Ticker

6/recent/ticker-posts

Biya Abin Da Ka Dauka Wa Mamaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ni ne na ɗauke abin wani, na je na sayar ba tare da ya sani ba. Yanzu kuma ya rasu, shi ne nake son in biya shi. To, zan biya asalin farashin abin ne, ko kuwa yadda na sayar da shi?

BIYA ABIN DA KA ƊAUKA WA MAMACI

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Ɗaukar kayan wani mutum ba da yardarsa da izininsa ba haram ne. Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:

یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ لَا تَأۡكُلُوۤا۟ أَمۡوَ ٰلَكُم بَیۡنَكُم بِٱلۡبَـٰطِلِ إِلَّاۤ أَن تَكُونَ تِجَـٰرَةً عَن تَرَاضࣲ مِّنكُمۡۚ

Ya ku waɗanda suka yi Imani! Kar ku ci dukiyoyinku a tsakaninku a bisa zalunci, sai dai in ya kasance a bisa ciniki ne, a bisa yarda daga gare ku. (Surah An-Nisaa’i: 29).

Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« فَإِنَّ دِمَاءَكُمْ وَأَمْوَالَكُمْ وَأَعْرَاضَكُمْ بَيْنَكُمْ حَرَامٌ كَحُرْمَةِ يَوْمِكُمْ هَذَا ، فِى شَهْرِكُمْ هَذَا ، فِى بَلَدِكُمْ هَذَا »

Domin jinainanku da dukiyoyinku da mutuncinku haram ne a tsakaninku, kamar haramcin yininku wannan, a cikin watanku wannan, kuma a cikin garinku wannan. (Sahih Al-Bukhaariy: 67,105, 1739; Sahih Muslim: 1218, 1679).

Kuma wajibi ne ga wanda ya aikata wannan ta’asar ya tuba ga Allaah (Tabaaraka Wa Ta’aala) a kan haka, don ya saɓa masa. Sannan kuma dole ya mayar da abin da ya ɗauka ga mai shi. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« لاَ يَأْخُذَنَّ أَحَدُكُمْ مَتَاعَ أَخِيهِ لاَعِبًا وَلاَ جَادًّا ، وَمَنْ أَخَذَ عَصَا أَخِيهِ فَلْيَرُدَّهَا »

Kar ɗayanku ya kuskura ya ɗauki kayan ɗan’uwansa ko da wasa ne ko da gaske. Kuma duk wanda ya ɗauki sandar ɗan’uwansa, to ya mayar da ita. (Abu-Daawud: 5003; At-Tirmiziy: 2160; Ahmad: 4/221; kuma Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Sahih At-Targheeb: 2808).

Malamai (kamar a cikin Tamaamul Minnah: 4/98-100) suka ce: A ƙarƙashin wannan akwai wasu abubuwan lura, kamar haka:

1. Ɗawainiya da wahalhalun mayar da kayan duk a wuyan shi da ya ɗauke su suke, ba a wuyar mai kayan na asali ba.

2. Idan kuma abin da ya ɗauken ya lalace ko ya salwance, to wajibi ne ya biya irinsa daidai-wa-daida, ko kuma ya biya ƙimarsa na kuɗi.

3. Sannan kuma ko da abin da ya ɗauka ya ƙaru ta hanyar hayayyafa ko ribar ciniki da makamantan hakan, to wannan ƙarin ma na mai kayan ne, kuma dole ya mayar masa.

4. Sannan kuma idan wani abu daga cikin abin da ya ƙarun ya salwanta a hannunsa, to shi ma dole ya biya mai kayan. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« لَيْسَ لِعَرَقٍ ظَالِمٍ حَقٌّ »

Babu wani haƙƙi ga jijiyar zalunci. (Abu-Daawud: 3073; At-Trimiziy: 1378; kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin Al-Irwaau: 1520).

Yanzu da mai kayan ya rasu, sai ya ci gaba da roƙa masa gafara, saboda cutar da shi da ya yi. Sannan kuma sai ya mayar da dukkan haƙƙoƙin ga magadansa.

Allaah ya ƙara mana ilimi mai amfani.

 Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments