Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin Azumin wanda ya yi mafarki da rana har Maniyyi ya fito masa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin Azumin wanda ya yi mafarki da rana har Maniyyi ya fito masa??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️                

                                             

Dangane da hukuncin Fitar Maniyyi ga wanda yake azumi mafi yawan Malamai cikinsu harda Mazhabobin nan guda huɗu wato:

1---Malikiyya

2---Shafi'iyya

3---Hanafiyya

4---Hanabila

Dukkansu suntafine a kan cewa fitar da Maniyyi da gangan ta hanyar da ba jima'i ba yana lalata azumi, danhaka idan Mai-Azumi ya yi Istimna'i, ko ya rungumi Matarsa, ko ya yi wasa da'ita, hartakai ga yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace, danhaka Malamai sukace dukkan Mutumin da yasan cewa Sha'awarsa tana da ƙarfin da indai zaiyi wasa da Matarsa Maniyyi zaifito masa to haramunne agareshi ya yi hakan da'ita, idan kuwa ya yi har Maniyyi yafita to wajibine sai yarama wannan azumin, amma idan yakasance Maniyyin yafitane ta hanyar mafarki kokuma tunani ko kallon Mace batare da ya yi wasa da'itaba, mafi yawan Malamai sukace azuminsa bai lalace ba saidai wajibine ya yi wankan janaba, amma Mazhabin MALIKIYYA sukace koda mafarki ya yi dolene sai yarama wannan azumin.

Danhaka Malamai sun yi Saɓani dangane da yanayin ramuwar azumin da Mutum zaiyi, Mafi yawan Malamai suntafine akancewa zai rama azumi guda ɗaya ne kawai batare da ya yi wata Kaffara ba, domin Nassin yin Kaffara yazone a kan wanda ya yi Jima'i da Matarsa da rana, Saidai Mazhabin MALIKIYYA suntafine akancewa idan Mutum ya yi Mafarki har yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace kuma dolene sai ya rama batare da kaffaraba, amma idan wasa ya yi da Mace ya rungumeta ko ya Shafata ko ya yi Istimna'i har yafitar da Maniyyi, to wajibine sai ya yi ramuwa tare da Kaffara, domin sun yi Ƙiyasine a kan hukuncin wanda ya yi Jima'i da Matarsa da gangan da rana.

Amma. Mazhabin ZAHIRIYYA suntafine a kan cewa wanda yafitar da Maniyyi da gangan ta dukkan wata hanyar da ba Jima'i ya yi da Matarsa ba, sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, domin babu wata Hujja afili Ƙarara daga cikin Al-Ƙur'ani ko Hadisi datace azuminsa ya lalace, to amma Saidai maganar Malaman da sukace azuminsa ya lalace tafi Ƙarfi.

Amma maganar da tafi inganci wacce mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da'ita shi ne, fitar Maniyyi ta hanyar mafarki baya karya azumi, domin Ɗan-Adam bashi da wani iko na ya'iya hana kansa yin mafarki alokacin da yake barci ba, hakanan magana mafi inganci fitar Maniyyi ta hanyar tunani ko kallo shima baya karya azumi, amma duk dahaka ba'ace Mutum yarika sanya irin wannan tunanin a cikin Zuciyarsa ba, amma fitar Maniyyi dagangan tahanyar wasa tsakanin Ma'aurata, ko tahanyar Istimna'i, wannan kam yana lalata azumi, kuma za'ayi ramuwane kaɗai batare da Kaffaraba, amma idan Mutum ya yi jima'i da Matarsa da gangan da rana, tofa koda baikawo Maniyyiba ramuwa da Kaffara sunhau kansa.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:

"المغني لإبن قدامة"

الشرح الممتع" (6/234)

"المجموع للنووي" (6/349)

 AMSAWA

 Mυѕтαρнα Uѕмαи

 08032531505

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments