Citation: Prof. Balarabe Zulyadaini and Yusufu Suleiman Ph.D (2022). Dabarar Bayar Da Labari: Nuna Kawaicin Mawallafiya A Wasu Littattafan Ƙagaggun Labaran Hausa Na Balaraba Ramat Yakubu. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 10, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
DABARAR BAYAR DA LABARI:
NUNA KAWAICIN MAWALLAFIYA A WASU LITTATTAFAN ƘAGAGGUN LABARAN HAUSA NA BALARABA RAMAT YAKUBU
Na
Prof. Balarabe ZULYADAINI
Yusufu SULEIMAN Ph.D
Tsakure
A wannan binciken an yi ƙoƙarin fito da wata dabarar bayar da labari da
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ta yi amfani da ita, wajen nuna kawaici a cikin
littattafan Budurwar Zuciya da Alhaki Kuykuyo Ne da kuma Matar Uba Jaraba. A
cikin binciken an gano dalilan da suka saka aka sami kawaicin mawallafiyar a
cikin labaran waɗanda suka haɗa da: jaddada labari, da rage nisa tsakanin mai karatu da
mawallafiya, da kuma ƙyale mai karatu ya
zantar da hukunci da kansa, dangane da wasu maganganu da aka fara, amma ba
a ƙarasa su ba, a cikin labari.
Gabatarwa
Yawancin marubuta ƙagaggun labaran Hausa akan same su da nuna kawaici a lokacin da
suke rubuta ƙagaggun labarai, musamman waɗanda suke rubutu cikin harshen Hausa. Wannan ba ya rasa nasaba da
yadda al’adun Bahaushe na jin kunya da kawaici suka tasiri a cikin rayuwarsa.
Kowa ya san Bahaushen mutum wajen kawaici, musamman domin ya kare mutuncinsa da
al’ummarsa. Shi kawaici yakan yi wa mai yin sa rana, domin mai yin sa akan ji
kunyarsa a kan abubuwa da yawa. Idan ma ba domin jin kunya ba, ai yakan taimaka
wajen taƙaita aukuwar fitintinu a tsakanin al’umma.
Ma’anar Kawaici
Kawaici kalma ce da ake amfani da ita domin a
bayyana kaucewa daga barin wani abu bisa wasu dalilai. An bayyana ma’anar
kawaici ta hanyoyi guda biyu kamar yadda aka nuna a Ƙamusun Hausa cewa, “(i) Alkunya ko kau-da-kai da kuma (ii) haƙuri ko shiru-shiru,” (CNHN, 2006, sh. 241).
Shi kuma Mukhtar, (2004, sh. 53) ya bayyana
ma’anar kawaicin mawallafi da cewa:
“Abin da ake nufi da kawaicin mawallafi shi ne,
a cikin labari inda shi mawallafin yakan yi shiru da zance sannan ya bar mai
karatu tare da wani tauraro wanda zai faɗi labarin kai tsaye, a
kan abin da ya shafi shi tauraro ɗin. A wani lokacin kuma
kawaicin mawallafi yakan bayyana idan ya yi shiru da wani zance a cikin labarin
ya ƙi faɗa ko ya ƙi ƙarasawa, ko ya ƙi fara labarin da wannan zancen, domin dai kawai ya bar mai karatu
ya cikasa da kansa.”
Daga waɗannan ma’anoni guda
biyu, za a iya cewa a ma’ana ta adabi, kalmar kawaici na nufin kawar da kai
daga barin wani zance ko al’amari saboda wasu daliliai. Wannan ya nuna cewa
lallai a cikin ƙagaggen labari ana samun yadda mawallafi ke
barin wani zance domin ya nuna kawaicinsa. Hausawa sukan ce “ruwa ba ya tsami
banza.” Wato a duk lokacin da aka sami kawaicin mawallafi ba a rasa dalili.
Wannan shi ne abin da za a duba nan gaba, sannan a fito da wasu misalai na
yadda mawallafiyar littattafan ta nuna kawaicinta.
Dalilan Da Kan Sa A Sami Kawaicin Mawallafa
Kamar yadda aka bayyana a sama, lallai
mawallafin ƙagaggen labari yakan nuna kawaici a cikin
labari. Wannan ya nuna cewa ita ma wannan mawallafiyar (Balaraba Ramat Yakubu),
ba a bar ta a baya ba wajen nuna irin wannan kawaici. Haka zalika takan nuna
kawaicin ne saboda wasu dalilai na aiki da dabarun bayar da labari kamar yadda
yake a cikin bayanin da ke biye.
Domin Jaddada Labari
Kalmar
jaddada na nufin “Ƙarfafa abu, musamman magana,” (C.N.H.N, 2006,
sh. 210). A cikin aikin bayar da labari, wasu mawallafan kan nuna kawaici domin
jaddada labari. Wannan yakan faru ne a lokacin da mawallafi ya kauce wa bayar
da labari na kai tsaye daga bakinsa. Wato yakan ƙyale ɗaya daga cikin taurarin ne ya bayar da labarinsa
da kansa domin ya sami jaddada dangane da labarin, (Mukhtar, 2004, sh.53).
A cikin
littafin Budurwar Zuciya, an sami kawaicin mawallafiyar domin a
nuna jaddadawa game da labarin. Wato a lokacin da Alhaji Usman ya kai matansa
unguwar Kurnar Asabe, inda ya gina sabon gida, sannan ya ce Kyauta ta ɗauki gini mai ɗakuna biyu da falo a
tsakiya. Ita kuma Asama’u aka bar mata ɗaki ɗaya da falo kawai. Domin a nuna jaddadawa a cikin labarin, sai
mawallafiyar ta miƙa wa ɗaya daga cikin taurarin,
wato Asama’u, ragamar bayar da labarin, inda take cewa:
“Malam ni ba na son wannan ɗakin. Yaya ni mai ‘ya’ya biyar za ka ba ni ɗaki ɗaya da falo, ita mai ‘ya’ya uku za ka ba
ta ɗaki biyu har da falo da banɗaki. Wato ni ba mace ba ce, ko kuwa ta fi ni ne? In haka ne, to ni
ka bar ni a wannan gidan, ita ka tare da ita a sabon gidan.” (Yakubu, 1987, sh.
5).
A nan an
sami jaddadawa dangane da labarin domin Asama’u ce da bakinta take bayyana
matsayarta game da rabon ɗakunan da Alhaji Usman ya yi. To a nan mai
karatu ya ji daga bakin tauraruwar cikin labarin, kuma wadda abin ya shafa kai
tsaye. Idan da a ce mawallafiyar ce ta ba da labarin abin day a faru tsakanin
Alhaji Usman da Asama’u, da ba a sami jaddadawar da ake tsammani ba.
Idan aka
duba cikin littafin Alhaki Kuykuyo Ne mawallafiyar ta nuna
kawaici domin samun jaddadawa a cikin labarin. An sami haka ne a lokacin da ake
rikici tsakanin Rabi da kishiyarta Delu da kuma mijinsu Alhaji Abdu. A lokacin
da mawallafiyar take bayar da labarin, sai kuma ta saki labarin a hannun
taurarin domin a sami jaddadawa game da labarin, inda Rabi take cewa:
“Ni na wuce banza a banza.” Ta miƙe a tsaye ta ci gaba da cewa, “’Yar iska ragowar ‘yan gwangwani.
Kin samu ya rufa miki asiri, ya auro ki. Shegiya komaɗaɗɗiyar wofi. Ai shi ne ya ɗaure miki gindi, don haka kike ɗaukar mutane banza. To
na gaji wallahi. Idan kika ƙara yi mini wata magana,
ubanki za ki ci a gidan nan.” (Yakubu, 1990, sh. 34).
A nan ma
mai karatu ya ji daga bakin taurauwar da abin ya shafa kai tsaye ne, ba daga
bakin mawallafiyar ba. Wannan ya nuna cewa lallai mawallafiyar ta nuna kawaici
a cikin labarin domin a sami jaddadawa dangane da labarin. Ita kuka Rabi da
abin ya shafa kai tsaye, ta ba wa maikaratu labarin kanta da kanta yadda ta
nuna cewa ita ba banza ce ba a gidan Alhaji Abdu.
Idan kuma
aka duba labarin cikin littafin Matar Uba Jaraba, za a sake samun
yadda mawallafiyar ta nuna kawaici a cikin labarin domin a sami irin wannan
jaddadawa da ake magana a kanta. A lokacin da aka dawo da Daso daga asibiti,
bayan likita ya tabbatar musu da cewa ciwon Daso ba na asibitinsu ba ne. Ana riƙe da Daso, tana tafiya, tana surutai har ta yi tuntuɓe da mesar ban ruwan filawa. Daga nan sai ta yi tangal-tangal za
ta faɗi, sai Ladidi ta yi sauri ta kama ta, ita kuma
sai ta ce:
“Kada ki sake riƙe ni, kin ƙwace mini fada a gurin mijina sai na rama…. zan koma gurin malam….
Hussaini ɗin ma sai na saka shi uwa duniya, kamar yadda
na ɓatar da Hassan ɗin naku…. Shi ma sai na ɓatar da shi.” (Yakubu,
2006, sh. 123).
Idan aka
lura a nan za a fahimci cewa mawallafiyar ta yi kawaici yayin da ta bar
tauraruwar take bayyana kanta da kanta. Daso ce ke bayyana wa Sa’idu da Ladidi
irin abubuwan da ta aikata da kanta. Kasancewar bayanan sun fito daga bakin
wadda abin ya shafa kai tsaye, sai aka sami irin jaddadawar da ake tsammani. Da
mawallafiyar ba ta saki ragamar bayar da labarin a hannun tauraruwar ba, ai ka
ga da jaddadawar ba ta samu kammar yadda ya kamata ba. Wato a nan ta bayyana
abubuwan da suka faru da kuma irin hanyoyin da ta bi har aka sami aukuwar wasu
munanan abubuwa kamar mutuwar Ummi da yadda Hassan ya shiga uwa duniya. Saboda
haka a nan mawallafiyar ta bar mai karatu ya ji daga bakin wadda abin ya shafa.
Rage Nisa Tsakanin Mai Karatu Da Mawallafiya
A cikin harkar karanta ƙagaggen labari akan sami yadda mai karatu ke tarar da mawallafi ya
kauce daga aikin bayar da labarin. Shi mawallafin yakan yi haka ne domin ya
rage nisan da ke tsakaninsa da mai karatu. Don haka a nan sai shi mawallafin ya
jawo mai bayar da labari daga cikin fage ya haɗa shi da mai karatu. Shi
kansa tauraron da ke bayar da labarin, kan sami rakiyar mawallafin. Abin lura a
nan shi ne, wani lokaci idan mai karatu na jin labari daga bakin mai bayar da
labari daga cikin fage, sai mawallafi ya sako maganarsa domin yi wa mai ba da
labari daga cikin fage rakiya, (Mukhtar, 2004, sh. 54-56).
A wasu
lokutan mawallafiyarwaɗannan littattafan ƙagaggun labaran Hausa da ake magana a kansu, kan koma gefe ɗaya, ta bar mai karatu tare da mai bayar da labari daga cikin
fage. Ba shakka takan yi haka ne domin ta rage irin nisan da ke tsakaninta da
mai karatun. Akwai wasu misalai daga littattafan Budurwar Zuciya da Alhaki
Kuykuyo Neda Matar Uba Jaraba na yadda mawallafiyar ta
sakar wa mai ba da labari daga cikin fage. A cikin littafin Budurwar
Zuciya an sami misali kamar haka:
“Sai Alhaji ya ce a’a kada ya tafi. Yana son ya
yi shawara da shi. Shi ke nan ya sake zama. Alhaji ya ce da shi, “Yanzu yaya ka
ga zan yi da yaran nan? Abin nasu fa ya yi yawa. Har ma ni na rasa abin da zan
ce.” (Yakubu, 1987, sh. 31).
Idan kuma
aka duba cikin littafi Alhaki Kuykuyo Ne akwai wani misalin
kamar haka:
“An fi minti goma sha biyar kafin Alhaji Abdu ya
fito wurin masu sallama da shi. Ya fita kuwa a murtuke, fuskarsa a ɗaure kamar sun zo roƙon gafara a gunsa. Suka
dai kanne, suka rabu da shi. Bayan sun gama gaisawa, sai Alhaji Bello yace da
Alhaji Abdu, “Ɗazu ne Malam Shehu ya je gidana, ya gaya mani
wata maganar da ban ji daɗinta ba. Don a kan faɗan mata, ai bai yi daidai a yi saki ba.”(Yakubu, 1990, sh. 38).
Haka
zalika idan aka sake duba labarin cikin littafin Matar Uba Jaraba an
sake kawo wani misali na yadda mawallafiyar ta saki ragamar ba da labarin a
hannun wani tauraro domin a rage nisan da ke tsakaninta da mai karatu kamar
haka:
“Nan da nan malaman nan suka sami gangara a
gurinta yayin da jarinta ya fara yin baya. Sai ta gaya musu, sai su ce, “Ai
Ladidi ce take yi miki sammu, ai ƙara dagewa za mu
yi.”(Yakubu,2006, sh. 52).
Idan aka duba waɗannan misalai
daban-daban guda uku, za a gane cewa mawallafiyar ceke yi wa taurari rakiya a
cikin labaran. Daga nan kuma sai ta saki ragamar bayar da labaran a hannun
taurarin. Wannan ya nuna cewa a lokacin da take yi wa taurao rakiya, tana rage
irin nisan da ke tsakaninta da mai karatu ne. Wato tana nuna wa mai karatu cewa
tana nan kusa da shi, ba ta yi nisa ba.
Daga waɗannan misalai za a gane
cewa mai bayar da labari daga bayan fage kan yi shiru a wani lokaci, sannan
ya ƙyale tauraro ya yi magana da bakinsa domin ya
kusantar da shi ga mai karatu. Saboda haka a nan akan bar mai karatu ya ji
kalaman daga bakin shi tauraron kai tsaye ba tare da wani ya shiga tsakani ba.
Ƙyale Mai Karatu Domin Zantar Da Hukunci Da Kansa
Wani lokaci a cikin ƙagaggen labari akan sami ra’ayin mawallafi da na mai ba da labari
ya zama iri ɗaya. Idan haka ta kasance, za a iya duba dangane
da sirrin sadarwa wanda ke tsakanin mawallafi da mai karatu. Wannan ya nuna
cewa irin wannan sadarwa kan faru ne ta bayan fage, wanda shi mai ba da labari
daga cikin fage bai san abin da ke akwai ba, tsakanin mai karatu da mawallafi.
Irin wannan ta fi faruwa musamman idan an bar mai karatu da wani tarƙoƙo a labarin kuma ana buƙatar ya warware abin da kansa. Haka kuma zai iya kasancewa ba tare
da mawallafi ya faɗi ra’ayin da bakinsa ba. (Mukhtar, 2004, sh.
56).
Idan aka
duba za a ga cewa ƙyale mai karatu ya kwance ƙullin labari da kansa zai taimaka wajen bayyana ra’ayinsa game da
labarin da kuma ra’ayinsa game da mawallafin shi kansa. An sami irin wannan
kawaici na mawallafiyar a labarin cikin littafin Budurwar Zuciya, a
lokacin da Ummi ta je Kantin Kwari domin yin magana da saurayinta da na ƙawarta Hadiza, wato Alhaji Ahmed da Alhaji Ahmadu. A nan ne Ummi
ke bayyana saƙo ga wani mutum inda take cewa: “To, don Allah
in sun zo, ka ce da su, Ummi ta yi musu waya, kuma ta ce….” (Yakubu, 1987, sh.
58).
A nan an
bar mai karatu ya yi tunanin sauran zancen da ita Ummi ba ta kawo ba. Wannan ya nuna cewa lallai akwai wani tarƙoƙo da ake so mai karatu ya warware da kansa. To,
ai ka ga a nan rashin ƙarasa maganar yana nufin cewa an bar mai karatu
ya yi ƙiyasi da kansa domin ya kawo cikon zancen da ya
rage.
Idan kuma
aka duba cikin littafin Alhaki Kuykuyo Ne an sami irin wannan
kawaici na mawallafiyar domin mai karatu ya yi hukunci da kansa dangane da
zancen Alhaji Abdu na ƙwace Ladidi daga hannun Rabi domin ya ba wa
Delu, inda ya fara da cewa: “Inna kin ga ita tana zaune babu kowa a gabanta,
kuma a gaskiya in kin lura, za ki ga cewar, Ladidi wahala take sha a wurin….”
(Yakubu, 1990, sh. 31).
Wannan ya
nuna cewa akwai sauran zance, don haka ana buƙatar mai karatu ya
yi hukunci da kansa wajen fito da ra’ayinsa game abin da ya rage da ba a faɗa ba. Hukuncin da mai karatu ya yanke game da sauran zancen, shi
ne zai kasance ra’ayinsa dangane da labarin. Wannan wata dabara ce ta bayar da
labari domin a nuna yadda mawallafiyar ta yi kawaici a cikin labarin.
Har ila
yau an sake samun kawaicin mawallafiya domin ƙyale mai karatu ya yi hukunci da kansa game da zancen da aka fara
amma ba a ƙarasa ba. A nan akwai Bilkisu ‘yar Alhaji Abdu,
lokacin da take bayyana wa mahaifiyarta Rabi dangane da haɗuwar da ta yi da mahaifinta Alhaji Abdu, inda take cewa: “Wallahi
ya gan ni. Abin da sai da muka haɗa ido da shi san….”
(Yakubu, 1990, sh. 90).
A cikin
wannan zance an rage wani ɓangare, don haka ana buƙatar mai karatu ya kawo abin da yake jin cewa shi ne ya rage. A
nan ma an yi kawaicin ne domin a ba wa mai karatu dammar yanke hukunci da
kansa, ya fito da ra’ayinsa dangane da labarin.
Wasu
misalan shafukan da aka sami kawaicin mawallafiya don ƙyale mai karatu ya yi hukunci da kansa a cikin littafin Alhaki
Kuykuyo Ne sun haɗa da:
“Ki yi haƙuri Hajiya, don na ga
dare ya yi ne a lokacin shi….” Shf na 66
“Ke fa ba ki da kunya. Ki dake ta, kuma
ki ce za ki yi wa mutane surutun banza me kike nufi ne? Ko….” Shf na 130
“Ba sai ka rama mata ba, da ita ‘yar mutane, ni
‘yar jakai, da ma ai kai ka ɗaure….” Shf na 130
“Alhaji Abdu ai sai haƙuri. Rumfarka kam, duk wannan layin ta ƙone. Wurin ma ba a iya isa, domin….” Shf na 140
“Delu, Delu ai na tsiyace. Delu rumfata da kayan
ciki da kuma kuɗina wajen naira dubu sittin duk sun ƙone, motar tawa ita ma an sace. Yanda nake ɗin nan shi ken an Delu na….” Shf na 144
“Allahu Akbar in ji mai kiran sallah. Yau ni kam
ai ban san abin da zan….” Shf na 149
“Ai Baba tun da nake aure ban taɓa samun matar arziki irin Saudatu ba, tun da ta zo nan gidan ban
taɓa yi mata kasshedi sau biyu ba, duk abin da na
ce ba na so to shi ke nan ta….” Shf na 151
“Ai madalla ma Baba, Allah ya ƙara masa. Wallahi ni ba zan je asibiti don na gan shi….” Shf na
152
“Saude ce ta ce a kawo mani wannan kayan har
da….” Shf na 156
“To tsaya mana ki ji ai maganar ba ta haka ba
ce. Rabi ki tsaya….” Shf na 160
“Ka san yanzu likita ya zo ya ce ka daina ɓata ranka. Masu irin wannan ciwon ba a so su riƙa yawan….” Shf na 167
“Kome ya same ni ma, ai alhakinku ne. Alhaki
kwikwiyo ne….” Shf na 167
“Yanzu ba ga shi ku ɗin ne a wurina ba. Naka ai komi lalacewarsa, shi ne naka. Don
Allah don Annabi ku yafe mani. Ko da mutuwa zan yin a sami sauƙin wata azabar. Don Allah ku yafe….” Shf na 167
Dukkan waɗannan misalan an tsakuro su ne daga shafuka daban-daban domin a
nuna cewa akwai su da dama a cikin labarin. Kowane daga cikinsu idan an duba,
za a ga cewa yana buƙatar mai karatu ya yi hukunci wajen kawo cikon
zancen da ba a ƙarasa ba.
An sake
samun irin wannan kawaici na mawallafiyar a cikin littafin Matar Uba
Jarabadomin a ƙyale mai karatu ya yi hukunci da kansa. Wannan
ya faru ne a lokacin da Alhaji Sani yake tunanin yadda zai yi da yaron da ya
tsinta, wato Hassan, inda yake cewa:
“To, wannan yaron yaya zan yi da shi? Ina zan
kai shi? Duk inda ma na kai shi, cewa za a yi sato shi na yi. Tun da Kurmi za
ni, sai kawai na tafi da shi tun da ba ya iya tuna komai, sai na canza masa
suna. Tun da ni Allah bai ba ni haihuwa ba sai in riƙe shi kamar ni na haife shi, kuma….” (Yakubu, 2006, sh. 73).
Alhaji Sani ya fara bayanin yadda zai yi da
yaron da ya tsinta, domin yana tunanin cewa duk inda ya kai shi za a gane cewa
ba ɗansa ne ba. Bayan yanke shawarar tafiya Kurmi da
shi kuma ya riƙe shi a matsayin ɗansa, sai kuma ya yanke sauran zancen. A nan ana buƙatar mai karatu ya yi tunanin sauran zancen da Alhaji bai ƙarasa ba. To, ai ka ga a nan ma an bar shi mai karatun da wani tarƙoƙon da ake so ya warware da kansa.
Har ila yau a cikin littafinMatar Uba Jaraba,
an sake samun irin wannan kawaici na mawallafiyar domin ta ƙyale mai karatu ya yi hukunci da kansa, a lokacin da Barmo ya raka
Aminu Fanshekara, kumayake cewa:
“Ai ina da wata matsala ce, don Alhaji nawa yana
asibiti tun jiya, to mun zo nan garinsu Fanshekara ni da Aminu, don mu gaya
musu, shi kuma Aminu ya yi nan. Wai ya gane makarantar, shi ne ya bar ni a nan
a tsaye ina….” (Yakubu, 2006, sh. 145).
Wani lokaci akan sami kawaicin da ake yi wanda
mai karatu ba zai sha wahalar yanke hukunci a kansa ba. Idan aka duba bayanin
da Barmo ya yi, sannan kuma ya yanke sauran zancen da bai ƙarasa ba, za a gane yana so ne ya bayyana cewa yana jiran Aminu.
Saboda haka ashe ana iya samun kawaici mai sauƙin yanke hukunci.
Akwai
misalai da dama a cikin labarin da ke nuna cewa akwai kawaicin da mawallafiya
ta yi domin ta ƙyale mai karatu ya yi hukunci da kansa waɗanda suka haɗa da:
“Wallahi Abba na je Fanshekara neman dangin
uwata domin….” (Yakubu, 2006, sh. 156).
“Ranka ya daɗe, a gaskiya dai to….”
Shf na 39
“Ni dai na gaya muku rance-rancen nan naku ya yi
yawa don….” Shf na 101
“In na je gida zan gaya wa Ummi cewar an ga wani
mai kama….” Shf na 106
“Ni ma zan je na gan shi da safe, ni ai zan gane
shi in….” Shf na 110
“Wallahi Abba na je Fanshekara neman sanin
dangin uwata domin….” Shf na 156
“Aminu, ka je neman dangin…. Barmo kai ka ba shi
wannan shawarar? Aminu ba na gaya….” Shf na 156
“Aminu ni kake gaya wa haka? Barmo dubi Aminu.
Barmo….” Shf na 156
“Kai ne wannan yaron Aminu. Kai ba ɗana ba ne, ba ni na haife ka ba. Tsintarka na yi. Tsoron rabuwa da
kai ne yake sawa kullum in ka yi maganar dangin uwarka, sai hankalina ya tashi,
ba na son kowa ya san cewar ba ni na haife ka ba. Aminu ba na son na rabu da
kai…. Aminu….” Shf na 166.
Idan aka duba cikin littatafan
da aka nazarta, za a ga cewa lallai mawallafiyar ta yi amfani da wannan dabara
ce domin ta fito da maganganu mabambanta manufa. Haka kuma kawaicin na
mawallafiyar zai ba da dama wa mai nazari ya fahimci cewa mawallafa sukan yi
amfani da kawaici domin kawar da kansu daga wasu abubuwan da ke faruwa a cikin
labarai kamar yadda aka gani. Dukkan maganganun da aka kawo a matsayin misalai
an kawo su ne domin a nuna cewa akan yanke zantuka domin a kawar da kai, ko jin
kunya ko kuma domin a nuna tsoro. Nuna tsoro ba laifi ba ne domin kowane ɗan’adam an halicce shi da
tsoro tare da shi.
Kammalawa
Daga waɗannan misalai da aka gani,
za a fahimci cewa mawallafiyar ta yi kawaicin ne domin ta ba wa mai karatu
damar yanke hukunci a kan waɗannan zantuka ko wani tarƙoƙon da ba a warware shi
ba. Saboda haka wannan ma
wata dabara ce da mawallafa ke amfani da ita wajen bayar da labari domin isar
da saƙo ga mai karatu. An gano cewa mawallafiyar
littattafan Budurwar Zuciya da Alhaki Kuykuyo Ne da Matar
Uba Jaraba, ta yi amfani da wannan dabara ta kawaici
domin barin mai karatu ya yi hukunci da kansa dangane da duk wata magana da aka
fara, sannan ba a ƙarasa ba aka katse ta. Wannan zai ba shi damar faɗaɗa da kuma zurfafa tunaninsa
dangane da al’amuran da suka faru a cikin labaran da aka nazarta.
Manazarta
C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.
Mukhtar, I. (1987). Bitar nazarce - nazarcen
salo a cikin rubutu. Taron Ƙara wa Juna Sani, Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Mukhtar, I. (1990). A stylistic study of
Sulaiman Ibrahim Katsina’s Hausa, Noɓels. [Ph.D. Thesis]. Department
of Nigerian Laguages, Bayero Uniɓersity, Kano.
Mukhtar, I. (1993). Yanayin ƙagaggun labarai na Hausa. Nazari A Kan Harshe Da Adabi Da
Al’adu. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Mukhtar, I. (2001). Al’amuran dubawa cikin
fasalin nazarin ƙagaggen littafi. Algaita Journal of
Current Research in Hausa Studies. Ɓol. 1No. 1
Mukhtar, I. (2004). Jagoran nazarin ƙagaggun labarai (Tsari na biyu). Benchmark Publishers
Mukhtar, I. (2010). Introduction to
stylistic theories, practice, and criticisms. Country side Publishers.
Suleiman, Y. (2005). Nazarin Dabarun Bayar Da
Labari A Littattafan Dare Ɗaya Da Budurwar Zuciya. [Kundin digiri na
biyu],.Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Suleiman, Y. (2019). Dabarun Bayar Da Labarai A
Wasu Littatafan Balaraba Ramat Yakubu. [Ph.D Thesis]. Depertment of Nigerian
Languages. Usmanu Ɗanfodiyo Uniɓersity, Sokoto.
Yakubu, B. R. (1987). Budurwar zuciya,
Gaskiya Corporation.
Yakubu, B. R. (1990). Alhaki kwikwiyo
ne, Gaskiya Corporation.
Yakubu, B. R. (2006).Matar uba jaraba.
Ramat General Enterprises.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.