Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanzu Dalibai Sun Fi Son Fara Gini Daga Sama

Abu-UbaidaSani

Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email 1: abuubaidasani5@gmail.com
Email 2: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
WhatsApp (Only): +2348133529736

YANZU ƊALIBAI SUN FI SON FARA GINI DAGA SAMA

Sai An Zubar Ake Ɗauka/Ɗiba

Wani abin burgewa da kare-karen maganar Hausawa shi ne, sannu a hankali wata rana mutum zai ci karo da karin maganar da ta dace da wani lamari, tamkar domin al’amarin aka ƙirƙire ta. Karin magana a Hausa takan yi aiki kamar yankan wuƙa ta hanyar dacewa sak da wani yanayi. Babban misali shi ne yadda karin maganar “sai an zubar ake ɗauka/ɗiba” ta dace da abin da yake faruwa ga ɗalibai, musamman masu karatun manyan digirori.

Kimanin shekaru goma sha huɗu (14) da suka gabata, na kasance ina mamakin yadda ake iya zama a rubuta littafi ko kundin bincike. A wajajen shekarar 2011, na taɓa bayyana damuwata ga Farfesa Sa’adiya Omar. Na ce: “Ni fa ina ga duk wasu abubuwa da suka kamata a yi rubutu a kansu, an riga an ƙare. Duk jikina mutuwa yake yi. Me ma mutum zai iya yin rubutu a kai?”

A lokacin sai ta yi dariya, sannan ta ce: “Ai ba a ma yi komai ba. Yanzu ne ma za a fara rubutu. Da zarar ka shiga cikin ‘system’ ɗin, za ka yi ta cin karo da ‘topics’. Yayin da kake karatu, a nan ne za ka riƙa ganin abububuwa masu tarin yawa da ba a yi rubutu game da su ba.” A zuciyata, na aminta da jawabinta ne kawai saboda girman yardar da na yi da ita, da kuma girmamata da nake yi. Amma a haƙiƙanin gaskiya, a lokacin zuciyata ta kasa fahimtar yadda hakan zai iya faruwa. Bayan tafiya ta fara nisa ne na gane zancenta dutse.

Fara Gini Ta Sama

A zahirin gaskiya, ɗalibai da dama da suke fuskantar bincike da rubutun kundayen manyan digiri, suna ƙoƙarin fara gini ne daga sama. Za ku iya yarda da ni yayin da kuka bibiyi misalaina:

Tun a farko, datacciyar hanyar zaɓan batun da ɗalibi yake son yin bincike a kansa shi ne “karatu da bincike tuƙuru.” Ya kamata ne ɗalibi ya duƙufa wajen karance-karance. Sannu a hankali zai naƙalci duk wani salo da siga na yadda ake rubutu. Daga nan zai fara fahimtar falsafar da marubuta da manazartar suke amfani da ita wajen zaƙulo matsalar da ta cancanci bincike, tare da bin matakan nazari tiryan-tiryan domin ƙalailaice ta. Yayin da ya kai gaɓar da ake yi wa take da “hannu ya iya, jiki ya saba,” zai fara fahimtar “giɓi” a wasu fannonin da ya yi nazari game da su. Idan tafiya ta ƙara nisa, adadin giɓi da zai riƙa gani za su ƙaru matuƙa. Daga nan zaƙami da tsumin bincike za su shige shi.

Da yawa daga cikin ɗalibai ba waɗannan matakai suke son bi ba. Hasali ma, wasu sun fi so ne su tambaya domin a ba su batun da ya kamata su yi bincike a kansa. Duk ɗalibin da ya tambayi a ba shi batu domin rubuta kundin babban digiri, ta tabbata bai shirya wa karatun ba. Shiri a nan shi ne, bai yi karatu da bincike da har ya samu cikakken fahimtar cancantar fara binciken babban digiri ba. So yake yi kawai ya fara gini daga sama.

Wani kuwa ba shi da zaɓin ɓangare taƙamaimai da yake son ƙwarewa a kai. Ya zama jemage tsakanin fannoni daban-daban. Buƙatarsa kawai ita ce ya samu batun da za a amince masa domin yin rubutu a kai – don a ba shi takardar kammala digiri. Shi ke nan, ta biya masa! Kai tsaye wannan daga sama yako son fara gini.

Wani kuwa, kundayen digiri zai bi domin ya riƙa zaƙulo yadda suka yi rubutunsu. A haka shi ma zai gina ƙunshiyar aikinsa wadda kai tsaye za a iya fahimtar yadda ta karkata daga haƙiƙanin batunsa zuwa ɗaukar naso da tsattsafin kwashe-kwashe da ya yo. Ilimin gina aiki ba a samun sa ta hanyar ɗaukar hannu daga kundaye tsiraru. Ana samun sa ne ta hanyar karatu turƙuru game da “dabarun bincike.” Kowane abu da mutum ya gani a cikin ƙunshiyar aiki (wanda ya aikatu), to akwai dalilin da ya sa yake nan, kuma akwai dalilin da ya sa ya kasance yadda ya kasance. Wanda ya yi karatu, ba ya buƙatar ganin ƙunshiyar aikin wani kafin ya gina ƙunshiyar binciken da ya saka a gaba (wannan ba ya nufin ba zai yi nazarin ayyuka makamantan nasa ba). A maimakon haka, yanayi da tsarin binciken da yake shirin yi, su za su bayyana yadda ƙunshiyar aikin ta dace ta kasance – bisa karɓaɓɓun ƙa’idoji da matakan rubutun binciken ilimi. Idan dai mutum ɗaukar hannu zai yi daga wasu tsirarun kundayen digiri, lallai so yake yi ya fara gini daga sama.

Abin yana da ɗaure kai yadda yake kasancewa har cikin ɗaliban manyan digiri akwai waɗanda ɓangarorin aikinsu kai tsaye hoto ne na wasu ayyuka. Da an karanta za a iya jin babu armashi. Kalaman suna ƙoƙarin komawa zuwa ga aikin asali – wurin da aka kwaso tare da ‘yar kwaskwarima. Kai tsaye wannan yana nuna karatun marubucin ya taƙaita ga inda ya kwaso. Bai yi karatun da ya karantar da shi salon bayanan da ya kamata su kasance a ƙarƙashin kowane take ba. Yana so ne kawai ya fara gini daga sama.

Duk wanda ya ce shi taken bincikensa “kaza” ne, ya rasa yadda zai yi don bai samu rubuce-rubuce da suka yi magana game da binciken da yake son yi ba – kai tsaye ya bayyana cewa bai yi karatu ba. Da ya yi karatu, da ya fahimci cewa, babu wani aiki da zai ɗauko face ya samu ayyukan da suka shafe shi (kai tsaye ko a kaikaice). Haka kuma, da zai fahimci cewa, rashin samun rubuce-rubuce game da binciken da yake son yi, nasara ce ga bincikensa ba ƙalubale ba. Babban abin da ake buƙata daga bincike shi ne “samar da sabon ilimi.” Rashin sanin haka yana nuna so yake yi ya fara gini daga sama.

Ta Yaya Ake Faro Gini Daga Ƙasa?

Abin yana da sauƙi ga wanda ya ɗauke shi da sauƙi. Babban sauƙinsa shi ne, da zarar ka yi, to ka huta. Kai da kanka za ka samu nitsuwa da kwanciyar hankalin cewa ba bisa ƙila-wa-ƙala kake ba. Kana rubutu ne bisa hujja da sanin dalilin da ya sa kake rubuta abubuwan da kake rubutawa. Yadda ɗaya a tara da ɗaya yake kasancewa biyu (1 + 1 = 2), haka matakan bincike suke yayin da aka naƙalce su (duk da tsarabe-tsarabe da ke ƙunshe cikinsa). A bisa haka:

1. Ka yi karatu cikin nitsuwa. Ka cire gaggawa da kasala yayin karatu. Ka karanta bayanai masu yawa tare da faɗaɗa bincike a kan duk wani ɓangare da ya ƙayatar da kai. Sannu a hankali za ka ci karo da wani fage/fanni da ya fi jan hankalinka sama da saura.

2. Ga ɗaliban harshe, misali Harshen Hausa, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ya kamata ka naƙalta shi ne ƙaidojin rubutu. Wani babban fage shi ne zurfafa karatu kan dabarun gudanar da bincike. Akwai rubuce-rubuce masu tarin yawa a wannan fannin, duk da mafi yawansu ba a cikin harshen Hausa suke ba. Daga nan kuma sai karatu a fannin Hausar ita kanta. Ya shafi manyan rassanta, wato harshe da adabi da alada.

3. Ka karkata bincike da nazarce-nazarcenka zuwa wannan fannin da ya fi burge ka, wanda kuma ƙwarewarka ta fi karkata zuwa gare shi. Sannu a hankali za ka fahimci muhimman batutu a fannin (major concepts) tare da fahimtar muhimman tattaunawar da suka gudana da waɗanda suke gudana a fannin (major arguments/issues). Daga nan kuwa za ka fara ganin giɓin da ya dace a cike. Shi ke nan, tarkonka ya yi babban kamu.

4. Idan ka bi waɗannan sauƙaƙan matakai, cikin ƙwarin guiwa za ka gina batun da kake son yin bincike a kai. Tun daga rubuta taken binciken, za a ga bajinta da alamun da suke nuna cewa, ka yi karatu ba ka kawo ne kama raaitan nasa ba. Bugu da ƙari, ka riga da ka sama wa kanka fagen da kake son ƙarewa (area of specialization). Za ka gina kanka a wannan fage cikin sauƙi kasancewar shaawarka ce da karkatar fahimtarka suka yi maka jagoranci zuwa fagen.

5. Ka riƙa neman shawara tare da tattaunawa da abokan karatu na kusa da na nesa. Ka riƙa neman tsokaci daga saoinka da na gaba da kai har ma da waɗanda suke ƙasa da kai a fannin domin fahimtar ɓangarorin da kake da naƙasu tare da bin matakan tayar da komaɗar.

Ba a Kama Zomo Daga Kwance

Wani malaminmu ya taɓa cewa, wani babban malamin falsafa ya ce: “Higher education is for ableliest and surest.” Duk da ban samu haƙiƙanin wanda ya yi wannan furuci ba a binciken da na yi, zancen da kuma bayanin malamin sun kama hakali wato karatun manyan mataki na waɗanda suka-ji-suka-gani cewa za su iya ne. A bisa haka, babu wani adadin karatu ko bincike da ya kamata ya kasance abin fargaba ko ƙorafi. Misali:

1. Babu dalilin da zai sa ɗalibin babban digiri na Hausa ya kasa sanin muhimman ƙaidojin rubutun Hausa (dokokin haɗe kalmomi da rabewa da kuma alamomin rubutu).

2. Babu dalilin da zai sa ɗalibin babban digiri ya kasa karanta “dabarun gudanar da bincike”, don kawai akwai ƙarancin rubuce-rubuce a fannin a cikin harshen Hausa.

3. Babu dalilin da zai sa ɗalibin babban digiri ya kasa karantawa tare da naƙaltar yadda ake tsara manazarta.

Idan za a sha giya, to a sha ta dubu!

Matsalar a Taƙaice

Akwai ƙarancin karatu da sabunta bincike a tsakanin ɗaliban ilimi a yau, har ma da wasu malamai. Wannan yakan haifar da ƙalubale sosai. Masana da suke duba binciken ɗaliban manyan digiri sukan wahala matuƙa saboda ɗaliban sun ƙi yin abin da ya dace. Sun ƙi tsayawa su yi karatu. Sun fi son su ɗauki abin daga sama – wato rubuta kundin digirin kawai, ko da kuwa ba su san komai game da shi ba bayan kammalawa.

Shawarar a Taƙaice

Lallai abu ne mai matuƙar muhimmanci ga ɗaliban manyan digiri su yi karatu kafin rubutu. Akwai buƙatar faɗakarwa a matakai daban-daban domin shawon kan wannan ƙalubale na ƙaruwar kasalar karatu da ɗabi’ar watsi da al’adar nazari da bincike. Ɗalibai musamman masu karatun manyan digiri, a koyaushe su tuna cewa, ba kwalin ba ne kawai abu mai muhimmanci. Wani abu mai muhimmancin (wataƙila ma muhimmanci mafi ƙoli) shi ne adalcin da ka yi wa kanka na cancantar kwalin, adalcin da ka yi wa masu duba ka ta hanyar sauƙaƙa musu (gabatar musu da rubutu mai tsafta) da kuma adalcin da ka yi wa ilimi da al’umma ta hanyar tabbatar da cewa, ba ka mayar da lamarin karatu je-ka-na-yi-ka ba.

Ɗalibai Suna Karatu

Post a Comment

2 Comments

  1. Masha Allah! Wannan takardar ta yi matuƙar taimaka man wajen gano me ya kamata in yi domin gudanar da binciken ilimi.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Masha Allah. Allah ya ƙara ilimi mai albarka Malam Mansur.

      Delete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.