Cite this Article as: Muhammad Mustapha Umar (2026). Kalmomin Masu Sayar da Man Fetur da Baƙin Mai a Cikin Garin Sakkwato. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 9(1), 7-13. https://doi.org/10.36349/easjehl.2026.v09i01.002
KALMOMIN MASU
SAYAR DA MAN FETUR DA BAƘIN MAI
A CIKIN GARIN SAKKWATO
Daga
Dr. Muhammad
Mustapha Umar
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Email: mustapha.umar@udusok.edu.ng
GSM: 07066933883
Tsakure
Wannan takarda ta yi nazarin kalmomin rukunin masu sayar da man fetur da baƙin mai a cikin garin Sakkwato. Manufar
ita ce zaƙulo yadda wannan rukunin ‘yan kasuwa suke sarrafa harshen Hausa, ta
hanyar fito da ma’anonin kalmomin da suke amfani da su a zantukansu na yau
da kullum. An taƙaita wannan bincike a kan nazarin kalmomi ne kawai, ba tare da nazarin
sassan jumla ko jumlolin wannan rukunin ‘yan kasuwa ba. An gabatar da hasashe
guda biyu (2), waɗanda aka gwada su ta hanyar gudanar da
lura ta kai-tsaye da hira ko tattaunawa da masu harkar sayar da man fetur da baƙin mai a wuraren kasuwancinsu. An
tattaro wasu lafuzzan da suke amfani da su domin tabbatar da samuwar wannan
Hausar dalilin zamantakewa da sauran ma’amalolin a wuraren kasuwancinsu.
Binciken ya gano cewa ‘yan kasuwar suna amfani da wasu ma’anoni na musamman waɗanda suka sha bamban da Hausar yau da kullum, wadda suke
samarwar ta hanyar faɗaɗa ma’ana da ƙirƙira da kuma sarrafa kalmomin aro. Daga ƙarshe an ba da shawarar faɗaɗa bincike a wannan fanni domin buƙasa harshen, musamman a yanzu da
kimiyya da fasaha suke taka rawa a cigaban harshe.
Fitilun Kalmomi: Walwalar Harshe, Hausar Rukuni, Man Fetur, Baƙin Mai
1.0 Gabatarwa
Fetur[1] mai
ne da ake zuba wa babur ko mota ko wani inji wanda ke ƙonewa
don ya ba inji ƙarfin
wuta da zai sa ya motsa.[2] Ana
haƙo man fetur
daga ƙasa
ko daga teku a tace a matsayin makamashi don amfani a injuna. A hukumance duk
wanda zai yi sana’ar fetur zai nemi lasisi daga gwamnati sannan a ba shi damar
ya gina gidan mai[3]. Zai
tanadi tankokin ɗauko mai da
ma’aikata, da sauran abubuwan buƙata
da za su taimaka tafiyar da wannan kasuwanci mai haɗarin
gaske. Sannan mai gidan mai ya fara saye da sayar da man fetur a ƙarƙashin kulawar hukumar DPR.[4] Daga
cikin masu kasuwancin man fetur akwai manyan dillalai, waɗanda
ke sayar da man fetur kan farashin gwamnati da kuma dillalai masu zaman kansu,
waɗanda a wasu lokuta suke sayar da man
fetur fiye da farashin da gwamnati ta ƙayyade. Shi ya sa wasu jama’a ke yi
musu kallon ‘yan kasuwar bayan fage, wato masu sayar da man fetur da tsada da
rashin lita mai kyau.
Baƙin mai[5], mai ne kore mai kauri da ake zuba wa injuna da zai sa sassansu su motsa
kamar yadda ya dace. Masu sayar da baƙin mai yawanci suna gudanar da sana’arsu ne a gefen tituna, inda suke aikin
zubar da baƙin mai na babur ko
mota ko wani inji idan ya gama aiki, su zuba sabo a biya su kuɗin baƙin mai. Suna sayar
da mataccen baƙin mai da suke tarawa ga jama’a mabuƙata. Wannan baƙin mai shi suke kira kwandem (condemn), kuma ana shafa shi
a jikin katako don kariya daga ƙwari. Masu ƙaramin ƙarfi ma na amfani da shi wajen juye, musamman kwandem wanda bai gama aiki
sosai ba. A yau masu wannan sana’a suna sayar da wasu abubuwa bayan baƙin man irin su: Ruwan birki da fulogai da omon wankin mota da wayar kuloci
da giris da man fetur da kalanzir da kayan janareta da kuma sauran
sassan abubuwan hawa.
Hausawa masu gudanar da sana’o’i sun saba ƙirƙirar nau’in Hausa wadda ta shafi
rukuninsu. Umar (2019) ya nazarci Hausar rukunin 'yan kasuwa a garin Sakkwato.
Sharu (2023) kuwa ya nazarci nau'in Hausar 'yan agwagwa-da-buje. Ƙarin misalan bincike da aka gudanar
game da Hausar rukunin masu sana'o'i sun haɗa da na Sani da Adamu (2023) da Mode (2024). Wannan ya ja hankalin mai
nazarin domin binciko shin ko su ma masu sana’ar sayar da man fetur da baƙin mai a garin Sakkwato suna da tasu
Hausar rukuni ?
Domin yin wannan nazari an kasa takardar gida biyar. Daga
farko akwai gabatarwa, sai hanyoyin gudanar da bincike da hasashen bincike.
Daga nan sai bayani kan Hausar masu sayar da man fetur da baƙin mai, tare da misalan kalmomi, kana
kuma aka kawo dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana, don tabbatar da
kasancewar sauyawar ma’ana ta hanyar faɗaɗa ma’anar kalmomi. A ƙarshe akwai jawabin kammalawa da sakamakon bincike.
2.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike
Wannan takarda sashe
ne da ya shafi kundin binciken gaba-ɗaya. Don haka, ne aka
tsakuro wasu hanyoyin gudanar da bincike, da za su sawwaƙa tattaro bayanan
bincike kamar yadda ya dace. An yi amfani da hanyoyin tattaro bayanai guda
biyu, wato hira ko tattaunawa
da kuma lura ta kai-tsaye, waɗanda suka tabbatar da samuwar
wannan nau’i na Hausa kamar yadda masu sayar da man fetur da baƙin mai suke amfani da
ita a wuraren da binciken ya shafa. An kasa waɗanda
aka yi hira da su zuwa gida huɗu:
a) Tattaunawa da masu sayar da man fetur
da gas da baƙin mai a gidajen
mai
b) Tattaunawa da masu sayar da man fetur a gefen tituna,
waɗanda ake kira ‘yan cuwa-cuwar man
fetur (black market)
c) Tattaunawa da masu sayar da baƙin mai a gefen tituna
d) Tattaunawa direbobi masu ɗauko mai da yaransu
A wannan takarda, mai bincike ya zaɓi yin amfani da ra’in Harris (1952) mai suna Discourse Analysis Theory wanda
yake nazarin yadda al’umma suke sarrafa harshe, ta fuskar ma’ana don zaƙulo dangantakar da ke tsakanin ma’anar da tarihin samuwar kalmomin harshe. Ra’in ya dace kuma yana da dangantaka da wannan
bincike domin ya shafi yadda wasu rukunan jama’a suke amfani da harshe bamban
da sananniyar ma’ana ta fuskar kalmomi a zamantakewarsu da sauran ma’amalolinsu
na yau da kullum. Ga wasu misalai na wasu ayyuka da aka gabatar ta amfani da
ra’in: Isah (2018) da Zailani (2019) da Sharu (2023) da kuma Mode (2024).
3.0 Hasashen Bincike
An yi kintacen abubuwa huɗu (4) da ake sa ran za su faru, waɗanda ake fatar idan aka gwada su, su dace ko su saɓa wa abubuwan da bincike ya gano a ƙarshe. Ga
hasashen:
i. Masu sayar da man fetur da baƙin mai a
garin Sakkwato suna da wata keɓaɓɓiyar
Hausa da suke amfani da ita wajen aiwatar da kasuwancinsu.
ii. Hausar waɗannan rukunin ‘yan
kasuwa ta ƙumshi kalmomi masu ɗauke da sababbin ma’anoni saɓanin
waɗanda aka san su da su.
4.0 Kalmomin Masu Sayar da
Man Fetur da Baƙin Mai[6]
‘Yan kasuwa sukan yi amfani da harshen Hausa wajen bayyana wasu abubuwa, waɗanda suka jiɓinci rayuwarsu ta yau da kullum, tare
da samar musu da sababbin ma’anoni, domin sadarwa cikin sauƙi. Kodayaushe idan wani
abu baƙo
da babu shi ya shigo a ƙasar
Hausa, akan yi ƙoƙarin samar masa suna
ta hanyoyin da suka dace. Misali, yin amfani da wasu fitattun hanyoyi kamar faɗaɗa
ma’ana da ƙirƙira da aro da ɗafi
da kuma tsira. Tun da haka ne, muna iya cewa wasu daga cikin waɗannan
hanyoyin sun taimaki Hausar kasuwanci, musamman sakamakon bayyanar abubuwan
zamani. Wani abin sha’awa shi ne, yadda kowane rukuni na ‘yan kasuwa ke ƙoƙarin ƙirƙira sabbin ma’anoni,
don tafiyar da al’amurransu.
Hausar masu sayar da man fetur tana samuwa ne tun daga tafiya ɗauko mai, inda direba da yaransa ke amfani da wata Hausa don bayyana wani
hali ko yanayi da suke ciki a lokacin gudanar da sana’arsu. Su ma ma’aikatan
gidan mai suna amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi
tsakaninsu domin sadarwa. Sannan akwai ‘yan cuwa-cuwar[7] man fetur masu sayar da mai a kan
tituna.
A taƙaice, akwai alaƙa tsakanin direbobi da yaransu
masu ɗauko mai a kurmi da ‘yan kasuwa masu
sayar da mai. Za a fahimci wannan dangantakar a ƙarƙashin misalan Hausar masu sayar da man
fetur da baƙin mai. Fagge
(2004: 126-127) ya kawo bayani kan Hausar ‘yan cuwa-cuwar man fetur kamar haka:
Sana’ar sayar da man fetur ta samu ne daga baya inda matasa kan sayi mai daga
hannun manyan dillalai, su kuma su kasa su sayar a gefen tituna. Sai dai galibi
masu gudanar da wannan sana’a matasa ne kuma yawancinsu ‘yan daba ko ‘yan
shaye-shaye. Kusan da wuya ka ga mai sayar da mai ko mai irin wannan sana’a[8] ba ya shaye-shaye, musamman
wiwi. Su ma suna da wasu
kalmomi nasu na daban waɗanda suke amfani da su a tsakaninsu
domin sadarwa.
Haka kuma, akwai ‘yan kasuwa masu sayar da baƙin mai a kan titi, waɗanda suka riƙe ta a matsayin hanyar sana’arsu da suke yi don gudanar da harkokinsu
na yau da kullum. Masu wannan sana’ar suna amfani da wata keɓaɓɓiyar Hausa wajen gudanar da sana’arsu,
musamman domin ambaton abubuwan da suke sayarwa da kayayyakin da suke amfani da
su wajen gudanar da sana’arsu.
4.1 Kalmomin da suka Shafi Faɗaɗa Ma’ana
Kalmomin da za a gani a wannan sashe. Kalmomi ne na Hausa kuma suna da
ma’ana ta asali, amma aka ba su wata ma’ana ta musamman saɓanin wadda aka san su da ita. Waɗannan ma’anoni
sabbi, da su ne masu sayar da man fetur da baƙin mai ke amfani wajen aiwatar da
kasuwancinsu.
Jadawali na 1: Faɗaɗa
Ma’anar Kalmomin Asali
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Méesàa[9] |
Suna |
Ƙatuwar macijiya mai haɗiye mutum ko dabba. Ana amfani da fatar ta wajen yin
takarmi da jakunkuna |
A jikin injin na sayar da mai akwai wata roba doguwa mai kauri, wadda ta
cikinta fetur ke fita, wadda a ƙarshenta tana da kai ko baki mai mariƙi na musamman, da ake matsawa a zuba
mai ko a tsayar da shi |
|
2 |
Sóoɓòo [10] |
Suna |
Fure ne da ake samu daga sure ko yakuwa |
Man fetur mai
launin ja-ja-ja |
|
3 |
Jùuyée |
Suna |
Saye abin da
budurwa ke talla, ko wani irin kitso |
Zubar da baƙin mai na abin hawa
ko inji idan ya gama aiki don a zuba sabo |
|
4 |
Hàlàmníyáa |
Suna |
Cin abinci da sauri don haɗama |
Cuwa-cuwar man fetur inda kowane ɗan bulakmaket ke sauri ko ƙoƙarin ya ba da roja[11] don ya sayi fetur fiye da sauran jama’a |
|
5 |
Sàndáa |
Suna |
Itace da aka karya
ko aka sara daga jikin bishiya don yin amfani da shi kamar a makami na dukan
wani abu ko don dogarawa |
Dogon ƙarfe mai zanen mita
a jikinsa wanda ake awon man fetur da ke cikin tankin ƙasa |
|
6 |
Náiràa bìyár |
Suna |
Takardar kuɗin
Nijeriya mai ɗauke da hoton
marigayi Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa |
Naira ɗari
biyar |
|
7 |
Náiràa góomà |
Suna |
Takardar kuɗin
Nijeriya mai ɗauke da hoton
marigayi Alvan Ikoku |
Naira dubu ɗaya |
|
8 |
Ɗígòo[12] |
Suna |
(i) Ɗison abu ruwa-ruwa (ii) ruwan baƙaƙe da ake yi wa wasu haruffan Ajami ko
na Larabci ko kuma Ingilishi (iii) aya ta nuna alamar tsayawa a cikin jumla
ko wajen karatu |
Lambobi ɗari da ke jujjuyawa, su bayar da lita
guda |
|
9 |
Bàasáajàa[13] (basaje) |
Suna |
Fakewa da wani hali
don samun riba |
Karkatar da man
fetur zuwa wani wuri ko wata ƙasa
maimakon zubawa a gidan mai a sayar wa jama’a, musamman don samun
riba sosai |
Waɗannan
misalai sun fayyace yadda ‘yan kasuwa suke ba kalmomin asali sababbin ma’anoni
saɓanin waɗanda
aka san su da su. Kuma wani lokaci ba tare da an canja fasalin kalmomin ba,
wato kalmomin suna nan zamansu kamar yadda suke. Kamar yadda aka gani ‘yan
kasuwa suna
amfani da wannan hanya ta faɗaɗa
ma’anar kalmomi, bayan sun lura da yanayin baƙin abubuwan da suka shigo waɗanda
ba su san su ba, kafin su yi amfani da kalmomi asali da za su dace.
4.2 Kalmomin da suka Shafi Ƙirƙira
A wannan sashe an kawo sabbin ma’anoni da ‘yan kasuwa suka ƙirƙiro, don sadarwa a tsakaninsu. Waɗannan sabbin ma’anoni sun keɓanta gare su ne kawai. Akasari duk inda
aka zagaya ba za a ji ana aiwatar da su ba, sai a Hausar rukunin masu sayar da
man fetur da baƙin mai.
Jadawali na 2: Ƙirƙira
Daga Kalmomin Asali
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jùuyèn náa-ìsáa |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Juye baƙin mai tun bai gama aiki ba |
|
2 |
‘Yán-sâ-káì[14] |
Harɗaɗɗen Suna |
Masu hidimar al’umma kyauta (‘Yan ganin dama) |
‘Yan alfarma waɗanda ba su bin layi ko ‘yan
cuwa-cuwar man fetur masu ba da cin hanci a sayar musu mai, ba tare da sun
tsaya layi ba ko kuma masu cin layi, sai dai su tsaya gefe idan an fara
shigar da abubuwan hawa sai su kutsa in sun sami kafa. |
|
3 |
Mân hánnúu[15] |
Harɗaɗɗen Suna |
Man gyaɗa |
Man cuwa-cuwa ko na
sata |
|
4 |
Másháaƙár ískàa[16] |
Harɗaɗɗen Suna |
Wuri ne ko kafa da
aka keɓe don wani abu ya riƙa zuƙar iska |
Fayib da ake haɗawa
da tankin mai na cikin ƙasa
don tanki ya riƙa
numfasawa musamman idan akwai mai a cikinsa, don gudun kada tanki ya fashe |
Jadawali na 3: Ƙirƙira ta Gamin-gambizar Kalmomin Asali da na Aro
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jákkwátàa (jar kwata) |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Robar maganin ƙwari mai launin ja |
|
2 |
Jùuyèn gáayèe[17] |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Baƙin mai da wani ya
juye wanda bai gama aiki ba |
|
3 |
Gárwár gáayèe |
Harɗaɗɗen Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Babbar robar yagot
mai mariƙi
ko hannu |
Jadawali na 4: Ƙirƙira Kalma Wadda Sam
Babu Ita a Hausa
|
Lamba |
Kalma |
Ajin Kalma |
Ma’ana ta Asali |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Róojà |
Suna |
Babu dunƙulalliyar ma’ana ta asali |
Cin hanci da ‘yan
cuwa-cuwar fetur ke ba ‘yan gidan mai kafin a sayar musu da man fetur |
Idan aka lura da dukan waɗannan misalan, za a ga sun samu ne ta
hanyar ƙirƙirar daga kalmomin asali, da ƙirƙira ta fasahar gamin gambizar kalmar
asali da ta aro,[18] da kuma ƙirƙira kalma wadda sam babu ita a wani
harshe. Ƙirƙira irin waɗannan kalmomi na bunƙasa rumbun kalmomin harshe. Duba da yadda ake daɗa samun masu sayar da man fetur da baƙin mai na ƙirƙira sababbin
ma’anoni, musamman waɗanda suka shafi yanayin aiwatar da
kasuwancinsu ko rayuwarsu ta yau da kullum. A wasu lokuta, ‘yan
kasuwar sukan cusa sabbin ma’anonin da suka samar a cikin harshe. Bayan
wani ƙanƙanin lokaci, sai a
tarar sun saje da sauran ma’anonin Hausa na asali.[19]
4.3 Kalmomin da suka Shafi Aro
A wannan sashe, an ga
yadda masu sayar da man fetur da baƙin mai
suka ɗauko kalmomi daga harshen Ingilishi da
na Yarbanci. Su mayar da
su na Hausa bayan an yi musu kwaskwarima, don su dace da tsarin Hausa. A
taƙaice, sukan Hausantar
da baƙin
kalmomin da suka aro ne don samun kafar sadarwa a tsakaninsu.
Jadawali na 5: Kalmomin
Aro
|
Lamba |
Kalma |
Asalin Kalma |
Sabuwar Ma’ana |
|
1 |
Jóokò (Jooko)[20] |
Kalmar aro ce daga Yarbanci |
Tsaiko cikin layin
lodin mai ko lalacewar mota kan hanyar dawowa |
|
2 |
Dìríilìn (Drilling) |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Sauran man fetur da
ke ragewa bayan an sauke mai a gidan mai. Ana yi masa kirari da ‘dirilin na yaron mota’ |
|
3 |
Míshìn gálàn (Measurement
galoon) |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Auna mitar bayar da mai ko ta inji na mai |
|
4 |
One-five (1,500) |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar |
|
5 |
Áftáasêl (Aftersale)[21] |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Sai an sai da mai sannan a biya mai man fetur |
|
6 |
Màanúwâl kóó kwàmfúutàa (Manual/computer)[22] |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Mitar auna abin da aka sayar a injimin sayar da mai, kuma tana iya
lissafin lita miliyan, wato daƙiƙa bakwai na lamba. |
|
7 |
Hâf (half) gáayèe[23] |
Kalmar aro ce daga Ingilishi |
Robar yagot mai
biye wa garwar gaye |
|
8 |
Ólóojì (awon mai) |
Kalmar aro ce daga Yarbanci |
Awon man tanka
kafin a zuba a cikin ramin ajiya na ƙasa[24] |
Daga waɗannan misalai an ga yadda ‘yan
wannan rukunin suke Hausantar da kalmomin aro, ta hanyar yi wa kalmomin kwaskwarimar da za ta sa su dace
da tsarin furucin Hausa. Daga nan sai su ba su sababbin ma’anoni da suka bambanta da na
asalinsu. Abin ban sha’awa shi ne, yadda baƙin kalmomin suka saje da na asali wani
lokaci akan kasa bambanta su. Kenan, wannan hanyar sarrafa kalmomin aro fitatta
ce kuma madoga ga harshe, musamman inda aka kasa nemo madadin sabuwar kalma
daga cikin na asali da ake da su a harshe. A ƙarshe, aro hanya ce mafi sauƙi da harsuna suke faɗaɗa rumbun
kalmominsu, bayan an samu hulɗa da cuɗanya tsakanin harsuna daban-daban. Kamar dai yadda masu sayar da man fetur da baƙin suke amfani da su a zantukansu na
yau da kullum.
5.0 Sakamakon Bincike
Wannan takarda ta gano cewa, Hausar masu sayar da man fetur da baƙin mai (sabuwar Hausar rukunin jama’a)
tana wanzuwa a garin Sakkwato. Masu wannan rukunin sana’a suna da wata hanyar
sadarwa a tsakaninsu, wadda ta bambanta da Hausar gama-gari ta fuskar kalmomi.
Yanakin kalmomin da suke amfnai da su da kuma salon sarrafa Hausar sun kasance
na musamman. Hakan ya sa ba kowa ne yake iya fahimtar Hausar ba.
Yayin gudanar da wannan bincike, an fahimci cewa ‘yan wannan rukuni suna
amfani da hanyoyi daban-daban da suke ba su damar samar da ma’anoni na musamman
ga kalmomi. Daga ciki akwai dabarar faɗaɗa ma’anar kalmomin Hausa na asali. Hakan yana ba su damar fitar da sabuwar
ma’ana daga cikin ire-iren waɗannan kalmomin waɗanda asali suna da ma’anonin da aka san su da su. Haka kuma, sukan sarrafa
kalmomin aro tare da ƙirƙira sababbin
kalmomi a cikin zantukansu na yau da kullum.
Bugu da ƙari, takardar ta gano ‘yan kasuwar suna amfani da dabarar ɓoye wasu ma’anoni, domin saye da ɓatar da bami. Wannan salo yana taimaka musu wajen sakaya haƙiƙanin ma’anonin zantukan da suke yi ga wanda ba ɗan rukuninsu ba. Sau da dama sukan sirranta maganganunsu ne domin ƙoƙarin samun riba mai yawa da sakaya lissafin kuɗi a cinikayyarsu.
6.0 Kammalawa
Daga abin da ya gabata a cikin wannan takarda, a fili yake cewa wannan
rukuni na ‘yan kasuwa suna amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi da suka shafi yanayin
kasuwanci. Sukan yi hakan musamman don tafiyar da hankulan masu sayen kaya tare
da tattauna wasu batutuwa a tsakaninsu ba tare da kwastomomin sun fahimci abin
da suke tattaunawa ba. Sun al’adanci yin amfani da kalmomi sanannu wajen samar
da sababbin ma’anoni, amma ba lalle ne ma’anar ta zo daidai da ma’anar asali
ba. Salon su na samar da sababbin ma’anoni daga kalmomin aro yana nuni ga ƙwarewarsu a sarrafa harshe. Sarrafa
harshe cikin aiwatar da kasuwanci a tsakanin ‘yan kasuwa ya taimaka wajen
haifar da ƙirƙire-ƙirƙiren sababbin kalmomi da jumloli, waɗanda ke daɗa bayyana hali da yanayin ciniki a
muhallan kasuwanci.
Wannan yanayi na tsirar Hausar rukuni fage ne mai matuƙar muhimmanci ga Harshe. Yana da kyau
cibiyoyin bincike masu alaƙa da Hausa da kuma sashe-sashe na nazarin Hausa su haɗa kai domin cigaba da gudanar da bincike a wannan fannin. Bincike tare da
bin hanyoyin zamani na kundacewa da sarrafa wannan ilimi zai taimaka wajen bunƙasa harshen, musamman yanzu da duniyar
kimiyyar harshe take komawa kan ƙirƙirarriyar basira
(AI).
Manazarta
Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Ahmadu Bello University Press Limited.
Fagge, U.U. (2004). Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni.
Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Harris, Z.S. (1952). ‘Discourse Analysis’ In Language,
V. 28, 1-30.
Isah, F.H. (2018). A Sociolinguistic Analysis of The Jargons
Used by Town Service Tricyclists (A-daidaita-sahu) in The Kano Metropolis.
Unpublished M.A Dissertation. Department of Liguistics. Bayero University, Kano.
Mode, A. (2024).
Nazarin Hausar ‘yan Koli a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Sani, A-U. & Adamu,
S. (2023). Daga Hausar Rukuni Zuwa Ɓoyayyiyar Al’ada: Keɓaɓɓen Nazari a Kan
Hausar Telolin Garin Gusau. Tasambo Journal of Language, Literature,
and Culture, (2)2, 115-123.
www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.013.
Sharu, Y. (2023). Hausar ‘yan Agwagwa-da-buje a Garin
Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Umar, M.M. (2019). Nazarin Hausar Wasu Rukunan ‘Yankasuwa a
Garin Sakkwato. Kundin Digiri Na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Jami’ar Usamanu Danfodiyo, Sakkwato.
Yusuf M.A. (2002). The Development of Hausa Neologism: The Role
of Urban Spaces. In Bichi, A.Y et al (eds). Studies
in Hausa Language, Literature And Culture. The Fifth Hausa International
Conference. Kano: Benchmark Publishers Limited. Page 105-113.
Zailani, A.A. (2019). A Study of Communication Strategies in
Hausa Request Act. Unpublished Ph.D Thesis. Department of Linguistics and
Foreign Languages. Bayero University, Kano.
RATAYE
MUTANEN DA AKA ZANTA DA SU
|
S/N |
Suna |
Shekaru |
Muhallin da aka
Tattauna |
Kwanan Wata |
|
1 |
Malami man Ada |
55 |
Gidan man ada titin
Kalambaina, Wamakko, Sakkwato. |
01/10/2024 |
|
2 |
Alh. Basiru Babawo |
44 |
Mai sayar da baƙin mai a bakin
gidan man Man Ada titin Kalambaina, Wamakko, Sakkwato |
05/10/2024 |
|
3 |
Nasiru Malami |
42 |
Mai sayar da man
fetur a hannun-riga da gidan man NNPC mega station kusa da
makarantar FGC, Sakkwato |
06/10/2024 |
|
4 |
Mustapha Dogon-daji |
33 |
Mai sayar da baƙin mai a gidan dare
bakin rawun na gidan ashana western bye-pass, Sakkwato ta Kudu,
Sakkwato |
21/10/2024 |
|
5 |
Ashiru Dabagin Arɗo |
24 |
Mai sayar da baƙin mai da fetur Dange-shuni |
18/11/2024 |
|
6 |
Mal. Ahmad Zaruku |
64 |
Gidan man
Bashariyya Global Resourses, Sakkwato ta Arewa |
25/12/2024 |
|
7 |
Bashar Yusuf
(police) |
41 |
Gidan man A.A Rano Nig.
Ltd. Rawun na gidan Man Ada, Sakkwato |
15/01/2025 |
|
8 |
Dogo Mai Gas |
48 |
Gidan man Altine
Muhammad Ƙaura
titin Kalambaina, Sakkwato |
16/01/2025 |
|
9 |
Umar Faruk (yellow) |
40 |
Mai sayar da baƙin mai da fetur Wamakko, Sakkwato |
07/02/2025 |
|
10 |
Bashar Ibrahim Maigayya |
35 |
Shiyar Arkilla Federal Low Cost kusa da ofishin NDLEA |
09/02/2025 |
[1] Masu sayar da man fetur iri biyu ne:
akwai ‘yan kasuwa masu sayar da mai a gidajen mai, akwai kuma masu sayar da mai
a gefen tituna a cikin jarka ko garwa. Fagge (2004:126-127) ya kira su ‘yan cuwa-cuwar man fetur. A wasu wurare ana kiran su da ‘yan bumburutu ko kuma ‘yan
bulakmaket. A hukumance, suna sayar da mai ba bisa ƙa’ida ba. A
wasu lokutan baya, har kamen masu sayar da mai a kan hanya ake yi.
[2] Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, “Ƙamusun Hausa” Ahmadu Bello University Press Limited, Kano,
2006, shafi na 140.
[3] Gidan mai wuri ne na hadahadar
mutane masu zuwa don saya wa abubuwa hawa mai da injunan haska wutar lantarki.
[4] Hukuma
ce wadda ke da alhakin sa ido kan fice da shigen ma’adinan da ake haƙowa a cikin Nijeriya. Ayyukan da
aka ɗora
mata sun haɗa
da: Sa ido ga yadda ake gudanar da ha}ar mai da samar da rijiyoyin mai da fitar
da ɗanyen
mai a ƙasashen
waje da wuraren tace ɗanyen
mai da depot na ajiyar mai da gidajen mai da sauran wuraren da ake ajiye mai ko
sayar da shi, da bututun da ke ɗauko ɗanyen
mai da gas da sauran ma’adinnan mai. Haka kuma, hukumar na tabbatar da
cewa, duk kamfunnan mai sun mallaki lasisi da gudanar da ayyukansu cikin tsabta
da ɗaukar
matakan kiyaye hatsarin gobara da bin doka da oda, musamman abin da ya shafi
farashi da cikar lita da kuma biyan haya ko haraji ga gwamnati kamar yadda ya
dace.
[5] Ana ganin sunan baƙin mai ya samo
asali ne daga launin da man na juye ke sauyawa idan ya gama aiki.
[6] Don ƙarin bayani sai a duba aikin,
Umar, Muhammad Mustapha, “Nazarin Hausar wasu Rukunan ‘Yan Kasuwa a Garin
Sakkwato” Kundin Digiri na Uku. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato,
2019, shafi na 38-59.
[7] Fifiƙewa
da ba da himma wajen ƙoƙarin samun wani abu ta hanyar cuta.
[8] Masu sayar da mai a gefen hanya
cikin jarkuna su ne, irin waɗannan matasa.
[9] Wasu suna kiran ta tiyo ko roba
ko hwanho ko kuma nozzle, musamman ganin irin yadda take aikin zuƙo mai.
[10] Man fetur wanda ake haƙowa a Nijeriya shi launinsa ke da kama da ja-ja-ja kamar yadda Dogo na
gidan man Alh. Altine
Muhammad Kaura ya shaida mini.
[11] An bayar da ma’anar roja a sashen 4.2.
[12] Amma a injunan man fetur na shekarun
baya masu kama da tuƙa-tuƙa ɗigo goma shi ne lita guda, kafin
bayyanar injunan zamani
masu amfani da digital.
[13]Gidajen mai masu karkatar da man fetur sukan yi amfani da
tankokinsu na ɗaukar mai waɗanda ba a
rubuta musu sunan kamfani a jikinsu ba, don kar hukuma ta gane su, musamman a
lokutan da ake fuskantar ƙarancin man fetur.
[14] Ƙungiyoyin sa-kai ko kuma
ƙungiyoyi masu zaman kansu.
[15] Sayen man fetur ko gas ta bayan
fage daga hannun direba ko yaransa ko wasu ma’aikatan kamfani ko kuma mutane
masu harka da kayan sata (ɗanyun kaya a Hausar wasu ‘yan kasuwa) ko kayan
rashin gaskiya.
[16] Tankin mai na ajiyar mai a cikin
ƙasa yana da marfi, wanda a jikinsa ake haɗa fayib mai zuƙar mai daga tanki
zuwa ga injin na sai da mai, da fayib na mashaƙar iska wanda ake kafewa a tsaye
tare da sunkuyar da kansa don rana ruwa shi cikinsa, da kuma kusurwar da ake
buɗewa a duk lokacin da za a zuba mai ko awon sa.
[17] Juyen matashi ɗan gayu.
[18] Wannan rukuni na ‘yan kasuwa ya yi amfani da wannan hanya
ta ƙirƙira wajen bai wa mazubi ko abin awon man fetur suna, kamar yadda misalan
suka nuna. Wani lokaci ma, ana amfani da hanyar fassara kalmar aro (loan
translation). A nan akan yi amfani da kalmomi ne a
fassara ainihin suna, aiki ko ma’ana ta baƙon
abu a harshen aro. Ga misali, ana amfani da dafa-duka (jalaf) domin wakiltar
motar nan Peugeot 504 (station wagon).
[19] Don ƙarin bayani a dubi, Yusuf (2002) ya bayyana
yadda ƙirƙirarrun kalmomi kan rikiɗe su koma karɓaɓɓun kalmomi bayan an baddala su cikin
harshe, kuma sannu a hankali za su yaɗu a riƙa
amfani da su kamar sauran kalmomin harshe.
[20] Ana cewa wane ya yi joko da yawa,
wato ya jima bai dawo ba, ko kuma a ce, direba ya hwaɗa joko.
[21] Ana
amfani da wannan salo ne don a tabbatar da man da aka kawo ya cika kuma mita da
difin na gidan mai na aiki daidai.
[22] Floor measurement shi ne ainihin sunan mitar a
harshen Ingilishi. Ita kuma kalmar kwamfuta wasu na fassara ta da
na’ura mai ƙwaƙwalwa.
[23] Akwai masu kiran ta ‘Yákkùnúu.
[24] Ana wannan awon ne
idan ana shakkun tankin mota ko wanda ya kawo mai, ko kuma don tabbatarwa
kawai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.