Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Bayarwa Ko Karbar Bashin Banki Da Ruwa (Interest)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wani malami ne ya ce wai idan mutum ya karɓi bashin banki domin ya yi kasuwancin da zai samu riba, to babu laifi domin ruwan da bankin suka ƙara a kan asalin bashin da ya karɓa. Mene ne gaskiyar wannan?

HUKUNCIN BAYARWA KO KARƁAR BASHIN BANKI DA RUWA (INTEREST)

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Haramcin bayarwa ko karɓar bashi-da-ruwa (interest) abu ne sananne a wurin dukkan masu addini ma, ba wai addinin musulunci [kaɗai] ba.

Dalilin haramcin riba a musulunci yana nan a cikin Ayoyi ne kamar maganar Allaah Ta’aala a cikin Alƙur’ani:

الَّذِينَ يَأْكُلُونَ الرِّبَا لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ الَّذِي يَتَخَبَّطُهُ الشَّيْطَانُ مِنَ الْمَسِّ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا إِنَّمَا الْبَيْعُ مِثْلُ الرِّبَا وَأَحَلَّ اللَّهُ الْبَيْعَ وَحَرَّمَ الرِّبَا فَمَنْ جَاءَهُ مَوْعِظَةٌ مِنْ رَبِّهِ فَانْتَهَى فَلَهُ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُ إِلَى اللَّهِ وَمَنْ عَادَ فَأُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ (275) يَمْحَقُ اللَّهُ الرِّبَا وَيُرْبِي الصَّدَقَاتِ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ (276)

Waɗanda suke cin riba ba za su miƙewa (a Lahira) ba sai dai kamar yadda wanda sheɗan ya kayar da shi da shafa yake miƙewa. Wannan kuwa saboda sun ce ne: Kaɗai shi ciniki kamar riba ne. Amma kuma Allaah ya hallata ciniki kuma ya haramta riba. Duk dai wanda wa’azi ya zo masa daga Ubangijinsa kuma sai ya hanu, to abin da ya gabata halal ne, kuma al’amarinsa yana wurin Allaah. Wanda kuma ya koma, to waɗannan su ne ’yan Wuta kuma su ɗin madawwama ne a cikinta. Allaah yana ɗebe albarkar riba, kuma yana ƙara albarkar sadaka, kuma Allaah ba ya son dukkan kafiri mai yawan zunubi. (Surah Al-Baƙarah: 275-276).

Sai kuma a cikin Hadisai Sahihai da suka zo a kan hakan, kamar wannan riwayar ta Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda ya ce:

« اجْتَنِبُوا السَّبْعَ الْمُوبِقَاتِ ». قَالُوا يَا رَسُولَ اللَّهِ ، وَمَا هُنَّ قَالَ « الشِّرْكُ بِاللَّهِ ، وَالسِّحْرُ ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِى حَرَّمَ اللَّهُ إِلاَّ بِالْحَقِّ ، وَأَكْلُ الرِّبَا ، وَأَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ ، وَالتَّوَلِّى يَوْمَ الزَّحْفِ ، وَقَذْفُ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ الْغَافِلاَتِ »

Ku nisanci abubuwa bakwai masu hallakarwa. Suka ce: Manzon Allaah, waɗanne ne su? Ya ce: ‘Shirka da Allaah, da sihiri, da kashe rai wanda Allaah ya haramta sai da haƙƙi, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juyawa a ranar haɗuwa da maƙiya, da kuma yi wa matan kirki muminai rafkanannu ƙazafi. (Sahih Bukhaariy: 2766, Sahih Muslim: 89).

Da kuma wannan riwayar ta Jaabir (Radiyal Laahu Anhu) mai cewa:

لَعَنَ رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- آكِلَ الرِّبَا وَمُوكِلَهُ وَكَاتِبَهُ وَشَاهِدَيْهِ وَقَالَ هُمْ سَوَاءٌ.

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya la’anci maciyin riba, da wakilinta, da marubucinta, da masu shaidarta. Ya ce: Su duk daidai su ke. (Sahih Muslim: 4177).

Sannan malamai masu yawa sun yi hikaito ijma’in malaman musulunci a kan haramcin mu’amala da riba, kamar Al-Imaam Al-Ƙurtubi a cikin Tafsirinsa: 3/241.

Kai! Maganar har ta kai ga kafirtar da mai musun haramcin cin riba. Ga abin da babban malami Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) ya faɗa:

وَقَدْ ذَكَرَ شَيْخُ الْإسْلَامِ - رَحِمَهُ اللهُ - فِي كِتَابِهِ «إبْطَالُ التَّحْلِيلِ»، أنَّهُ جَاءَ مِنَ الْوَعِيدِ فِي الرِّبَا مَا لَمْ يَأْتِ فِي أيِّ ذَنْبٍ آخَرِ سِوَى الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ. وَهُوَ مُجْمَعٌ عَلَى تَحْرِيمِهِ، وَلِهَذَا مَنْ أنْكَرَ تَحْرِيمِهِ مِمَّنْ عَاشَ فِي بِيئَةٍ مُسْلِمَةٍ فَإنَّهُ مُرْتَدٌّ؛ لِأَنَّ هَذَا مِنَ الْمُحَرَّمَاتِ الظَّاهِرَةِ الْمُجْمَعُ عَلَيْهَا.

Haƙiƙa Shaikhul Islaam (Rahimahul Laah) ya ambata a cikin littafinsa mai suna: Ibtaalut Tahleel cewa: Abin da ya zo na alƙawarin azaba a kan cin riba bai zo a kan wani zunubin da ba shi ba, in ban da shirka da kafirci. Kuma shi cin riba malamai duk sun haɗu a kan haramcinsa. Shiyasa duk wanda ya yi musun haramcin cin sa daga cikin wanda ya rayu a cikin al’umma musulma, to ya yi ridda. Domin yana daga cikin abubuwan da haramcinsu yake a bayyane, wanda kuma malamai duk sun haɗu a kansa. (As-Sharhul Mumti’u: 8/393).

Sannan kuma ‘shi bashi-da-ruwa (cin riba ko interest) ɗaya ne daga cikin abubuwa biyun da suka ruguza tattalin arzikin manyan ƙasashen duniya irin su Rasha a shekarun 1920 da 1930. Na biyun kuma shi ne yaɗa hotunan batsa da luwadi, waɗanda kuma duk Yahudawa ne suka jagoranci yayata su tun a waɗancan lokutan har zuwa yau. Shiyasa Hitla ya haramta su a lokacin da ya zama shugaban ƙasar Jamus. Kuma da ya yi hakan, sai ga shi a cikin shekaru shida kacal ƙasar ta Jamus ta zama babba daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi a duniya. (Haka wani malamin Yahudu mai suna Rabbi Yaron Reuven ya faɗa, kamar yadda wani saurayi daga baƙaƙen fatar Amirka wai shi Joshua Isaiah - shi kuma wataƙila Kirista - ya ambato kwanan baya a cikin shafinsa na whatsapp).

Saboda waɗannan dalilan bai halatta musulmi ya nemi bashi daga irin waɗannan bankuna masu ta’ammali da riba (interest) ba. Wannan shi ne asalin da malamai suka tabbata a kansa kamar yadda ya gabata.

Amma idan aka lura cewa rashin karɓar zai janyo wani abu daga cikin haƙƙoƙi na wani ko wasu musulmi na ƙasa zai salwanta, ko kuma hakan zai bai wa arna da fasiƙai iko da dama har su ci gaba da danne musulmi. A nan ne waɗansu malamanmu suke ganin za a iya karɓar bashin a bisa ƙaidar malaman Fiƙhu na halaccin aikata mafi sauƙin laifuffuka guda biyu.

Amma tun da akwai bankunan da ba su yin ta’ammali da riba, to ya wajaba musulmi ya yi ƙoƙarin mayar da harkokinsa a can. Sai dai ko in an gano cewa su ma ɗin ba da gaske suke yi ba, ungulu ne da kan zabo suke yi, ko yaudara ce kawai domin neman yawan masu ajiya. Allaah ya kiyaye.

Sannan kuma ko da kuma yarjejeniya ce suka ƙulla da bankin a kan ya je ya yi kasuwanci da rancen da suka ba shi, shi ma dai akwai matsala. Domin a tsarin mudaarabah ta sharia wani kaso na ribar da aka samu ake fayya cewa kowane sashe, kamar rabi ko kwata ko sulusi da sauransu. Amma ba wani adadi na kuɗi ayyananne ba.

Wal Laahu A’lam

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa... 

Post a Comment

0 Comments