𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum waramatullah, inaso Asanar Dani yadda ake ciyarwa a
madadin azumi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam. Ciyarwa abune mai sauƙi, kamar yanda musulunchi gaba dayansa sauƙi ne.
Ga Wanda laruri yakamashi ba zai iya azumi ba, kuma azumin ya wajaba
akansa, To sai ya ciyar da marar ƙarfi
mutum ɗaya A madadin Azumi Ɗaya.
Na abinda yake ci madaidaici na
gidansa, ba tare da Tsanantawa ba, ba kuma ƙaranci, Amma lalle amfison kaciyar daga irin abinda kuke
ci, kaman yanda Aka tambayi Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya bada amsa, da
"kada ku ciyar da su ( marassa ƙarfi
) da abinda ku baku ci" kamar Yanda imam Ahmad ya futar da hadisin,
haithami ya ingantashi, Ibn kathi ya kafa hujja da shi cikin Tafsrin sa, ƙarƙashin
[267 baƙra ].
Son samu a ba shi a dafe, idan babu dafaffe, abashi da kayan dafi!
@Tsoho/Tsohuwan da basa iya azumi, suna iya chiyarwa ko su sa yayan su, su
ciyar musu, idan basuda hali.
@marar lafiyan da aka ɗebe Tsammanin Warkewa, Alhalin yana da
hankalinsa.
@mace mai ciki ko shayarwan da bazata iya ba, saboda Tsoron kanta da abinda
ke. tare da ita ( Ɗa
) seta chiyar.
Ibn kathir 1/320...
WALLAHU A'ALAM
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
5 Comments
ASSALAMU Alaikum mallam ya kishi mallam za mu iya bawa masu gadin gidahaka kokuwa sai farin.kuma azumin har na shekara uku zuwa hudu duk ciyarwan iri dayane kokuma akwai wani hukunci na daban
ReplyDeleteASSALAMU Alaikum mallam nace ya adadin kwanon awon da za abada abinci
ReplyDeleteThis comment has been removed by a blog administrator.
DeleteAbin da yake wajibi shi ne ka ciyar daidai kwatankwacin yadda mutum zai iya ci ya ƙoshi a wannan lokaci.
DeleteDomin samun ƙarin bayani kuna iya tura tambayoyinku ta lambobin da aka samar cikin hoton da ke sama.
ReplyDeletePost your comment or ask a question.