𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamaalaikum. Mlm ina da tambaya Sallar shafa'i da
wutiri
Aka ce raka'ar farko suratul A'ala za a karanta ta biyu
suratul kafirun ta ƙarshe kuma suratul iklas Mlm
haka ne Kuma Mlm ni bana iya karanta suratul kafirun sai na kalli Alƙur'ani da suratul A'ala shin Mlm zan iya karanta
surorin danake da haddarsu akaina ko wa'inanne
Kuma wai da gaske Idan anfara ba a denawa ko wataran irin Idan m
utum ya ji ya gaji haka?𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Waalaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.
Alhamdulillahi Ala Ni'imatul Islam.
"Bayan haka: haƙiƙa Allah maɗaukakin sarki ya wajabta
bauta akanmu mu bayin sa shi kaɗai domin nuna godiyar mu a
bisa halitta da kuma fifikon da ya yi mana a kan sauran bayin sa"
"Ni a iya sanina gaskiya ban san inda aka ƙayyade cewa a sallar wutri ga wasu surori da aka keɓancesu ake karanta su a
cikinta ba, yawancin wannan kuma yana zuwa ne daga gurin masu ta'ammuli da
bid'ah"
"Tabbas a cikin sallolin nafilah akwai irin waɗanda suka zo a hadisai masu
yawa waɗanda suke nuni da cewa Manzon Allah sallallahu alaihi
wasallama yana karanta Surah kaza a cikin sallar nafila kaza, to amma kuma
hakan bawai yana nuna wajabci ba ne, yin hakan sunnah ne bawai farillah ba,
idan ka wajabtawa kanka, to lallai bawai musulunci ne ya wajabta maka ba"
"A cikin sunnah babu inda aka keɓance wata sallah ta nafilah
ko ta farillah cewa dole ga irin wata surar da za a karanta mata, sai dai wata-ƙila a sami cewa Annabi ya fi karanta sura kaza a cikin sallah
kaza da sura kaza"
"Sannan kuma shi Alƙur'ani duk inda ka karanta shi a
cikin sallah to alƙur'ani ka karanta, bawai sai
dole ka haddace shi ba ne sannan za ka iya bautawa Allah, mutum zai iya karanta
kowace Surah a cikin sallarsa, amma duk da hakan baya hana kuma mutum ya ƙara neman ilmin alƙur'ani, ma'ana ya dage da
haddar wasu surorin domin daɗa yalwata karatun sa ta
mabanbantan surori"
"Malamai suka ce babu laifi idan mutum bai iya
karanta alƙur'ani ba a haddace, zai iya
buɗewa ya kalla musamman idan sallar tasa ta kasance ta nafilah
ce, duba da hadisin Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda da take
umurtar bawan ta ya buɗe alƙur'ani ya karanta domin ya
jagorance su sallah da azumi"
"Hadisi ya zo daga Manzon Allah sallallahu alaihi
wasallama ya ce: mafi soyuwar aiyuka a gurin Allah maɗaukakin sarki, shi ne aikin
da bawa ya dauwama yana akansa yana aikata shi ko da kuwa ɗan kaɗan ne"
"Amma wannan baya hana kuma idan mutum ya yi
ibadar ya gaji wataran kuma sai ya ɗan taƙaita domin ya huta"
Wallahu A'aalmu.
Ya Allah ka yafe mana dukkanin laifukan mu, Ameen.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/F1YV6JhrD89EfJddPLvƘ32
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.