Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutuwar Shahada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. A halin da ake ciki yanzu yadda kafirai kamar a Jihar Filato da Kudancin Jihar Kaduna suke ta yunƙurin karkashe musulmi da tarwatsa su da raba su da garuruwansu, to idan waɗansu musulmi suka tsaya suka tunkari waɗannan kafiran har kuma suka rasa rayukansu a kan haka, za a iya cewa sun yi mutuwar shahada irin na jihadin musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Sahihin Jihadin Musulunci yana da sharuɗɗa da ƙaidoji da dokokinsa, kamar yadda malamai masana suka yi bayani musamman a cikin littaffan Fiqhu.

Amma haƙƙi ne na wajibi a kan musulmi a duk inda su ke su kare addininsu da rayukansu da iyalansu da dukiyoyinsu da gwargwadon ƙarfi da ikonsu ko iyawarsu.

Idan musulmin da su ke zaune a wani wurin da aka fi ƙarfinsu suka kasa kare kansu daga masu yi musu taaddanci, to wajibi ne a kan sauran musulmin da su ke kusa dasu su taimaka musu.

Bai halatta ba musulmi su bari ana zaluntar sashensu, ko kuma a riƙa amfani da su wurin zaluncin, balle kuma su da kansu su zama masu shiryawa ko zartar da zaluncin.

Ya halatta ga musulmin da ake ƙuntata musu su yi hijira zuwa inda za su iya yin addininsu ba da takurawa ba, har zuwa lokacin da za su samu iko da ƙarfin tsayawa da ƙafafuwansu a garuruwansu.

Duk lokacin da wani musulmi ya rasa ransa a wurin ƙoƙarin kare addininsa ko rayuwarsa ko iyalinsa ko dukiyarsa, ko kuma wurin hana a zalunce shi, to yana da hukuncin wanda ya yi mutuwar shahada.

Bai halatta ba musulmin da su ke a cikin rauni da rashin ƙarfin tattali su bari a yi amfani da su wurin tayar da wata fitinar da za ta janyo a yi ta kashe su ko yan uwansu ko da kuwa da suna jihadi ne.

Domin manufa mafi girma na halittar mutane da aljanu shi ne su tsayu da bautar Allaah shi kaɗai, amma ba wai su yi ta mutuwa suna barin duniya haka nan ba tare da ilimi da ilmantarwa ba.

Shi Jihadin Musulunci Allaah Ta’aala ne yake kawo shi a lokacin sa. Abin da yake a kan musulmi dai kawai shi ne yin tattali da shirin ko-ta-kwana, kar su yi sakaci har arna su murƙushe su gaba-ɗaya.

Kuma ko da a lokacin da musulmi su ke da ƙarfin iya tunkarar kafirai, ba a yarda su yi fata ko burin hakan ba sai ya zama tilas. Domin zaman lafiya da aminci a rayuwa shi ya fi komai.

Al-Bukhaariy (2965-2966) da Muslim (4640) sun riwaito hadisin Sahabi Abdullaah Bn Abi-Aufaa (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya miƙe a cikin Sahabansa da yamma a wani yaƙin da ya fita, ya ce

« أَيُّهَا النَّاسُ ، لاَ تَتَمَنَّوْا لِقَاءَ الْعَدُوِّ ، وَسَلُوا اللَّهَ الْعَافِيَةَ ، فَإِذَا لَقِيتُمُوهُمْ فَاصْبِرُوا ، وَاعْلَمُوا أَنَّ الْجَنَّةَ تَحْتَ ظِلاَلِ السُّيُوفِ »

Ya ku mutane! Kar ku yi burin haɗuwa da maƙiya. Ku roki Allaah kariya da lafiya. Idan kuma kuka haɗu da su to sai ku jajirce. Kuma ku san cewa: Aljannah dai a ƙarƙashi inuwar takubba su ke.

Daga nan sai kuma ya ce

« اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ ، وَمُجْرِىَ السَّحَابِ ، وَهَازِمَ الأَحْزَابِ ، اهْزِمْهُمْ وَانْصُرْنَا عَلَيْهِمْ »

Ya Allaah! Ya Masaukin Littafi, kuma Mai gudanar da giragizai, kuma Mai ruguje rundunoni! Ka rushe su, kuma ka ba mu nasara a kansu.

Hanyoyin samun shahada suna da yawa a cikin sahihin musulunci, kamar yadda hadisai sahihai daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) suka nuna

1. Mutuwa a wurin yaƙi da kafirai a jihadin ɗaukaka Kalmar Allaah.

2. Mutuwa a kan hanyar tafiya jihadin ɗaukaka hanyar Allaah.

3. Mutuwa a cikin annoba.

4. Mutuwa da matsalar ciwon ciki.

5. Mutuwa ta hanyar nutsewa a cikin ruwa.

6. Mutuwa a cikin girgizar ƙasa ko rushewar gini.

7. Mutuwar mace mai naƙuda ko mai ciki.

8. Mutuwa a cikin gobara.

9. Mutuwa ta dalilin tarin huka.

10. Mutuwa ta dalilin cutar bulala.

11. Mutuwa wurin kare addini ko rai ko iyali ko dukiya.

(Dubi dalilan waɗannan a cikin: Ahkaamul Janaa’iz, shafi: 35-41)

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« مَنْ قُتِلَ دُونَ مَالِهِ فَهُوَ شَهِيدٌ ، وَمَنْ قُتِلَ دُونَ أَهْلِهِ ، أَوْ دُونَ دَمِهِ ، أَوْ دُونَ دِينِهِ فَهُوَ شَهِيدٌ »

Duk wanda aka kashe shi yana kare dukiyarsa to shi shahidi ne. Kuma duk wanda aka kashe shi yana kare iyalinsa, ko yana kare jininsa, ko yana kare addininsa, to shi shahidi ne. (Abu-Daawud: 4774, kuma Al-Albaaniy a cikin Ahkaamul Janaa’iz, shafi: 42 ya ce: Sanadinsa Sahihi ne).

Haka kuma ya ce

« كُلُّ مَيِّتٍ يُخْتَمُ عَلَى عَمَلِهِ ، إِلاَّ الَّذِى مَاتَ مُرَابِطًا فِى سَبِيلِ اللَّهِ ، فَإِنَّهُ يُنْمَى لَهُ عَمَلُهُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ ، وَيَأْمَنُ مِنْ فِتْنَةِ الْقَبْرِ »

Kowane mamaci ana rufewa a kan aikinsa, sai dai wanda ya mutu a kan ribaɗi a cikin hanyar Allaah. Shi kam ana yi masa renon aikinsa har zuwa Ranar Ƙiyama, kuma ana amintar da shi daga fitinar ƙabari. (As-Saheehah: 549, Sahih Abi-Daawud: 1258)

Kuma ko da musulmi bai samu mutuwar shahada a filin jihadin ɗaukaka Kalmar Allaah ba, wannan ba ya hana shi samun matsayin masu shahadar

Al-Imaam Muslim (5039) da wasu As-Haabus Sunnan sun riwaito maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

 « مَنْ سَأَلَ اللَّهَ الشَّهَادَةَ بِصِدْقٍ ، بَلَّغَهُ اللَّهُ مَنَازِلَ الشُّهَدَاءِ ، وَإِنْ مَاتَ عَلَى فِرَاشِهِ »

Duk wanda ya roƙi Allaah mutuwar shahada da gaskiya, Allaah zai kai shi masaukin masu mutuwar shahada, ko da kuwa a kan gadonsa ya rasu.

Kar wani ya ɗauki waɗannan bayanan kamar kashe gwiwa ko karya zuciya, amma dai ƙarin faɗakarwa ko zaburarwa ne ga fahimtar haƙiƙanin yadda alamura su ke, tare da samu kyakkyawar hanyar zartar da su bisa dacewa da sharia. Sannan kuma tare da sanin cewa shi musulmi mabiyin sharia ba ya yin asara a cikin komai a duk inda ya ke, in shà Allâh.

Allaah ya yi mana maganin dukkan fitintinu, da dukkan masu tayar da su. Kuma ya zaunar da mu a cikin ƙasashenmu lafiya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments