Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mijin Da Ya Saki Matarsa Don Tsoron Tsinuwar Mahaifiyarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, mahaifiya ce ta ce za ta tsine ma ɗanta in bai saki matarsa ba. To, idan ya sake ta a kan haka sakin ya yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

W Alkm Slm W Rhmtul Laah.

Malamai sun yarda cewa sakin wanda aka tilasta shi a kan sakin ba ya aukuwa, saboda hadisin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda Al-Imaam Ibn Maajah (2045) ya riwaito kuma Al-Albaaniy a cikin Sahih Al-Jaami’ (1836) ya inganta shi cewa:

« إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِى الْخَطَأَ ، وَالنِّسْيَانَ ، وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ »

Haƙiƙa Allaah ya yafe wa alummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta su a kan sa.

Wannan maganar kuma ita ce gaskiya in shaa’al Laah, domin ko ba komai wanda aka takura wa ba sakin ya yi nufi ba. Ya dai yi nufin kauce wa cutar kisa ko salwantar wata gaɓa ko asarar dukiya ko ɗauri ne kawai.

Amma kuma malamai sun sanya sharuɗɗan da sai an cika su kafin a ce saki ya zama na wanda aka tilasta masa:

1. Ya zama tilascin ta fuskar zalunci ne a gare shi, amma ba kamar wanda yake cutar da matarsa kuma don haka alƙali ya tilasta masa ya sake ta ba.

2. Ban da kamar wanda matar take hana shi sauke haƙƙoƙin addini kamar sallah da azumi, idan iyaye suka tilasta shi ya sake ta. Wannan ma ba tilasci ba ne.

3. Ya zama tilascin daga wani mai ikon sarauta ko wani azzalumi ne a kansa, kamar wani ɗan fashi ko mai garkuwa da mutane.

4. Ya zama shi yana da marinjayin zato a kan cewa mai sarautan ko azzalumin zai zartar da barazanar da ya yi masa idan bai saki matar ba.

5. Ya zama abin da za a zarta masa wani abu ne da zai cutu da shi cutarwa mai girma, kamar kisa ko duka mai tsanani ko ɗauri ko tsarewa na tsawon lokaci.

6. Amma zagi ko tsinuwa ko ƙwace wani abu kaɗan na dukiyarsa, da sauran makamantansu duk ba tilasci ba ne. (Tamaamul Minnah: 3/146-7)

Don haka, barazanar tsinuwa daga mahaifiya bai isa ya zama tilasci ba a gare shi. Kuma ko da ya saki matarsa a kan haka, sakin bai tabbata ba.

Sai dai ko in ta kafa hujja a kan hakan ne da cewa: Matar tana hana mijin nata tsai da addini ne kamar zuwa sallah a kan lokaci saɓanin yadda yake kafin ya aure ta, kuma an rasa hanyar hana ta hakan sai ta hanyar sakin. A nan idan ta tilasta shi ya sake ta daidai ne, kuma sakin ya tabbata, saboda shahararriyar nan ta ƙissar Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa).

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments