Ticker

6/recent/ticker-posts

Mata A Ma’aunin Sarrafa Harshen Hausa

Citation: Abdullahi Lawal DIKKO (Ph.D) (2022). Mata A Ma’aunin Sarrafa Harshen Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Ɓol. 10, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State Uniɓersity, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

MATA A MA’AUNIN SARRAFA HARSHEN HAUSA

By

Abdullahi Lawal DIKKO (Ph.D)

Tsakure

Wannan maƙala yunƙuri ne domin fito da mata a ma’aunin sarrafa harshen Hausa. An yi binciken ne da niyyar gano yadda jinsin matan Hausawa ke amfani da sarrafa harshe domin a tabbatar da cancantar mata a ma’aunin sarrafa harshe. Wato an zaƙulo yadda mata ke amfani da hikimarsu wajen amfani da harshen Hausa ta fuskoki mabambanta tare da bayyana irin kalmomin da suke amfani da su a cikin maganganunsu na yau da kullum, kamar karin magana da habaici, da sara da saye saboda haka wannan maƙala ta nazarci irin gudummuwar da jinsin mata ke ba da wa wajen amfani da harshen Hausa, wanda kusan in an gwama su da maza ana iya cewa sun yi wa mazan zarra wajen amfani da hikimomin sarrafa harshe da kuma yin amfani da wasu keɓaɓɓun zantuka da kalmomin harshen Hausa. Manufar wannan maƙala ita ce a fito da wasu muhimman al’amura da suka shafi sarrafa harshe waɗanda mata suka fi amfani da su, da kuma zayyana yadda suke amfani da su fiye da maza. Maƙalar ta gano cewa jinsin mata suna taimakawa wajen fito da al’adun Hausawa ta hanyar mata. Baya ga haka dukkanin saƙon da mata ke ƙoƙarin isar wa ta hanyar waɗannan fuskoki da aka nazarta, yana isa dai dai babu wani cakuɗeɗeniya ko caɓewar zantuka. A ƙarshe an fahimci cewa jinsin mata sun cancanci ma’aunin nazarin harshensu, saboda muhimman bayanai da aka samu da kuma irin saƙonni da suke isar wa cikin hikima da adana harshen ya tabbata har tsawon rayuwa, kuma mata sun kasance ma’ajiya da makaranta ta sarrafa harshe ga ‘ya’yan Hausawa. A lokacin gudanar da wannan nazari an fuskanci waɗansu matsaloli dangane da halayar mata musamman abin da ya shafi kunya wajen gano muhimman bayanai daga bakinsu. Sa’annan sun fi yin al’amuran su tskaninsu da ‘yan uwansu mata.

Gabatarwa

Harshe na taka muhimmiyar rawa wajen sadarwa ga kowace irin al’umma. Wajen yin magana, ana iya banbance jinsin ta mace da na namiji. A cikin wannan takardar an yi ƙoƙarin ankarar da abubuwan da suka shafi jinsin matan Hausawa wajen amfani da harshe, sakamakon haka, an nuna damar da harshen mata ya samu wajen walwala ta fuskar magana ta hanyar shimfiɗa zantukansu akan turbar da ta dace, domin isar da saƙonsu cikin hikima da zalaƙa da nuna basirarsu wajen amfani da harshen. Sa’annan a cikin wannan maƙala an fito da misalai dabam – daban daga sara da saye da karin magana da kuma habaici inda aka zayyana irin Hausar matan, tare da kawo misalan kalmomin da suka ta’allaƙa ga mata. Bugu da ƙari wannan takarda ta ƙyallaro mana harshe na da tasiri wajen fito da al’adar Malam Bahaushe a fili ta hanyar bayyana wasu muhimman al’amurran da suka shafi hikimar matan Hausawa da ayyukansu. Sannan kuma an tattauna wasu muhimman batutuwan da suka shafi jinsin mata a cikin maƙalar.

Ma’anar Harshe

Bunza (2013, sh. 209) ba wani abu ne harshe, face hanyar sadarwa da ke wakana tsakanin mutum da mutum ta fuskar magana da daidaitaccen lafazi da aka saba da shi, sadarwa ta fuskar magana ita ce, harshe, kuma ita ce sunan da ake bai wa kowane harshe a doron ƙasa.”

Harshe shi ne tubalin gina duk wata zamantakewa da cuɗanya a tsakanin al’umma, sai dai dabarun sadarwa na iya zuwa ta sigogi mabanbanta, wato hanyoyi da dama, daga ciki akwai ishara, akwai magana da baki, akwai taɓa mutum a sassan gaɓoɓi da makamantansu.

Bita

Masana kimiyyar harshe da nazarin walwalar harshe da sarrafa harshen sun yi ƙoƙarin bayyana mana al’amurran da suka shafi waɗannan fage ta fuskoki da dama, da kuma irin rawar da suka taka. Saboda haka, za mu yi waiwaye kaɗan don mu fa’idantu ga abin da suka furta domin ya zama matashiya ko ishara ga manazarta. Daga ciki akwai waɗanda suka bayyana mana irin cigaban da aka samu a harshen Hausa. A yau tare da ba da shawarwari irin waɗannan masana sun haɗa da Abubakar (2006) da Muhammad (2006) da Amfani (2011).

Abubakar (2006) ya yi tsokaci a kan Hausa a yau, in da ya waiwaya baya, ya zayyana cewa in ana son a san yau sosai to dole a kalli jiya a fahimce ta da kyau sosai, ya cigaba da bayyana yadda aka fara amfani da harshen Hausa.

Muhammad (2006) kuwa ya nusar da mu game da muhimmancin harshen da yake cewa: “in ka ɗebe iskar shaƙa da ruwa da abinci, kusan babu wani abin da ya kai harshe muhimmanci ga ɗan Adam, in ban da ilimi wanda shi ɗin ma kuma sai da harshen ake naƙaltarsa sosai.

Hudson (1996) da Wardhaugh (2007) sun yi tsokaci kan abin da ya shafi walwalar harshe inda Hudson (1996, sh. 43) ya yi tsokaci dangane da irin abubuwan da suka shafi nazarin kimiyyar harshe musamman ma a nazarin ilimin walwalar harshe binciken ya tabbatar da ana iya samun banbance – banbance na karin harshe na yanki da na rukuni ko shiyya. Amma Wardhugh (2007, sh. 11) ya yi sharhi game da surki, ya nusar da cewa duk inda aka sami mutum guda ko biyu suna tattaunawa a tsakaninsu to dole a samu tasirin surki a cikin zantukansu.

Dangane da maƙaloli da suka shafi ɗabi’un mata ta fuskar kunya a cikin al’amurran rayuwar mata a yau akwai aikin Bilkisu (1991) da Gusau (1994) da Rabi (2010).

Bilkisu (1991) ta yi bayani a kan gwagwarmayar mata wajen bunƙasa halin da suke ciki a yau. Ita kuwa Rabi (2010) ta bayyana cewa “kunya hanya ce ta nuna ɗa’a da kawaici, wato, idan mutum zai yi abu, ya duba abin da zai je ya dawo ta ɓangaren kansa da tsakaninsa da jama’a da kuma mahaliccinsa.”

Ƙwarewar Mata Wajen Sarrafa Harshen Hausa

Wasu dalilai ne d za’a iya tabbatar da haka. Abin da ya takalo wannan batu a wannan wuri shi ne ra’ayin da ake da ita game da amfani da harshe ta fuskar fifiko a tsakanin mata da maza Laboɓ (1982, sh. 191). Mata suna ganin sun fi maza laƙantar harshe da sarrafa shi, amma wannan batu bai hana maza su ma su rinƙa ganin sun fi mata ba. Babbar hanyar da za a iya tantance haka ita ce ta yin la’akari da abin da manazarta da masana suka hango, da kuma muhimmancin harshe, A tsarin zamantakewar al’ummar Hausawa, akwai waɗansu muhimman abubuwa da ba a taɓa iya kauce musu, sai da su rayuwa ke tabbata cikin nasara da walwala. A nan, ana iya bugun ƙirji a ce harshe shi ne farko, wato ginshiƙi ne na rayuwar kowace al’umma. Dukkanin al’amurran rayuwa da harshe ake yin su, dole mutum ya yi magana da ɗan uwansa ko abokin zamantakewarsa domin rayuwa ta bunƙasa. Harshe ke gina al’umma, harshe ke gina ƙasa a samu ci gaba. Harshe ake amfani da shi a makarantu na ilimin addini ko ilimin boko. Makarantar farko ga al’umma ita ce mata, domin su ne ke fara koyar da magana da tarbiyya kai har ma da karatu a kowane fage. In haka ne mata suna taka muhimmiyar rawa wajen amfani da harshe da tabbatar da muhimmancinsa.

Majid (2012, sh. 105) ta yi bayani kamar haka: “Ji nan Bashir ka da ka sa na yi magana da yawa, ka san abin da zai ja ni na ce. Don haka, bari ka ji. Na riga na zartar da auranka. In kuma za ka ƙi, sai ka ƙi. Ka san ni, ka san abin da zan iya yi maka tasiri kuma ka san zamowar ka ɗan aba zai yi maka komai ba.”

Kalamanta sun nuna cewa a nan, mata ba su faye yawan son magana ba, ko su biyu ne ko kuma fiye. Sun fi son a yi magana kai tsaye ‘yar kaɗan. Tsarin zamantakewar Hausawa ya yo naso daga tarbiyyar da suka samu daga addinin Musulunci saboda ba a yarda ka saki matarka ta tafi duk in da ta ga dama ba. Dole sai da kulawa. Abu ne da addinin Musulunci ya yarda da shi. Ba a yarda mace ta shiga cikin maza tana cakuɗeɗeniya da su ba, ko kuma ta riƙa garari kamar maza. Adamu (2001, sh. 79) ta bayyana cewa: “keɓanta da mata ke yi ya takura su daga yin al’amuran da suka shafi gida sai dai da taimakon ‘ya’yansu mata da yara, wajen sayo musu duk wani abu da suke buƙata, ko kuma sayar da wani abu na ƙaruwa da suke yi.” Saboda haka, zaman gida ya taimaka masu wajen amfani da harshe sosai.

Wani abin la’akari cikin wannan batu mata shi ne akwai banbancin fahimta a cikin al’amuran da suka jiɓanci lamarin jinsintaka, Yakasai (2009, sh. 191). Haƙiƙa masana irin su Ma da Broker sun nazarci matsalar rashin fahimta tsakanin maza da mata, kuma sun amince tasirin al’ada ne ya haifar da bambanci tsakanin maza da mata cikin sadarwa. Haka kuma nazarin maganganun yara, sun gano cewa matan Turawa suna da al’ada mabambanciya kuma hakan ya yi tasiri kan mu’amala tsakanin maza da mata. Keɓantuwa da shiga jama’a kowane akwai irin tasiri da yake haifarwa. 

Ma’aunin Harshen Mata

Yakasai (2012, sh. 95): ya nuna cewa ana amfani da abubuwa daban – daban wajen sadarwa da suka haɗa da kalmomi da ishara da gaɓuɓɓa da kuma ɗabi’a. Wannan bayani ya yi daidai domin ai ita sadarwa yanayi ne da ake sarrafa bayanai tsakanin al’umma, cikin tsarin kalmomi da ishara da kuma ɗabi’a wato kafin sadarwa ta tabbata. Wajibi ne a sami fahimtar juna tsakanin mai magana da kuma wanda ake yi wa magana. Idan har waɗannan kalamai da aka zayyana na da muhimmanci ga al’umma a matsayin sinadarin gina zantuka a rayuwa. Duk inda aka sami jinsin namiji da mace, za a iya gane waya fi cin gajiyar abin ko ya fi amfani da shi, ko wa ya fi zama kan gaba a wajen amfani da harshen. Mata sun cancanci ma’auni a wajen nazarin harshensu, domin kuwa yadda suke amfani da harshen Hausa ana iya cewa abin a duba ne musamman abubuwan da suka danganci sarrafa harshe.

A nan, ba mun yi la’akari da yawan kalmomu ne da kowane ke amfani da su ba, illa mun bi wasu muhimman bayanai ne da nazarin ya hango ta hanyar amfani da sarrafa harshe a bakin matan Hausawa.

Matan Hausawa da kansu sun bigi ƙirji, sun tabbatar da cewa sun fi maza amfani da karin magana. Babban dalilin su shi ne mata suka fi zaman gida, sa’annan ga zama cikin kishiyoyi. Domin haka ba a raba su da habaici ga kishiyoyinsu a cikin gida saboda ta wannan hanya ce suke iya mayar da martani da cusa wa kishiya baƙin ciki. Mu’amalarsu da ɗabi’unsu na zamantakewa sun ta’allaƙa da cikin gida.

Harshen mata ya cancanci ma’auni wajen yin nazari, akwai su da cuɗanya da mutane da gudanar da hulɗoɗi sosai a tsakanin su da juna da kuma sauran al’ummomi ta fuskoki mabanbanta. Sakamakon haka, suna da ƙoƙarin son a san sun san harshe ta hanyar amfani da harshe a cikin maganganunsu na yau da kullum.

A lokacin tattaunawa da aka yi da mata kai tsaye, sun kawo waɗannan misalan habaici.

i.Wash Allah! Uwar Sani wash Allah!

Na ciwo Uwar Sani na ciwo.

Daddanna Uwar Sani

Daddanna Uwar Sani ƙungurun Uwar Sani ya Karye

ii.Tankarin Gida ɗa namiji 

Ko mace tankar gida ce don ko ba ta so a fidda rabonta.

iii.Bana mun yi ɗa,

Bana babu kaɗi,

shekarata goma ina kaɗi,

Banga amfanin ka ba auduga,

Bari in raurau da maje gaba

Dan maje gaba ya fi zani wuya

Gaskiyar magana ita ce, mata a nan, sun yi amfani da sarrafa harshe ta hanyar habaici domin mayar da martini da kishiyoyinsu kamar yadda muka gani a misalan da ya gabata. Wani abin la’akari shi ne mata akwai su da nuna kaɗifiri da son a sani da nuna burgewa a lokacin da suke tattaunawa. Ba ka raba su da amfani da kalmomin sara a cikin zantukansu.

Kalmar da ake kiran kishiya:

Kalma

 Ma’ana Wurin mata

Shu’uma

 Mace mai kissa da kinibibi

Kalmar da ake kiran dangin miji:

 Kalma

Ma’ana Wajan Jama’a

Ma’ana Wurin Mata

 Gidan ƙaya

Inda ba mafita ko gidan wahala

Gidan da ake zaune da uwar miji

Kalmomin da ake kiran samari:

Kalma

Ma’ana Wajan Jama’a

Ma’ana Wurin Mata

Na waje na

Na kusa da ni

Saurayin da ake so

Haƙiƙa mata na amfani da saye domin sakaya ko ɓoye wani abu da ba a son a faɗi kai tsaye, ko ba a son wani ya san abin da ake nufi ko aka faɗa. Haka kuma mata na amfani da saye domin sirrantawa a tsakaninsu. Irin waɗannan kalmomi da mata kan yi sayensu sun haɗa da kalmomin jinin al’ada. Misali su kan kira su da sunaye kamar haka:

Ta hau danja    file ya fashe

Jar mota     tana busy

Manja     baƙo daga ɗanja

Kalmomin sara da suka danganci aure:

Kalmar saye

Ma’ana

Baya kwanciya da ni

Baya jima’i da ni

Ba ya ɗaukar kwano na

Ba mu saduwa

Karin magana na daga cikin zantukan hikima da matan Hausawa ke amfani da su acikin zantukansu na yau da kullum, yana taimakawa wajen tattauna a tsakanin da juna wajen mayar da martini kan wani magana da ya auku, misali: Gyaran hali ko wata matsala da ke aukuwa ko nishaɗantarwa ko nuna haɗin kai da zumunta.

Misalan Karin Maganan da Mata ke yi sun haɗa da:

i.Haka tara, inji kishiyar mai mageɗuwa.

ii.Allah uba inji shegiya.

iii.Ƙaƙa zan yi da abin da ya gagari wuta, inji kishiyar ƙonanniya.

iv.Karuwa, ba ta kiwon kaza.

v.Jiya ba yau ba tsohuwa da ɗaga azzakari.

Ta fuskar sarrafa harshe, an sami mata da suka ciri tutar yabo da basira a harkar waƙoƙi na Hausa tun daga ƙarni na 19 har zuwa ƙarni 20 da na 21. Waɗannan mata mawaƙa sun yi waƙoƙi a fannoni da dama. Maƙasudin wannan, shi ne bayyanar da sunayensu, domin su zama masu amfani ga manazarta kuma mu tabbatar da cewa lallai in ana batun ƙwarewa a maganar harshe to, mata a wannan fage ba baya ba, kama tun daga waƙoƙin addini da na Nishaɗantarwa. Daga ciki irin waɗannan mata akwai:

Mawaƙiya

Jigon Waƙoƙi

i.Burmani Choge

Sana’a/kishi/ilimi

ii.Ladi mai kutinga

Zuga/tarihi/salsala

iii.Uwaliya mai Amada

Soyayya/aljanna

iv.Nana Asma’u Ɗiyar Shehu Usman Ɗanfodiyo

Tuhidi/gargaɗi/wa’azi

v.Modibbo bilo

Wa’azi gargaɗi

vi.Hauwa Gwaram

Faɗakarwa/ra’ayin mata

Babu shakka, siyasa na da muhimmanci, sanadiyyar walwalar harshe da ake samu a ciki, matan da suka yi fice na amfani da sarrafa harshe sosai. Akwai mata da suka yi fice ana gwagwarmaya da su wajen taka muhimmiyar rawa domin ƙwato wa mata ‘yancinsu, waɗannan mata kan hau duro su yi jawabi don a san da zaman su da tsarinsu. Daga ciki sun haɗa da:

i.Hajiya Gambo Sawaba Zaria

ii.Asabe Reza Kano

iii.Hajiya Jummai ‘Yar rawar Banjo Zaria

iv.Hajiya Lela Dogon Yaro Kaduna

v.Naja’atu Muhammad Kano

Dangantakar Harshen Mata Tsofaffi da Mata Matasa

A sauƙin fahimta, da sanin makaman mata, dangane da batun magana tsakanin mata tsofaffi da mata matasa, akwai abubuwan lura da suka kamata a yi la’akari da su. Bahaushe kan ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Saboda haka a wannan fage an yi hira da tattaunawa da mata domin wannan takarda ta bayyana abin da ake so a isar sosai. Ga abin da nazari ya samar:

a)   Mata matasa akwai ƙuruciya, amma mata tsofaffi suna haɗawa da karin magana.

b)   Mata Matasa ba a raba mu da zagi. Misali: Uwarka, Ubanka. Amma da wuya ka ji tsofaffi suna zagi sai dai a ce: “ɗan danbolan uwa ka ci gidanku” da sauransu.

c)   Wurin magana ta yau da kullum, mata tsofaffi sukan ce kin yi kalace? ‘Yammata matasa kuwa sai su ce: “kin yi break fast?”

d)   A wajen zantukan hikima tsofaffi kan ce: “Ai hali ya ce je ki kar ki daɗe.” Ma’anar wannan zance duk in da ka ke halinka zai bika.

e)   Wani lokaci mu mata tsofaffi in mun yi magana sai a ce “ɗumin tsufa ce”.

f)   A wajen murya akwai bambanci tsakanin muryar mata tsofaffi da mata matasa. Muryar tsofaffi ba ta ƙara kamar ta mata matasa. Akwai su da tausasa murya da yi mata kwaskwarima domin ta yi zaƙi ta ratsa zukata. Misali: mata tsofaffi kan ce ni ban iya da kayan tambaɗar banza.

Babu shakka ana iya bugun ƙirji, idan aka yi la’akari da wannan bayanai na mata tsofaffi da mata matasa. Sai dai su kan su ‘yan mata sun tabbatar da cewa mata tsofaffi akwai su da amfani da karin magana da yin amfani da tsofaffin kalmomi irin na dauri, fiye da mata matasa. Sannan tsofaffi akwai su da amfani da tsara magana cikin azanci da hikima. Amma wajen amfani da sarrafa harshe kamar sara da saye da surki mata matasa sun fi zarra a nan, sanadiyyar karatun boko a zamanance.

Kammalawa

Daga ƙarshe wannan maƙalar ta cimma nasarar bayyana cancantar mata a ma’aunin sarrafa harshen Hausa, kamar yadda taken takardan ya bayyana. An fito da manufar takardar, sannan an fito da muhimman bayanai da suke tabbatar da keɓantuwar mata a wasu muhimman fage na hikimomin malam Bahaushe tare da nuna zantukan da suke da alaƙa ga matan Hausawa da kuma irin gudunmuwar mata wajen amfani da keɓantattun zantuka na mata da kuma kalmomin da mata ke amfani da su. Bugu da ƙari takardar ta bayyana muhimman abubuwan da ke tabbatar da ƙwarewar mata wajen sarrafa harshe da kuma irin abubuwan da ake dubawwa wajen tabbatar da cancantar zama ma’auni a wajen nazarin harshe. Sannan an fahimci cewa duk wani abu da maza ke amfani da su wajen sarrafa harshe mata ma ba a bar su baya ba. Mafi yawan lokuta kamar yadda aka gano a wannan bincike zaman gida ya bai wa mata damar taka gagarumin rawa wajen yin amfani da harshe da koyar da shi musamman ga yara. Sannan waɗansu al’amuran sarrafa harshe ya keɓanta ga mata su suka fi amfani da su.

Daga cikin abubuwa da wannan aiki ya gano ta fuskar ƙwarewa wajen sarrafa harshe shi ne ta hanyar amfani da harshe a cikin zamantakewar al’ummar Hausawa sakamakon harshe ginshiƙi ne na rayuwar Hausawa wajen magana. Makarantar farko na koyar magana ita ce mata, domin kamar yadda binciken ya gano nan ne ake koyar da yaro iya magana. Saboda haka, ilimin addini da na boko sai da harshe ake iya sarrafa shi. Sa’annan binciken ya gano yadda ake iya tantance harshe mace da namiji, wadda binciken ya danganta shi da irin kayayyakin da ake tanada su tabbatar har tsawon rayuwan, daga ciki akwai muhimman abubuawan da aka yi rikodin a faya-faye ko aka dauka a rediyo ko kuma litattafai da aka rubuta domin amfanin al’umma. Bugu da ƙari, binciken ya tabbatar da cewa duk abin da maza ke iya yi mata na yi wani lokaci har su fi mazan. Sannan kowani irin aiki da maza ke yi a yau mata na yi tun daga aikin ofis har zuwa karantarwa, harkan siyasa da saursansu. Dagane da amfani da harshe an yi ƙoƙarin nazartan wasu muhimman al’amura da suka shafi karin magana saye da sara an fito da su da ma’anar su da yadda mata suka fi ta’ammali da su. A ƙarshe an zayyana nau’in maganar mata tsofaffi da mata matasa a wajen sarrafa harshe. Ana fatan wannan takarda ta zama mai amfani ga manazarta da masana wajen yin bayanin abubuwa da ke tabbatar da mizanin ma’aunin sarrafa harshe a bakin mata. Haka kuma zai zama kundi na sarrafa harshen mata a ɗakunan karatu.

Manazarta

Abubakar, A. (2006). Matsayin nazarin harshen Hausa a yau, Algaita. The Journal of Current Research in Hausa StudiesƁol. 1 No. 12 – 15.

Adamu, F.L (2001). My wife’s tongue deliɓers more punishing blows than Muhammad Ali’s first bargaining power in Nigerian Hausa society. Chester Academy Press.

Amfani, H.A. (2011). Hausa language and Hausa people: Yesterday, today and tomorrow, One Day Symposium. Ahmadu Bello Uniɓersity.

Bilkisu, Y. (1999). Hausa Fulani women. The state of struggle. In Catherine Coles and Beɓerly Mark Hausa women in the 20th century. Wisconsin Press.

Bunza, M.A. (2013). Don me ake karatun Hausa? Harsunan Nigeria Ɓol. ƊƊIII.

Gusau, S. M. (1994). Dubar alkunya: nazarin ma’anarta da nasonta a waƙoƙin makaɗan baka. Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Hudson, R. A. (1996). Cambridge books in linguisticsSociolinguistics second edition. Cambridge Uniɓersity Press.

Laboɓ, W. (1982). The study of language use social conteɗt sociolinguists. Harmones Worth Penijuine 1972. Pride & Holmes.

Muhammad, Y.M. (2011) . Hausa a yau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press.

Rabi, G. (2010). Kunya adon matan HausawaƊunɗaye Journal of Hausa Studies Ɓol. 1 No. 3. 20 – 30.

Wardhaugh, R. (2010). An introduction to sociolonguistics, siɗ edition. Wiley - Black Publication.

Yakasai, A. S. (2009). Harshe a bakIn maza da mata, wariya ko bambanci. Himma Journal of Contemporary hausa StudiesƁol 1 No. 1.

Yakasai, A. S. (2007). Dangantakar harshe da al’umma: Nazarin halaye da ɗabi’un magana a al’ummar Hausawa. Maƙalar da aka gabatar a Taron ƙarawa Juna Sani. Sashen Harsunan Asiya da na Afirka. Jami’ar Koyan Harsunan Waje ta Beijing 06-06-2007.

Yakasai, A. S. (2012). Jagoran ilimin walwalar harshe. Garkuwa Media Serɓices.

 Yobe Journal

Post a Comment

0 Comments