Ticker

6/recent/ticker-posts

Kurman Baki! (Hikayar Wani Jaki Da Dansa)

KURMAN BAƘI! (HIKAYAR WANI JAKI DA ƊANSA)

A wani gari a wani gida a cikin wani garken jakuna wanda ya haɗa uba da ƴaƴa, aka samu wani jaki ya yi hushi ya shiga yajin cin abinci, ya mayar da kansa bai da wani aiki sai karatun wasiƙar jaki kwatankwacin wanda aka sanar da shi ranar mutuwa, aka dauƙi lokaci ba ya cin abinci ko hira da sauran ƴan'uwansa jakuna. Yau da gobe hasara ga mai rai, bayan nazartar halaye sai uban wannan jaki ya fahimci cewa ɗansa fa na ramewa kamar ɗan akuyar mayya ko kuɗin guzuri, kuma ga shi bai cikin walwala kamar sauran ƴan'uwansa. Sai wannan uban nashi ya riƙa aika masa da wata dawa mai daɗi da niyyar ya ci, ko jikinsa yana dawowa, amma sai ya zamto duk lokacin da aka aika masa da ita haka yake yin kunnen uwar shegu da ita sai dai sauran ƴan'uwansa su cinye, har ya kai idan yana tafiya kamar a hura shi ya faɗi kamar talakan Nijeriya a lokacin mulkin Aramma Bala, ga shi kuma kunnuwansa sai daɗa fitowa suke kamar maficin fankar sama.

Ka san tsakanin uba da ɗa ba ta bar komai ba, bayan duk waɗannan dabarun da uban ya yi haɗe da lallashi ya ga ba a kai ga wata natija ba, kamar dai gyaran wurar lantarki a Nijeriya, sai ya sauya salo, gama Hausawa sukan ce "idan lela ta ƙiya sai koma basha" wannan ya sa uban nashi ya iske ya keɓanta da shi saboda shi ya ga jiya kuma ga shi cikin yau, sai ya riƙa jero masa tambayoyi kamar haka don ya yaye masa damuwarsa;

Jaki: ya ɗana mene ne ya same ka, ka daina cin abinci ka daina walwala, ga shi kuma na aiko maka da mafi kyawon abinci a wajen jakuna ka ƙi ci, sai ƴan'uwanka ne suka cinye shi?

Ɗan jaki: (ya ɗaga kansa kusan da ƙyar, kamar wanda aka ɗora wa Dutsin zagi a kai), ya ce wa mahaifinsa. "Eh lallai haka ne ya babana, ƴan'adam su ne suka kai ni ga wagga baƙar kama.

Jaki uba: Abin mamaki ta yaya ƴan'adam suka yi sanadiyyar ka shiga wanga halin?

Jaki ɗa: Haba baba! Ba ka ji suna izgili da mu ba, mu jakuna?

Jaki uba: Ta yaya, yi min bayanin filla-filla mana, ko na hango abin da ka hango.

Jaki ɗa: Ba ka ganin duk lokacin da wani daga cikin mutane ya yi niyyar ya zagi ɗan'uwansa mafi munin zagi sai ka ji ya ce masa ya jaki, ko kuma jakin banza, ko ya ce masa mai ƙwaƙwalwar jaki, shin haka muke kamar yadda suke siffanta mu? Ta yadda suke siffanta mafi wautar cikinsu da jaki, mu fa muna ji kuma muna gani kuma muna fahimtar lamurra.

Jaki uba: (A lokacin sai hankalin jaki uba ya tashi har ya rasa amsar da zai ba ɗansa, kamar ƙwararren ɗan jarida ya ritsa da ɗan siyasa, amma kuma sai wata natsuwa ta zo masa domin ya fahimci ɗan nashi ya yi nisa sosai wajen jin haushin yan'adam, sai ya kaɗa kunnensa na dama, sannan ya kaɗa kunnen hagu, sai kuma ya kori kuɗa da bindinsa waɗanda ke damunsa, sai ya yi tunani mai zurfi) ya ce "ya ɗana, haƙiƙa Allah ya fifita ƴan'adam a kan mu, da ma sauran halittun da ya halitta, sai dai so da dama sukan zalunci kawunansu, kafin su zalunce mu, mu jakuna.

Ya kai ɗana ka taɓa ganin jaki mai irin shekarunka ya saci kayan wani? Amma ƴan'adam suna yi. Ya kai ɗana ka taba ganin jaki yana azabtar da ƴan'uwansa saboda kawai ya fi su ƙarfi, ko kuma kawai saboda ba su birge shi? Ya kai ɗana ka taɓa ganin jaki yana ƙyamar ɗan'uwansa jaki kawai saboda banbancin launin fata ko banbancin yare ko saboda ba gidansu guda ba? Amma duk mutane suna yin duk waɗannan, saboda wanga yana baƙi, wancan yana fari ko saboda wannan Bahaushe ne ko Bayarbe, kai har da wata irin ƙiyayya suka ɗauko wa kayukansu ta babu gaira babu sabab, wai ita ƙiyayya saboda  ƙwallon ƙafa ko siyasa, ka ga dai yadda waɗannan ƴan siyasa suke haɗe suna ta azurta kansu da dukiyar ƙasa, idan ba su da lafiya sai su je ƙasashen Turai ko Asiya neman magani, karatun ƴaƴansu su je ƙasashen Turai da Amurka, idan za su yi siyayyar kayan aure su je Dubai ko birnin Sin ko Istanbul kuma da dukiyar ƙasa, amma idan suka mutu sai a dawo da su a cikin maƙabartar talakawa a binne su tare, amma duk da hakan talakawan bil'adama sun gaza fahimtar yaƙin da suke tunkara, ka dubi mu dai duk yadda muke jin yunwa idan muka ci abinci, muka ƙoshi muna rage shi ga jakai yan'uwanmu, amma sai ka ga mutum guda ya karkatar da dukiyar mutane fiye da miliyan shi kaɗai ya keɓanta kansa da ita, ta yadda ko zai shekaru ɗari biyu zai yi a bayan ƙasa, ba zai iya sa cinye ta ba, amma haka zai ƙyale maƙota da sauran yan'uwansa suna ta fama da yunwa, shi kuma idan ya tashi karin-kumallo ko kalaci haka za a jera masa abinci kala-kala ta yadda ko cikin giwa ke gare shi ba zai iya cinye rabin abincin ba. Idan ka koma wajen ƙwallon ƙafa ka dubi yadda wani ɗan'uwa bai iya magana da dan'uwansa, kai a wani waje ma har kisan juna ake yi saboda banbancin kulob ɗin ƙwallon kafa, ko ka ga yaro ƙarami saboda ƙungiyanci yana zagin sa'an babanshi, ka taɓa ganin haka a duniyar jakuna?

Ya kai ɗana ka taɓa ganin jakin arewa ya kashe na kudu saboda banbancin yare ko banbancin addini kamar yadda su ƴan'adam suke riyawa? Ko ka taɓa ganin jaki ya sace ɗan'uwansa yana jiran a ba shi kudin fansa, ko ka taba ganin jaki ya shiga da nakiya da abubuwan da ke fashewa a wuraren ibada ya kashe ƴan'uwansa? Ka taɓa ganin jaki ya yanka ɗan'uwansa kawai saboda ya yi asirin kudi da shi, ko ka taɓa ganin jaki yana neman jaki ɗan'uwansa namiji da niyyar jin daɗi, duk matan da suka yi yawa kamar ƙarya a bakin ƴan siyasa, ko ka taɓa ganin jaki namiji ya takarkare ya mayar da kansa mace, yana ɗabi'a da halaye irin na matan jakai, ko ka taɓa ganin jaka mace tana wani abu na rashin hankali wai shi gwagwarmayar ƙwatar hakkin matan jakai da addini ko al'ada ta karɓe musu?

Jaki ɗa: (cike da murna da jin daɗi da murmushi) ya ce "A'a wallahi baba ban taɓa ganin haka ba a duniyar jakuna, amma duk ina ganin haka a tsakanin ƴan'adam".

Jaki uba: Haka ne, kuma za ka taɓa gani ba, duk da cewa mu ba a halicce mu don mu yi bauta kamar yadda aka halicci ƴan'adam ba, amma a haka za ka ga wani cikin ƴan'adam yana cewa Allah uku ne, wani ma ya ce komi Allah ne, wani ya ce Allah yana ko'ina wani kuma idan ya sha ta fi ƙarfin cikinsa sai ya yi musun samuwar Allah, ya kai ɗana yanzu ka yi dubi kuma ka yi tunani da hankalinka na jakuna shin da mu da waɗancan ƴan'adam waye ya fi cancanta a siffanta shi da jaki? Ya kai ɗana ka ƙyale ƴan'adam su faɗi duk abin da suka ga dama, mukam ya ishe mu alfahari duk da kasancewar mu jakai, amma kuma ba mu yin ƙarya, ba mu kisan juna, ba mu sata, ba mu jin haushin juna, ba mu zagin juna, namijin jaki bai neman namiji!

Waɗannan kalmomi sun burge jaki ɗa, ya yi farin ciki sosai ya yi alƙawali ga mahaifinsa a kan zai ci gaba da kasancewa jaki ɗan jaki har lokacin da Allah zai mayar da shi turɓaya.

Abbas Musa Jega
25101447H
13042026M

AMSOSHI

Post a Comment

0 Comments