𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum warahamatullah. Malam Barka da warhaka, Allah ya ƙara wa malam lafiya. Dan Allah malam ina son a taimakamin da shawara da kuma addu'a da zan ringa yi saboda zan yi aure kwanan nan in sha Allah. Gaskiya Alhamdulillahi gidansu kuma tanada tarbiyya ba wata matsala a'Alhamdulillahi kuma tanada addini Saura kwana goma sha takwas na gode.
Wannan rubutu yana ƙunshe da shawarwari ga ma'aurata ko masu shirin yin aure.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum Salaam Wa
Rahmatullahi Wa Barkatuhu. Ameen Ya Yayyu Ya Ƙayyum:
Abu na farko dai yakamata ka
sani cewa shi Aure Sunnah ce daga Sunnar Annabawan Allah, a cikin Annabawan
Allah wadda bai yi Aure ba shi ne Annabi Isah (A.S). Sa'annan shi Aure Amana ce
wadda Allah ya dankawa Bayin Sa musamman ga Kai Namiji da kake shugaba ga wadda
ka Auro ta, shiyasa Allah ya ce saki yana gurin ka ne bawai yana gurin Matar ka
ba, kada ka ɗauki Aure cewa Jima'i da Matar ka shi ne
babbar dalilin da ya sa zaka Auro Yar mutane ka ajiye a gidan ka, shi Aure
kamar misalin ne a ce Mace ta haihu yanzu da haihu shin mene ne babbar burin ta
da Buƙatar ta akan wannan Yaro da haifa? Ka ga
burin ta shi ne ta ba shi Ilmi, Tarbiya, ta kula da shi da rayuwar sa har girma
ya zama mutumin Kirki wadda duniya zatayi Alfahari da samun sa har ma wasu suyi
kwadayin ina ma su ma Allah ya ba su irin wannan Yaron, Shin wannan Matar da
tayiwa Ɗan ta haka yaya kake tunanin rayuwar ta
zai kasance anan duniya da kuma zuwa Lahirar ta?
Ka ga duniyar ta zai yi kyau
a dalilin Yaron ta, Lahirar ta zai yi kyau a dalilin ba shi kulawa da ilmi da
Tarbiya da tayiwa rayuwar sa, amma idan a ce ta bar shi kara zube fa? ka ga
duniyar ta ba zai taɓa yi mata daɗi ba
haka Kuma Lahirar ta akwai matsala, toh haka misalin Aure yake Amana ce Allah
ya bawa Namiji har da ita Macen amma naka ya fi yawa domin kaine Shugaba idan
ka ce Jima'i kawai shi ne Buƙatar
ka toh Lahirar ka akwai matsala, sa'annan ka sani cewa a ranar Alƙimaya sai Allah ya tambaye ka abisa
wannan Amanar da Allah ya ba ka na shugabantar Matar ka da Yaran ka.
Annabi Muhammad Sallallahu
Alaihi Wa Sallam Ya ce a ranar Alƙimaya
za ka zo a ɗaure abun da zai kunce ka daga wannan Ɗaurin da Allah ya yi ma, shi ne irin
yadda ka gudanar da zamantakewar Auren ka tsakanin ka da Matar ka da Yaran ka
irin Adalci da ka yi mata da kyautatawa da ta samu a gurin ka ba tare da ka
kuntatawa rayuwar ta da na Yaran ta ba, toh wannan Adalcin shi ne zai kunce ka
daga wannan Ɗaurin, amma idan aka
samu cewa ka zalunce ta ka kuntatawa rayuwar ta ba ka yi Adalci gare ta ba
kullum aikin ka kenan sanya ta cikin bakin-ciki da kunci da yin nadamar Auren
ka, toh dalilin wannan za ka shiga cikin ukubar Allah ayyukan ka na alkhairi
kab ɗin
su suna iya zubewa a dalilin wannan kaɗai.
Ka sani cewa Aure ba wasa
bane Aure ibada ce, kamar yadda za ka yi Sallah Azumi ka samu Lada ka ƙi yin sa ka samu Zunubin da zai sa ka
shiga Wuta toh haka Aure ma yake, kuma duk yadda ka ɗauki
rayuwar Aure a waje toh a cikin gidan ka kana iya samun saɓanin
tunanin ka, ka sani cewa daga ranar da aka ɗaura
Auren ka da ita toh an ɗauki wani nauyi ne mai
girman gaske an ɗaura ma, abu na farko akwai
Amanar iyayen ta a kanka domin sun yarda da kai 100% shiyasa suka ɗauki
Yar su suka ba ka domin sun san cewa ba za ka taɓa
cutar da rayuwar Yar su ko cin Amanar ta ba, sun amince da kai sosai bawai Yar
su ta rasa ma nema bane shiyasa suka ba ka ita a'a, wasu wadda suke neman ta ma
wata kila ba za a taɓa haɗa ka
da su ba domin sun fi ka komai amma sabida sun amince da kai ne suka ce ga Yar
su sun ba ka ita ka Aura, ka ga akwai Amanar su a kanka idan ka ci Amanar su
Allah ba zai bar ka ba.
Ka sani cewa akwai Amanar
Allah da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a kanka, da a ce a yanzu Allah
zai ɗauki
rayuwarka ka mutu bakayi Aure ba, toh da sauki a gurin Hisabin ka, amma a yanzu
da ka zama Mijin wata toh ka sani cewa akwai Amanar Allah da Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam a kanka na zaman ka Mijin ta, idan ka Mutu sai Allah
ya tambaye ka akan wannan Baiwar Allah ɗin,
kenan duk wasu Haƙƙoƙin ta da Allah Shimfida ma a kanka, dole
ne ka sauke daga kanka, duk wasu abubuwan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Sallam ya yi magana akan ayiwa Mace, dole ne idan kana da shi ka sauke su a
kanka, idan ka ƙi
sauke su toh nan ne ake cewa ka ci Amanar Allah da Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam domin ga abun da Shari'ar Musulunci ta ɗaura
ma akai, amma ka ƙi ka
biyewa son zuciya ka je kana cutar da ita.
Ka sani akwai Amanar
Waliyyan ku 2, domin sun yarda da Kai sun Amince da Kai ne ya sa suka wuce ma
gaba sukayi Ruwa suka yi tsaki har yau Allah ya sa ka Mallaki Matar ka, da a ce
ba su yarda da kai ba, da ba za su taɓa
wucewa gaba domin nema ma Auren ta ba, toh ka sani cewa su kansu idan ka
kuskura ka ci Amanar su gurin yin abun da bai dace ga ita ba, toh Allah ba zai
bar ka ba, ga kuma Amanar iyayen ka dalilin da ya sa suka ce ka aure ta domin
sun yarda da Kai sun Amince da Kai sun San waye Ɗan
su, shiyasa duk wani sheda sun je sun bayar a kanka domin ka Mallaki Matar ka
toh ka sani cewa idan ka yi abun da ya saɓawa
abun da suka je suka fada a kanka toh ka ci Amanar iyayen ka Allah ba zai bar
ka ba.
Kuma Waliyyin Matar ka da
Waliyyin ka dole ya zama kana Jin maganar su matukar abun da suka gayawa bai Saɓawa
Shari'a ba, sa'annan ya kasance kana Kiran su kana gaishe su bawai daga an ɗaura
Auren ku shikenan Kai ba ka ma San Waliyyin Matar ka ba, ba ka San Waliyyin ka
sai abu ya faru ka fara neman su waye ne Waliyyin Matar ka da naka, Kuskure ne
wannan dole ka girmama masu ka ji maganar su ka rika zuwa kana gaishe su da
Matar ka domin sune shugabannin Auren ku.
Ka sani cewa a yanzu da ka
zama Mijin ta, itama kanta akwai Amanar ta a kanka, domin wata kila Samarin da
suke zuwa neman ta sun fi uku (3) kuma wata kila duk lokacin da za ta fita waje
ba za ta rasa waɗanda za su ce suna Son ta da
Aure ba, sa'annan inda a ce yau za a ɗauke
ka a zayawa Anguwar ku ko garin ku wallahi kai wata kila a gurin wata Macen kai
ba ka ise ta kallo ba, balle ma har ta ji wai tana son ka, toh amma ita ta ce
ta ji ta gani duk duniya babu wadda ta ke so a rayuwar ta ya zama Mijin ta Uban
Yaran ta sai kai, iyayen ta da ƙawayen
ta da wasu wata kila sun hanata kar ta Kuskura ta Aure ka amma ta ce a'a kai
mutumin Kirki ne, kai mai addini ne ai kana son ta tsakanin ka da Allah zaka
rike ta da gaskiya da Amana, toh ka sani cewa idan ka ci Amanar ta gurin
kuntatawa rayuwar ta gurin rashin yin Adalci ga rayuwar ta wallahi Allah zai ma
azaba, ka sani cewa bawai ta rasa waɗanda
ta ke so bane ya sa ta amince ka zama Mijin ta, Kuma ka sani a yanzu sabon
rayuwa ce za ta shiga domin na farko idan garin ku ɗaya
ne Anguwar ku Ɗaya ne toh daman ba'a
gidan ku ta ke ba, idan kuma garin ku ɗaya
ne toh Anguwar ku ba ɗaya bane yanzu ta shigo
sabon Anguwa da ba ta san kowa ba sai kai, ta zo cikin gidan da bata saba da
kowa ba sai kai, idan garin ku ba ɗaya
ba haka ta zo inda Bata son kowa ba sai kai, ta ce ta ji ta gani a haka zatayi
rayuwa da kai ko a cikin Rami ne, ba ta San Namiji ba a fannin Jima'i kai ne
mutumin farko da za ta sa a cikin Farjin ta, toh kada ka yarda ka ci Amanar ta
domin Allah ba zai bar ka ba.
Ka sani cewa daga ranar da
aka ɗaura
Auren ka da ita toh duk wasu Haƙƙoƙin da suka rataya wuyar iyayen ta toh a
yanzu ya sauka daga wuyar su ya koma kanka, Cin ta yana kanka, idan ka ci dole
ne itama ta ci, shan ta yana kanka, gurin kwanan ta yana kanka, idan ta yi Rashin
lafiya, idan rashin lafiyar wadda za a Sha magani ne a gida a warke toh dole ne
ka yi gaggawar zuwa siyo mata magani ta Sha, idan kuma na zuwa Asibiti ne dole
ne ka ɗauke
ta zuwa Asibiti a ba ta lafiya sai ta warke ka ɗauke
ta ka dawo da ita gidan ka, Tufãfin Sawan ta idan ka dinkawa kanka sabon Tufãfi
toh itama ka yi mata, Ilmin ta da duk wasu Bukatun ta na yau da kullum dole ne
idan kana da shi ka yi mata su, idan Allah ya ba ku Yara duk wani abu da ka San
Uba yana yiwa Ɗan sa ko Yar sa toh
wajibi ne a kanka. Matukar kana da abun da zaka wadatar da Matar ka sai ka ƙi yi bawai babu ba, amma kana iya yiwa
kanka ita kuma ko oho idan ma ta tambaye ka ka yi fushi ka kama Zagin ta ka
tsanewa iyayen ta bayan Haƙƙin
ka ne ka yi mata toh ka sani cewa yin haka Zalunci ne da rashin Adalci Kuma
Allah ba zai bar ka ba.
Mata suna son Miji me nuna
kulawar sa da damuwar sa a kansu, sabida haka ka kasance ɗaya
daga cikin Namijin da ko ciwon kai ne Matar ka ta ce tana fama da shi, toh ka
tsaya dakyau gurin nuna damuwar ka da kulawar ka da Tausayin ka a kanta sosai,
kai idan ma akwai kuɗin cefene a Wannan ranar toh
ka ce yau ba za ka je gurin Sana'ar ka ba har sai ka kula da ita ta samu lafiya
gobe za ka je aikin ka ka zauna ka yi ta kallon ta ka lallaɓa ta
akan ta Sha Magani, idan kuma za ka je gurin aikin ka, toh ya kasance cewa duk
mintuna ko Awanni ka kira ta ka ce yaya ciwon kan naki? ka tambaye ta ta Sha
Magani? A Yinin dai ka kira ta irin Sau 20 da tura Mata love messages wadda zai
kwantar mata da hankalin ta, wallahi wata kila ko ba ta Sha Magani ba za ka iya
samun cewa a dalilin yadda ka nuna damuwar ka da kulawar ka da Tausayawa
rayuwar ta hakan zai sa ciwon ya warke ko ba ta Sha Magani ba, sabida haka ita
Mace tana nan ne kamar Jariri duk yadda Jariri ya kai ga yiwa Mahaifiyar sa
Kuka idan ta ɗauke shi tana Lallaɓa
shi tana Rarrashin sa sai ka ga ya yi shiru har rika yin dariya kamar ba shi
yake ta Kuka ba, toh haka rayuwar Mace yake.
Mace tana son Namijin da zai
damu da damuwar ta ko matsalar ta, Mace tana son ganin Namiji me kyautatawa
sosai Yawan kyauta, misalin tana da Yan uwa ko iyaye suna raye ka rika ware
kyauta na musamman daidai Karfin ka kana yi musu shi, misalin a ce a wannan
wata sai ka ware wani dan kyauta ko da a ce Sabulun naira 100 ne ka siya ka ce
mu je mu gaishe da iyayen ki sai ku je bayan kun je Kun gaisa sai ka ce ki ba
su wannan, wani watan ka ware wani abu ka ce mu je gurin iyaye na Suma ka yi musu
irin yadda kayiwa nata iyayen, sa'annan zuwa Sada Zumunci ziyara idan an yi
mata rasuwa ko Haihuwa a cikin Yan Uwan ta da naka duk ka ware lokacinka ka
rika ba ta izinin zuwa gurin su Koda a ce ba za ka ɗauke
ta da kanka zuwa gurin ba kawai ɗauki
kuɗin
moto ko Mashin ka ba ta ka ce yau ki je yini a gurin Iyayena ki Taya su aiki
karfe kaza ki dawo, wani watan ka ce ga kuɗin
mota ko Mashin ki je gurin Iyayenki ki Yini ki taya su aiki ki dawo karfe kaza,
ko kuma mu je Ta'aziyya ko yin barka gidan su wane, wani lokacin ka ce ga shi
kuɗin
Mashin ki je gidan Abokina wane ki yi ziyara wani lokacin gidan ƙawayen ta, wani lokacin gidan Waliyyin
ka ko nata, ko ba ta nema yin hakan ba ka nuna mata mahimmancin sada Zumunci ga
Yan Uwa da Abokan Arziki abu ne me kyau idan kuma ta nema hakan kar ka hanata,
nuna kulawar ka a kanta wallahi hakan zai sa duk inda ta zauna Addu'a zatayi ma
da yin Alfahari da cewa ta samu Miji kai za ta iya bugan zuciya ta ce Mijin ta
ya fi kowa.
Mace tana son Namiji me
Addini sosai da riko da shi, idan ka ga Mace ba ta damu da irin wannan Namijin
ba, toh fa gaskiya ka yi Rashin Sa'a, sabida haka Mace tana son Namiji me
Addini da riko da shi sosai don haka ka zama mutum Mai Addini da riko da shi da
tsoron Allah a Zuciyar ka, sa'annan Mace tana son Namiji wadda yake faɗin
gaskiya komin ɗacin ta da riko da Amana da aiki da su,
sabida haka dukkan dare ya kasance cewa kana ware lokacin ka ka tayar da matar
ka ce ta yi Alwala idan tayi, sai kuyi Sallar Nafila ko da kuwa Raka'a 2 tak
kuka yi ka yi Addu'a gobe ma kuyi hakan kace yau ki yi mana Addu'a, toh wallahi
ba Karamin kara karɓuwa zakayi a gurin ta ba
indai Mace ce ita mai addini, sa'annan Allah zai Kara haɗa
kanku duk wani Sharrin sheɗan ko na mutane Allah zai
tsare ku daga wannan, domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam har Addu'a
yayiwa Ma'aurata Ya ce Allah ya jikan wadda zai tashi cikin dare domin yin
Sallar Nafila amma idan ya tashi sai ya tayar da Matar sa in ta ƙi tashi sai ya dan zuba Mata Ruwa Domin
ta tashi, ka ga kenan ya zama a duk dare kana tayar da matar ka kuna yin Sallar
Nafila ko da Raka'a 2 ce.
Mace tana son Namiji me son
yin Ibada kada ka taɓa yarda a ce kana gida amma
har ayi Sallah a idar ba ka fita zuwa Masallaci yin Sallah tare da Jama'a a
cikin Jam'i ba, kowane Sallah indai ya same ka a cikin gidan ka toh ka yi gaggawar
yin Alwala ka je Masallaci, ita kuma ka Umarce ta duk aikin da ta ke yi ta bar
shi ta je ta yi Sallar ta idan ta dawo ta ci gaba, idan kana gurin aiki ne da
zarar ka ga lokacin Sallah ya yi ɗauki
wayar ka, ka tura Mata Sakon message na soyayya sa'annan ka ce mata duk abun da
ta ke Yi indai ba ta yi Sallah ba toh a yanzu ta bar komai ta je ta yi Sallar
ta, ya kasance cewa duk lokacin Sallah idan ya yi kana Kiran ta a waya ko da a
ce ta yi kar ka damu ka kira ta sake jaddada mata, ka damu da ibadar ta cewa ka
kira ta ka ji cewa ta yi ko ba ta yi ba idan ta yi shikenan sai ka yi mata
Addu'a da fatan Alkhairi idan batayi ba nan ma ka yi mata da Addu'a da fatan
Alkhairi sai ka ce ta je tayi.
Ka sani cewa abubuwan ɗaura
kake da Matar ka akai, da abubuwan da kake yi a cikin gidan ka toh fa sune
Yaran ka za su tashi da shi, idan ya kasance ka yi aiki da waɗannan
abubuwan gurin kiyaye ibadar ta da gurin ɗaura
ta a Hanya mai kyau da naka kuma kana yin irin abubuwan da na gaya ma toh In
Sha Allah Yaran ka za su samu Tarbiyar da Addini me kyau kuma Kai kanka za ka
ji daɗin
rayuwa da ita.
Idan kana da ilmin Addini ya
kasance kullum kafin ku kwanta Bacci ka yi mata Nasiha ka tunatar da ita ka
nuna mata Addini idan akwai abun da ba ta sani ba ka ce ta tambaye ka, in ma ba
ka sani ba ka ce za ka nema mata amsar ta, da Asubahi haka idan ka dawo daga
Masallaci ya kasance ka zauna da ita ka yi mata Nasiha ko da na mintuna 2 ne
yayi, domin Mace tana son Namiji me Addini da nuna kulawar sa gare ta akan
ibadar ta don haka ka zama irin wannan.
Mace tana son Namiji Mai
Tsafta, sabida haka idan ba ka da Tsafta toh ka Koya tun yanzu ya kasance kana
da Tsafta sosai da son Sanya Turare a kullum sa'annan kar ka zama agogo sarkin
aiki kai kullum kana hanyar aiki ba ka da lokacin dawowa sai dare can toh akwai
matsala, ya kasance kana dawowa gida akan lokaci sa'annan idan ka dawo ka yi wanka
ka sa kaya Masu kyau ka ce ta zaba ma kayan da za ka sa? idan ta ba ka su sai
ka sa ka Sanya Turare ka zauna kusa da inda take aiki kana Hira da ita kana
wasa da dariya da ita, wani lokacin ka ware rana guda ka ce yau zaka taya ta
yin aikin cikin gida ko ba ka iya ba ta Koya ma ka taya bayan kun gama ka yi wanka
ka Sanya Turaren ka ka zauna a gaban ta ka ce wannan wankan naki ne ka zauna
kawai ta yi ta kallon ka kuna Hira kana ɗebe
mata kewar komai nata na rayuwar ta, idan ka kasance kana haka wallahi Matar ka
ba za ta kalla wani Namiji a waje ta yi Sha'awar Ina ma da shi na Aura ba, amma
idan ba ka irin wannan toh akwai matsala sosai domin mata suna son Namiji Ɗan gaye Mai Tsafta da nuna kulawa gare
su, kamar yadda kaima kake son Mace Irin wannan su ma haka suke so.
Sa'annan Mace tana son Yabo
sosai musamman daga gurin Mijin ta, shi Yabo a Shari'ar Musulunci abu ne me
kyau bawai Haramun bane, toh ya kasance komin kankantar aiki idan Matar ka ta
yi ma shi ko bai yi ma kyau ba ka Yabe ta ka nuna mata cewa duk duniya ma babu
wata Macen da ta isa ta yi irin wannan sai ita kaɗai,
ka nuna cewa ka ji daɗin hakan sosai fiye da
tunanin ta, ka yi mata Addu'a sosai kayiwa iyayen ta Addu'a sosai kai a lokacin
ma idan kana da ɗan wasu Kuɗi ka
ce gashi na ba ki kyauta dalilin wannan abun da kika yi, ka yi mata Addu'a ka
sanya mata albarka ka yi mata fatan Alkhairi duniyar ta da Lahirar ta toh in
sha Allah gobe zatayi wadda ya fi wannan kyau domin Jin daɗin
kalaman ka, kar ka Kuskura Matar ka ta yi wani abu ka ce zakayi shiru ba ka ce
komai akai ba, ko Kwalliya ta yi Kai ko wanka ta yi a yanzu ta fito daga wankan
ba ta yi kwalliyar ba, toh ka ce kai ai ko bakiyi Kwalliyar nan ba wannan
wankan kaɗai ya wadatar ka Yabe sosai, idan ta yi kwalliyar
ka Kara Yabon ta sosai ka sanya mata albarka, idan ta yi girki ko ta yi wani
abu a ckin gidan ka ko Shara ne ko gyara cikin Ɗakin
kwanan ku, Kai komin kankantar wannan abun indai ita ne ta yi shi toh kada
Bakin ka ya yi shiru ka tsaya dakyau sosai ka Yabe ta, ka yi mata Addu'a sosai
in ma kana da wani Abu ka yi mata kyauta toh ka yi idan babu kalaman ka kaɗai
sun isa, in Sha Allah za ka ga yadda Matar ka za ta kara Jin son ka sosai fiye
da yadda ba ka tsammani, amma idan ba ka yin waɗannan
abubuwan gaskiyar magana ana iya samun matsala.
Mace tana son Namiji wadda
zai Rika zama da ita yana Hira da ita Yana wasa da dariya da ita, Sabida haka
ka Rika ware lokaci duk dare kafin kuyi Bacci ka zauna da ita kuyi ta Hira kana
wasa da dariya ita, ka tambaye ta mene ne matsalolin ta da Bukatun ta kar ta Ɓoye ma komai ta gaya ma cikin wasa da
dariya ka yi Hira da ita ko da na awa 1 ne kafin nan ku je ku kwanta, kullum
haka toh in sha Allah Matar ka ba za a samu matsala a gurin ta ba, amma idan ka
ce a'a wayar ka shi ne abokin hiran ka don yanzu ta zo gidanka ka samu abun da
kake so a jikin ta, Kai ba ka da lokacin ta ai idan ka dawo Kai ka gaji ba kada
lokacin zama da ita kana Hira da ita Amma kana iya chatting Sama da awa 3, toh
gaskiyar magana za ka iya samun matsala da ita duk hakurin ta akwai ranar da za
ta gaji da wannan, don haka Mata suna son Namijin da zai ɗauke
su abokin wasan su abokin rayuwar su, kuma ƙawar
su, idan kana Yawan zama da Matar ka kana bata lokacin ta da lokacin yin Hira
da ita da wasa da dariya da ita, wata kila in an gan ku tare ma za a ce ai wa
da ƙanwa ce ba mata da Miji bane toh za ka
ji daɗin
zama da ita sosai.
Mace tana son Namiji mai
hakuri da juriya da Tausayi da yafiya, don haka akwai ranar da in ta yi ma wani
abun za ka ji duk duniya ka tsane ta sosai ba ka son ganin ta, akwai lokacin da
kuma idan ta yi abu wallahi za ka ji duk duniya babu kamar ta, sabida haka ka
zama Namiji mai hakuri da yafiya da Tausayi idan ta yi ma abu, domin Hankalin
ta da naka ba ɗaya bane, Hankalin Mace wani lokacin
yana nan kamar na Yaro karami ne, don haka duk lokacin da ta yi ma abun ɓacin
Rai toh kawai ka danne zuciyarka ka nuna ma abun bai dame ka ba idan ma ka
fahimci kamar za ta gane cewa abun ya dame ka toh ka zo ka kwantar mata da
hankalin ta ka nuna mata babu komai ka ce ka yafe mata ka yi mata Addu'a da
fatan Alkhairi a rayuwar ta, idan ba ta yi ma abun da kake so ba, toh ka tsaya
ka tuna abun da ta yi ma a baya wadda ka ji daɗin
sa, sa'annan ka yi mata uzuri idan ta yi ma Kuskure kar ka yarda a ce komai ta
yi laifi ne a gurin ka, ya kasance kana yi mata uzuri idan ta yi Kuskure tare
da yafe mata abun da ta yi ma na Kuskuren, idan ka kasance kana yin haka in Sha
Allah Matar ka za ka ji daɗin zama da ita.
Ka sani cewa duk wasu iyayen
Matar ka toh naka ne kai ma, ya kasance ka San yadda za ka kare Darajar iyayen
ta da duk dangin ta a gaban ta ne ko a bayan ta, kamar yadda za ka iya kare
Darajar iyayen ka da Mutuncin su da Ƙimar
su da na Yan Uwan ka, toh ka sani cewa su ma iyayen Matar ka da Yan uwan ta
naka ne, idan ba ka son a Zagi iyayen ka ko Yan Uwan ka a gaban ka toh kada ka
yarda ka bari a Zagi iyayen Matar ka ko Yan Uwan ta a gaban ka, sa'annan kai ma
kar ka yarda ka Zagi iyayen ta ko Yan Uwan ta ko a gaban ta ne ko a bayan ta
duk ɓacin
ran da ta sa ka kar ka yi hakan, dole ne ya kasance ka kare Darajar su da
Mutuncin su.
Ka San Darajar Matar ka da
yadda za ka kare Ƙimar
ta da Mutuncin ta domin Kiwo ne Allah ya ba ka kuma sai Allah ya tambaya akan
wannan ko ba ka so, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam kafin ya bar
duniya sai da ya yi ta maimaita Wasiyya akan Mace akan cewa a kyautatawa mata
ayi Adalci a kansu a ji Tausayin su, toh dole ne ka kasance mai yin Adalci gare
ta da kyautata mata idan ka ƙi
kuma toh Alkiyama yana tafe.
Ya kasance cewa lokaci bayan
lokaci daidai wadatar ka, daidai Karfin ka idan ka fahimci cewa kayan Kwalliyar
ta ko kayan wankan ta, ko wani abun da take amfani da shi na yau da kullum
domin faranta ma rai ya kusan karewa, toh ka siyo da Kuɗin
ka ka kawo mata ka ce ga shi, sa'annan ka rika ware lokacin ka domin zama da
ita kana neman shawarar ta a dukkan lamuran ka da kake son yi ko kuma wani abun
da yake damun ka a rayuwar ka, sa'annan ka ba ta damar ba ka shawara da duk
wasu abubuwan da ta ke son gaya ma kar ta ji tsoron fitowa Fili ta gaya ma su,
sa'annan idan ka yi abun Kuskure in ta yi ma magana ko ka ta ba ka shawara akai
toh kar ka yarda ka ƙi ɗaukar
shawarar ta indai shawarar mai kyau ce, sa'annan idan kana abu wadda bai dace
ba idan tazo ta ce Abban wane abu kaza da kake son yi ba daidai bane toh ka ɗaure
ka ɗauki
abun ka sa mizanin Adalci ka ɗauki shawarar ta ka rika ba
wa Matar ka yarda da 100% da gaskiya da Amana, ka nuna mata Kai abokin shawarar
ta ne kar ta Ɓoye ma komai ka manna
Matar ka a jikin ka tamkar Yar ka ce ita, sa'annan ka rika ba ta daman zama da
ita kana jin matsalolin ta da Bukatun ta, idan tana da Buƙatar abu misalin abun ya kai guda 10 sai
ka ce zakayi mata 5, biyar kuma sai wani lokacin idan ka samu, idan Kuma kana
da iKon yin dukka goman toh cikin Farin ciki da Jin daɗi ka
amsa mata cewa zakayi mata su In Sha Allah, rashin ɗaukar
Shawarar Matar ka da rashin ba ta lokacin Hira da ita gurin fadin matsalolin ta
da Bukatun ta, ya kasance kai babu Ruwan ka da ita sai dai idan dare ya yi in
kana son Jima'i ka zo gurin ta ka ce ta ba ka kanta kuyi Jima'i, toh hakan ba
karamin illa zai jawo a gidan ka ba, Matar ka za ta dawo ta tsane ka, Matar ka
za ta dawo idan ta kalla Mazan wasu a waje ta Rika kwaɗayin
ina ma da mijin ta ma haka yake, sabida haka Matar ka, kar yarda a ce ba ka ɗauke
ta a matsayin Abokiyar Shawarar ka ba, sa'annan a ce duk abun da ta gaya ma ba
ka ɗauka
sai naka ra'ayin kawai toh za ka samu matsala sosai.
Sa'annan a Fannin Jima'i a
duk lokacin da za ka yi Jima'i da ita ya kasance kun rufu ma'ana kar ka yi Jima'i
da ita kuna kallon Tsiraicin junan ku ta yadda in wani ya shigo zai gan ku a
Tsirara, baya ga Hakan ku rika yin Addu'a kafin fara yin Jima'i, sa'annan idan
Maniyyin ka ya fita Buƙatar
ka ta biya, toh ka Jira ta itama sa'annan ka tambaye ta akan cewa shin ta gamsu
da Jima'in da kuka yi a yanzu ta wadatu da hakan? Idan ta ce ma eh ta gamsu
shikenan sai ka tashi, idan ta ce ma a'a ita ba ta gamsu ba, sai ka tambaye ta
akan ta gaya ma tsakanin ta da Allah wanne irin abubuwa take so wadda idan ka
yi mata su zai gamsar da ita, ta San cewa ta yi Jima'i me daɗi
wadda Hankalin ta zai kwanta? Idan ta yi ma bayanin komai shikenan sai ka yi mata
irin yadda ta ke so, nan ma ka sake tambayar ta ta gamsu? idan ta ce Eh
shikenan sai ka tashi, kada ka yarda a ce wai duk lokacin da ka yi Jima'i da
Matar ka kai kawai da Maniyyin ka ya zuba cikin Farjinta shikenan Hankalin ka
ya kwanta sai ka tashi ka bar ta sai kuma gobe, toh kana iya samun matsala da
ita sosai, domin wata kila a lokacin da Maniyyin ka ya zuba cikin Farjinta toh
ita kuma a lokacin ne ma Sha'awar ta yake fara motsawa ka ga kenan Kai Buƙatar ka ta biya ka gamsu ta yi ma abun
da kake so amma ita kuma nata bai biya ba, yau ka yi mata haka, gobe ma haka,
toh Matar ka za ta fara tsanan ka, kuma Matar ka duk inda ta zauna wannan
rashin gamsuwa da ba ta samu a gurin ka shi ne zai mata illa ga rayuwar ta ta
dawo ta ji ba ta son ka.
Sabida haka duk lokacin da
ka yi Jima'i da ita toh ka tambaye ta wannan, sa'annan ka rika tambayar ta mene
ne take so ayi mata wadda za ta gamsu? za ta gaya ma komai, kaima ka gaya mata
naka salon, sa'annan idan Matar ka ta neme akan cewa kuyi Jima'i toh kada ce
a'a, kai ba za ka yi ba duk yadda za a yi ka San Yaya zakayi gurin yadda zaka
biya mata Buƙatar ta a lokacin da
ta neme ka, kamar yadda kake da Sha'awa har kake neman ta da Jima'i toh itama
hakane ta ke ji da Sha'awa, kenan itama idan ta ce ka zo kuyi Jima'i kada ka ƙi amsa mata, rashin amsa Kiran ta hakan
zai jawo ma matsala, amma idan kana amsa Kiran ta toh itama za ta gane cewa ita
mutum ce me Daraja a gaban ka, sa'annan duk lokacin da ka neme ta ba za ta ta ƙi amsa Kiran ka ba domin kaima kana yi
mata, sabida haka idan ta ce Abban wane muyi kaza kawai ka tashi a lokacin ka
zo gurin ta kuyi abun da ta ke so, idan Kun yi Ka tambaye ta ta gamsu? Idan ta
ce eh shikenan sai ka bar ta idan ta ce a'a sai ka yi iya kokarin ka gurin
gamsar da ita, In Sha Allah idan kana gamsar da Matar ka ba za ka samu matsala
ba.
Sa'annan ka sani Mace duk
dukiyar ka duk kyan ka duk Mulkin ka duk Arzikin gidan ku, wallahi idan ba ta
samun Kulawar ka, ba ka nuna damuwar ka a kanta, ko Yabon ka a kanta, ba ta
samun gamsuwa a gurin Jima'i, ba ka yin wasa da dariya da ita, ba ka zama kana
Hira da ita, ba ka bata lokacin ka, Kai wayar ka ya fi ta Daraja shiyasa sai ka
fi awa 3 kana online, ba ka ɗaukar Shawarar ta, ba ka
zama da ita ka tattauna wasu matsalolin ka ko nata, ba ka neman shawarar ta,
toh Wallahi ko akan Jima'i ne kaɗai
da rashin kulawar ka a kanta, toh Hakan na iya sawa ka samu matsala sosai da
ita, duk Tarbiyar gidan su duk Ilmin ta, duk dukiyar ka, za ta wasar da su ne,
ita damuwar ta shi ne waɗannan abubuwan, don haka duk
yadda za a yi ka yi kokarin aiki da waɗannan
Shawarwarin da kuma naka fahimtar, matukar ka ɗauki
waɗannan
abubuwan da na gaya ma gaba ɗayan su, wallahi za ka dawo
ka ce min ai zaman ku Alhamdulillah da ita, babu abun da ka rasa a gurin ta har
gurin iyayen ta da dangin ta, amma idan ba ka ɗauki
waɗannan
abubuwan ba toh ana iya samun matsala sosai. Fatan ka gane ko??? ka yi hakuri
bayanin dayawa.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.