Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Zan Iya Fada Wa Saurayina Ko Mijina Cewa Na Taba Aikata Zina?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam. Mace ce ta tashi aure, sai wanda za ta aure ya tambayeta ita budurwa ce, toh mallam gaskiya dai ba cikakkiyar budurwa ba ce. toh mallam ya kamata ta faɗa mishi gaskiya ko kuwa a'a? Kuma idan matar aure ta yi zina shin lallai sai ta tona asirin kanta ga mijinta sannan yafiyarsa gareta za ta karɓu ga Ubangiji??

SHIN ZAN IYA FAƊA WA SAURAYINA KO MIJINA CEWA NA TAƁA AIKATA ZINA?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Bazata gaya masa ba. Domin babu Maslaha idan ta gaya masa. Koda bai Aureta ba, sai kuma yaje yana yaɗawa a Cikin mutane. Kuma Nasan ma zaiyi wahala ya Aureta.

Batun mijinta kuma wannan akwai wata ƙa'ida ta Fiƙhu suka ce wai Tunkuɗe ɓarna shi ake gabatarwa memakon a janyo maslaha, DAR'UL MAFSADA MUƘADDAMUN ALA JALBUL MASLAHA kin ga anan gayawa mijin naki cewa kinyi zina yayafe miki wannan babu shakka maslaha ne, to amma kuma bakida tabbacin cewa mijin zai hakura yayafe miki kuma yaci gaba da zama dake bayan kin gaya masa, kekanki zaki riƙa tunanin infa kika gayamai kinyi zina ze iya cewa ya sake ki, wanda sakin shikuma ɓarna ce, bayan sakin kuma waɗanda basu san kinyi wannan zinan ba duk sesun sani musamman iyayenki kuma hakan bazai musu daɗi ba kema kuma mutuncinki zai zube kin ga wannan duk ɓarna ce, sannan kuma kin tonama kanki asiri bayan Allah ya rufa miki wannan shima duk ɓarna ne.

Dan haka malamai suka ce wacce tasamu kanta a cikin irin wannan halin to kawai taroƙi mijin yayafe mata dukkan laifukan da ta yi masa waɗanda ta sani da wanda bata saniba, amma karta kuskura ta gaya mishi cewa ga abin da ta yi saboda karta buɗe ƙofar waɗancan ɓarnace ɓarnacenda zasu iya biyo baya.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments