Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummuwar Majema a Farfajiyar Magungunan Gargajiyar Mata da Yara

Citation: Aminu IBRAHIM (2022). Gudummuwar Majema a Farfajiyar Magungunan Gargajiyar Mata da Yara. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 10, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

GUDUMMUWAR MAJEMA A FARFAJIYAR MAGUNGUNAN GARGAJIYAR MATA DA YARA

Na

Aminu IBRAHIM

Tsakure

Wannan aikin ya nazarci magungunan da majema suke samarwa ne don magance cututtukan da suke addabar mata da yara. Magungunan sun haɗa da na riga-kafi da na tattali da kyautata kiwon lafiya da kuma na kau da cuta gaba ɗaya. Yin cikakken nazari a kan ire-iren magungunan da majema suke bayarwa, zai taimaka wajen fahimtar irin rawar da suke takawa a wannan fuskar. Majema sun shahara ƙwarai wajen bayar da magungunan da suka shafi yara, musamman ƙanana, da kuma mata. An yi amfani da hanyoyin gudanar da bincike da suka haɗa da yin hira da mutane ma’abotan sana’ar, watau majema wanda haka ya bayar da damar tattara muhimman bayanai da aka samo daga ainahin masu sana’ar da ma waɗanda suke ‘yan haye ga sana’ar. An kai ziyara na gani da ido, domin tabbatar da waɗansu muhimman bayanan da aka samo daga hiran da aka yi. Binciken ya gano wasu sirrika na ɓoye a kan mahaɗan magungunan gargajiya da majema suke amfani da su wajen warkar da cututtuka. Wannan bincike ya tabbatar da majema a matsayin ɗaya daga cikin fitattun rukunnan masu sana’o’in gargajiya da suke bayar da magani a ƙasar Hausa.

Gabatarwa

A da can, watau kafin shigowar baƙi a ƙasar Hausa, masu sana’o’in gargajiya su ne likitocin gargajiya masu bayar da magungunan wasu cututtukan da suke addabar al’umma. Kowanne rukunin masu sana’o’in gargajiyar Hausawa da irin nau’ukan magungunan da suke bayarwa. Haka kuma, suke da cikakken sirrin yadda ake sarrafa magungunan, har su yi tasiri a jiki. Sirrikan magungunan sun keɓanta ne musamman ga ‘yan gado da kuma ‘yan hayen da suka yi matuƙar biyayya, sai kuma waɗanda suka ga dama suka laƙƙana wa, saboda wasu dalilai. Haka kuma, da zarar wani abu ya faru na tsotsayi, an san gidan mai sana’ar da za a garzaya, domin neman ɗauki. Don haka, ana iya cewa ba ƙaramar gudummuwa suke bayarwa ta wannan sigar ba, watau ta fuskar magani, domin maganin cuta, da kuma samar da magungunan riga-kafin wasu cututtuka da suke takura al’umma. Bisa ga haka, su ma majema ba a bar su a baya ba; kuma a kan gudummuwarsu ne a wannan fannin, wannan maƙalar ta sa gaba. Ƙamusun Hausa na CNHN (2006) ya fassara kalmar jima da “sana’ar fid da gashi daga jikin fata” (Sh. 217). Bisa ga la’akari da wannan fassarar, ana iya cewa, jima aiki ne na ƙoƙarin fid da ko raba gashi daga jikin fatar dabbar da aka yanka, aka kuma feɗe. Irin wannan ɗawainiyyar da ake yi wa fata ta amfani da hikimomi ko fasahohin da aka gada, watau na gargajiya da kuma na zamani, domin a cire gashi daga jikin fata, shi ake cewa jima.

Haka kuma, akwai ra’ayoyin masana da na manazarta da dama dangane da ma’anar kalmar magani da suka haɗa da:

Magani shi ne duk wani abu da ɗan’adam kan yi don samun warkarwa da buƙata da ɗaukaka a rayuwarsa ta kullum. Don kuwa ɓangaren rayuwar ɗan’adam duk tafiya take wajen fafitikar neman maganin warkewa daga cututtuka da kwantar da damuwar zuciya, in ya samu, sai kuma ya shiga neman maganin ɗaukaka da kariya wajen abokan hamayya. Haka kuma rayuwar ɗan’adam take tafiya kullum. In ya yi maganin wannan yana buƙatar maganin wancan (Tukur, 1988, sh. 14-15).

Masanin ya kalli magani a matsayin wata hanyar rayuwa da ɗan’adam ya ginu a kanta, kuma yake gudanar da rayuwarsa a kanta.Wannan ra’ayin ya nuna yadda magani yake biya wa ɗan’adam buƙatu na rayuwa da suka haɗa da buƙatun zuciya da na jiki da kuma na kariya daga abokan hamayya. Ɗan’adam ba ya zama haka kawai, ba tare da neman magunguna da suke zaman sinadiran gudanar da rayuwarsa ba. Baya ga wannan masanin, an kuma samu wani masanin da ya dubi magani da:

Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta haɗari, ko kuma neman kariya ga cuta ko abokan hamayya ko neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi (Bunza, 1990, sh. 134).

Idan aka yi duba da ma’anar da wannan masanin ya bayar, za a ga ba wani abu ba ne “magani,” face hanyoyin da ake bi waɗanda suke cike da ilmi wajen magance dukkan wata cuta, ko sauƙaƙa raɗaɗinta, ko kuma kwantar da cuta. Haka kuma, ya ƙara nuna yadda mutane suke amfani da magani a wajen neman kariya daga cututtuka da ka iya kama su, ko kuma neman kariya daga cutarwar da abokan gaba, ko na hamayya, za su iya yi masu. 

Idan aka yi la’akari da waɗannan ra’ayoyin da masanan suka gabatar, kuma aka dubi ƙunshiyar ma’anonin, za a ga duk suna magana ne a kan hanyoyin da ɗan’adam yake bi wajen kawar da cuta da kuma kariya daga wasu cututtukan da wani yake iya kamuwa da su. Wannan hanyar ba ta tsaya ga warkar da cuta kaɗai ba, hatta magungunan da ɗan’adam yake nema, kuma yake amfani da su wajen biyan buƙatar rayuwa da kuma na neman buwaya daga abokan gaba ko na hamayya. 

 Ana iya fassara kalmar magani da hanya ko fasaha da ɗan’adam yake amfani da ita wajen neman lafiya a yayin da yake cikin lalurar rashin lafiya ko kariya daga cuta ko neman tsari daga cutarwar abokan hamayya, ko kuma ya yi fice, watau ya buwaya a kan wani abu.

Kamar yadda kowane rukuni na masu bayar da magungunan gargajiya ke amfani da mahaɗai wajen samar da magungunan da aka san su da su, haka su ma majema, suna da irin nasu kayayyakin haɗin da suke amfani da su wajen samar da magungunan da suke bayarwa. Majema na samun waɗannan mahaɗan ne daga kayayyakin da suke amfani da su wajen gudanar da sana’arsu. Mahaɗan suna daga cikin tarin abubuwan da ake samu daga itatuwa da tsirrai da sauran ire-irensu, domin haɗa magani. Wasu daga cikin kayayyakin haɗin, jiƙa su ake yi, sai sun tsima, a yayin da wasu kai tsaye ake amfani da su, watau ba tare da an sarrafa su ba, kuma su biya buƙatar da ake so. Mafi yawan magungunan da aka san majema na bayarwa, sun danganci na cututtukan jiki ne. Da yawa daga cikin mahaɗan, ana samo su ne daga cikin albarkatun ƙasa da kuma fatu na jikin dabbobi da masu sana’ar suke sarrafawa, domin samar da magani. Waɗannan mahaɗan sun haɗa da: ruwa da fatakka da gashin dabbobi da kanwa da naman kanni da gishiri da nonon shanu da ruwan ruɓi da kuma bagaruwa.

 Taƙaitaccen Bayani Game Da Maganin Yara

Hausawa sun tanadi magunguna da dama na yara a kan cututtukan da suke yawan damun su, domin tattali da kuma inganta lafiyar yara. Waɗannan cututtuka suna kama yara ne saboda yanayi da kuma rashin ƙarfin garkuwar jikinsu. Wannan dalili, ya sa aka samu wasu rukunnan mutane masu bayar da magungunan yara na gargajiya a ƙasar Hausa. A al’adance, waɗannan mutane suna da gurbi na musamman a farfajiyar bayar da magani. Masu gudanar da sana’o’in garjiya na bayar da muhimmiyar gudummuwa a wajen bayar da magani a farfajiyar ƙasar Hausa. Akwai wasu daga cikinsu da suka gwanance, kuma suka shahara a wajen bayar da magunguna na wasu fitattun cututtuka da suke hana yara walwala. Misali, akwai waɗanda suka ƙware wajen bayar da magungunan lalurorin fitsarin kwance da firgitar yara da kuma cutar hiƙa, watau ƙazamin goyo. Ana danganta waɗannan cututtuka ga yara ne, musamman ƙanana, saboda lalurorinsu ne, kuma da wahala a samu manyan mutane da ke kamuwa da su. Majema suna amfani da wasu sirrika na sarrafa mahaɗun magungunansu, kuma suna aiwatar da su daidai yadda yara za su iya sha ba tare da matsala ba. Haka kuma, waɗannan magungunan da majema suke bayarwa ga yara suna kasancewa garkuwa ga lafiyarsu (Sallau, 2010).

Wasu Daga Cikin Magungunan Da Majema Suke Bayarwa

Magungunan da majema suke bayarwa domin warkar da cututtuka suna da yawa, kuma suna bayar da su dangane da rukunnan da mutane suka faɗa a ciki, musamman ta fuskar shekaru da jinsinsu, watau akwai taimakon da suke bayarwa ga yara ƙanana da kuma na manya. Haka kuma, akwai magungunan da suka keɓanta ga mata. Gudummuwar da majema suke bayarwa ta fuskar magani bai tsaya ga mutane kaɗai ba, hatta dabbobin da mutane ke kiwo, su ma ba a bar su a baya ba, domin sun kasance suna amfana daga magungunan da majema ke samarwa.            

Magungunan Yara Da Jarirai

Majema sun shahara wajen samar da magunguna, don warkar da wasu tarin cututtukan da ke addabar yara ƙanana a cikin al’umma. Wannan gudummuwar da suke bayarwa ba ƙaramin agazawa take yi ba wajen tattali tare da kiwo ko kyautata lafiyar yara ba. Akwai wasu cututtukan da ke damun yara, amma kuma Hausawa sun fi amincewa da maganin gargajiya bisa ga na asibiti, watau na zamani. Jinkirin da ake yi kafin a nemi taimako daga wurin da ya dace yakan haifar da salwantar rayukan yara kamar yadda wani majemi ya tabbatar![1]. Ga wasu daga cikin magungunan da majema suke bayarwa:

Shan Nonon Ɗan Yaye

Bisa ga al’ada ta Bahaushe, akwai adadin lokacin da yaro ƙarami ke kai wa kafin a raba shi da shan nonon mahaifiyarsa. Ana raba yaro daga shan nono bayan ya kai shekara biyu da haihuwa. Akan yi tanadi na musamman tare da bayar da waɗansu taimako, don yaron da za a yaye ya samu sauƙi daga yanayin da zai samu kansa a ciki, kuma ya sa ya yi saurin dangana da nonon. Akan fara aiwatar da matakan yaye yaro ne ya zuwa mataki-mataki, watau ba lokaci ɗaya ake datse shi daga shan mama ba. Bayan yaye da wani lokaci, watau bayan an yaye yaro, kuma jiki ya fara sabawa da sabon yanayin da ya samu kansa a ciki, akan samu tsotsayi bisa kuskure yaro ya sake kama maman ya sha; inda a sanadiyyar haka zai sha nono mai tsami wanda kan haifar wa yara da matsanancin ciwon ciki da murɗewar ciki, kuma zai ta zawo babu ƙaƙƙautawa. Idan aka yi sake ruwan nonon mai tsami da yaro ya sha ya game jikinsa, kuma aka yi rashin sa’a ba a yi dace da zuwa ga majema a kan lokaci ba, rayuwar yaro kan iya salwanta, watau a rasa shi gaba ɗaya. A irin wannan yanayin ne, waɗanda ke da masaniyar inda za su samu magani, ke garzayawa wajen majema, domin samun ɗauki.[2]

 Majema kan ba yaro ruwan ruɓi wanda yake haɗi ne na wani ganye da ake kira da fatakka, ko fattaku, wanda ke game da ruwan jiƙon fatu da ake haɗawa, domin a ruɓa fatu a ciki, shi ake ba yaro tare da ɗan ɓirɓishin gishiri da ake zubawa a ciki. Da zarar yaro ya sha, a nan take zai amayar da dukkan ragowar sinadarin tsattsaman nonon da ya sha, kuma daga nan sai yaro ya samu lafiya.[3]

Fitsarin Kwance

A al’adance, akwai adadin shekarun da idan yaro ya kai, kuma bai daina fitsarin kwance ba, watau fitsari a yayin da ake kan shimfiɗa, ana barci, hankalin iyayen yaro kan tashi su shiga damuwa, tare da nema wa yaro magani kafin a makara. Irin wannan yanayi, ya fi haifar da matsala ga mata, inda wasu har sukan kai shekarun da za a aurar da su, amma ba su rabu da matsalar ba, wanda haka kan sa iyaye su dukufa ga neman magani. Majema suna daga cikin waɗanda suke taimakawa ga wannan matsalar. Su kuma, sukan bayar da ruwa da aka samar daga fatar ruƙumin da aka jeme wadda aka jiƙa, wasu kan haɗa da karkaɗa bindin raƙumi a cikin ruwan, kafin a sha. Cikin ikon Allah, akan samu waraka daga lalurar.[4]

Hiƙa (Ƙazamin Goyo)

Hiƙa wani nau’in kumburin jiki ne da ciwo ke haifarwa, musamman ga yara ƙanana waɗanda ba a yaye daga shan nono ba. Akan yi amfani da magungunan da majema ke bayarwa wajen nema wa yara tsari daga wasu cututtuka da ke da nasaba da iska. Akwai ciwon da ke haifar wa yaro ko yarinya kumburin jiki wanda haka yana faruwa ne daga nonon da yaro ke sha. Wannan yanayin yana faruwa ne a sanadiyyar da burkucewar nonon uwa ke yi. Ana kyautata zato iska ne ke haifar da wannan lalurar. Majema na bayar da ruwan ruɓi ga yaro, bayan an tace shi, kuma an ƙara masa ruwa, domin ya rage kauri, sai a ba yaron ya sha tare da yi masa hayaƙi da gashin dabbobin da ake cirewa daga fatun da majema ke jemewa. Wannan hayaƙin yana taimakawa wajen raba yaron da iskar ke addabar sa, tare kuma da yi masa karewa daga kamuwa da wasu miyagun iskokan da ka iya haddasa masa wasu nau’ukan ciwon ƙwalwa. Haka kuma, in yaro bai isa shan maganin ba, akan ba uwar ta sha, domin ya bi jikinta, yadda yaron zai sha ta hanyar tsotsa a yayin da ya sha mama.[5]

Maita

Maita wani nau’in abu ne, da masu ita ke sakar wa wasu ciwo, domin su cutar da su wanda idan ba a yi sa’a ba, akan iya salwantar da rai. Maita a al’adance, nau’i ne na asiri wanda ake amfani da iskokai wajen kama kurwar mutane, musamman yara. Da zarar masu maitar sun samu galabar damkar kurwa, sukan samu zarafin azabtar da yaran da tsotsayin ya faɗa a kansu. Dukkan maita da ke da alaƙa da iska, majema na bayar da magani, domin samun waraka daga lalurar. Akan yi amfani da ƙwaro na iccen faru tare da gashin da aka jeme daga jikin fatu a yi turare da su, domin neman warakar ciwon da aka kamu da ita ta daliln maitar, kuma yana taimakawa wajen neman kuɓuta daga sharrin mayun.[6]

Magungunan Kyautata Lafiyar Mata

Majema na taka rawa wajen samar da magungunan da ke tallafa wa mata ga warkar da su daga lalurorin rashin lafiyar da suke fa ma da su, da kuma kyautata lafiyarsu, da na abin da suke ɗauke da shi. Gudummuwar da majema ke bayarwa ba ta tsaya ga yara kaɗai ba, hatta iyayensu mata, watau su ma suna daga cikin waɗanda ke amfana, kuma suna da gurbi na musamman; saboda sai in suna cikin ƙoshin lafiya, sannan yaran da ke ƙarƙashin kulawarsu ke samun walwala da kuma kula.[7] Daga cikin cutukan mata da majema ke warkarwa, akwai:

Ciwon Nono

Daga cikin magungunan da majema ke ba da wa har da na maganin ciwon nono da mata ke yawan fama da shi, musamman bayan haihuwa. Wasu mata na jin zafi mai raɗaɗi a yayin da suke shayarwa. Wannan ciwon, kumburi yake sa nono, ya kuma hana su matan masu shayarwa sukuni ta yadda suke shiga wani yanayi mai tayar da hankali. A wasu lokuta, ba kasafai ake dace da magungunan zamani da ka iya kauda lalurar gaba ɗaya ba; ko an samu sai dai ya kwantar da ciwon na wani lokaci, kuma yana sake dawowa a duk lokacin da mai irin lalurar za ta sake shayar da wani yaron. Akwai kuma yanayin da ake samu, wanda ruwan nonon ne ke yin ƙaranci, ko ya ɗauke wanda in ba a ɗauki mataki ba, yaro ko yarinya na iya kamuwa da yunwa, don rashin samun isasshen abinci da zai rayar da shi har jikinsa ya ginu.[8]

Idan aka samu mace mai ɗauke da ɗaya daga cikin waɗannan lalurorin, a kan yi amfani da ruwan ruɓi da majema ke samarwa, a ɗebi kaɗan a ba ta, don ta sha, sannan a yi amfani da gashin da ake fitarwa a yayin gurza, a yi mata turare da shi. Da zarar an yi wa mace mai ciwon nono wannan, mamanta kan saki ya bar ciwo, kuma ruwan nonon ya komo, kuma ya wadatu.[9]

Kumburin Jikin Mai Jego Bayan Haihuwa

A yayin da mace ta haihu, ana samun wasu matan su yi ta fama da ciwon kumburin jiki. A zamanance, ana alaƙanta wannan yanayin da ciwon hawan jini da wasu matan ke kamuwa da shi a yayin da suke da juna biyu. Wasu na samun sauƙi da zarar sun haihu, a yayin da wasu ke ci gaba da fama da shi bayan haihuwarsu. Idan ciwon hawan jini ne, a kan nemi magungunan da ke saukar da ciwon, ko ma a kauda shi gaba ɗaya. A wasu lokutta, ana fahimtar cewa ba hawan jini ba ne, musamman bayan an jarraba magungunan hawan jini da dama. Garwashin wuta ake samowa, sai a ɗebi gashin da ake samu a majema a zuba ciki, sannan a sa mace ta yi amfani da mayafi mai yalwa ta lulluɓe kanta a ciki tare da hayaƙin turaren, yadda turaren zai ratsa jikinta ko’ina. Idan ciwon na da alaƙa da iska, akan samu sauƙi a warke, domin turaren gashin yana da wani sirri na musamman, kuma yana taimakawa wajen raba, ko kwantar da ciwon da iska ke haddasawa a jikin mutane, musamman mata[10].

Gyara Jikin Mai Jego

Akan nema wa mata, musamman sabbin haihuwa taimako daga wajen majema, domin su mayar da komaɗa, kuma su samu sauƙi daga wahalhalun da suka sha a yayin goyon ciki da naƙuda da ma dai sauran yanayin da suka samu kansu a baya. Rashin samar da ingantattun magungunan tattalin lafiyar jiki, kan iya sa jikin mace ya lalace, watau ya saki. A irin wannan halin ne iyaye ke neman taimako a gargajiyance daga ma’abutan magungunan, don su tallafi lafiyar mai jego. Bisa ga al’ada, majema na daga cikin waɗanda ake neman agajinsu, domin a samar wa mace lafiya, kuma a mayar da ita sabuwa kamar yadda take a da. Akan nema wa mai jego garin bagaruwa, sai a jiƙa ta, ta riƙa amfani da ruwan a yayin da za ta yi tsarki, watau kafin ta sa ruwa, sai ta yi tsarki da ruwan bagaruwan, sannan ta sa ruwa ta yi tsarki na sosai. Idan mace ta ɗabi’antu da yin haka, zai taimaka ya sa jikinta ya game, watau duk inda ya buɗe ya matse.

Kammalawa

A cikin wannan aikin da aka gudanar, an yi ƙoƙarin fitowa da ire-iren magungunan da majeman ƙasar Hausa ke samar wa ga jama’a. Waɗannan magungunan sun kasance suna taimakawa wajen tattali da kyautata lafiyar al’ummar da take rayuwa a farfajiyar da ake dangantawa da ƙasar Hausa. Wannan gudummuwar da majema suke bayarwa ta wannan sigar, gagaruma ce, domin magunguna da suke haɗawa ta amfani da mahaɗan da suke haɗawa sun ƙara tabbatar da wannan sana’ar a matsayin ta gida, watau wadda Hausawa suka gada kaka da kakanninsu. Ta hannun masu sana’o’in gargajiya ne al’umma ke samun taimako na magungunan wasu cututtuka, kuma su ma majema suna daga cikin rukunin masu sana’ar da mutane suke dogara da su wajen samun magunguna. Wannan bincike ya gano wasu sirrika na ɓoye a kan mahaɗan magungunan gargajiya da majema suke amfani da su wajen warkar da cututtuka. Haka kuma, wannan aikin, ya gano irin gudummuwar da majema suke bayarwa a kan harkar tattalin lafiyar ƙananan yara da iyayensu, mata.

Manazarta

Bunza, A. M. (1990). Hayaƙi fid da na kogo (nazarin siddabaru da sihirin Hausawa) [Unpublished M. A Dissertation]. Jami’ar Bayero, Kano.

C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa. cibiyar nazarin harsunan Nijeriya,

      Jami’ar Bayero.

Sallau, B. A. (2010). Wanzanci da muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. M. A. Najiu Professional Printers.

Tukur, A. (1988). Nazari a kan cututtukan da suka shafi fatar jiki da magungunansu a Bahaushiyar al’ada [Unpublished B. A Project]. Jami’ar Bayero, Kano.

 



[1] Hirar da aka yi da majemi Abdulkarim Ma’aruf Garo ɗan kimanin shekara 50, a majemarsa da ke garin Garo da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mashi, Jahar Katsina a ranar 03/12/2020.

[2] Hirar da aka yi da majemi Abdulkarim Ma’aruf Garo ɗan kimanin shekara 50, a majemarsa da ke garin Garo da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mashi, Jahar Katsina a ranar 03/12/2020.

[3] Hirar da aka yi da majemi Abdulkarim Ma’aruf Garo ɗan kimanin shekara 50, a majemarsa da ke garin Garo da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mashi, Jahar Katsina a ranar 03/12/2020.

[4] Hirar da aka yi da Malam Sa’idu Bishir S-power, shugaban matasan Abatuwa, kuma majemi na garin Katsina ɗan shekara 32 a wurin Sana’arsa da ke a mayankan Abatuwa da ke cikin ƙwaryar garin Katsina a ranar 28/10/2020.

[5] Hirar da aka yi da Dattijo Baba Salihu ɗan kimanin shekara 85 a majemarsa mai suna Godada da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wurno da ke cikin Jihar Sakkwato a ranar 18/02/2021.

[6] Hirar da aka yi da majemi Abdulkarim Ma’aruf Garo ɗan kimanin shekara 50, a majemarsa da ke garin Garo da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mashi, Jahar Katsina a ranar 03/12/2020.

[7] Hirar da aka yi da Majemi Abubakar Ahmad ɗan shekara 37 a majemarsa da ke unguwar Cake da ke cikin garin Katsina a ranar 08/11/2020.

[8] Hirar da aka yi da Alhaji Mustapha Labaran, shugaban majema na Jihar Sakkwato ɗan shekara 48 a gidansa da ke unguwar Rogo a cikin garin Sakkwato a ranar 06/02/2021.

[9] Hirar da aka yi da Dattijo Baba Salihu ɗan kimanin shekara 85 a majemarsa mai suna Godada da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wurno da ke cikin Jihar Sakkwato a ranar 18/02/2021.

[10]Hirar da aka yi da Dattijo Baba Salihu ɗan kimanin shekara 85 a majemarsa mai suna Godada da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wurno da ke cikin Jihar Sakkwato a ranar 18/02/2021.

Yobe Journal

Post a Comment

0 Comments