da suka shafi al’adar wasan danben gargajiya, waɗanda ba a amfani da su a
fagen yaƙi.
A misali
na 2-3 kuwa Ummaru ya riƙa amfani da kalmar hwaɗa da rigima matsayin wasan damben gargajiya dangane da muhallin da
kalmomin suka fito a cikin ɗiyan waƙoƙin da aka ba da misali a sama. A nan ya kamata mai karatu ya
fahinci cewa bambancin kalmar hwaɗa da rigima da kuma damben gargajiya a fili yake. Faɗa da rigima ba su da
dokokin aiwatarwa, kuma ana iya amfani da makami, ba alƙali a tsakani ba kuma lokacin gamawa da sauransu. Amma damben
gargajiya yana da ƙa’idoji da dokoki da kuma
kyaututtuka ga wanda ya yi nasara.
A misali
na 5 kuwa kalmar wasa tana nufin damben gargajiya dangane da
muhallin da kalmar ta fito a cikin ɗiyan waƙar da aka ba da misali a sama. Duk da cewa ana kiran damben na
gargajiya. Sai dai kalmar wasa tana ɗaukar ma’anar wani abu da yaro ko babba ko mace ko namiji ke iya
yi. Amma a ƙa’idar damben gargajiya na Hausawa mata da yara ƙanana ba sa yi.
Dangane
da bayanan da suka gabata za a ga cewa waɗannan kalmomi yaƙi da rigima da hwaɗa da kuma wasa suna ɗaukar ma’ana guda wato,
damben gargajiya a harshen Ummaru Bagobiri ta la’akari da muhallin da kalmomin
suka fito da kuma saƙon da suke ɗauke da shi a cikin ɗyan waƙar da aka ba da misali da su a sama. Wannan ya sa aka kira su da
kinin ma’ana.
Ta
la’akari da bayanan da suka gabata, waɗannan kalmomi: yaƙi da hwaɗa da rigima da wasa
suna ɗaukar
ma’ana guda a matsayin kinin ma’ana.
Bayan kalmomin da aka kawo a sama waɗanda Ummaru Bagobiri ya yi
amfani da su a cikin ɗiyan waƙoƙinsa kuma suke da bambanci a rubuce amma kuma
dangane da saƙon da kalmomin
ke ɗauke da shi, suna tafiya da ma’ana ɗaya wanda aka kira kinin
ma’ana kamar yadda aka yi bayani a sama. Yanzu za a ƙara kawo misalin wasu rukunin kalmomin waɗanda
ke ɗauke da irin wannan mataki na ma’ana.
Kwanta dama: wanda ba ya da rai
faɗi: faɗuwar wani abu ƙasa
Mutuwa : ƙarshen ran duk wani abu mai rai
Kwana lahira: Wanda ya mutu
Kashe : Mutuwa
Kamar yadda aka gani waɗannan kalmomi suna da bambancin rubutu,
amma kuma suna tafiya da kinin ma’ana kamar yadda Ummaru Bagobiri yay i amfani
da su. Sai irin ma’anar da Ummaru Bagobiri y aba kalmomin ta sha banban da
ma’nar da kalmomin ke ɗauka lokacin da suke su kaɗai. Dubi waɗannan
misalai da ke tafe.
5a. Waƙar Hamza ƙanan Alhaji Ada
Jagora: Ashe ranar mutuwa.
‘Yan anshi. Eh ranar mutuwa ba a da kwana.
Jagora: Eh sai ga dangi nai ma shi kuka,
Lawalli bai sami hita ba,
Mutuwa tai ma shi sauri,
Allah kai mana gyara,
aikin ba shi da daɗi,
Hamza ƙanan Alhaji Ada.
b. Waƙar Bature Gora
Jagora: Ina Kandami yay yi, Ina mamman Burus yak kwana
Duka mutuwa ta gama da su sai watarana
Sun ja Bature ɗanmutanen Gora
6a. Waƙar Jafaru Kura
Jagora: Allahu Akbar ina shagon Ahmadi.
Wannan ya hwaɗi kwance,
ya kwanta-dama.
Sai ga 'yan'uwa nai sunai ma shi jaje.
b. Waƙar Hamza ƙanen Alhaji Ada
Jagora: Ashe ka tuna bugun da kai ma Dogo.
Dogo ya hwaɗi kwance ya gaza tashi.
Ya hwaɗi ƙanan Alhaji Ada.
b. Waƙar Bature Gora
Jagora: Yaƙi ya baci,
Ina Akushi ɗanmutan Musawa
Akushi ya hwaɗi ya tsattsage
Sai dai musa tuwonmu a ƙwarya.
7a. Waƙar Shagon NamaiAngo
Jagora: Yaƙin nan da kai da Ƙasimu mai kasa.
Ƙasimu ya kwanta
b. Waƙar Bature Gora
Jagora: Bawa ban san ka gaza ba
Bawa ban san ka gaza ba sai ka kwanta
8a. Waƙar Shagon Batajemu ba
Jagora: Na hi son maza a gama.
Yan anshi: Wani sai ya kashe wani,
Tsoronka akai hwage,
shagon Bata-jemu-ba.
b. Waƙar Alin Mura
Jagora: yaƙi ya kashe jan
buzu
Yam anshi: sai yay yi yamma da walkinai
Sa maza su ji tsoro nai
Ali ɗanmutan Mara ci fansa
Waƙar Bature Gora
Jagora: Duna waɗanda kakkashe
Duna waɗanda kakkashe naka zaɓe
Amman waɗansu na manta su.
Dangane
da waɗannan ɗiyan waƙa da aka kawo a sama za a ga cewa an ba wasu kalmomi muhimmanci
inda aka rubuta su da rubutu mai duhu. Idan aka nazarci ainafin ma’anar da
kalmomin ke ɗauke da ita lokacin da suke tsuransu, za a ga cewa sun sha bamban
ta fuskar ma’ana. Amma idan aka kalli ma’anonin da kalmomin suke ɗauke da su dangane da
bigiran da kalmomin suka fito a cikin ɗiyan waƙoƙin da aka kawo, za a ga cewa Ummaru Bagobiri ya yi amfani kalmomin
a matsayin kalmomi masu kinin ma’ana duk da cewa ma’anonin kalmomin sun
bambanta dagane da yadda aka yi bayanin ma’anonin kalmomin a ƙamusun harshen Hausa kamar yadda aka kawo a sama.
A misali
na 5a-b Ummaru Bagobiri ya riƙa amfani da Kalmar mutuwa, wadda
take nufin wanda aka yi nasara a kansa a wasan damben gargajiya, dangane da
ma’ana ta muhallin magana. Amma a ma’ana ta ƙamusu
mutuwa na nufin rasa rayuwa.
A misali
na 6a-c kuwa kalmar hwaɗi / hwaɗuwa na nufin wanda aka yi
nasara a kansa a wasan damben gargajiya. Sai dai ya kamata a fahinci cewar ba
dole sai mutum ya faɗi ƙasa ba ake nufin an yi nasara a kansa ba. Dangane da dokokin
damben gargajiya, idan hannu ko guiwar mutum ta taɓa ƙasa, to an yi nasara a kansa. Ummaru Bagobiri ya yi amfani da
kalmar hwaɗi a wannan bigire
saboda akasarin nasarar da ake samu a damben na gargajiya ana faɗuwa ne.
A misali
na 7a-b kuma mawaƙin ya yi amfani da kalmar kwanta a matsayin wanda
aka yi nasara kansa a wasan damben gargajiya, sai dai kwanta / kwanciya na
nufin wani aiki da aka yi cikin natsuwa. Amma dangane da kwanciyar da Ummaru
Bagobiri ke nufi aiki ne da aka yi ba shiri wato kenan kwanciya na nufin wanda aka
yi nasara a kan kenan.
A misali
na 8a-c Ummaru ya riƙa amfani da kalmar kashe a matsayin wanda aka yi
nasara a kansa a wasan damben gargajiya. Kashe kalma ce da ke
nuna aikin da ya wuce wadda ke nufin mutuwa ko fitar rai, a ma’ana ta yau da
kullum. Sai dai, ba a cika samun fitar irin wannan yanayi na fitar rai ba.
Ummaru Bagobiri yay i amfani da wannan kalma ne domin nuna gwanancewa a harshe
da kuma ƙarawa waƙoƙinsa armashi. Saboda haka, dangane da ɗiyan waƙar da aka nazarta a sama kalmomin mutuwa da kasha, da hwaɗi, da kwanta, na nufin abu
guda. Watau, wanda aka yi nasara a kansa kenan a wasan danben gargajiya na
Hausawa.
4.1
Sakamakon Bincike
1- Wannan aiki ya gano cewar
Ummaru Bagobiri na amfani da kalmomi mabambanta wajen zuga jarumansa duk da
cewa sana’a ɗaya suke. Wannan dalili ya sa ake samun kinin ma’ana dangane da
kalmomin da yake amfani da su wajen isar da saƙo.
2- Wannan bincike ya gano
cewar Ummaru Bagobiri na amfani da hikimarsa wajen samar da kinin ma’ana ga
kalmomin da ba kinin ma’ana dangane da ainafin ma’anar da kalmomin ke ɗauke da ita a harshen
Hausa.
3- Wannan bincike ya gano
cewar yawancin kalmomin da Ummaru Bagobiri ke amfani da su wajen zuga jarumansa
ma’anarsu ba ta fita sai an yi laakari da bigiran da kalmomin suka fito a
cikin ɗiyan waƙoƙin.
4- Wannan bincike ya gano
cewar wani lokaci Ummaru Bagobiri na samar da kinin ma’ana a wasu kalmomin ta
hanyar amfani da tsarin harɗantawa, kamar yadda ya fito a kalmomin yaƙi da yaƙin hannu, da kwana-lahira da kwanta-dama.
5- Wannan bincike ya gano
cewar Ummaru Bagobiri na amfani da karin harshe wajen gina waƙoƙinsa, wannnan ya sa ake kinin ma’ana dangane da kalmomin da yake
amfani da su wajen gina waƙoƙinsa.
5.0
Kammalawa
Dangane
da jawaban da suka gabata an ga yadda wannan takarda ta yi ƙoƙarin kawo bayanai da misalai waɗanda suka shafi yadda kalmomi ke samun ma’ana ta ƙamusu watau lokacin da kalmomin suke tsuransu. Haka kuma, wannan
takarda ta yi bayanin abin da ake kira kinin ma’ana da kuma yadda kalmomi ke
kasancewa suna da kinin ma’ana a cikin harshe. Wannan takarka ta kawo misalai
kai-tsaye daga cikin ɗiyan waƙoƙin Ummaru Bagobiri waɗanda ya rerawa jarumansa. An ga yadda mawaƙi Ummaru Bagobiri ke amfani da hikima wajen zaɓar kalmomin da zai
gina ɗiyan waƙoƙinsa. Haka kuma, akasarin kalmomin da Ummaru Bagobiri ke amfani da
su wajen gina ɗiyan waƙoƙinsa ba sa ɗauke da kinin ma’ana dangane da ma’anonin kalmomin na ƙamusu, amma sai ya yi amfani da hikimarsa da ƙwarewarsa a harshe wajen tanƙwasa kalmomin ta yadda za
su kasance suna ɗaukar ma’ana ɗaya a matsayin kinin ma’ana, ba tare da sun kawo targarda wajen
isar da saƙo ba. Wannan salo na Ummaru Bagobiri ya sa bai cika maimaita baiti
a cikin waƙoƙinsa ba. Haka kuma, yana amfani da kalmomi daban-daban wajen zuga
jarumansa ta yadda kowane da irin kalmar da yake amfani da ita wajen zuga shi
duk da cewa sana’a iri ɗaya suke.
Manazarta
1. Almajir da Bello (2022). Kebabben Nazari Kan
Kalmar Hannu ta Fuskar Muhallin Magana a Hausa. Algaita Journal of
current research in Hausa. Ɓol 15, No1.
2. Aitchison, J. (1987). Words in the
Mind. Oɗford: Blackwell Publishers.
3. Bello, M. Z. (2018). Nazarin Ma’ana a Kalmomin
Amsa-kama na Hausa. Un published M.A Disertation submitted to the Department of
Nigerian Language, Bayero University, Kano.
4. Bello, M. Z. (2023). Gamayyar Ƙirar Kalma da Ginin Jumla a Kalmomin Amsa-kama
da Bayanau na Hausa. Un published PhD Disertation submitted to the Department
of Nigerian Language, Bayero University, Kano.
5. Bauer, L. (1983). English Word –
formation. Cambridge: Cambridge University Press.
6. Cann, R. (1993). Formal Semantics: An
Introduction. Cambridge: Cambridge University Press.
7. Gusau S.M (2014:3). Diwanin Waƙoƙin Baka: (Juz'i na biyu). Nigeria, Kano Century Research And
Publishing Limited.
8. Gusau S.M (2012a) "Makaɗan Hausa Jiya da
Yau" takardar da aka gabatar a taron makon Hausa na 3a, wanda ƙungiyar Hausa ta Jami'ar Bayaro Kano ta shirya.
9. Griffiths, P. (2006). An Introduction to
English and Semantics and Pragmatics: Edinburgh. Edinburgh University
Press Ltd.
10. Harris, R. (1983). F. de Saussure:
Course in General Linguistics. Translation: Oxford. Gerald Duckworth.
11. Hurford, J. R. (2007). Semantics. New
yourk: Cambridge University Press.
12. Katz, J. (1972). Semantic Theory. New
Yourk: Harper and Row.
13. Lobner, S. (2002). Understanding
Semantics. London: Hudder Education, UK.
14. Lowe, J. E (1965). Locke on Human
Understanding: London. Routledge.
15. Matthews, P. H. (1997). A Dictionary of
Linguistics. Cambridge: Cambridge University Press.
16. Newman, P. (2000). The Hausa Language:
An Encyclopedic Reference Grammar New Haven, US. Yale University
Press.
17. Saeed, J. I. (2003). Semantics. USA:
Blackwell Publishers.
18. Spencer, A. (1991). Morphological
Theory: An Introduction to Words Structure in Generative
Grammar. London: Basil Blackwell.
19. Sperber, D.& Wilson, D. (1986). Relevance:
Communication and Cognition. Oxford: Blackwell.
20. Stalnaker, R. C. (1972) “Pragmatics’’ in D. Davidson and G. Harman (eds). Semantic of natural languages. Dordrecht: Reidel.
21. Syal, P. & Jindal. D. Ɓ. (2014). An Introduction to
Linguistics. Delhi. PHI Learning Ltd.
Verschueren, J. (1990). Understanding
Pragmatics. London: Arnold.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.