Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Kamancin Sigogi Da Fasalolin Rubutattun Waƙoƙin Gazal Na Larabci Da Na Hausa

Citation: Abdulrahman Aliyu (2024). “Nazarin Karancin Sigogi da Fasalin Rubutattun Waƙoƙin Ghazal na Larabci da na Hausa” Himmaa: Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol. 9, No. 1 August, 2024. Department of Nigerian Languages Umaru Musa Yar’adua University, Katsina. Pg 89–100, ISSN: 2276-6685

NAZARIN KAMANCIN SIGOGI DA FASALOLIN RUBUTATTUN WAƘOƘIN GAZAL NA LARABCI DA NA HAUSA

DAGA

Abdulrahman Aliyu
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
ksarauta@gmail.com 08036964354

Tsakure

Wannan Maƙalar za ta yi duba ne kan Sigogin da Fasalolin Rubuttattun Waƙoƙin Gazal na Larabawa da na Hausawa. Manufar maƙalar ita ce, yin kwatancin sigogi da fasalin waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa ta fuskar gano yadda kowane ɓangare suke shirya nasu waƙoƙin tare da yin duba a waƙoƙin na Larabawa da na Hausa. An bi hanyoyi da yawa wajen ganin an samu nasarar wannan bincike. hanyoyin sun haɗa da tattara waƙoƙin Gazal na Larabci da fassara su zuwa Hausa. Akwai  ganawa da masana da yin tambayoyi ga wasu mutane da suke da alaƙa da waɗannan waƙoki. An yi amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen samo bayanai da suka taimaka aka gina kwatancin ta yadda aka riƙa musayar bayanai daga Larabci zuwa Hausa. Wannan nazarin ya yi amfani da Ra’in Kwatancin Adabi (Comparative Literary Theory) wanda Hugo Meltzl ya samar a shekarar 1877.  Ra’i ne da ya samu goyon bayan masana irinsu H.M Posneet a wani fitaccen aikinsa mai suna “Comparative Literature (1886. Wannan ra’i ana amfani da shi wajen kwatancen adabin al’ummomi, waɗanda ake ganin suna da wata dangantaka ko kuma wasu kamanni a wasu ɓangarori na adabi ko al’adu domin a tabbatar da alaƙarsu. A ƙarshen wannan maƙala, an gano abubuwa masu kama da juna ta fuskar siga da kuma fasali na waƙoƙin al’ummomin biyu. Har ila yau, nazarin ya gano irin yadda Hausawa suka ari wani reshe na Gazal suka samar da nasu na Hausa.

1.0  Shimfiɗa

Nazarin ayyukan adabi masu kama da juna a tsakanin al’ummomi guda biyu ba sabon abu ba ne a fagen nazari. Waƙoƙin Gazal sun samo asali ne daga waƙoƙin ƙasida na Larabci, in da suka kasance kamar shimfiɗa ce ga duk wanda zai yi waƙar ƙasida. Baitukan da suke ɗauke da waƙoƙin Gazal basu wuce biyar zuwa sha biyar ba, ɗauke da bayanin irin raɗaɗin da mawaƙi ke ji game da wata masoyiyarsa da ta yi masa nisa ko ya rasa ta. Kamar yadda irin waɗannan waƙoƙin a Hausa su ma an tusgo su ne daga cikin waƙoƙin soyayya da kuma waƙoƙin da suka shafi kaɗaita Allah da malaman Sufaye ke aiwatarwa ta fuskar yaba wa kyau ko zatin mace.

Bincike a kan waƙoƙin Gazal wani shafi ne da aka buɗe domin yin nazarin wasu ayyukan adabi da ake ganin kamar ɓoyayyu ne, ba a cika fito da su fili ba domin a nazarce su, amma a zahiri ire-iren waɗannan fagage suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar adabi da kuma ƙara faɗaɗa shi. An yi tunanin yin wannan aikin ne ganin yadda                   da yawa Hausawa suke kallon kamar waƙoƙin Gazal ba su da muhalli a Hausa. Wasu kuma suna yi musu kallon fanɗararru ne. Wasu kuma suna kallon bayan waƙoƙin soyayya a Hausa babu wasu waƙoƙi na Gazal. Shi ya sa aka yi wannan bincike domin a yi kwatancen siga da fasalin waƙar Gazal tsakanin Larabawa da Hausawa, da kuma faɗakar da cewa akwai waƙoƙin Gazal a Hausa masu zaman kansu.

2.0 Ma’anar Gazal

Tushen kalmar ‘Gazal’ asalinta daga Larabci ne. A lugga, ‘Gazal’ na nufin “Tufafin da aka saƙa da auduga”. A ma’ana ta ilimi kuwa ‘Gazal’ na nufin mai da hankali a kan hirar mata da nuna matsananciyar soyayya ko yawan raɗaɗin rabuwa da mace a lokacin da ake tafiya cikin tawaga.  (Al-Harthi: 2010)

A fagen waƙa, kalmar tana nufin, wani nau’in waƙa da ke da turke na bayyana tsananin raɗaɗin ciwon rashi ko rabuwa a ɓangare guda, da kuma nuna matsanancin kyawo na masoyi ko masoyiya duk a lokaci guda tare da yaba kyan hali ko ɗabi’a. (Badr Ibn Ali: 2007)

A taƙaice dai ‘Gazal’ wani nau’in waƙa ne da mawaƙi yake sarrafa tubalin bayyana tsananin ƙaunarsa ga abin da yake wa waƙar ta hanyar yabo da siffanta kyawun jiki da na hali da ɗabi’a. Wani lokaci ma har da yanayin mu’amular soyayyarsu.

2.1 Ma’anar Siga

Siga a nazarin rubutattun waƙoƙi ta shafi zubi da tsari na waƙoƙi (Ɗangambo: 2007, sh 19)

Siga a wannan aiki ita ce bayyana yadda siffofin waƙokin Gazal suke da kuma yadda za a iya gane su da rarrabe su da waɗanda ba na Gazal ba. Sai kuma fasali wanda shi ne yake fayyace irin saƙo ko kuma ƙunshiyar da waƙoƙin Gazal na Larabci da na Hausa suka ƙunsa, domin suna da fasalinsu wanda da zaran an kuskure daga gare shi, to an fita maganar waƙoƙin Gazal.

2.2 Fasali

Babbar manufar wannan maƙala ita ce gano sigogi da fasalolin waƙoƙin Gazal a Larabci da na Hausa da kuma fito da kwatancin da ke akwai tsakanin rubutattun waƙoƙin Gazal na Hausawa da na Larabawa.

An bi hanyoyi da dama wajen gudanar da wannan bincike. Hanyoyin da aka bi sun haɗa da fassara matanoni waƙoƙin Gazal na Larabci zuwa Hausa, da ganawa da masana da kuma yin tambayoyi ga waɗansu mutane da suke da dangantaka da waƙoƙin da aka yi amfani da su.

An yi amfani da wallafaffun Litattafai da kundayen bincike wajen samun bayanai da suka taimaka wajen gudanar da wannan bincike. Haka kuma, an yi amfani da kafafen sadarwa na zamani domin neman bayanai da suka taimaka wajen kammaluwar wannan aiki.

Wannan maƙala ta yi kwatanci ne tsakanin sigogi da fasalolin waƙoƙin Gazal na Hausawa da Larabawa tare da yin kwatanci a tsakanin waƙoƙin ta fuskar fasalinsu da kuma irin sigogin da waƙoƙin suke ɗauke da su. An fara kallon fasali da sigar waƙoƙin Gazal na Larabwa ne aka kwatanta su da na Hausa duba da cewa Gazal ɗin daga Larabawa aka samo shi, Hausawa aron shi suka yi tare da wasu sigogi da fasalolin waƙar suka samar da tasu. Daga ƙarshe wannan maƙala ta yi amfani da waƙoƙin Gazal na Hausa da aka gina su kan Siga da fasali irin na waƙoƙin Gazal na Larabci.

3.0    Ra’in Bincike

A wannan maƙala an yi amfani da Ra’in Kwatancin Adabi (Comparative Literary Theory) Wannan Ra’i na Kwatancin Adabi ya fara ɓullowa ne a yankin Hungarian a ƙarni na   (18) daga wani masani mai suna Hugo Meltzl (1846-1908) wanda ya kasance shi ne edita kuma mamallakin mujallar “Journal Acta Comparationis Litterarum Universarum (1877)” da kuma wani masani mai suna H.M Posnett wanda yake zaune a yankin Irish, wannan mutum shi ne  ya fara samar da littafin kwatancin Adabi mai suna‚ Comparative Literature (1886)” Wannan tunani na H.M ya samo asali ne daga shawarar Johann Wolfgang von Goethe Ƙwararren masanin adabin duniya. (H.M. Posneet, 1886)

Daga cikin waɗanda suka biyo bayan waɗannan masana wajen amfani da wannan ra’i, akwai Alexander Veselovsky (1838-1906) da Viktor Zhirmunsky (1891-1971). Wannan ra’i ya fara tsayuwa da dugadugansa a ƙarni na 19 daga rubuce-rubucen Zhirmunsky qtd in Rachel Polonsky, da littafinsa mai suna English Literature and the Russian Aesthetic Renaissance. Wannan ra’i ya wanzu a yankin Jamus a a ƙarshen ƙarni na sha tara (19), bayan kammala Yaƙin Duniyan na Biyu ta hannun masana irin su Peter Szondi (1929–1971). Shi wannan mutum shi ne

 wanda ya rubuta littafin kwatanci adabi na waƙoƙi da wasan kwaikwayo mai suna "General and Comparative Literary Studies" har zuwa lokacin da Tübingen, Wuppertal. Ya rubuta littafinsa na kwatancin Adabin da Jamusanci mai suna Der kleine Komparatist (2003).

A ƙasar Hausa wannan ra’i ya samu karɓuwa sosai in da aka samu ayyuka da suka yi magana kan kwatancin adabi kamar haka: Sankalawa (2005) da aikinsa mai suna “Kwatanta waƙoƙin Aliyu Namagi da Takwarorinsu na Sani Yusuf Ayagi” da aikin Rabi’u (2018) “ Kwatancin Habarcen Nijeriya da Nijar: Tsokaci A Kan Tatsuniya” da aikin Adamu (2019) ”Kawatanci Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Jumhuriya Ta Uku Da Na Jumhuriya Ta Huɗu A Nijeriya” da aikin Salihi (2020) “Kwatanta Littafin Kitsen Rogo Da Jatau Na Kyallu Dangane Da Dabarun Jawo Hankali” da aikin Yahya (2021) mai taken “Kwatanta Jigo Da Zubi Da Tsarin Waƙoƙin Bello Muhammad Aji Mai Karama Da Na Sani Abubakar Hotoro” da sauransu da dama. Wannan ra’i na kwatancin Adabi yana da manufofi da suka haɗa da:

·         Kwatanta wasu ayyukan adabi da sauran ɓangarori na rayuwar al’umma

·         Kwatanta wasu ayyukan adabi masu alaƙa da juna, misali kwatanta wata waƙa da wata makamanciyarta daga mabambanta marubuta

·         Kwatanta wasu ayyukan adabi da ke sajewa a cikin al’adu domin fito da abubuwan                         da suke tattare da su na adabi da kuma na al’adun.

·         Nuna bambancin da ke akwai tsakanin wasu ayyukan adabi masu kama da juna,  domin a rarrabe su.

·         Samar  wa ayyukan adabi mazauni na kwatanci tsakanin wasu mabambanta ɓangarori na duniya da ake ganin suna da alaƙa da juna. Da sauransu

 

3.1 Dangantakar Manufar Ra’in da Manufar Aikin da aka Aiwatar

Kamar yadda aka gani daga cikin manufar wannan ra’i akwai kwatanta wasu ayyukan adabi masu alaƙa da juna. Misali kwatanta wata waƙa da wata makamanciyarta daga mabambantan marubuta ko al’umomi mabanbanta.

Wannan aiki daga cikin manufofinsa akwai kwatanta fasali da sigogi na waƙoƙin Gazal na Hausa da na Larabawa domin gano inda suke da alaƙa da kuma inda suka sha bamban a tsakanin al’umomin guda biyu.

Haka kuma, manufar wannan ra’i ita ce a  samar wa ayyukan adabi mazauni na kwatanci tsakanin wasu mabanbanta ɓangarori na duniya da ake ganin suna da alaƙa da juna.  Shima wannan aiki ya duba mazaunin waƙoƙin Gazal ta fuskar fasalinsu da sigoginsu tsakanin Larabawa da Hausawa domin ganin irin kamanci da bambanci da suke ɗauke da shi. Kazalika  manufofin wannan ra’i da na wannan aiki sun tafi  daidai ta fuskar kwatancin waƙoƙin Gazal na Larabawa da na Hausawa.

4.0  Kamancin Sigogi da Fasalolin Waƙoƙin Gazal a Larabci da Hausa

Kamanci na nufin kwatantan wasu abubuwa guda biyu ko fiye domin gano inda suka haɗu ko suka rabu. (CNHN, 2006). Waƙoƙin Gazal a Larabci ba haka kawai suke kara-zube ba, suna da manyan sigogi waɗanda sharɗanta waƙa ta amsa sunanta na Gazal. A Hausa ma waƙa ba ta amsa sunanta Gazal sai an sami waɗannan sigogi a tattare da ita, duk da cewa akwai sigogin da ake samu a  Larabci amma ba a cika samun su a Hausa ba. Waɗannan sigogi sun Haɗa da:

 

4.1  Yanayin Baitoci

Dangambo, (1988) ya bayyana yanayin baitoci da yadda aka tsara baitocin waƙa bisa ƙa’idar ɗangaye bibiyu ko uku ko huɗu ko biyar. Asalin Waƙar Gazal ta Larabci ana yin ta ne ɗango biyu (ƙwar biyu) a kowane baiti. Haka ake gina ta a ɗango biyun kuma tana da fasali biyu. Fasali na farko shi ne kowane layi yana kasancewa mai zaman kansa, bai da alaƙa da mai bi masa. Sai fasali na biyu kuma ana gina ta yadda ake gina sauran waƙoƙi, wato a ƙulla alaƙa da tsakanin layi na farko da sauran layukan, (Ojolowo, 2023, sh. 6). Misali waƙar Imru’al Qais mai suna Kifa Nafki Min Zikira Habibi Wa Irfani (Da Alama Wadda Ke Nuna Sun Zauna a Nan).

 

قفا نبك من ذكرى حبيب وعرفا ن 

 وَر   سَ م عَف ت  آياتُه مُنذ أ زمَا ن 

 

Da alama wadda take nuna sun zauna  a nan,

Alamomin da suke tabbatar da gidan duk sun tsufa tun da daɗewa.

 

A Hausa waƙoƙin Gazal na farko su ma an gina su bisa irin wannan sigar ta Larabci, wato ana samar da waƙoƙin Gazal na Hausa ƙwar biyu. Da tafiya ta yi tafiya a Hausa, sai aka riƙa samun waƙoƙin Gazal na Hausa masu ɗauke da ƙwar uku zuwa huɗu har biyar. Haka kuma fasali na biyu na yin kowane baiti da ma’anarsa daban, ba a same shi ba a Hausa. Misali a waƙar Ibrahim Sodangi mai suna Ƙarshen Tafarkin Hankali na.

Duk alamu na gidan babu su,

Fentin gidan, Dakali da maina.

 

Sun zamo tarihi abin kwatance,

Surarki ce kawai ta rage a idona.

 

4.2  Adadin Baitoci

Dangambo, (1988) ya bayyana adadin baitoci “matsayin yawan baitukan da marubuci ya rubuta a waƙarsa” waƙa Waƙar Gazal wadda ake samu a cikin ƙasida tana da adadin baitoci da suka fara daga                  biyar zuwa goma sha biyar. Ba su wuce sha biyar kuma ana samun su ne a farkon waƙar ƙasida bayan mawaƙi ya gama ambaton ƙasarsa ta haihuwa da abubuwan da suka shuɗe a cikinta da kuma yin kira ga abokan tafiyarsa, domin su saurare shi. Daga nan sai ya faɗa kashin Nasib (wani sashe ne  na cikin waƙoƙin Ƙasida wanda mawaƙi ke bayyana kewa da irin radaɗin da yake ji na rabuwa da gida) inda a nan ne ake shigo da waƙar Gazal baiti biyar har zuwa sha biyar ba a wuce sha biyar. Bayan ya kawo waɗannan baitoci, sai ya ci gaba da waƙarsa (Al Harthi, 2010, sh. 39).

A mafi yawan lokutta waɗannan baitukan biyar zuwa sha biyar da ake tsarmawa a cikin waƙoƙin ƙasida ba ainafin jigon ƙasidar ba ne kawai, an kawo su ne a matsayin bayyana kewa ko raɗaɗin rabuwa. A Hausa ma wannan siga ana samun ta domin ana samun waƙoƙi masu kama da waƙoƙin ƙasida waɗanda a ciki ake tsarma waƙar Gazal daga baiti biyar zuwa baiti sha biyar sannan mawaƙi ya ci gaba da waƙarsa kan manufar da ya tsara waƙar a kai. Misali, a wata waƙa ta ƙasida ta Imri’al Qais, mai suna “ Li’amruka ma ƙalbi Ila Ahlihi Bakhur”. wadda take ɗauke da baitoci goma sha tara, amma sai ya kawo baituka goma na farko a matsayin Gazal sai kuma sauran baitukan tara waɗanda su ne asalin abin


 da ya gina waƙar a kansa wato zambo ga Hani ibn Ma’sud. Ga misalin wasu baitukan da suke ɗauke da Gazal inda kuma waɗanda ya ci gaba da yi na zambo bayan kammala baituka goman farko:

لَعَمْرُكَ ما قَلْبي إلى أهْلِهَ بِحُر

ولا مقصر يوماَ فيأتيني بق رَ

 

ألا إن مَا ال دهرَ لَيَا لَ وَأعْصُ رَ

وليسَ على شيء قويم بمستمر

 

ليا لَ بذاتَ الطلحَ عند مح

أحَ بَ إلَيْنَا من لَيَا لَ عَلى أُقُرَ

 

أغادي الصبوح عند ه رَ وفرتنيَ

وليداَ وهل أفنى شبابي غير هرَ

 

إذا ذقتَ فاها قلت طعم مدامة.

  معتقة مما تجيءَ به التجر

******

لَعَمْرُكَ ما إنَ ض رني وَسْطَ حِميَ رَ

وأوقولها إلا المخيلة والسكرَ

 

وغيرَ الشقاء المستبين فليتنيَ

أج رَ لساني يومَ ذلكم مجرَ

 

لَعَمْرُكَ ما سَعْد بخُل ة آثِ مَ

وَلا نَأنَإَ يَوْمَ الحِفاظَ وَلا حَصِرَ

 

لَعَمرِي لَقَوْ مَ قد نَرَى أمسِ فيهِمَ

مرابط للامهار والعكر الدثرِ

 

Na rantse da mai raya ka, zuciyata ba ta iya haƙuri ta kyale mace irin wannan,

Zuciyata ba ta taɓa samun sawaba  wajen ƙyale son mace irin wannan.

 

Ku saurara ita rayuwa kwanaki ne da zamani-zamani,

Kuma su zamunnan ba sa taɓa barin rayuwa ta tsaya yadda take.

 

Akwai darare da yawa da muka yi su a gonar ayaba, a nan Muhajar ,

Waɗannan dararen su suka fi soyuwa a zukatanmu fiye da walimar da muka yi a Uƙur.

 

A lokacin da nake sammakon karin kummalo wajen Hirru ko Fartana,

Tun ina yaro, yo in ba Hirru ba wa ya ƙarrar da ƙuruciyata.

 

Idan na ɗanɗani bakinta (Hirru) ka ce zaƙin bakin nan irin zaƙin giya ce mafi shahara,

Irin giyar da fatake suke zuwa da ita yar oda, ba wadda aka yi yanzu-yanzu ba.

 

******

Na rantse da mai raya ka, babu abin da ya cutar da ni a zama cikin mutanen Himyar,

Da kuma sarakunansu in ban da girman kai da kuma tsabar maye.

 

Da kuma rashin arziƙi na ƙiri-ƙiri,

Sa’ar da nake cikin su kamar an tsage man harshe ne an hana ni magana.

 

Na rantse da mai raya ka, shi Sa’adu ba ya abota da mai saɓo,

Kuma baya taɓa taƙaitawa a ranar fama, baya suƙewa da wanda ya maƙwabce shi,

 

Na rantse da rayuwarka akwai mutanen da mun fi son su,

fiye da mutanen da ke rayuwa a ƙololuwar dutse.

      (Imru’al Qais: Li’amruka ma Ƙalbi)

Baituka goma na farko su ne ke ɗauke da Gazal, sauran baitukan kuma zambo ne da

Imru’al Qais ya ci gaba da yi, an dan tsakuro su ne domin misali. Irin wannan siga ta Gazal a Hausa ma akwai ta inda marubuci yake ƙulla waƙarsa da wata manufa ta daban, amma kuma sai ya fara kawo wasu baitoci da Gazal ko kuma a tsakiyar waƙar ko ƙarshenta sai ya rubuta baitocin Gazal da ba su wuce biyar ba zuwa sha biyar. Misali waƙar Dr. Yusuf Ali wadda ya ba suna “ Mai Shimfiɗa ya Naɗe”, waƙa ce da ya shirya domin yin habaici da zambo ga wata mata da ta takurawa masoyiyarsa Mairo a lokacin da ta kawo masa ziyara, cikin waƙar ya yi kira ga waccan mata da ta san abin da take ta rage tsananin kishi domin tsananin kishi ba abu ba ne mai kyau. Amma a cikin waƙar sai ya yi baiti takwas na Gazal sannan ya ci gaba da yin zambo da habaici ga wadda yake so ya yi wa habaicin bambancin da aka samu tsakanin wannan waƙar da ta Imru’al Qais, ita wannan waƙar baiti (37) ce yayin da ta Imru’al Qais ke baiti (19) inda aka samu Gazal baiti goma nan kuma aka samu takwas saura baiti sha tara kuma suka kasance habaici da zambo kamar dai yadda ta Imru’al Qais ta kasance. Ga misalin waƙar:

 

Ni me na ce ne ne,

Wai har ake magana.

 

Don na cane Mairo,

Ita ce a rayina.

 

Mai shimfiɗa ya naɗe,

Mai gun fa zai zauna.

 

Zuma farar saƙa,

Ni me nake da guna.

 

Na ɗau jahannama nai-

Watsi da Aljanna.

 

Ga lafiyayya me,

Nake da shan-Inna.

 

Mai hankali ga ta,

Ya za na ɗau sauna.

 

Ya zan ƙi kyakkyawa,

Na zaɓi mummuna.

 

******************

 

Jikinta duk kirci,

Kamar icen kurna.

 

Ƙafa kamar dagi,

Fuska kamar ɓauna.

 

Cikin kamar taiki,

Kayi ya kan jimina.

 

Me zan da tsigalla-

Hu, mai faɗa ya rina.

(Dr.Yusuf Ali:Mai Shimfiɗa Ya Naɗe)

 

4.3 Rashin Yabon Farawa

Waƙar Gazal a Larabci ba ta da mabuɗi na ambaton sunan Allah ko yabonsa a baitukan farokonta. Ana gina ta ne kai tsaye kan abin da ke damun mawaƙin da kuma abin da yake son bayyanawa. A Hausa ma duk waƙoƙin da hannun wannan nazari ya kai gare su, ba a samu wata waƙa ta Gazal da ke ɗauke da yabon farawa a tare da ita ba. Ke nan, duk waƙar da ta fara da yabon buɗewa ta sauka daga Gazal a Larabci da kuma Hausa.

5.1. Tuna Rayuwar Baya

 Kamar yadda aka sani dai rayuwa na nufin zaunawa da mutum ku yi abubuwa tare na wani lokaci ko ma din-din, in aka rabu to wani lokaci akan tuno irin abubuwan da aka yi tare na daɗi ko akasin haka.  Suma mawaƙan Gazal sukan shirya waƙa kacokan kan irin rayuwar da ta faru baya tsakaninsu da masoyansu ko ta daɗi ko akasin haka. Daga cikin fasalolin waƙar Gazal akwai tuna  rayuwar baya ko wajen da aka yi rayuwar da bayyana irin abin da aka yi a bayan, wanda daga nan ne ake fito da sauran fasalolin  rabuwa da kuma kewa. A                                                                                                                wannan fasali mawaƙi kan bayyana irin rayuwar da ya yi a baya tare da masoyiyarsa ko kuma waƙe wurin da suka taɓa haɗuwa ko zama da masoyiyar tasa a baya. A Hausa ma akwai irin waɗannan waƙoƙi na Gazal da yawa da aka gina su kan tuna  rayuwar baya ko wajen da aka taɓa rayuwa a baya. Misali waƙar “Kifa Nafki Min Zikira Habibi wa Irfani” wadda Imru’al Qais ya rubuta ta ne a ƙarshen rayuwarsa lokacin da mutuwa ta zo masa yana cikin ƙasƙancin rayuwa ba ya iya kome, jarumta da tashensa duk sun ja baya ga kuma rashin lafiya a lokacin,  saboda haka sai ya riƙa lallashin kansa da yi wa kansa kirari. A cikin waƙar bayan ya isa wata unguwa da ya taɓa yin soyayya da wata masoyiyarsa wadda  a lokacin  ba ta unguwar, amma ko da ya ga  gidansu, sai ya tuno masa da rayuwar da suka yi da ita a baya, ga misalin wasu daga cikin baitocin waƙar kamar haka;

قفا نبك من ذكرى حبيب وعرفا ن

وَرَسْ م عَفتْ آياتُه مُنذ أزْمَا ن

 

أتت حج ج بعدي عليها فأصبحت

كخ ط زبور في مصاحف رهبا ن

 

ذكَرْتُ بها الحَ ي الجَميعَ فَهَي جَتْ

عقابيل سقم من ضمير وأشجان

 

فَسَ حتُ دُموعي في ال ردا ء كأن هَا

كُلى من شَ عي ب ذاتُ سَ ح وَتَهْتا ن

 

إذا المرءُ لم يخزن عليه لسان ه

فَلَيْسَ على شَيْ ء سوَاه بخَ زا ن

 

فإما تريني في رحالة جاب ر

على حرج كالق ر تخفقُ اكفان ي

 

فَيا رُ ب مَكرُو ب كَرَرْتُ وَرَاءَه .

وعا ن فككت الغ ل عنه ففدان ي

 

وَف تيا ن صدْ ق قد بَعَثْتُ بسُحرَة.

فقاموا جَميع ا بَينَ عا ث وَ نَشْوَا ن

 

Da alama wadda take nuna sun zauna  a nan,

Alamomin da suke tabbatar da wannan shi ne gidan duk sun tsufa.

 

Alamomin shekaru sun bi ta kansu, tun bayan barina wajen,

Sai wurin ya zama tamkar irin tsofaffin litattfai ne na masu bauta.

 

Na tuna mazaunan unguwar nan baki ɗayansu da na zo wurin,

Wannan tunanin ya motsa man da rashin lafiyar zuciya da kuma takaici.

 

Sai hawayena ya kwarara a cikin mayafina,

Tamkar ruwa na kwarara daga cikin a salka[1] ma’abociyar tsiyaya.

 

Idan mutum bai taskace harshensa a kan sirrinsa ba,

To ba zai taɓa kiyaye asirin waninsa ba tun da ya gaza kare nasa.

 

Ya ke wannan masoyiya da nake wa waƙa, don kin gan ni a maɗauki na Jabir,

An ɗora ni a kan makara likkafanina yana mosti to ba abin aibu ba ne.

 

Da yawa akan samu mutum cikin baƙin ciki na kai ɗauki  a gare shi

Da yawa an samu ribatacce ni na je na kwance masa mari

 

Da yawa akwai samari na gaskiya na tashe su da asuba

Baki ɗayansu suka tashi suna magagi da maye sakamakon tsawata. (Imru’al Qais: Da Alma...)

 

 A baitocin da ke sama an ga yadda Imru’al Qais ya tuna rayuwar da suka yi da masoyiyarsa a baya sakamakon ganin kufan gidansu da ya yi. Wannan dalilin ne ya motso ma shi da sonta da ke cikin zuciyarsa, har ya fara tunanin yanzu ta guje shi ne saboda halin da yake ciki na rahin lafiya, wanda hakan ya sa ya ƙara tuno mata da irin jarumtarsa ta baya da kuma yadda ya buwayi mazaje a wancan lokacin, saboda haka ganinsa yanzu cikin wannan hali ba wani abu ba ne, tun da a baya shi jarumi ne kuma ya yi abin da ya kamata.

 A Hausa ma akwai irin wannan fasali. Misali waƙar Ibrahim Sodangi mai suna, “Ƙarshen Tafarkin Hankalina” waƙa ce da aka gina a kan tuna rayuwar baya tsakaninsa da wata masoyiyarsa da ba su tare, amma sakamakon ganin gidan da masoyiyar tasa ta ke sai ya tuno masa da irin rayuwar da suka yi a baya. Ga wasu daga cikin baitocin waƙar;

Yanzu ma ba na gane kowa,

Kofar gidan shi ne ido da ruhina.

 

Duk alamu na gidan babu su,

 Fentin gidan, dakali da maina[2].

 

Sun zamo tarihi abin kwatance,

Surar ki ce kawai ta rage a idona.

 

Kuma ba ni gane ni da kaina,

Cikin mir'ati da inuwar jikina.

 

Idan da ni ma ni ban shina ba,

Kawai gidan ne ke ɗaukar idona,

 

Bari in yo adon riga da wando,

shigar da na saba zuwa mu gana.

 

A fagen ado babu ya tamkar ni,

A samarinki kaf sun mini jinjina.

 

Na fi su arziƙi na gida da mota,

Duk cikinsu ba tamkar ya irina.

(Ibrahim Sodangi: Ƙarshen Tafarkin hankalina)

 

            Ita ma wannan waƙa kamar ta Imru’al Qais Ibrahim Sodangi ya bayyana irin halin da yake ciki na tuna rayuwar baya da masoyiyarsa, bayan da ya zo wani gida da masoyiyar tasa ta taɓa zama. A cikin waƙar ya bayyana wa masoyiyar irin abubuwan da suka faru da shi a baya saboda ita. Wannan fasalin wani ginshiƙi ne da dole sai ya bayyana a cikin waƙoƙin Gazal suke zama Gazal ko da kuwa a baiti biyu ne ko uku na dukkan rukunonin waƙoƙin Gazal.

4.5 Rabuwa

 Masana sun bayyana kalmar rabuwa a matsayin barin abin da kake tare da shi ta wasu dalilai,  rabuwa na ɗaya daga cikin fasalin gina waƙar Gazal a Larabci akwai rabuwa, ta yadda mawaƙin zai bayyana irin taren da suka yi da masoyiyarsa ko masoyi a wani zamani da ya shuɗe, amma kuma yanzu sun rabu na har abada. Irin waɗannan waƙoƙi su ne waɗanda Qais ibn Mu’walla (Majnun Laila) ya riƙa rubuta wa Laila bayan sun rabu. Akwai kuma waƙar Umar bin Abi-rabi’a mai suna, Amin Ali  Nu’umi Anta Gadi Fa Mubakur’. Wadda ita ma kan rabuwa aka gina ta. Yawancin wannan fasalin mawaƙan Gazal ba su ne a karin kansu suke waƙar dominsu ba, suna yi ne domin wasu abokannansu ko ‘yan uwansu ko ma wanda ba su sani ba, da  wata masoyiyarsa ta tafi ta barshi, kamar yadda wannan waƙar ta Umar ya yi ta ne ga wani abokinsa da wata masoyiyarsa ta bar shi. Ga kaɗan daga cikin baitocin waƙar;

 

أمن آل نُـعْـم ٍ أنت غاد ٍ فمبكر ُ

 غداة غد ٍ , أم رائح ٌ فمهجِّـــر ٌ

 

لحاجة نفس ٍ لم تقل في جوابها

فتبلغ عذرا ً والمقالة تعــــــذر

 

تهيم إلى نُــعْـم ِ ,فلا الشمل جامع

ولا الحبل موصول ٌ,ولا القلب مقصر

 

ولا قرب ُ نُـعْــم ٍ إن دنت لك نافع ٌ

ولا نأيها يسلي , ولا أنت تصبر ُ

 

وأخرى أتت من دون نُـعْـم , ومثلها

نهى ذو النهى لو ترعوي أو تفكر ُ

 

Shin saboda Al-Nu’umin za ka yi sammako da jijjiɓin safiya?

Gobe, amma za ka yi tafiyar marece ne da garjin rana.

 

Don biyan wata buƙata wadda ba ka amsawa duk wanda ya tambaye ka,

Bare ka ba da uziri, kuma amsa tambaya ma ai uziri ne.

 

Ka na ruɗuwa da kiɗimewa akan Nu’umin, zuciyarka ba ta tattaru ba,

Haka abin da ka ke nema baka samu ba, kuma zuciya ba ta yi ƙasa a guiwa ba.

 

Haka nan Kusantar Nu’umin idan ta kusanto ka bai zama mai amfani ba,

Hakannan nisantarta ba zai lallashe ka ba, kuma ba ka zama mai haƙuri ba.

 

Wata macEn wadda ta ke ƙasa da Nu’umin ta zo, har da wadda bata kai ta ba,

Hankali yaƙi amincewa da su, da  hankali ya san abin da ya kamata da ya amince da su.

(Umar bin Abi Rabia: Amin Ali  Nu’umi Anta Gadi Fa Mubakur’)

 

 A Hausa ma akwai makamantan irin waɗannan waƙoƙin na Gazal masu ɗauke da bayyana tsananin rabuwa tsakanin masoya misali. Alƙali Hussaini Ahmad Sufi ya yi irin wannan fasali a waƙarsa mai suna “Begen Asama’u” inda ya yi wa wani yaro da ya ga ya faɗa kogin son wata yarinya mai suna Asama’u a lokacin da suke aiki hajji a shekarar (1989), kuma ya lura yaron ya rasa yarinyar sun rabu, sai ya shirya waƙar Gazal yana bayyana irin raɗaɗin da yaron ke ji a zuciyarsa na rabuwa da Asama’u, ga kaɗan daga cikin baitukan waƙar:

Asama’u kin tafi kin barni,

Begenki ban yi da wasa ba.

 

Muna zamanmu muna taɗi,

Tamfar ba za mu gushe nan ba.

 

Aka ce da ni tafiya za kui,

Ba za mu sake gamewa ba.

 

Ni sai na ɗauka wasa ne,

Ko zuci ban yi tunanin ba.

(Ahmad Sufi:Begen Asama’u)

 

 Waɗannan fasaloli guda biyu sune muhimmai da ake gina waƙar Gazal a kansu, kuma wajibi ne kowace waƙar Gazal ta hau ɗaya daga cikin fasalolin nan guda biyu kafin a kira ta Gazal a Larabci da kuma a Hausa. Sai dai akan samu bambanci wajen gina na Hausa, inda a mafi akasari sukan saɓa wa na Larabci wajen yawan baitukansu, yayin da a Larabci ba za a iya wuce baiti biyar zuwa sha biyar ba, a fasalin rabuwa ko tuna rayuwar baya, amma a Hausa har baiti 40 ana samu, sannan a Larabci ba  samu wata waƙa ba da mutane biyu suka haɗu suka tsara bisa wannan fasaloli, wanda a Hausa na samu waƙokin da mutum biyu suka haɗu suka rubuta su a bisa wannan fasali.

4.6  Sakamakon Bincike

Babu ko shakka duk wani bincike da aka gudanar to daga ƙarshe akwai buƙatar a ga wane irin sakamako wannan bincike ya samar, musamman ga al’ummar da aka yi binciken domin su, don haka wannan maƙala akwai sakamakon da ta samar wanda ya haɗa da:

  • Maƙalar ta gano cewa al’ummar Hausawa da Larabawa tamkar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai kan abin da ya shafi ayyukan adabi na rubutacciyar waƙa, domin kwatancen waƙoƙin Gazal na Larabawa da na Hausa ya taimaka ƙwarai wajen sanin yanayin yadda Larabawa ke gudanar da rayuwarsu da kuma abubuwan da suke da alaƙa tsakanin Larabawan da Hausawa.
  • Maƙalar ta gano cewa a waƙoƙin Gazal na Larabci ana gina su ne bisa sigar da ta shafi yanayin baitoci da adadin baitoci da kuma rashin buɗe waƙar da ambaton sunan ubangiji a Hausa ma an gano cewa duk waɗannan sigogin.
  • Haka kuma binciken ya gano cewa, rubutattun waƙoƙin Hausa musamman na Gazal sun samo asali ne daga Larabawa, domin duk fasalin waƙoƙin da kuma zubin su irin na Larabawa ne, kuma suna ɗauke da saƙo ne iri ɗaya.
  • Maƙalar ta gano cewa babu wani nau’in waƙa da ya kai na Gazal sanya hikima da kuma nuna gwanitar harshe da naƙaltarsa, kasantuwar mafi yawan waƙoƙin Gazal sai an yi fashin baƙinsu sannan ake fahimtar su, saboda yadda ake sanya salo da adon harshe da fasaha da naƙaltar harshe a cikinsu.

6.1 Naɗewa

 Wannan maƙala ta yi duba ne kan sigogi da fasalolin waƙoƙin Gazal na Larabci da kuma kwatancinsu da na Hausa, tare da kawo misalai akan sigogin da fasalolin tsakanin Larabci da Hausa. Da farko an yi sharar fage in da aka duba ma’anar Gazal da kuma kawo manufar wannan bincike da fayyace hanyoyin da aka yi amfani da su tare da fito da fitattun sigogin wakokin Gazal da fasalolinsu tsakanin Larabawa da Hausawa ta fuskar yin kwatanci a tsakaninsu, sannan sai aka kawo sakamakon da binciken ya samar bayan kammala shi. A ganin mai maƙalar ya kamata hukumomi da jami’o’i su riƙa samar da wani taro na ƙarawa juna sani wanda za a riƙa daddaage ayyukan kwatancin adabi ko na al’adu ko harshe domin ganin irin yadda wasu al’umomin ke da alaƙa da juna ta fuskoki da dama.

Manazarta

Abdullahi, Y. (2016). Al-Muzanatu baina ƙasidatal ash-shai’raini, amirul-mumina

Muhammu Bello wa Muhammadul-Bukhari firasat’ ammihima Al-Ustazu Abdullahi Bn Fodiyo. A Dissertation Submitted to the Posgraduate School Usman Danfodiyo Unversity.

Ainu, H.A. (2005). Rubutattun waƙƙoƙin addu’a na Hausa: Nazarin jigonsu da salailansu.

[Kundin Digiri na Uku] Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’a Usmanu Danfodiyo.

Al-Harthi, M.J. (2010). I have never touched her: The body in al-ghazal al-‘udhri.

[Unpulished PhD, Thesis] University of Edingburgh College of Humanities and Social Science School of Litereatures, Languages and Cultures Department of Islamic and Middle Estern Studies.

Al-askandariya da Wasu (BS) Taikhul Adab. Naqada Printing and Publishing  

Company,.

Al-alamiyya, J.D (2001).  Al-adab Wannusu Wal Balaga wan Nakad. Jami’atul Da’awatul

Islamiyya.

Adamu, M. (2019). Kawatanci tsakanin rubutattun waƙoƙin siyasar jumhuriya ta uku da na jumhuriya ta huɗu a Nijeriya [Kundin Digiri na Uku] Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.

Babangida, A.Y (2011). A comparative literary study of the hamziyya panegyric poetry of 

the prophet ( p.b.u.h) by Ahmad Shawqiy and Aliyu Jarim. [Unplished Masters Degree] Department of Arabic. Bayero University.

Baffa, S.A (2021). Sabon zubin waƙoƙin Hausa a ƙarni na ashirin da ɗaya. [Unpublished

Ph.D Dissertation] Usman Danfodiyo Unversity.

Funtua, A.I (2002). Waƙoƙin Siyasa na Hausa a Jamhuriya ta Uku: Jigoginsu da Sigoginsu”.

Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa Juna Ilimi, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Ibrahim, A. (2004). Nazarin jawo hankali cikin rubutattun waƙoƙin soyayya na

Abdullahi Bayaro Yahaya. [Kundin Digiri na Ɗaya] Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Ibn Khutaiba (BS). Kitab Al-shi’r Wa-al-shua’ara. Dar-Alma’arifa.

Isah, H (2021). Salon tsakuren nassi cikin waƙoƙin Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu.

[Unpublished Dissertation of  Masters of Arts] Department of Nigerian Languages. Usman Danfodio University.

Jalajel, D (2007). “A short history of Ghazal” Ghazalpage

Jangebe, M.M (1991). Nazari kan rubutattun waƙoƙin yabo na garin Sakkwato [Kundin

Digiri Na Biyu] Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Nuhu, A  (2012). Sauye-sauye a tsarin waƙoƙin zamani: Nazari a kan waƙoƙin finafinan

Hausa [Kundin Digiri Na Biyu] Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ojolowo, S.A (2013). A comparative study of erotic poetry of Imru’ul Qais and Umar bn abi

Rabi’ah. [Unpublished  Dissertation Masters Degree] Submitted to the Department of Arabic Bayero University.

Posnett, H.M (1886). Comparative Literature . Landon

Ramlatu, M.A. (2015). Fannu al-rasa’ilada al-sha’ir al-shaikh Usmanu Naliman: Dirasah

adabiyyah tahaliliyyah [Unpublished  Dissertation of  Masters of Arts]  Department of Arabic. Usman Danfodio University.

Sa’id, B (1982). Dausayin Soyayya. Northen Nigerian Publishing Company.

Satatima, I.G (2009). Waƙoƙin baka na ɗarsashin zuciya: Yanaye-yanayensu da sigoginsu.

[Kundin Digiri na Uku] Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Yahaya, A.B (2014). Gudale WaƘar Soyayya: Misalin Ghazal a cikin rubutattun waƙoƙin

Hausa. Cikin Feschcript na Farfesa Abdulqadir Ɗangambo.

Zaiti. A (2007). Tarikhul Adbil Arabi. Dar-al-ma’arifa.



[1] Wata jikka ce da matafiya ke amfani da ita domin zuba ruwan sha ana yin ta ne da fata.

[2] Iccen bedi ko kuma dogon yaro a wasu wuraren

Waƙoƙin Gazal

Post a Comment

0 Comments