Cite this article as: Umar M. M. (2025). Kalmomin Masu Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai a Garin Sakkwato. Zamfara International Journal of Humanities, 4(1), 91-99. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2025.v04i01.010.
KALMOMIN
MASU SAYAR DA MAN FETUR DA BAƘIN MAI A GARIN SAKKWATO
Na
Dr.
Muhammad Mustapha Umar
Department
of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Tsakure:
Wannan
takarda ta yi nazarin kalmomin rukunin masu sayar da man fetur da baƙin mai a
cikin garin Sakkwato. Manufar ita ce, zaƙulo yadda wannan
rukunin ‘yan kasuwa suke sarrafa harshen Hausa, ta hanyar fito da
ma’anonin kalmomin da suke amfani da su a zantukansu na yau da kullum. An taƙaita
wannan bincike a kan nazarin kalmomi ne kawai, ba tare da nazarin sassan jumla
ko jumlolin wannan rukunin ‘yan kasuwa ba. An gabatar da hasashe guda biyu
(2), waɗanda aka
gwada su ta hanyar gudanar da lura ta kai-tsaye da hira ko tattaunawa da masu
harkar sayar da man fetur da baƙin mai a wuraren
kasuwancinsu. An tattaro wasu lafuzzan da suke amfani da su domin tabbatar da
samuwar wannan Hausar dalilin zamantakewa da sauran ma’amalolin a wuraren
kasuwancinsu. Binciken ya gano cewa ‘yan kasuwar suna amfani da wasu
ma’anoni na musamman waɗanda suka sha bamban da yadda sauran jama’a suka san su a Hausar yau
da kullum. Binciken kuma ya gano cewa ma’anonin da suke amfani da su sun samu ne daga faɗaɗa ma’ana da ƙirƙira da kuma sarrafa kalmomin aro.
Fitilun
Kalmomi: Kalmomi, Man Fetur, Baƙin Mai.
1. Gabatarwa
Fetur[1] mai ne da ake zuba wa babur ko mota
ko wani inji wanda ke ƙonewa don
ya ba inji ƙarfin wuta da zai sa ya motsa.[2] Ana haƙo man fetur daga ƙasa ko
daga teku a tace a matsayin makamashi don amfani a injuna. A hukumance duk
wanda zai yi sana’ar fetur zai nemi lasisi daga gwamnati sannan a ba shi damar
ya gina gidan mai[3]. Zai tanadi tankokin ɗauko mai da ma’aikata, da sauran abubuwan
buƙata da za
su taimaka tafiyar da wannan kasuwanci mai haɗarin gaske. Sannan mai gidan mai ya fara saye da sayar da man
fetur a ƙarƙashin
kulawar hukumar DPR.[4] Daga cikin masu kasuwancin man fetur
akwai manyan dillalai, waɗanda ke sayar da man fetur kan farashin gwamnati da kuma dillalai
masu zaman kansu, waɗanda a wasu lokuta suke sayar da man fetur fiye da farashin da
gwamnati ta ƙayyade.
Shi ya sa wasu jama’a ke yi musu kallon ‘yan kasuwar bayan fage, wato masu
sayar da man fetur da tsada da rashin lita mai kyau.
Baƙin mai[5], mai ne kore mai kauri da ake zuba wa
injuna da zai sa sassansu su motsa kamar yadda ya dace. Masu sayar da baƙin mai yawanci suna gudanar
da sana’arsu ne a gefen tituna, inda suke aikin zubar da baƙin mai na babur ko mota ko
wani inji idan ya gama aiki, su zuba sabo a biya su kuɗin baƙin mai. Suna sayar da mataccen baƙin mai da suke tarawa ga
jama’a mabuƙata.
Wannan baƙin mai
shi suke kira kwandem (condemn), kuma ana shafa shi a jikin
katako don kariya daga ƙwari. Masu ƙaramin ƙarfi ma na amfani da shi
wajen juye, musamman kwandem wanda bai gama aiki sosai ba. A yau masu wannan
sana’a suna sayar da wasu abubuwa bayan baƙin man irin su: Ruwan birki da fulogai da
omon wankin mota da wayar kuloci da giris da man fetur da kalanzir da kayan
janareta da kuma sauran sassan abubuwan hawa.
Domin yin wannan nazari an
kasa takardar gida biyar. Daga farko akwai gabatarwa, sai hanyoyin gudanar da
bincike da hasashen bincike. Daga nan sai bayani kan Hausar masu sayar da man
fetur da baƙin
mai, tare da misalan kalmomi, kana kuma aka kawo dangantakar ma’ana ta asali da
sabuwar ma’ana, don tabbatar da kasancewar sauyawar ma’ana ta hanyar faɗaɗa ma’anar
kalmomi. A ƙarshe akwai jawabin
kammalawa da sakamakon bincike.
2. Hanyoyin Gudanar da
Bincike
Wannan
takarda sashe ne da ya shafi kundin binciken gaba-ɗaya. Don haka, ne aka
tsakuro wasu hanyoyin gudanar da bincike, da za su sawwaƙa tattaro
bayanan bincike kamar yadda ya dace. An yi amfani da hanyoyin tattaro bayanai
guda biyu, wato hira ko tattaunawa da kuma
lura ta kai-tsaye, waɗanda suka
tabbatar da samuwar wannan nau’i
na Hausa kamar yadda masu sayar da man fetur da baƙin
mai suke amfani da ita a wuraren da binciken ya shafa. An kasa waɗanda aka yi hira da su zuwa
gida huɗu:
a) Tattaunawa da masu sayar
da man fetur da gas da baƙin mai a gidajen mai
b) Tattaunawa da masu sayar da man fetur a
gefen tituna, waɗanda ake kira ‘yan cuwa-cuwar man fetur (black market)
c) Tattaunawa da masu sayar
da baƙin mai
a gefen tituna
d) Tattaunawa direbobi
masu ɗauko mai da yaransu
A wannan takarda, mai bincike ya zaɓi yin amfani da ra’in Harris (1952) mai suna Discourse Analysis
Theory wanda yake nazarin yadda al’umma suke sarrafa harshe, ta fuskar ma’ana don zaƙulo dangantakar da ke tsakanin ma’anar da tarihin samuwar kalmomin
harshe. Ra’in
ya dace kuma yana da dangantaka da wannan bincike domin ya shafi yadda wasu
rukunan jama’a suke amfani da harshe bamban da sananniyar ma’ana ta fuskar
kalmomi a zamantakewarsu da sauran ma’amalolinsu na yau da kullum. Ga wasu
misalai na wasu ayyuka da aka gabatar ta amfani da ra’in: Isah (2018) da
Zailani (2019) da Sharu (2023) da kuma Mode (2024).
3.0 Hasashen Bincike
An yi kintacen abubuwa huɗu (4) da ake sa ran za su faru, waɗanda ake fatar idan aka gwada su, su dace ko su saɓa wa abubuwan da bincike ya gano a ƙarshe. Ga hasashen:
1. Masu sayar da man fetur da baƙin mai a garin Sakkwato suna da wata keɓaɓɓiyar Hausa da suke amfani da ita wajen aiwatar da kasuwancinsu.
2. Hausar waɗannan rukunin ‘yan
kasuwa ta ƙumshi kalmomi masu ɗauke da sababbin ma’anoni saɓanin waɗanda aka san su da su.
4.0 Kalmomin Masu Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai[6]
‘Yan kasuwa sukan yi amfani da harshen Hausa wajen
bayyana wasu abubuwa, waɗanda suka jiɓinci rayuwarsu ta yau da kullum, tare da
samar musu da sababbin ma’anoni,
domin sadarwa cikin sauƙi. Kodayaushe idan wani abu baƙo da babu
shi ya shigo a ƙasar Hausa, akan yi ƙoƙarin
samar masa suna ta hanyoyin da suka dace. Misali, yin amfani da wasu fitattun
hanyoyi kamar faɗaɗa ma’ana da ƙirƙira da
aro da ɗafi da
kuma tsira. Tun da haka ne, muna iya cewa wasu daga cikin waɗannan hanyoyin sun taimaki
Hausar kasuwanci, musamman sakamakon bayyanar abubuwan zamani. Wani abin sha’awa shi ne, yadda kowane
rukuni na ‘yan kasuwa ke ƙoƙarin ƙirƙira
sabbin ma’anoni, don tafiyar da al’amurransu.
Hausar masu sayar da man fetur tana samuwa ne tun daga
tafiya ɗauko mai, inda direba da
yaransa ke amfani da wata Hausa don bayyana wani hali ko yanayi da suke ciki a
lokacin gudanar da sana’arsu.
Su ma ma’aikatan gidan mai suna
amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi tsakaninsu domin sadarwa. Sannan akwai ‘yan cuwa-cuwar[7] man fetur masu sayar
da mai a kan tituna. A taƙaice, akwai alaƙa tsakanin direbobi da yaransu masu ɗauko mai a kurmi da ‘yan kasuwa masu sayar da mai. Za a fahimci wannan
dangantakar a ƙarƙashin misalan Hausar masu
sayar da man fetur da baƙin mai. Fagge (2004: 126-127) ya kawo bayani kan
Hausar ‘yan cuwa-cuwar man fetur kamar haka: Sana’ar sayar da man fetur ta
samu ne daga baya inda matasa kan sayi mai daga hannun manyan dillalai, su kuma
su kasa su sayar a gefen tituna. Sai dai galibi masu gudanar da wannan sana’a
matasa ne kuma yawancinsu ‘yan daba ko ‘yan shaye-shaye.
Kusan da wuya ka ga mai sayar da mai ko mai irin wannan
sana’a[8] ba ya shaye-shaye,
musamman wiwi. Su ma
suna da wasu kalmomi nasu na daban waɗanda suke amfani da su a tsakaninsu domin sadarwa. Haka kuma, akwai ‘yan kasuwa masu sayar
da baƙin mai
a kan titi, waɗanda suka riƙe ta a matsayin hanyar
sana’arsu da suke yi don gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Masu wannan
sana’ar suna amfani da wata keɓaɓɓiyar Hausa wajen gudanar da sana’arsu, musamman domin ambaton abubuwan da suke sayarwa da
kayayyakin da suke amfani da su wajen gudanar da sana’arsu.
4.1 Kalmomin da suka Shafi Faɗaɗa Ma’ana
Kalmomin da za a gani a wannan sashe. Kalmomi ne na Hausa
kuma suna da ma’ana ta asali, amma aka ba su wata ma’ana ta musamman saɓanin wadda aka san su da ita. Waɗannan ma’anoni sabbi, da su ne masu sayar da man fetur da baƙin mai ke amfani wajen
aiwatar da kasuwancinsu.
(A) Faɗaɗa Ma’anar Kalmomin Asali
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Méesàa[9] |
Suna |
Ƙatuwar macijiya mai haɗiye mutum ko dabba. Ana amfani da fatar ta wajen yin takarmi da jakunkuna |
A jikin injin na sayar da mai akwai wata roba doguwa mai kauri, wadda ta
cikinta fetur ke fita, wadda a ƙarshenta tana da kai ko baki mai mariƙi na musamman, da ake matsawa a zuba mai ko a tsayar da
shi |
|
2 |
Sóoɓòo [10] |
Suna |
Fure ne da ake samu daga sure ko yakuwa |
Man fetur mai
launin ja-ja-ja |
|
3 |
Jùuyée |
Suna |
Saye abin da
budurwa ke talla, ko wani irin kitso |
Zubar da baƙin mai na abin hawa
ko inji idan ya gama aiki don a zuba sabo |
|
4 |
Hàlàmníyáa |
Suna |
Cin abinci da sauri don haɗama |
Cuwa-cuwar man fetur inda kowane ɗan bulakmaket ke sauri ko ƙoƙarin ya ba da roja[11] don ya sayi fetur fiye da sauran jama’a |
|
5 |
Sàndáa
|
Suna |
Itace da aka karya
ko aka sara daga jikin bishiya don yin amfani da shi kamar a makami na dukan
wani abu ko don dogarawa |
Dogon ƙarfe mai zanen mita
a jikinsa wanda ake awon man fetur da ke cikin tankin ƙasa |
|
6 |
Náiràa bìyár |
Suna |
Takardar kuɗin
Nijeriya mai ɗauke
da hoton marigayi Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa |
Naira ɗari
biyar |
|
7 |
Náiràa góomà |
Suna |
Takardar kuɗin
Nijeriya mai ɗauke
da hoton marigayi Alvan Ikoku |
Naira dubu ɗaya |
|
8 |
Ɗígòo[12] |
Suna |
(i) Ɗison abu ruwa-ruwa (ii) ruwan baƙaƙe da ake yi wa wasu haruffan Ajami ko na Larabci ko kuma Ingilishi (iii)
aya ta nuna alamar tsayawa a cikin jumla ko wajen karatu |
Lambobi ɗari da ke jujjuyawa, su bayar da lita
guda |
|
9 |
Bàasáajàa[13] (basaje) |
Suna |
Fakewa da wani hali
don samun riba |
Karkatar da man
fetur zuwa wani wuri ko wata ƙasa
maimakon zubawa a gidan mai a sayar wa jama’a, musamman don samun
riba sosai |
Waɗannan misalai sun fayyace
yadda ‘yan kasuwa suke ba kalmomin asali sababbin ma’anoni saɓanin waɗanda aka san su da su. Kuma
wani lokaci ba tare da an canja fasalin kalmomin ba, wato kalmomin suna nan
zamansu kamar yadda suke. Kamar yadda aka gani ‘yan kasuwa suna amfani da wannan hanya ta faɗaɗa ma’anar kalmomi, bayan sun lura da yanayin baƙin
abubuwan da suka shigo waɗanda ba su
san su
ba, kafin su yi amfani da kalmomi asali da za su dace.
4.2 Kalmomin da suka Shafi Ƙirƙira
A wannan sashe an kawo sabbin ma’anoni da ‘yan kasuwa
suka ƙirƙiro, don sadarwa a
tsakaninsu. Waɗannan sabbin ma’anoni sun keɓanta gare su ne kawai. Akasari duk inda aka zagaya ba za
a ji ana aiwatar da su ba, sai a Hausar rukunin masu sayar da man fetur da baƙin mai.
1. Ƙirƙira Daga Kalmomin Asali
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jùuyèn náa-ìsáa |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Juye baƙin mai tun bai gama aiki ba |
|
2 |
‘Yán-sâ-káì[14] |
Harɗaɗɗen Suna |
Masu hidimar al’umma kyauta (‘Yan ganin dama) |
‘Yan alfarma waɗanda ba su bin layi ko ‘yan
cuwa-cuwar man fetur masu ba da cin hanci a sayar musu mai, ba tare da sun
tsaya layi ba ko kuma masu cin layi, sai dai su tsaya gefe idan an fara
shigar da abubuwan hawa sai su kutsa in sun sami kafa. |
|
3 |
Mân hánnúu[15] |
Harɗaɗɗen Suna |
Man gyaɗa |
Man cuwa-cuwa ko na
sata |
|
4 |
Másháaƙár ískàa[16] |
Harɗaɗɗen Suna |
Wuri ne ko kafa da
aka keɓe don wani abu ya riƙa zuƙar iska |
Fayib da ake haɗawa
da tankin mai na cikin ƙasa don tanki ya riƙa numfasawa
musamman idan akwai mai a cikinsa, don gudun kada tanki ya fashe |
2. Ƙirƙira ta Gamin-gambizar Kalmomin Asali da
na Aro
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jákkwátàa (jar kwata) |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Robar maganin ƙwari mai launin ja |
|
2 |
Jùuyèn gáayèe[17] |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Baƙin mai da wani ya
juye wanda bai gama aiki ba |
|
3 |
Gárwár gáayèe |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Babbar robar yagot
mai mariƙi
ko hannu |
3. Ƙirƙira Kalma Wadda Sam Babu Ita a Hausa
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Róojà |
Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Cin hanci da ‘yan
cuwa-cuwar fetur ke ba ‘yan gidan mai kafin a sayar musu da man fetur |
Idan aka lura da dukan waɗannan misalan, za a ga sun samu ne ta hanyar ƙirƙirar daga kalmomin asali,
da ƙirƙira ta fasahar gamin
gambizar kalmar asali da ta aro,[18] da kuma ƙirƙira kalma wadda sam babu
ita a wani harshe. Ƙirƙira irin waɗannan kalmomi na bunƙasa rumbun kalmomin harshe.
Duba da yadda ake daɗa samun masu sayar da man
fetur da baƙin mai
na ƙirƙira sababbin ma’anoni,
musamman waɗanda suka shafi yanayin
aiwatar da kasuwancinsu ko rayuwarsu ta yau da kullum. A wasu
lokuta, ‘yan kasuwar sukan cusa sabbin ma’anonin da suka samar a cikin harshe.
Bayan wani ƙanƙanin lokaci, sai a tarar sun saje da sauran ma’anonin Hausa na
asali.[19]
4.3
Kalmomin da
suka Shafi Aro
A wannan
sashe, an ga yadda masu sayar da man fetur da baƙin mai suka ɗauko kalmomi daga harshen
Ingilishi da na Yarbanci. Su mayar da su na Hausa bayan an yi musu kwaskwarima, don su dace da tsarin
Hausa. A taƙaice,
sukan Hausantar da baƙin kalmomin da suka aro ne
don samun kafar sadarwa a tsakaninsu.
|
Lamba |
Kalma |
Asalin Kalma |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jóokò (Jooko)[20] |
Kalmar aro ce daga Yarbanci |
Tsaiko cikin layin
lodin mai ko lalacewar mota kan hanyar dawowa |
|
2 |
Dìríilìn (Drilling) |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Sauran man fetur da
ke ragewa bayan an sauke mai a gidan mai. Ana yi masa kirari da ‘dirilin na yaron mota’ |
|
3 |
Míshìn gálàn (Measurement
galoon) |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Auna mitar bayar da mai ko ta inji na mai |
|
4 |
One-five (1,500) |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar |
|
5 |
Áftáasêl (Aftersale)[21] |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Sai an sai da mai sannan a biya mai man fetur |
|
6 |
Màanúwâl kóó kwàmfúutàa (Manual/computer)[22] |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Mitar auna abin da aka sayar a injimin sayar da mai, kuma tana iya
lissafin lita miliyan, wato daƙiƙa bakwai na lamba. |
|
7 |
Hâf (half) gáayèe[23] |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Robar yagot mai
biye wa garwar gaye |
|
8 |
Ólóojì (awon mai) |
Kalmar aro ce daga Yarbanci |
Awon man tanka
kafin a zuba a cikin ramin ajiya na ƙasa[24] |
Daga
waɗannan misalai an ga
yadda ‘yan wannan rukunin suke Hausantar da kalmomin aro, ta hanyar yi wa kalmomin kwaskwarimar da za
ta sa su dace da tsarin furucin Hausa. Daga nan sai su ba su sababbin ma’anoni da suka
bambanta da na asalinsu. Abin ban sha’awa shi ne, yadda baƙin kalmomin suka saje da na
asali wani lokaci akan kasa bambanta su. Kenan, wannan hanyar sarrafa kalmomin
aro fitatta ce kuma madoga ga harshe, musamman inda aka kasa nemo madadin
sabuwar kalma daga cikin na asali da ake da su a harshe. A ƙarshe, aro hanya ce
mafi sauƙi da
harsuna suke faɗaɗa rumbun kalmominsu, bayan
an samu hulɗa da cuɗanya tsakanin harsuna daban-daban. Kamar dai yadda masu sayar da man fetur da baƙin suke amfani da su a
zantukansu na yau da kullum.
5.0 Kammalawa
Daga abin da ya gabata a fili yake cewa, wannan rukuni na
‘yan kasuwa na amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi da suka shafi yanayin kasuwanci, musamman don
tafiyar da hankulan masu sayen kaya, inda suka al’adanci yin amfani da kalmomi sanannu wajen samar da
sababbin ma’anoni, amma ba lalle ne ma’anar ta zo daidai da ma’anar asali ba. Da ƙirƙiro sababbin ma’anoni daga
kalmomin asali ko daga na aro ko ta gamin gambiza inda za a haɗa kalmar asali da ta aro a tashi sabuwar
kalma, ko kuma ƙirƙiro ma’anonin da sam babu
su a harshe. Haka kuma, sarrafa harshe cikin aiwatar da kasuwanci a
tsakanin ‘yan kasuwa ta taimaka wajen haifar da ƙirƙire-ƙirƙiren sababbin kalmomi da
jumloli, waɗanda ke daɗa bayyana hali da yanayin ciniki a muhallan
kasuwanci.
6.0 Sakamakon Bincike
A taƙaice,
wannan takarda ta gano abubuwa kamar haka:
1. Wannan takarda ta gano cewa, Hausar masu
sayar da man fetur da baƙin mai (sabuwar Hausar rukunin
jama’a) a cikin garin Sakkwato suna da wata hanyar
sadarwa a tsakaninsu, wadda ta bambanta da
Hausar gama-gari
ta fuskar kalmomi, domin ba kowa ke iya
fahimtar ma’anarta ba.
2. Binciken
ya gano cewa ‘yan wannan rukuni suna amfani da dabarar faɗaɗa ma’anar kalmomin Hausa na asali da sarrafa kalmomin aro da kuma ƙirƙira sababbin
kalmomi a
cikin zantukansu na yau da kullum.
3. Bugu da ƙari, takardar ta gano ‘yan kasuwar suna amfani da dabarar ɓoye wasu ma’anoni, domin saye da ɓatad da bami wanda ba ɗan rukuninsu ba. A taƙaice, sukan sirranta
maganganunsu ne domin ƙoƙarin samun riba mai yawa da sakaya lissafin kuɗi a cinikayyarsu.
MANAZARTA
1. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Ahmadu Bello University
Press Limited.
2. Fagge, U.U. (2004). Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers limited.
3. Harris, Z.S. (1952). ‘Discourse Analysis’ In Language,
V. 28, 1-30.
4. Isah, F.H. (2018). A Sociolinguistic Analysis of The Jargons Used
by Town Service Tricyclists (A-daidaita-sahu) in The Kano Metropolis.
Unpublished M.A Dissertation. Department of Liguistics. Bayero University, Kano.
5. Mode, A. (2024). Nazarin Hausar ‘yan Koli a
Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
6. Sharu, Y. (2023). Hausar ‘yan Agwagwa-da-buje a Garin Sakkwato.
Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
7. Umar, M.M. (2019). Nazarin Hausar Wasu Rukunan ‘Yankasuwa a Garin
Sakkwato. Kundin Digiri Na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar
Usamanu Xanfodiyo,
Sakkwato.
8. Yusuf M.A. (2002). The Development of Hausa Neologism: The Role
of Urban Spaces. In Bichi, A.Y et al
(eds). Studies in Hausa Language, Literature And Culture. The Fifth
Hausa International Conference. Kano: Benchmark Publishers Limited. Page
105-113.
9. Zailani, A.A. (2019). A Study of Communication Strategies in Hausa
Request Act. Unpublished Ph.D Thesis. Department of Linguistics and Foreign Languages. Bayero
University,
Kano.
RATAYE
MUTANEN DA AKA ZANTA DA SU
|
S/N |
Suna |
Shekaru |
Muhallin da aka
Tattauna |
Kwanan Wata |
|
1 |
Malami man Ada |
51 |
Gidan man ada titin
Kalambaina, Wamakko, Sakkwato. |
01/10/2024 |
|
2 |
Alh. Basiru Babawo |
40 |
Mai sayar da baƙin mai a bakin
gidan man Man Ada titin Kalambaina, Wamakko, Sakkwato |
05/10/2024 |
|
3 |
Nasiru Malami |
38 |
Mai sayar da man
fetur a hannun-riga da gidan man NNPC mega station kusa da
makarantar FGC, Sakkwato |
06/10/2024 |
|
4 |
Mustapha Dogon-daji |
29 |
Mai sayar da baƙin mai a gidan dare
bakin rawun na gidan ashana western bye-pass,
Sakkwato ta Kudu, Sakkwato |
21/10/2024 |
|
5 |
Ashiru Dabagin Arɗo |
20 |
Mai sayar da baƙin mai da fetur Dange-shuni |
18/11/2024 |
|
6 |
Mal. Ahmad Zaruku |
60 |
Gidan man
Bashariyya Global Resourses, Sakkwato ta Arewa |
25/12/2024 |
|
7 |
Bashar Yusuf
(police) |
41 |
Gidan man A.A Rano Nig.
Ltd. Rawun na gidan Man Ada, Sakkwato |
15/01/2025 |
|
8 |
Dogo Mai Gas |
47 |
Gidan man Altine
Muhammad Ƙaura
titin Kalambaina, Sakkwato |
16/01/2025 |
|
9 |
Umar Faruk (yellow) |
35 |
Mai sayar da baƙin mai da fetur Wamakko, Sakkwato |
07/02/2025 |
|
10 |
Bashar Ibrahim Maigayya |
30 |
Shiyar Arkilla Federal Low Cost kusa da ofishin NDLEA |
09/02/2025 |
[1] Masu sayar da man fetur
iri biyu ne: akwai ‘yan kasuwa masu sayar da mai a gidajen mai, akwai kuma masu
sayar da mai a gefen tituna a cikin jarka ko garwa. Fagge (2004:126-127) ya kira su ‘yan cuwa-cuwar man fetur. A wasu wurare
ana kiran su da ‘yan bumburutu ko kuma ‘yan bulakmaket. A hukumance,
suna sayar da mai ba bisa ƙa’ida ba. A wasu lokutan baya, har kamen masu sayar da
mai a kan hanya ake yi.
[2] Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, “Ƙamusun Hausa” Ahmadu Bello University Press
Limited, Kano, 2006, shafi na 140.
[3] Gidan mai wuri ne na
hadahadar mutane masu zuwa don saya wa abubuwa hawa mai da injunan haska wutar
lantarki.
[4] Hukuma ce wadda ke da
alhakin sa ido kan fice da shigen ma’adinan da ake haƙowa a cikin Nijeriya.
Ayyukan da aka ɗora mata sun haɗa da: Sa ido ga yadda ake gudanar da ha}ar
mai da samar da rijiyoyin mai da fitar da ɗanyen mai a ƙasashen waje da wuraren
tace ɗanyen mai da depot na
ajiyar mai da gidajen mai da sauran wuraren da ake ajiye mai ko sayar da shi,
da bututun da ke ɗauko ɗanyen mai da gas da sauran ma’adinnan
mai. Haka kuma, hukumar na tabbatar da cewa, duk kamfunnan mai sun mallaki
lasisi da gudanar da ayyukansu cikin tsabta da ɗaukar matakan kiyaye hatsarin gobara da bin doka da oda,
musamman abin da ya shafi farashi da cikar lita da kuma biyan haya ko haraji ga
gwamnati kamar yadda ya dace.
[5] Ana ganin sunan baƙin mai ya samo asali ne
daga launin da man na juye ke sauyawa idan ya gama aiki.
[6] Don ƙarin bayani sai a duba
aikin, Umar, Muhammad Mustapha, “Nazarin
Hausar wasu Rukunan ‘Yan Kasuwa a Garin Sakkwato” Kundin
Digiri na Uku. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, 2019, shafi na 38-59.
[7] Fifiƙewa da ba da himma wajen ƙoƙarin samun wani abu ta
hanyar cuta.
[8] Masu sayar da mai a
gefen hanya cikin jarkuna su ne, irin waɗannan matasa.
[9] Wasu suna kiran ta
tiyo ko roba ko hwanho ko kuma nozzle, musamman ganin irin yadda take aikin zuƙo mai.
[10] Man fetur wanda ake
haƙowa a
Nijeriya shi launinsa ke da kama da ja-ja-ja kamar yadda Dogo na gidan man
Alh. Altine
Muhammad Kaura ya shaida mini.
[11] An bayar da ma’anar roja
a sashen 4.2.
[12] Amma a injunan man fetur
na shekarun baya masu kama da tuƙa-tuƙa ɗigo goma shi ne lita
guda, kafin
bayyanar injunan
zamani masu amfani da digital.
[13]Gidajen mai masu karkatar da man
fetur sukan yi amfani da tankokinsu na ɗaukar mai waɗanda ba a rubuta musu sunan kamfani a jikinsu ba, don
kar hukuma ta gane su, musamman a lokutan da ake fuskantar ƙarancin man fetur.
[14] Ƙungiyoyin sa-kai ko kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.
[15] Sayen man fetur ko
gas ta bayan fage daga hannun direba ko yaransa ko wasu ma’aikatan kamfani ko
kuma mutane masu harka da kayan sata (ɗanyun kaya a Hausar wasu ‘yan kasuwa) ko kayan rashin gaskiya.
[16] Tankin mai na ajiyar
mai a cikin ƙasa
yana da marfi, wanda a jikinsa ake haɗa fayib mai zuƙar mai daga tanki zuwa ga injin na sai da
mai, da fayib na mashaƙar iska wanda ake kafewa a tsaye tare da sunkuyar da
kansa don rana ruwa shi cikinsa, da kuma kusurwar da ake buɗewa a duk lokacin da za a zuba mai ko awon
sa.
[17] Juyen matashi ɗan gayu.
[18] Wannan rukuni na ‘yan
kasuwa ya yi amfani da wannan hanya ta ƙirƙira wajen bai wa mazubi ko abin awon man
fetur suna, kamar yadda misalan suka nuna. Wani lokaci ma, ana amfani da hanyar
fassara kalmar aro (loan translation). A nan akan yi amfani da kalmomi ne a fassara ainihin suna, aiki ko
ma’ana ta baƙon abu a harshen aro. Ga misali, ana amfani da
dafa-duka (jalaf) domin wakiltar motar nan Peugeot 504 (station wagon).
[19] Don ƙarin bayani a dubi,
Yusuf (2002) ya bayyana yadda ƙirƙirarrun kalmomi kan rikiɗe su koma karɓaɓɓun kalmomi bayan an baddala
su cikin harshe, kuma sannu a hankali za su yaɗu a riƙa amfani da su kamar sauran kalmomin harshe.
[20] Ana cewa wane ya yi joko
da yawa, wato ya jima bai dawo ba, ko kuma a ce, direba ya hwaɗa joko.
[21] Ana amfani da wannan
salo ne don a tabbatar da man da aka kawo ya cika kuma mita da difin na gidan
mai na aiki daidai.
[22] Floor measurement shi ne ainihin
sunan mitar a harshen Ingilishi. Ita kuma kalmar kwamfuta wasu na fassara ta da na’ura mai ƙwaƙwalwa.
[23] Akwai masu kiran ta
‘Yákkùnúu.
[24] Ana wannan awon ne
idan ana shakkun tankin mota ko wanda ya kawo mai, ko kuma don tabbatarwa
kawai.
Kalmomin
Masu Sayar da Man Fetur da Bakin Mai a Garin Sakkwato
Cite this
article as: Umar M. M. (2025).
Kalmomin Masu Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai a Garin Sakkwato.
Zamfara International Journal of Humanities, 4(1), 91-99.
www.doi.org/10.36349/zamijoh.2025.v04i01.010.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.