Citation: Abdullahi Haruna IMAM da Shamsuddeen ISMA’IL (2022). Bambanci Tsakanin Waƙoƙin Siyasa na Ƙarni Na 20 da na Ƙarni Na 21. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Ɓol. 10, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State Uniɓersity, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
BAMBANCI TSAKANIN WAƘOƘIN SIYASA NA ƘARNI NA 20 DA NA ƘARNI NA 21
Na
Shamsuddeen ISMA’IL
Abdllahi Haruna IMAM
Abstract
Hausa poems have been one of the major weapons
for stimulating politics in Northern Nigeria. These poems are termed as
political poems used for campaign. This paper is an attempt to compare the 20th and
21st centuries Hausa political poems where different poetic
features served as bedrock to the analysis. The paper is a complete library
research in which different literary works such the collection of poems and
recorded poems serve as our sources of data. The work is based on Birniwa
(1987)’s model of approach which shows that this class of Hausa poems have been
in used for political propaganda since 1956-1983. The paper reveals that the
two generations of poems (20th and 21st centuries)
are similar but slightly different in terms of their themes, structure, and
style and language proficiency.
Gabatarwa
Tun wajen ƙarni na sha bakwai (17)
Turawa suka fara zuwa ƙasashen Hausa da niyyar binciken ƙasa, da sanin kogunan da suka ratsa Afirka. Daga baya suka dinga
zuwa saboda sha’anin ciniki. A ƙarshe dai farkon ƙarni na ishirin, Turawan Faransa da na Ingila suka karɓe mulkin ƙasashen Hausa daga hannun sarakunan Hausawa. Su
waɗannan Turawa, sun canza tsarin mulkin waɗannan ƙasashe, da irin nasu tsarin mulkin. Ban da
tsarin mulki kuma, Turawa sun kawo wa Hausawa wata sabuwar hanyar karatu da
rubutu irin nasu. A hankali har Hausawa suka koyi yadda za su rubuta Hausa ba
baƙaƙen Turanci, wato rubutun boko. Haka kuma Turawa
sun kawo wa Hausawa wasu sababbin kayayyakin fasaha da kimiyya, kamar su jirgin
sama da jirgin ƙasa, da mota da basukur, da keken ɗinki da su wayar Magana (telephone). Duk waɗannan abubuwa sun yi tasiri wajen rubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin. Wani
abin da ya kawo canji wajen rubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin shi ne, yadda tunanin Bature
ya yi tasiri a kan Bahaushe. Kafin zuwan Turawa, duk sha’anin Bahaushe ya tafi
kan sha’anin addini ne. Yadda zai kiyaye addininsa a zamaninsa na duniya, da
kuma yadda zai samu tsira gobe ƙiyama. A wannan lokaci
Bahaushe bai da wani tunani a kan yadda zai kyautata rayuwar duniya, domin
bai ɗauki duniya wurin zaman jin daɗi ba. Shi a wurinsa, duniya wuri neman jin daɗin zaman lahira ne kawai. Wannan shi ya sa duk waƙoƙin da Bahaushe zai rubuta kafin zuwan Turawa,
zai rubuta su ne kan sha’anin da ya shafi addini. Jamhuriya ta huɗu wadda kusan ita ce ta fi ƙawatuwa da rubutatun waƙoƙin siyasa, kuma a daidai wannan lokaci ne ƙarni na ishirin da waƙoƙinsa suka zo ƙarshe, an samar da rubutattun waƙoƙi masu yawan gaske, wanda Allah ne kaɗai ya san adadinsu. A zangon farko na wannan jamhuriya wanda ya
gudana daga shekarar 1999-2003, jam’iyyun P.D.P da A.P.P su ne jam’iyyun da
suka yi fice a wannan ƙasa. A wannan zangon farko an samar da
rubutattun waƙoƙi ga waɗannan jam’iyyu na P.D.P da A.P.P.
Waƙoƙin Siyasar Ƙarni Na Ishirin (Ƙ.20)
Birniwa, (1987) ya bayyana yadda ake amfani da
waƙoƙi don yin farfagandar zaɓe da neman goyon bayan jama’a tun shekarar 1956-1983. An kuma raba
wannan kundi zuwa gida biyu, kashin farko ya ƙunshi nazarin waƙoƙin siyasar farko, waɗanda aka samar a shekarar 1940-1966, waɗannan waƙoƙin suna nuni ne a kan
ra’ayin riƙau ta fuskar addinin Musulunci daga jam’iyyar
N.P.C sai kuma wasu waƙoƙi masu ra’ayin kawo
sauyi bisa tafarkin addinin Musulunci daga jam’iyyar N.E.P.U. Sai kuma sashe na
biyu wanda ya ƙunshi yadda aka gina waƙoƙin zamanin siyasa ta biyu tun daga shekarar
1978-1983. Manazarcin ya bayyana yadda jam’iyyar N.P.N wadda ita ce ta gaji
jam’iyyar N.P.C ta canza bisa ra’ayinta na riƙau bisa ga sassauƙan ra’ayin addini ta fuskar siyasa. A ɓangaren jam’iyyar ceton al’umma kuma wato jam’iyyar P.R.P wadda
kuma ita ce ta gaji N.E.P.U tare da manufofinta, tana nan bisa aƙidar nan ta kawo sauyi ba tare da wani bayyanannen canji ba. A
jamhuriya ta farko jam’iyyun N.P.C da N.E.P.U su ne suka samu gindin zama a
wannan yanki, an kuma samu rubutattun waƙoƙi da marubuta suka yi na tallata jam’iyu ko aibanta abokan
adawarsu. Marubuta irin su Sa’du Zungur, Gambo Hawaja, Mudi Sipikin, Lawal
Maiturare, Aƙilu Aliyu da Yusufu Kantu da dai sauransu duk
sun bayar da gudummowa ta wannan hanya, misali: Gambo Hawaja da Aƙilu Aliyu duk sun yi rubutattun waƙoƙi na jam’iyyar N.E.P.U, wato jam’iyyar adawa, a lokacin, cikin waƙoƙin suke caccakar jam’iyyar N.P.C, ga abin da
Gambo Hawaja ke cewa a cikin baiti na goma da na goma sha ɗaya:
Albarkacin Manzonka zan yabi jam’iyya,
Mai son tunɓuke zaluman Nijeriya.
Ita jam’iyar N.E.P.U ta ɗau anniya,
Sai ta ga bayan zalumai mashaya giya.
Shi kuwa Aƙilu Aliyu ya aibata
jam’iyyar N.P.C a cikin waƙarsa baiti na biyu, inda yake cewa:
Kuzo talakawa in baku,
Abin da yake amfaninku,
Mazanku da mata taronku,
Ku zaɓi sawaba ce taku,
Ku yada zalama N.P.C.
A can gaba kuma, a baiti na goma sha ɗaya ya ƙara da cewa:
Mu karɓi nasihar nan tamu,
Mu zaɓi talakawa namu,
Waɗanda suke jin tausanmu,
Saboda suka kai kakarmu,
A wargaza mulkin N.P.C.
A jamhuriya ta biyu kuwa, jam’iyyar N.P.N da
P.R.P da G.N.P.P su ne jam’iyyun da suka yi tashe a wannan yanki, su ma waɗannan jam’iyyu sun samu marubuta waƙoƙi da suka rubuta waƙoƙi na tallatawa ko kuma na kushe wata jam’iyya, kamar yadda Isah
Bunguɗu yake aibata jam’iyyar N.P.N mai mulki a wancan
lokaci, a cikin waƙarsa da yake yi wa jam’iyyarsa ta P.R.P, ga
yadda yake nuna ƙiyayyarsa ga jam’iyar N.P.N a baiti na sha tara:
N.P.N ba ni sha’awarki,
Ba na sha’awar aƙidarki,
Ba na son komai na mulkinki,
Ban yarda a baki mulki ba.
Shi kuwa Malam Muhammadu Ɗunɗaye a waƙarsa mai taken “’yan santsi kun zama ƙaya” ya yabi jam’iyyar N.P.N, inda yake cewa:
Jama’a yau gara ku gane,
N.P.N alheri ne,
Don Alhaji Shehu mutum ne,
Kuma shi mai kyan asali ne,
Kuma N.P.N ba maita.
N.P.N goshi jirgi,
Ita ta wuce ai mata gigi,
Kada ma ka sake kai wargi,
N.P.N ba ta zagi,
Domin ta tsare girmanta.
Ita ma dai jamhuriya ta uku ko da ba ta yi tsawo
rai ba, jam’iyyun da suka yi zamani a wannan lokaci su ne jam’iyyar N.R.C da
S.D.P su ma an samu marubuta waƙoƙi da suka rubuta waƙoƙi a kan waɗannan jam’iyyu, sai dai
saboda taƙaitaccen lokaci, wannan tafiya ba a samu
fitattun waƙoƙi da yawa ba, domin waƙoƙin da za a iya samu akasari waƙoƙin baka ne, ba rubutattu ba amma duk da haka,
wani marubuci mai suna Garba Gashuwa ya samar da wata rubutacciyar waƙa da ta haɗe jam’iyyun biyu kamar yadda baitin amshin waƙar ya nuna:
Allah kiyaye jam’iyyu biyu da an kai bana,
Ya taimaki jama’armu ba zasu kure ba.
Bayan rugujewar wancan tsari a jamhuriya ta uku
sai kuma gwamnatin marigayi Janar Sani Abaca ta sake aza tubalin wani zango na
jamhuriya ta uku inda a wannan lokaci jam’iyyun U.N.C.P da D.P.N da C.N.C da
G.D.M da N.C.P.N suka kutso fagen, jam’iyyun U.N.C.P da D.P.N su ne suka yi
zarra, to a wannan karo ma an samar da rubutattun waƙoƙi ga waɗannan jam’iyyu, misali
jam’iyyar U.N.C.P wadda kusan za a iya cewa ita ce take da rinjaye an yi waƙoƙi domin tallata ta, kamar waƙar Malam Garba Gwandu inda yake bayyana manufofin jam’iyyar, ga
abin da yake cewa a wani baiti na waƙarsa:
U.N.C.P fatinmu na shirin ƙwarai ƙauyukka,
Birane su zama irin ƙwarai.
Abinci za shi lirwanta har sutura ƙwarai,
Mu zama har da zama lafiya to ji kai,
Zo yi musafaha kar ka yarda da ruɗuwa.
Shi kuwa Alhaji Aminu Ibrahim Ɗandago, shi ma ya waƙe jam’iyyar U.N.C.P inda
ya tabbatar da anniyarsa ta nema wa jam’iyyar magoya baya, ga abin da yake cewa
a wani baitin waƙar:
Ni jam’iyya mai Kwando,
Ranar zaɓe zan zaɓa,
Nai alƙawari ran zaɓe,
Kowa na gane shi a raɓe,
Zan masa ƙaimi yai zaɓe.
Ɗan’illela (2012)
Waƙoƙin Siyasa Na Ƙarni Na Ishirin Da Ɗaya (Ƙ.21)
Jamhuriya ta huɗu wadda kusan ita ce ta
fi ƙawatuwa da rubutatun waƙoƙin siyasa, kuma a daidai wannan lokaci ne ƙarni na ishirin da waƙoƙinsa suka zo ƙarshe, an samar da rubutattun waƙoƙi masu yawan gaske, wanda Allah ne kaɗai ya san adadinsu. A zangon farko na wannan jamhuriya wanda ya
gudana daga shekarar 1999-2003, jam’iyyun P.D.P da A.P.P su ne jam’iyyun da
suka yi fice a wannan ƙasa. A wannan zangon farko an samar da
rubutattun waƙoƙi ga waɗannan jam’iyyu na P.D.P da A.P.P.
Alhaji Ibarhim Aminu Ɗandago da Muhammadu Ɗanmusa na daga cikin
jerin waɗanda suka samar da fitattun waƙoƙin tallata jam’iyyar A.P.P a lokacin.
Alhaji Aminu Ɗandago shi ya samar da
sananniyar waƙar nan da ta mamaye ƙasar nan baki ɗaya, ta jam’iyyar A.P.P,
wadda ke da amshi kamar haka:
Ba ma shakka cikin ƙasa ita ce ja gaba,
A.P.P jam’iyyar mutanen Nijeriya.
Shi kuma Muhammadu Ɗanmusa ya samar da wata
waƙa mai taken:
A.P.P zan zaɓa,
Don ta kare hakkin talakawa.
Ta ɓangaren jam’iyyar P.D.P
kuwa, ita ma marubuta kamar irin su Haruna Aliyu Ningi ya rubuta wa jam’iyyarsa
ta P.D.P waƙoƙi guda biyu, sun yi matuƙar fice a wannan ƙasa musamman a lokacin
yaƙin neman zaɓe. Waƙar farko tana da amshi
kamar haka:
P.D.P jam’iyya ta,
Abar so a zukata,
Mutanen Nijeriya ku taso mu riƙe ta.
Da kuma waƙarsa mai amshi kamar haka:
P.D.P muke so ku zo, ga jam’iyya mu sa ta a
zuciya
Al’ummar Nijeriya.
Zango na uku na jamhuriya ta huɗu kuwa ya soma ne a shekarar 2007 ya kuma ƙare a shekarar 2011. Wannan ne ya samar da jam’iyyun masu yawa a
wannan ƙasa, kamar irin su A.N.P.P, P.D.P, D.P.P, C.P.C
da yake a wannan lokaci jam’iyun A.N.P.P da P.D.P suna da marubuta waƙoƙinsu da suke da su tun farko, marubuta waƙoƙin siyasa sun yo ca, gun waƙe sababbin jam’iyyu, kamar irin jam’iyyar C.P.C da D.P.P. Fitattu
daga ciki sun haɗa da Auwwal Gwammaja da S.Y. Rigacukum da
makamantansu.
Auwal Gwammaja ya samar da fitattu waƙoƙi biyu na jam’iyyar D.P.P waɗanda ke ƙunshe da jan hankalin jama’a da bayyana
manufofin jam’iya zuwa ga jama’a, waƙar farko tana da amshi
kamar haka:
Mu mun yi na’am da maraba,
Da saukar jam’iyyar nan,
D.P.P ta burge ni,
Yau ita ni zan zaɓa,
Don na yaba kyan halinta.
Sai kuma waƙa ta biyu mai amshi kamar haka:
Mu ba gaba muka zo ba,
Alheri mu muka kawo,
D.P.P alheri ce,
Kowar rasa ta a je mishi jaje.
Sai waƙar S.Y Rigacukum wadda ya yi wa jam’iyyarsa ta
C.P.C mai amshi kamar haka:
Mu mun koma jam’iyyar Buhari,
Mai alƙalamin da bai
rubita ƙarya,
C.P.C taimako ga kowa.
Waƙoƙin da aka samar na jam’iyyun siyasun wannan ƙarni na ishirin da ɗaya sun kasance da
ire-iren waɗannan fuskoki da aka ambata, ma’ana wasu daga
cikin rubutattun waƙoƙin an gina su ne da
manufar koɗawa da wasa jam’iyyu, yayin da wasu marubuta waƙoƙin suna yi wa wasu muhimman mutane ko kuma ‘yan
takarar jam’iyyu.
Su dai waɗannan waƙoƙin na koɗawa da kambama jam’iyyu
akan yi ƙoƙarin wasa jam’iyya tare
da fifita jam’iyya a kan sauran jam’iyyu. Su kuwa rubutattun waƙoƙin da ake yi wa wasu shuwagabanni ko ‘yan
takara, akan yi ƙoƙarin kamanta adalcinsu
da riƙon amanarsu da kwatanta gaskiyarsu, da kuma
siffanta su da kyawawan halaye da mutunci da dattaku tare da bayyana wa masu zaɓe alfanun da ke tattare da zaɓen waɗannan shugabanni.
Jigon Waƙoƙin Ƙarni Na 20 Da Na Ƙarni Na 21
Yahaya (2016), ya nuna jigo shi ne saƙo ko manufa ko bayani ko ruhin da waƙa ta ƙunsa wanda kuma shi ne abin da waƙar ke son isarwa ga mai
sauraro ko mai karatu ko mai nazari. A nan za a yi ƙoƙarin bayyana jigogin waƙoƙin ƙarni na ishirin (20) da
na ishirin da ɗaya (21).
Zuwan Turawan mulkin mallaka ya yi sanadiyyar
wasu daga cikin Hausawa suka fara tunani a kan sha’anin duniya. Irin wannan
tunani shi ya kawo wasu marubuta da yawa a ƙarni na ishirin, suka
rubuta waƙoƙi a kan wani jigo na
sha’anin duniya, kamar siyasa ko wasu baƙin abubuwa, kamar mota,
basukur da sauransu.
Wani marubucin waƙa da ya fara kawo canji
a cikin waƙoƙin ƙarni na ishirin, shi ne, Sarkin Zazzau Aliyu Ɗansidi, ƙasaitaccen malami ne, masani kuma mai aiki da
sani. Ya rubuta waƙoƙi da yawa kan sha’anin
addini, kamar waƙarsa ta Mu Sha Falala. Ya kuma rubuta wasu waƙoƙi kan sha’anin duniya, kamar waƙarsa ta Nazmu Amir Za-zak. An ce ita wannan waƙa ya rubuta ta ne a lokacin da hanyar jirgi ƙasa ya iso Kano. Domin murnar wanna abu, sai aka kira babban taron
dukkannin sarakunan Arewacin Nijeriya a Kano. Gwamna Janar Lugard shi ya
jagoranci wannan taro, to bayan gama wannan taro da Sarkin Zazzau ya koma gida
ya tsara wannan waƙa, wadda a cikin ta ya bayyana yadda ya zo Kano
daga Zariya da yawan sarakunan da suka zo taro, da abubuwan sha’awa da sarakuna
suka zo da su, da kuma abubuwan mamki da ya gani a Kano, da sunayen unguwannin
birnin Kano, da kuma labarin wata sukuwar dawaki da aka yi a taron da kuma waɗanda suka ci sukuwar. Ita wannan waƙa kusan duniya ce
tsantsa babu abin da ya haɗa jigonta da addini. Kusan kuma wannan waƙa ita ce farkon rubutacciyar waƙar da aka yi ba kan
sha’anin addini ba, tun bayan wucewar jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
Wani misali, wani mawaƙi da ya biyo bayan Sarkin Zazzau shi ne Alhaji Aliyu Namangi. Shi
kuwa wani makaho ne malami, taƙiyi, mutumen Zariya ya rubuta waƙoƙi da yawa kan sha’anin addini, musamman waƙarsa da fi fice a duniya ta Imfiraji mai juzu’i ɗaya zuwa tara. Ya rubuta wasu waƙoƙi guda biyu masu ɗauke da jigon duniya
wato, waƙar basukur da waƙar ƙazama. Gaba ɗaya dai, daga shigowar ƙarni na ishirin sai jigon waƙa ya fara canzawa, daga
waƙoƙi masu jigon addini tsagwaronsu, zuwa waƙoƙi masu jigon addini da duniya.
A farkon ƙarni na ishirin yawancin
waƙoƙin addini sun kasance ne, ko dai yabon waliyai
ko malamai, misalin waɗannan waƙoƙi su ne waƙoƙin Gangar Wa’azu da Waƙoƙin Bagauda ta Kano da waƙar Mu Sha Falala ta Sarkin Zazzau Aliyu Ɗansidi da sauransu. Waƙoƙin yabo a farkon ƙarni na ishirin su ne,
waƙar Imfiraji ta ɗaya da waƙar Tusamma Aibatul Fuƙara na Aliyu Namangi da
waƙar yabon Shehu Tijjani wadda Shehu Atiku Kano ya yi, da kuma wasu
waƙoƙi da yawa da aka yi don yabon Annabi Muhammadu
(S.A.W).
An samu wanzuwar rubutattun waƙoƙin siyasa a ƙasar nan tun farkon
samuwar jam’iyyun siyasa, wato tun daga jamhuriya ta farko har zuwa yau. Yin
amfani da waƙoƙin siyasa a wanan ƙasa na ɗaya daga cikin matakan da jam’iyyu ke ɗauka na tallata manufofinsu da kuma ‘yan takararsu zuwa ga jama’a
masu zaɓe domin neman goyon bayansu.
Su kuwa waƙoƙin ƙarni na 21 sun sha bamban da na ƙarni na 20 ta fuskar jigo. Manyan jigogin da suka yi fice a cikin
waƙoƙin wannan ƙarni na 21 su ne jigon
soyayya da yabon Annabi da kuma na siyasa, wannan ya samu ne sakamakon shigowar
finafinan Hausa inda aka samu mutane da yawa suka riƙa rubuta waƙa ana sawa a cikin fina-finai, domin ƙara masu armashi. Mawaƙa irin su Mudassir Ƙasim da Sadi Sidi Sharifai da Maryam A. Baba da Yakubu Muhammad da
Yusuf Ayagi sun bayar da gudummowa wajen samar da waƙoƙin fina-finan Hausa. Misali: Yakubu Muhammad ya
rubuta waƙa mai suna “Oh! Dizan-Dizan” a cikin wani fim
mai suna NADAMA inda shi da Rabi Mustafa ke rerawa, Ali Nuhu da Abida Muhammad
ke bibiyan waƙar (mamin) wato suke bin sautin faifan. Ga yanda
waƙar take:
Soyayya da shi nake,
Tun asali da ni yake,
Na kama ku kun fake,
Kin biya ta ƙarƙashin ƙasa kina sheɗana.
Zubi Da Tsarin Rubutattun Waƙoƙin Ƙarni Na Ishirin (Ƙ.20) Da Na Ƙarni Na Ishirin Da Ɗaya (Ƙ.21)
A nan za a yi ƙoƙarin kawo bambance-bambancen da ke tsakanin waƙoƙin ƙarni na ishirin (20) da
kuma ƙarni na ishirin da ɗaya (21) kamar haka:
Marubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin yawancin su malamai ne na addini
ko da sun yi boko za a samu sun yi karatun fiƙihu a gida. Misali irin
Sa’adu Zungur, mahardacin Alƙur’ani ne. Haka ma marubuci Malam Aƙilu Aliyu malami ne na addini da ajami yake rubuce-rubucen waƙoƙinsa da sauransu.
Marubuta waƙoƙin wannan ƙarni na ishirin da ɗaya suna amfani da kayan kiɗa baƙi, ko amshi, ko taɓi da rawa da karɓa kamar yadda Kabiru
kilasik ke yi, wanda ya saɓawa rubutacciyar waƙa, wanda marubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin ba su amfani da waɗannan kayan kiɗa da amshi a waƙa, sai ɗan abin da ba a rasa ba.
Marubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin da ɗaya suna zuwa wani ɗaki da ake rera waƙa (studio) suna rera waƙa daga su sai makaɗan sutudiyo da ‘yan amshi, su ba shi kiɗa, su daidaita masa waƙa da kiɗa, saɓanin marubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin, wanda tun daga jamhuriya ta
farko har zuwa ta biyu sai dai su rera waƙoƙinsu wurin yaƙin neman zaɓe ko wani dandali da
suke zama.
Mawaƙan ƙarni na ishirin da ɗaya kamar maroƙa suke, waƙa suke ba jam’iyya ba, sun fi mayar da hankali
wurin yi wa ‘yan takara waƙa, ko kuma idan ya nemi wani abu bai samu ba sai
ya koma wata jam’iyya, misali irin Aminu Ibrahim Ɗandago ya yiwa ɗantakar jam’iyyar DPP
Alhaji Abubakar Gari Malam na jihar Kebbi waƙa a lokaci guda kuma ya
yi wa Aliyu Magatarda Wamakko na jam’iyyar PDP waƙa a shekara ta 2007, saɓanin marubuta waƙoƙin ƙarni na ishirin ‘ya’yan jam’iyya ne masu aƙidarta. Misali kamar Shekara Sa’adu ko Muhammadu Giɗaɗo ko Lawan Maiturare ko Gambo Hawaja, jam’iyya
kawai suke yi wa waƙa ba yantakara ba.
Haka ma, mawaƙan ƙarni na 20 sai buƙatar yin waƙar ya taso suke tsara waƙa, su kuwa mawaƙan ƙarni na 21 ko ba a hanya
su yin waƙar ba za su tsara su rera domin kawai a san da
su ko don samun abin duniya
Ana samun wasu daga cikin marubuta waƙoƙin ƙarni na 21 sun zama
jemagu, kowa suna yi wa waƙa, da ɗan jam’iyyarsu da wanda
ba ɗan jam’iyyarsu ba, wanda ba a samun haka a cikin
mawaƙan ƙarni na 20.
Kwaɗayi da neman abin duniya
ya yi wa marubuta waƙoƙin ƙarni na 21 yawa, saɓanin marubuta waƙoƙin ƙarni na 20.
Marubuta waƙoƙin ƙarni na 21 sun mayar da waƙa sana’a kuma abin dogaro, saɓanin mawaƙan ƙarni na 20.
A ƙarni na 21 ana amfani da
salon barbaranyayawa. Sai ka ga mawaƙi ya rubuta waƙa kowane baiti yana ɗauke da layuka goma ko
ma fiye da haka.
A ƙarni na 21 aka samu
rubutattun waƙoƙi da salon karɓa-karɓa a cikin waƙa, kuma kusan a ce a
cikin kowane baitin waƙa, kamar yadda Kabiru Kilassic ke yi. Amma
a ƙarni na 20 mutum guda ke waƙarsa har ya ƙare.
Ana samun luguden nassi a cikin waƙoƙin ƙarni na 20, amma mafi
yawan waƙoƙin ƙarni na 21 ba a samun wani abu mai kama da haka.
Mawaƙan ƙarni na 20 ba su kiran sunayen mutane suna zagi, sai dai su yi
zambo da habaici, amma mawaƙan ƙarni na 21 suna kiran
sunan mutum ƙarara, kamar yadda Aminu Dumbulun ya yi a cikin
waƙarsa ta sai an canza.
Mawaƙan ƙarni na ishirin suna bin ƙa’idojin rubutacciyar waƙa, ta hanyar yi la’akari da fara waƙa da rufewa da marufi da
yawan layuka da da samar da jigo.
Mawaƙan ƙarni na ishirin da ɗaya ba yanboko ne zalla
ba, wasu daga cikinsu ma ko bokon ba su yi ba, fasaha ce kawai ta waƙa suke da ita wajen waƙa. Idan har sun yi
karatun addini to ba zai kai irin mawaƙan ƙarni na ishirin ba.
Mawaƙan ƙarni na ishirin da ɗaya ba su damu da buɗa waƙa da addu’a kamar mawaƙan ƙarni na ishirin ba.
Salon Sarrafa Harshe
Idan aka ce salo, ya ƙunshi abubuwa da ake so kowace waƙa ta same su. Daga ciki
akwai salon sarrafa harshe. Ga ta yadda waƙoƙin ƙarni na 20 da na ƙarni na 21 suka sha bamban.
Mawaƙan ƙarni na 20 sun naƙalci harsuna biyu ko ma fiye da hakan. Misali
yadda Sa’adu Zungur yake ɗaukar nassi na Alƙur’ani ko Hadisi ko Fiƙihu ya sarrafa shi cikin waƙa ba a cika samun haka
ba a cikin waƙoƙin ƙarni na 21 ba. Haka shi ma Malam Aƙilu Aliyu da Shekara
Sa’adu suke yi da sauransu.
Mawaƙan ƙarni na 20 ba su cika aron kalmomi da sarrafa su daga harshen
Larabci ba sai dai harshen Turanci
Ƙoƙarin zaƙulo tsofaffin kalmomi a
juya su cikin hikimar waƙa da fito da manufar harshe.
Su kuwa waƙoƙin ƙarni na 21 waƙoƙi ne da ake gudanar da su a wannan zamani wanda salon su ya sha
bamban da sauran rubutattun waƙoƙi ta fuskar aiwatarwa da
wannan ya faru ne sakamakon shigowar fina-finan Hausa
Kamanci Da Bambancin Waƙoƙin Ƙarni Na 20 Da Na 21
Waɗannan rukunin mawaƙa sun sha bamban ta wajen jigo da zubi da tsari da salo. Haka ma,
wuraren da suka yi kama da juna.
Sun yi kama ta wajen shirya waƙa don isar da saƙon jam’iyya ko ɗantakara.
Sun yi kama ta wajen ƙafiya. Misali a waƙar Malam Gambo Hawaja wanda mawaƙin siyasa ne na ƙarni na 20 da kuma waƙar Aminu Ibrahim Ɗandago mawaƙin siyasa na ƙarni na 21. A cikin waƙar Malam Gambo Hawaja “Waƙar NEPU Sawaba Maƙiya Turawa” ga misali a baitin farko na waƙar:
Ta’ala ka ban taimako kan mu,
Ka maishe mu kayin magautan mu,
Ka kawo sawaba ƙasashen mu
Ka sa talakawa su zaɓe mu
Ka maishe mu ‘ya’ya kamar kowa
A wannan baiti na waƙa da ya gabata Malam Gambo Hawaja ya samar mata da ƙafiya guda biyu, ƙafiya ta ciki da
kuma ƙafiya ta waje. Kowane baiti yana da ɗango biyar, ɗango huɗu na farko suke ɗauke da ƙafiyar ciki wanda ɗango na biyar ke ɗauke da ƙafiyar waje, ƙafiyar ciki a wannan baiti ita ce, Ma,
sai kuma ƙafiyar waje ita ce Wa, wannan ƙafiyar ta waje kowane baiti na waƙar tun daga farko
har ƙarewa da ita za a yi amfani, ita kuma ƙafiyar ciki takan canja daga baiti zuwa baiti. Sai misali a cikin
waƙar Aminu Ibrahim Ɗandago ta “Adon
gaskiya”:
Bismillahi Jalla gwani na,
Haliƙi mai dare mai rana,
Bani iko ka gyara shiri na,
In yi waƙa ga zakin fama.
Duk waɗannan misalai da aka
kawo sun yi kama ta fuska ƙafiya, kowace waƙa daga ciki tana ɗauke da ƙafiya ta ciki da ta waje.
Dukkanninsu da sigar waƙa suke gabatar da jigoginsu. Misali, waƙar Auwalu Isah Bunguɗu wanda mawaƙi ne na ƙarni na 20 a cikin waƙar da ya yi wa Malam Aminu Kano da kuma waƙar Aminu Ibrahin Ɗandago wanda ya rera waƙar “Adon Gaskiya” wadda ya yi wa ɗan takarar gwamnan jihar Sakkwato a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a shekara ta 2007. Duk waɗannan waƙoƙin jigonsu na
tallata ɗan takara ne, ba jam’iyya ba, ga misali daga
cikin waƙar Awwalu Isa Bunguɗu da ya yi wa Malam Aminu Kano:
Ni na bi Aminu Kano masoyi na,
Tawa siyasa nan na koyi
Ka Musulunci nan nake yi
Don haka bani biyar mashayi
Don ni ba zan sha giya ba.
Sannu aminu da fama
Ni dai yau murna nake ma
Yanzu duk ƙasa ta yaba ma
Dubi Imodu yana yaba ma
Bai san ƙoshin lafiya ba.
Sai misali na biyu daga cikin waƙar Aminu Ɗandago waƙar “Adon Gaskiya”:
Sarkin yamma albishirinka,
Sakkwatawa suna bayanka
Sun kasance suna ra’ayinka
Sun yada hauni sun riƙe dama.
A wani baiti kuma yana cewa:
Sakkwatawa ku bar tababa,
Ali wallahi shi ne a gaba,
Dole maƙiyinka sai ya tuba,
In ya ƙi ya je ya taka kunama.
Waɗannan waƙoƙi da aka ba da misalai da su, waƙoƙi ne da aka samar a lokuta mabambanta, amma kuma
duk sigar jigo ɗaya suke ɗauke da shi wato jigon
tallata ɗan takara.
Kammalawa
Wannan nazari ya yi dubi ne game da waƙoƙin ƙarni na 20 da jigoginsu
da ƙarni na 21 da jigoginsu, kuma wannan nazari ya
taɓo bayani akan waƙoƙin siyasa na ƙarni na 20 zuwa ƙarni na 21 tun daga jamhuriya ta farko har zuwa wannan jamhuriyar
da muke ciki, tare da misalai. Haka kuma a cikin wannan bincike an kawo
bambance-bambance da ke tsakanin waƙoƙin ƙarni na 20 da ƙarni na 21.
Manazarta
Ɗanillela, A. (2010), Rubtattun waƙoƙin siyasa: Nazari a kan jihohi Sakkwato da Kebbi da Jihar Zamfara.
[Kundin Digiri Na Biyu]. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Birniwa, H. A. (1987), Conserɓatism and dissent: A comparatiɓe study on N.P.C/N.P.N
And N.E.P.U/P.R.P., Hausa political ɓerse from circa
1946-1984. [Kundin Digiri Na Uku]. Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar
Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yahya, A. B.
(2016). Salo asirin waƙa. Guaranty Printers.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.