Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin wanda ya yi istimna'i da rana ana azumi?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Mene ne hukuncin wanda ya yi istimna'i da rana ana azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, Istimná'i shi ne mutum ya yi wasa da al'aurarsa har ya fitar da maniyyi ba ta hanyar jimá'i ba. Yin hakan laifi ne babba, amma laifin yinsa a watan Ramadana yana ƙara girmama fiye da a sauran watanni.

An tambayi Allama Ibn Utsaimeen Rahimahullahu a game da wanda ya yi Istimná'i, shin kaffara ta wajaba a kansa? Sai Allama ya ba da amsa da cewa: "Idan mai azumi ya yi wasa da al'aurarsa (istimná'i) har ya fitar da maniyyi, to ya wajaba a kansa ya rama azumin wannan yini da ya yi istimná'i a ciki, amma babu kaffara a kansa, saboda kaffara ba ta wajaba sai idan jimá'i ne aka yi".

Duba Majmú'u Fataáwá na Ibn Uthaimeen 19/233.

Kuma wanda ya sami kansa a wannan mugun aikin, bai halasta a gare shi ya ci abinci ko abinsha a wannan yinin saboda an ce azuminsa ya karye ba, wajibi ne a kansa ya kiyaye alfarmar watan ta hanyar kamewa daga ci ko sha duk da karyewan azumin nasa. Sannan ya wajaba a gare shi ya yi nadama tare da kyakkyawar tuba zuwa ga Allah, saboda wannan babban zunubai da ya aikata na Istimná'i da kuma karya azumi, kuma ya yawaita kyawawan ayyuka, saboda kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments