Takardar da aka Gabatar a Taron Makon Hausa wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Northwest Kano ta Shirya, wanda aka Gabatar a babban Ɗakin Taro na ‘Yanganau da ke Farfajiyar Jami’ar a Ranar Alhamis 29/01/2026
TUN KAFIN A HAIFI UWAR MAI SABULU BALBELA TAKE DA FARINTA: NAZARIN HANYOYIN ADANA KAYAYYAKIN HAUSAWA NA
GARGAJIYA
Daga
Sashen Koyar Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Northwest, Kano
magaya@nwu.edu.ng /magajiahmadgaya@gmail.com
08066009039
Tsakure
Al’ummar Hausawa, mutane
ne waɗanda tun fil’azal suna
da hikimominsu da suka gada tun kaka da kakanni, waɗanda suke aiwatar da su
har yau. Suna amfani da fasahohinsu da hikimimominsu da basirarsu ta hanyar
sarrafa albarkatun da suke kewaye da muhallansu, waɗanda suka haɗa da adana kayayyakin
Hausawa na gargajiya domin su samar da kayayyakin amfanin kansu. Manufar wannan
takarda ita ce bayyana wasu hanyoyin adana kayayyakin gargajiya wanɗanda suke amfani da su
tun kafin haɗuwar su da baƙin al’ummu. An yi amfani da hanyoyin gudanar
da bincike, waɗanda suka haɗa da tattaunawa da gani da ido da karantawa
daga wasu rubutattun bayanai. An ɗora wannan bincike ne bisa ra’in adana al’adu da cigaban
al’umma wato (Cultural Sustainability Theory), shi ya fi dacewa da wannan
bincike. Gusau (2015: 55) ya kira makarantar da ta fito da wannan ra’i da suna
‘‘mazahabar adana al’adu” Shi kuma Sha’aibu (2013: 78), ya kira makarantar da
ke da’awar wannan ra’i na adana al’adu da suna “mazahabar Muhafaza”. Sakamakon takardar
ya nuna cewa, Hausawa suna da hanyoyin adana kayayyaki na gargajiya tun kafin
haɗuwarsu da baƙin al’ummu kuma suna
amfani da su wajen adanawa haɗi da taskacewa.
Muhimman Kalmomi: Adana, Kayayyaki, Hausawa,
Gargajiya
1.1 Gabatarwa
Wannan takarda za ta yi duba ne a kan kayayyakin da al’ummar
ƙasar Hausa
suke amfani da su wajen adanawa. Waɗannan kayayyakin gargajiya da za a yi tsokaci a kansu,
har gobe da su suke amfani wajen aiwatar da ajiye-ajiye da aikace-aikace. Akwai
tarin fasahohi da hikimomi da suka shafi yadda Hausawa suka samar da
kayayyakin, musamman in aka yi la’akari da yadda suke taimaka musu wajen
gudanar da adana kayayyakinsu cikin sauƙi, ba tare da samu matsala ba. Haka kuma, an
nazarci yadda masu sana’ar suke amfani da su kuma an kawo bayanin yadda suke
samar da su da kuma nau’o’in aikace-aikacen da ake yi da su. Hausawa suna
inganta wasu kayayyakin domin su dace da buƙatun mutane da kuma wannan zamanin da muke
ciki. Hakan zai taimaka wajen yin riƙo da tsofaffin kayayyakin domin maimakon a yi
wasarere da su gaba ɗaya, akwai buƙatar ƙara inganta
su don tafiya da zamani.
1.2 Manufar Gudanar da
Bincike
Manufar wannan takarda ita ce, bayyana wasu hanyoyin da
ake adana kayayyakin gargajiya wanɗanda al’ummar Hausawa suke amfani da su wajen yin
ajiye-ajiye ko taskacewa ko domin gudun salwanta ko kuma domin tarihi da
makamantansu. Wata manufar kuma ita ce, bayyana ko fayyace wasu tsofaffin
kayayyakin da ake adanawa haɗi da amfani da suke samarwa ga al’umma. Wannan takarda za
kuma ta bayyana alfanun da kayayyakin suke da shi wajen adanawa da kuma jan hankalin
masu bincike wajen nazarinsu don ceto su daga neman gushewa.
1.3 Ra’in Bincike
Wannan bincike an ɗora shi ne a kan Ra’in Haƙiƙa wannan bincike ya bibiyi ra’o’in binciken
al’adun Hausawa daban –daban don tantance wanda ya dace da wannan bincike: inda aka gano cewa ra’in adana al’adu da
cigaban al’umma wato (Cultural Sustainability Theory), shi ya fi dacewa da
wannan bincike. Gusau (2015: 55) ya kira makarantar da ta fito da wannan ra’i
da suna “mazahabar adana al’adu”. Shi kuma Sha’aibu (2013: 78), ya kira
makarantar da ke da’awar wannan ra’i na adana al’adu da suna “mazahabar
Muhafaza”.
1. 3. 1 Salsalar Ra’i
Wannan ra’i ya samo asali ne ta hanyar gudummawar masana
da hukukmomi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, amma duk da haka mutum guda ne ya fi
shahara wajen inganta wannan ra’i John Hawkes ana yawan ɗaukarsa a matsayin jagoran wannan ra’i.
1. 3. 2 Mabiya Ra’i
Ko da yake John Hawkes ne ya fi shahara wajen
gabatar da wannan ra’i, amma akwai masana da hukumomi da dama da suka rungumi
kuma suka bunƙasa wannan ra’in na
adana al’ada. Daga cikin su akwai:
• Unesco da UNDP (United Nations Deɓelopment Programme)
• Daɓid
Throsby,
• Jown Hawkes Australian Coucil for the art
• Katrilna Soini & Inger Birkeland
• Nancy Duɗbury
• Keith Nurse
• Graham Fairclough
1. 3. 3 Ayyukan da aka Ɗora Ra’in
Akwai bincike – bincike da dama da aka gudanar
a baya waɗanda suka yi amfani da wannan ra’i na adana
al’ada daga cikin su akwai John Hawkers (2001) ya yi littafi mai suna The Fourth Pillar of sustainability: Cultures' Essential Role in Public Planning.
Ya jaddada cewa dole ne a haɗa al’adu cikin
tsare tsaren cigaba.
Sannan da Daɓid
Throsby (2008-2010), ya gabatarda linking
cultural and ecological sustainability. The economics of cultural policy ma’ana
dangantakar da ke tsakanin al’adu, tattalin arziki da ɗorewar su. Sannan kuma akwai binciken da Unesco ta tallafa a shekara ta (2003-2015), mai taken al’adun
gargajiya marasa ganuwa (Intengible cultural heritage), da ilimin gargajiya na
asali, sai kuma harsuna da ke fuskantar shuɗewa.
Haka kuma akwai binciken da aka gabatar a
jami’o’in gida a kan al’adun Hausawa, daga cikinsu akwai:
• Aminu Lawan, ya yi bincike a kan “Ɗorewar al’adun Hausawa a zamanin zamani”. jami’ar Bayero, Kano
• Zainab Sadiƙ, ta yi bincike a kan “Rawar bukukuwan gargajiya wajen raya al’adu”. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto
• Abdullahi Musa. ya yi bincike mai taken
“Tasirin zamani da adabin baka na Hausa”. Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya
• Hadiza Bello, ta yi bincike mai taken
‘‘Rawar ‘yammata wajen kare da ɗorewar al’adu a
arewacin Najeriya”. Jami’ar Ilorin
• Sani Ibrahim, ya yi bincike a kan
“Gudummuwar sarautun gargajiya wajen ɗorewar
al’adu”. Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua
1. 3. 4 Dangantakar Ra’i da Nazari
Bayanan cikin wannan ra’i suna da dangantaka
ta kai tsaye da wannan nazari, sannan za su zamo wani dandamali da wannan
bincike zai taka ya hau har wannan bincike ya samu kammaluwa. Saboda ra’in yana
bayani ne ta yadda za a tseratar da al’adu daga salwanta, wanda wannan shi ne ƙudirin wannan bincike da za a gudanar.
2. 0 Hanyoyin
Gudanar da Bincike
Kamar yadda aka sani babu aikin da za a yi ba
tare da bin wasu hanyoyi na gudanar da shi ba. Fayyace waɗannan hanyoyi a cikin bincike irin wannan
yana da matuƙar muhimmanci, domin yana taimakawa wajen tabbatar da
sahihancin bayanan da aka kawo a cikin aiki. Ba a bar wannan binciken a baya ba
ta wannan fuska, domin shi ma an yi amfani da wasu hanyoyi wajen tattara
bayanan da suka taimaka wajen aiwatar da shi. Daga cikin hanyoyin, akwai
tattaunawa da domin samun nasarar
wannan bincike, an yi la’akari da matsayi da kuma shekaru. Mutanen da aka
tattauna da su sun haɗa da tsofaffi maza
da mata waɗanda suka taimaka wajen fito da
wasu muhimman bayanai na waɗannan kayayyakin
aiki. An kuma kai ziyarar gani da ido, inda kai tsaye aka ziyarci masu gabatar
da ayyukan kaba da maginan ƙasa da fatu kuma aka tabbatar da wasu bayanan da aka samo daga gare su. Baya
ga waɗannan hanyoyin da aka gabatar,
an kuma tuntuɓi masana na sana’o’in
gargajiyar Hausawa, kuma an bibiyi rubuce-rubucen magabata inda aka samu tarin
bayanai da suka taimaka wajen rubuta wannan takarda.
3. 0 Nazarin
Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa na Gargajiya
Akwai hanyoyin da
ake amfani da su wajen adana kayayyakin Hausawa na gargajiya da iri-iri, amma wannan takarda ta kawo wasu daga ciki,
tare da bayaninsu kamar yadda suke a gargajiyar Bahaushe.
3. 1 Rumbu
Rumbu shi ne, “Ɗakin da ake ginawa da ƙasa ko karen dawa
ko gamba don adana hatsi” (Sa’id, B. da wasu 2006). Ana saƙa rumbu da ciyawar gamba wadda take da tsawo da ƙwari a kan ɗora ta bisa dirkoki ko kuma ƙaton duwatsu ko kuma a kan gungume saboda ƙwari ko ɓeraye ko ruwa wasu lokutan kuma saboda
danshi lema. A kan ɗora masa boto don zuba amfanin gona musamman saboda adanawa.
Ana adana gero ko dawa ko gyaɗa ko wake ko maiwa inda za a ɗauro cikin zangarniya.
Idan ana buƙata sai a tsakura ko kuma a ɗebo a zuba
zanganniya a makayin ƙwarya domin biyan buƙatar yau da kullum.
3. 2 Randa
Wannan wani mazubi ne da ake ajiye ruwa
a cikinta. Magina ƙasa sune suke gina randa. Yayin da za a
gina ta sai a samo taɓo ƙasa ta jangargari haɗi da ruwa a cakuɗa, a hankali sai a
fitar da surarta, ana bi ana gyarawa har dai a samar da ita. Sa’id da wasu,
(2006) sun bayyana ta da cewa, wata ƙatuwar tukunya ce
da galibi ake zuba ruwa a cikinta, ko kuma ta zamanto taskar ajiye kuɗi. Sannan marina
suna amfani da ita a matsayin rijiyar karofi ta rini. Don haka, randa ta daɗe da kasancewa ɗaya daga cikin kayayyakin
da Hausawa suke amfani da ita wajen adanawa da taskacewa domin abubuwan da za
su iya tasowa haɗi da abubuwan yau da kullum.
3. 3 Ruzu
Wata irin ƙaramar jaka ce saƙaƙƙiya. Ruzu wata jaka ce wadda ake saƙata da kaba ko kuma zare. Tana da ɗan faɗi da tsayi sannan tana
da maratayi da ake rataya shi a kafaɗa. Mafarauta suna amfani da ita wajen
saka namun daji idan sun kamo a ciki, yayin da suka fita farauta, ko sharani ko
ƙuloto. Sannan idan suka dawo gida sukan ajiye naman da
suka samo a cikinsa wato Ruzu (Tattaunawa da Baba Sayyadi).
3. 4 Taskira
Ana saka ta don aikin kaɗin zare da abawa
tana da fadi kamar faranti ƙarami ko plate na zamani. Sai a shimfiɗa mata fatu ribi-ribi kamar talatin ko
ashirin. Maiɗakin kan ajiye wasu abubuwa masu muhimmanci da suka haɗa da kuɗi da ‘yan kunnaye
da sarƙoƙi da sauransu ba
tare da wani ya gane ƙarƙashin da aka zuba ba.
Ana yi wa taskira kirari, “taskira asirin mai ɗaki”. Don haka za a iya cewa, taskira
wani ɗan ƙaramin Kwando-kwando ne da aka saƙa da kaba wanda mata ke amfani da shi suna zuba auduga da
mazari da alli don yin kaɗi (Sa’id da wasu 2006).
3. 5 Gajiran/Gajirami
Wannan shi ma wata ma’ajiya ce ta
gargajiya wadda Hausawa suke ginawa tare da jera su a ɗaki. Akan yi rami
matsakaici kamar yadda tukunya ƙarama za ta shiga cikin ramin a layanta
su a bango da ƙasa, sai kuma a binne amma bakinsu yana
kallon sama. A kan ajiye wake ko gyaɗa ko riguna, ko zannuwa ko hatsi da
sauransu, wasu ma har kuɗaɗe suke a jiyewa (Tattaunawa da Maisalati Durɓindai).
3. 6 Adudu
Adudu wata fasahar Hausawa ce wanda ake
sarrafa kaba yayin da da ake saƙa ta da gazari da kaba domin ajiye
sutura a rufe don kada ƙwari su lalata su. Kuma ta kasance ɗaya daga cikin
kayayyakin da Hausawa suke amfani da shi musamman wajen ajiye ko adana wasu
haja tasu domin kaucewa daga salwanta ko kuma lalacewa. Sa’id da wasu (2006)
sun bayyana ta a matsayin wata ma’ajiyar sutura mai zurfi da kuma murfi wanda
ake yi da kaba.
3. 7 Lefe
Mazaubi ne da ake saƙawa da kaba don kaɗar auduga wadda za a kaɗa zare. Yayin da
Sa’id da wasu (2006) suka ƙara da cewa, wani makai da ake saƙawa da kaba don saka ko ajiye kayan kaɗi ko zuba kayan
aure. Haku kuma, wannan ya sanya Hausawa suke zuba sutura a ciki don kai toshi
gidan amaya kafin a yi aure kuma ake kiransa da kayan lefe. Domin cikin lefen
kaɗai ake saka waɗannan kayan.
3. 8 Kuratandu
Kuratandu wani ɗan ƙaramin tandu da ake zuba kwalli a ciki. Yayin da ake so a
samar da shi akan sami fata ta zamo sarrafaffiyar akuya ko kuma ta tinkiya ko
kuma dai ta wata ƙaramar dabbar da ake sarrafawa domin
zamar da ita abin da za a saka tozali, sannan kuma a saka matashi haɗi da murfi domin gudun
kada ya zube ko kuma ya salwanta. Mazubi ne na tozali da ake sanyawa a ido.
3. 9 Akurki
Akurki ana yinsa ne da itace geza, za a
zubar da ganyayyakin dake maƙale a jikin itacen, sai kuma a tsaga
itacen gezar gida biyu ko uku a tsaye. Ana saƙa kamar yadda ake
kife kwarya, ana yi masa ƙofa da ƙasa, yayin da aka
kamala sai samo kashin shanu sai a mamaye ka shin ciki da waje. Yana daga cikin
kayyakin Hausawa na gargajiya da ake amfani da shi musamman wajen ajiye da kuma
adana tsuntsaye nau’in kaji ko agwagi da zabbi da agwagi yayin da aka saka su a
ciki ko kuma suka shiga da daddadare sai a saka murfi a rufe wannan ƙofar ta yadda wani abin cutarwa bazai sami damar cutar da
su ba.
3. 10 Cali
Wannan wani abu ne raga-raga wanda ake
saka tuluna ko ƙore da makamantansu wasu lokutan akan ɗorawa jaki. Sannan
kuma a wasu cali kan kankasance mazubi ne da zuba kayan gona kamar albasa ko
yalo wadda ake yinsa da igiya yana da kofofi don kayan su sha iska. Ana amfani
da cali a ɗora kan jaki ko takarkari don ɗaukar kaya.
3. 11 Taiki
Mazubi ne na jemamiyar fata wadda ake ɗinkawa wadda za a ɗura tsabar gero ko
dawa ko shinkafa wadda zai kwanta kan jaki ko takarkari don kai kayan amfanin gona
kasuwa ko kuma wurin da ake da buƙata. Akan zuba
tsabar gero ko dawa ko rimi da makamantansu.
3. 12 Kwatanniya
Kwatanniya wani matsakaicin mazubi ne
wanda masu sana’ar ginin ƙasa suke samarwa. Ana samun taɓo da jangaggari da
ruwa sai a haɗa a kwaɓa, sai kuma samo wata tsohuwar
kwatanniyar a mamaye bayanta ana bi ana bugawa kaɗa-kaɗan har ta zama anyi kwafin ta farko. Sai
a bi a gaygyara har ta zama abin da ake so ta zama. Ana ajiye ruwa musamman
idan za a yi wanka na yara ko kuma manya. Haka kuma ana amfani da ita wajen
wanki ko wankin kalwa, sannan ana ajiyewa dabbobi kamar awakai da tunkiyoyi
ruwan da zasu sha idan sun dawo gida daga kiwo. Da sauran wasu ƙanana kayayyakin da ake ajiye-ajiye.
3. 13 Akushi
Shi ma kamar sauran ya kasance kwanon
da ake cin abinci a gargajiyance, sai dai shi ana sassaƙashi daga itace gungume, ana ajiya a cikinsa kamar tuwo,
miya sannan kuma shi ne ake cin abinci a cikinsa. Don haka akushi ya kasance
abin amfanin na yau da kullum da ake zuba abinci ko kuma ajiye shi.
3. 14 Ƙwarya
Ana samun ƙwarya daga ɗan duma yayin da ya zama babba ya riƙa. Bayan an ɗebe kayayyakin amfanin gona, sai masu
fafar ƙwarya su bi su ɗebo shi sai su raba
shi biyu, inda za su fitar da totuwar. Daga nan kuma sai su fafe ciki sarai da
haka har ta bushe, sai kuma a sake fafewa ta yadda da za a fitar da dukkan wata
totuwa. Ita ma ana amfani da ita wajen ajiye kayyayaki masu yawa a
gargajiyance, yayin da ake ajiye dawa ko gero ko wake ko deɓo hatsi daga
rumbu, sannan kuma ana amfani da ita wajen shiƙar hatsi idan an yi
casa.
3. 15 Tukunya/Talle
Maginan gargajiya na Hausawa sune suke
gina tukunyar ƙasa kuma tana daga cikin kayayyakin da
ake amfani da su wajen adana ko ajiye kayayyaki wanda Hausawa suke saka
suturarsu ko kuɗi ko ko kuma abinci domin gudun salwanta ko ɓata. Kamar yadda,
Sa’id da wasu (2006). Suka tabbatar cewa, makai da aka gina da laka aka gasa
don dafa abinci ko zuba ruwa ko ajiyewa wani lokaci ma da adanawa. Shi kuwa Talle,
wata ‘ya ƙaramar tukunya ce da ake ɗafa miya a cikinta.
Ya kasance kamar tukunya sai dai, bai kai ga tukunya girma ba, da shi ake
amfani wajen yin miyar abinci. Yayin da aka gama miya kuma a kan ajiye miyar a
ciki saboda kada ta lalace ko kuma ta salwanta wasu lokutan ma a kan adana
saboda kada akuya ko yaro ko wata dabbar ta zubar da ita.
3. 16 Asusu
Wannan ya kasance wurin ajiyar kuɗi da ake ginawa a
jikin bango ko ɗan kurtun yumɓu mai ƙaramar tsaga, ko
gwangwani da aka yi masa ‘yar tsaga. Asusu wata ma’ajiya ce da Hausawa suke
samarwa ta hanyar sarrafa ƙasa ta yumɓu haɗi da sauran
kayyayakin samar da shi. Ana yi masa ‘yar ƙofa kaɗan yadda hannu ba
zai iya shiga ba. Dalili kuwa shi ne, duk abinda aka zura a cikinsa ya shiga
kenan idan har ana da buƙata sai dai a fasa ko kuma a ɗauki lokaci mai
tsawo kafin wani abu ya fito. Daga samansa ana yi masa mariƙa ta ƙasa. Akan zuba kuɗi domin yin ajiya
(Tattaunawa da Mukhtar A. Isma’ila).
3. 17 Ragaya
Ita ma hanya ce da Hausawa suke amfani
da ita wajen ajiye tare da adana kayayyaki domin kada su salwanta ko kuma kada
sulale. Sa’id da wasu (2006) sun ce, ragaya ita ce maratayin ƙore ko kaya da ake ɗaurawa ko ajiye wani a jinkar ɗaki daga ciki,
wanda kuma ake saƙawa da tufkakkiyar kaba ko yawa. ” Ragaya
ita ce wadda ake saka ƙoƙo ko akwashi a
cikin yadda zata zama an sarrafa ta da kaba sannan a yi mata gida-gida ko kuma
hawa-hawa musamman domin ajiyar wani abu.
3. 18 Kula
Kula wata babbar butar ce ta ƙasa da ake zuba ruwan sha a ciki domin ya yi sanyi. Ta
kasance tana daga cikin jerin kayayyakin ajiyar Hausawa na gargajiya. Ana yin ta
da taɓo da jangargari da ruwa. Maginan tukwane da sauran
nau’o’in sarrafa ginin ƙasa ne suke samar da ita. Kula na iya
zama ƙarama sannan kuma akwai babba, ƙaramar ita ce, wadda ake ajiye ruwa a ciki, musamman
lokacin sanyi ko ɗari, a wasu lokutan a kan ɗora ta akan garwashin wuta, ruwan ya yi
ɗimi domin samun biyan buƙatar da ake so a
samu. Ita kuwa babbar kula, ana ajiye ruwa a ciki, sai dai ba kasafai ake
sakata a garwashin wuta ba, an fi ajiye ruwa a ciki ko buƙatar ruwan ka iya tasowa daga kowanne lokaci (Tattaunawa da
Muhammad Sani).
3. 19 Ƙaho
Ƙaho ya kasance wani abu ƙashi-ƙashi wanda yawanci guda biyu da yakan fito a kan dabba,
kamar saniya ko rago ko akuya ko barewa (Sa’id da wasu 2006). A Baushiyar
al’ada, Hausawa suna amfani da hanyoyin gargajiya musamman wajen ajiya a ciki, musamman
ƙahon rago ko kuma ƙahon wata dabbar
da ban, domin sukan yi ajiya a cikin sannan su rataya shi inda suke buƙata kamar a ƙofar gida ko a
tsakar gida a binne domin yin kafi ko kuma dai wani muhimmin al’amari ko kuma domin
neman kariya daga al’ajanu ko kuma ɓarayi da dai sauransu.
3. 20 Adada
Wannan wata rumfa ce wanda ake yin ta a
tsakar gidan Bahaushe. Ana yin ta da gwafanni da bunu ko ciyawa wasu lokutan
kuma akan haɗa da zana da igiya da sauransu. A kan ajiye kayayyaki
irin su fatar buhu ko kayayyakin aikin gona da suka haɗa da; magirbi,
sungumi, garma, fatanya, gatari, sannan kuma akan ajiye karbi da dai sauran kayyakin
da ake da buƙata a ajiye (Tattaunawa da Kawu Mu’azu).
3. 21 Batta
Wani ɗan kuttu ne na ƙirgi wanda ya ɗan ɗara girman kuratandu wanda ake zuba
taba gari a ciki (Sa’id da wasu 2006). Wannan yana ɗaya daga cikin
kayayyakin Hausawa da suke yin ajiya haɗi da adanawa domin kada su salwanta. Haka
kuma matan Hausawa sukan yi ajiyar kayan kwalliya da sauran wasu abubuwa
muhimmai kamar tozali ko gyatuma raɗau ko kuma aɗaɗa ko janbaki ko
hoda ko jar koya da makamantansu. Don haka Batta tana da siffa kamar haka, a kan
shirya da tsara ta kamar siffar adaka sai dai da katako ko kuma ita ce sai kuma
a lulluɓeta da fata wanda Dukawa wato masu sana’ar sarrafa fata sune
suke samar da ita (Tattaunawa da Malam Gambo).
3. 22 Angara
Kamar sauran kayyayin ajiyar Hausawa, angara
ta kasance wata ƙaramar jaka ce mai kama da zabira ta
wanzamai amma galibi maharba ne uka fi amfani da ita domin adana kayayyakin
harbinsu kamar’ya’yan datsi ko toka ko tsakuwa ko ashana da sauransu. Dukawa ne
suke samar da ita saboda ta kasance ta fatar kowacce dabba in dai ta kasance
mai faɗi (Tattaunawa da Malam Gambo).
3. 23 Akwatsa
Wani ɗan ƙaramin wuri ne da
ake samarwa mai kama da kanta, sai dai bai kai kanta girma ba. Wani lokaci ma
ana yin ta adaf da kofa daga cikin ɗaki ko kuma daga waje. Akan yi ajiyar
kayyayakin buƙata kamar su guntun man ƙuli ko ashana ko kuka ko manda ko kanwa ko gishiri ko barkono
da sauransu (Tattaunawa da Sa’idu Nakande).
3. 24 Bankaɗe
Ya zama daga cikin kayayyakin da
Hausawa suke yin ajiya domin adanawa sannan ya kasu gida-gida akwai bankaɗen tabarma da
bankaɗen gado da bankaɗen lefe da bankaɗen mataki da bankaɗen faifai da
sauransu. Hausawa sukan yi masa waƙa da cewa: “Bankaɗan lefe na ka zuba mini bani bari
sallah ta wuce ni” (Tattaunawa da Adamu Isyaku).
3. 25 Kuikuita
Wata hanya ce ta Hausawa da suke yin
ajiya a ciki kuma ana yin ta da kaba. Tana da siffar kuttu, sai dai ba ta kai
kuttu girma ba. Kuikuita tana ɗan zurfi kaɗan, tana da murfi,
sannan akan yi mata ‘yar mariƙa kamar yadda jaka take. Akan adana
kayan kwalliyar mata kamar ɗan kunnaye ko barima ko duwatsu ko murjani
ko sarƙa ko awarwaro, ko zobba ko tagulla ko azurfa
da sauransu (Tattaunawa da Maisalati Durɓunde).
3. 26 Salka
Wata sarrafaffiyar fata ce da mahauta kan
yi wa dabba fiɗar zugazugi, inda za su zare fatar ba tare da an yanka
taba, musamman daga wuya zuwa ƙasa. Yayin da su kuma Dukawa suke
jemeta wato su kawar da gashin da take ɗauke da shi, sai kuma su rina ta don ta
bayar da kalla. Sai kuma a ɗaure dukkanin ƙofofin ƙafar ko a ɗinke su domin kada
abin da aka ajiye ko adana su zube. A kan ajiye wasu muhimman abubuwa kamar
ruwa ko mai ko hatsi ko gari da sauransu. Sannan kuma a wasu lokuta matafiya ko
kuma fatake su kan yi jagami da ita, ko kuma su ɗora akan Jakuna ko Alfadarai (Tattaunawa
da Maisalati Durɓunde).
3. 27 Sanho
Shi ma yana daga cikin sahun kayayyakin
da ake yin ajiya ko kuma adana wasu muhimman abubuwa wanda al’umar Hausawa suke
amfani da shi a cikin al’amuransu na yau da kullum. Sanho wata saƙaƙƙiyar kaba ce da masu sana’ar saƙa kaba suke sarrafawa, yana da siffar saƙa irin takumkumi, amma ya kasance bashi da ƙofofi ko raga irin ta takumkumi, ya kasance haɗaɗɗiyar saƙa ce irin ta mangala. Akan ajiye kayayyakin amfani gona
kamar gero ko dawa ko alkama ko Dankali ko wake da sauransu (Tattaunawa da
Abdullahi Madaki).
4. 0 Kammalawa
Wannan takarda ta karkata akalarta ne a kan kayayyakinn
da ake amfani da su wajen adanawa ta hanyar gargajiya, inda aka kawo bayanansu
da kuma yadda Hausawa suke amfani da su a lokacin da buƙatar hakan
ta samu. Kayayyaki ne na gargajiya, kuma suna da inganci da sauƙin samuwa haɗi da sauƙin sarrafawa. Amfani da waɗannan kayayyaki ya haifarwa Hausawa da samuwar
hanyoyi masu yawan gaske wajen adana kayayyakinsu domin amfanin yau da kullum. Takardar
ta mayar da hankali kan kayyayaki da ake amfani da su wajen adanawa da kuma
bayyanawa masu nazari da ‘yan baya masu tasowa su sansu don kada su wofantar da
su.
4. 1 Sakamakon Bincike
Bayan kammala wannan takarda. Babu aiki mai manufa da za
a gudanar a kasa samun sakamakn da ya haifar. Daga cikin sakamakon da aka samu
bayan kammaluwar wannan maƙala, sun haɗa da yadda aikin ya gano waɗansu hanyoyi da Hausawa suka bi cikin hikima da fasaha
suka ƙirƙiri kayayyakin aikinsu waɗanda suka da ce, kuma suka yi daidai da yadda za su yi
amfani da su, ba tare da yi barazana ba.
Da farko, takarda ta gano cewa ta hanyar amfani
kayayyakin da ake yin ajiya ko kuma adanawa ake samar da wasu abubuwan da ke
taimakawa wajen taskacewa don gudun salwanta. Misali, kamar sanho da randa da
rami da makamantansu.
Haka kuma, takardar ta ƙara fito da sunayen wasu kayayyakin gargajiya
masu amfani waɗanda ake
samarwa, sannan kuma al’umma suke amfani da shi don gudun ɓacewarsu. Misali kamar kuikuito da salka da sanho
rumbu da sauransu.
Kazalika, takardar ta a gano cewa mutane masu sarrafa kayayyakin
adanawa ko ajiyewai suna bayar da gagarumar gudummuwa wajen kyautata al’adu da
kuma haɓaka tattalin
arziƙin ƙasa. Domin sakamakon amfani da su na samarda abubuwan
gargajiya don amfanin yau da kullum.
Bayan nan kuma, takardar ta lalubo waɗansu kayayyaki waɗanda a yau Hausawa sunayensu kawai suka sani
ko suke ji. Amma a ada suna ganinsu tare da amfani da su yadda ya kamata. Misalin
irin kayayyakin su ne irin su: zunguru
da akwatsa da tulu da sauransu.
Bayan da aka ƙare wannan takarda, an gano cewa har ma
gwamnati da sauran hukumomin gwamnati na sayen wasu kayayyakin da aka sarrafa kayayyakin
gargajiya suna adanawa a gidajen adana kayan tarihi na jihar Kano da sauran
jahohin ƙasar nan da nuna su a wajen taron baje koli da nuna su
musamman lokacin da ake nunin kayan amfanin gona da dai sauran tarurruka da
makamantansu.
4. 2 Shawarwari
Wannan takarda tana bayar da shawarwari ga wasu rukunnan
al’umma da ƙungiyoyin cikin al’ummar ƙasar Hausa kamar haka:
Da farko, ana bayar da shawara ga al’umma, musamman waɗanda suke amfani da waɗannan kayayyakin a cikin gonaki da gidaje da
muhalli baki ɗaya, da su
ci gaba da amfani da su. Dalili kuwa shi ne, rashin amfani da waɗannan kayayyaki za ya iya janyo sakaci da
lalaci da karya guiwar masu yin su wanda daga ƙarshe ma suna iya yin fatali da su baki ɗaya.
Haka kuma, ana bayar da shawara ga hukumomi da mahukunta,
musamman gidajen tarihi da gidajen sarauta da cibiyoyin koyar da al’adun
Hausawa da cibiyoyin ilimi na kwalejojin ilimi da jami’o’i na jihohi da na
tarayya da su riƙa ba masana da manazarta ƙwarin guiwa da goyon baya a duk lokacin da
suka je yin irin wannan bincike a wurarensu.
Kazalika, ana bayar da shawara ga ɗalibai, musamman matasa masu jini a jika da
su tashi tsaye, tsayin daka, su bada himma da ƙwazo wajen yin nazari da bincike dangane da
abin da ya shafi irin wannan ɓangare. Dalili kuwa ma fi yawancin ɗalibai sun karkata ne a kan jigo da salo da
sarrafa harshe. Abin nufi a nan shi ne, ya kamata mu fuskanci al’adunmu na
gargajiya kar mu guje su mu faɗa ga na wasu.
Bayan nan kuma, wannan takarda tana shawartar masana da
manazarta da su ƙara ba ɗalibai ƙwarin guiwa dangane da yin nazarce-nazarce waɗanda suka danganci irin waɗannan al’adu musamman amfani da kayayyakin da
ake adanawa, don ta yin haka ne za a gano waɗansu abubuwa da aka riga aka manta da su. Sannan a san waɗansu sabbi waɗanda ba a san da su ba. Amma hakan ba za ya yiwu ba har
sai idan an zurfafa a irin wannan fagen, sannan za a iya cimma wannan buri.
Wata shawarar ita ce ga gwamnati da masu hannu-da-shuni
da su tallafa wa masu irin waɗannan sana’o’i na sarrafa kayayyakin da ake amfani dasu a
riƙa ba su
tallafi na jari ko kayan aiki, za a samu ci gaban da ba a tunani.
Haka kuma, wata shawarar ga gwamnati, ita ce, ya kamata
gwamnati ta tabbatar da aiwatar da koyar da sana’o’in gargajiya a manhajojin
ilimi tun daga matakin firamare har ya zuwa matakin jami’a, wannan zai ƙara haɓaka sana’o’in gargajiya da bunƙasa al’adu
da tattalin arziƙi baki ɗaya.
Manazarta
Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Goɓernment Printing Press, Nigeria.
Alhassan H. Da Wasu, (1982). Zaman Hausawa. Bugu na Biyu, Kaduna: Islamic Publication Bureau.
Bargery, G. P. (1934). English Hausa Ɓocabulary. London:
School of Oriented Studies, Uniɓersity Press.
Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Publication Company.
Sa’id, B. da wasu, (2006). Ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Muhammad, M. S. (2020). Bahaushiyar Al’ada. Tetfund. Kano: Bayero Uniɓersity Press.
Soba, S. A. (2012). “Muhallin Bahaushe Jiya
da Yau”. Kundin Digiri na Biyu da Aka Gabatar ga Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
MUTANEN DA AKA TATTAUNAWA DA SU
|
Lamba |
Suna |
Shekaru |
Sana’a |
Gari |
Rana |
|
1. |
Saidu Nakande |
60 |
Manoni |
Ɓangashe |
20/1/2026 |
|
2. |
Ibrahim Abubuakar |
65 |
Manomi |
Aku |
21/1/2026 |
|
3. |
Mustapha Ibrahim |
40 |
Maƙeri |
Gaya |
2/1/2026 |
|
4. |
Malam Gambo |
65 |
Baduku |
Gaya |
13/1/2026 |
|
5. |
Tabawa Adamu |
61 |
Sana’ar Kaba |
K/ Gabari |
11/1/2026 |
|
6. |
Baba Sayyadi |
43 |
Maƙeri |
Gaya |
5/1/2026 |
|
7. |
Mukhtari A. Isma’ila |
45 |
Magini |
Ƙwandaroso |
11/1/2026 |
|
8. |
Dr. Abdullahi Madaki |
62 |
Malamin Jami’a |
Gaya |
6/1/2026 |
|
9. |
Kawu Mu’azu |
57 |
Wanzami |
Tarauni |
3/1/2026 |
|
10. |
Maisalati Durɓundai |
58 |
Magini |
Kumbotso |
1/1/2026 |
|
11. |
Adamu Isyaku |
68 |
Masanin Al’adu |
Gamoji |
15/1/2026 |
|
12. |
Sadiya Sabo |
60 |
Saƙar Kaba |
Aku |
29/1/2026 |
|
13. |
Dauda Yusif |
50 |
Manomi |
Gaya |
26/1/2026 |
|
14. |
Muhammad Sani |
65 |
Sana’ar Fafa |
Shagogo |
19/1/2026 |
|
15. |
Mu’azu Adamu |
72 |
Mai Unguwa |
Matamawa |
20/1/2026
|
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.