A ranar 24/10/2025 a zauren WhatsApp na www.amsoshi.com an yi tambaya a kan fassarar "Artificial intelligence (AI)" zuwa Hausa. Wato sunan da Hausawa ya kamata su ringa kiran kalmar dashi a Hausance. Ɗalibai, Malamai da Manazarta sun bayar da gudummawa ilimi sosai a cikin zauren. Daga ƙarshe an ɗakko wasu daga cikin bayanan, an kundace su wuri ɗaya domin ajiye tarihi da kuma yaɗa ilimi.
[24/10/2025] Maman Akram: Aslm Alkm, malamai na don Allah ya za a fassara A I( Artificial intelligence) zuwa Hausa?
[24/10/2025] Isah Aminu: Basirar wucin-gadi.
[24/10/2025] Isah Aminu: Basirar Kwarewa na wucin-gadi.
[24/10/2025] Muazzam Rabiu Nabature: Ƙirƙirarriyar Basira.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Abin da ya fi sanuwa ke nan. 👍👍
[24/10/2025] Mabunza: Anya!
[24/10/2025] Mabunza: Malamanmu ku sa hannu. Mun gode.
[24/10/2025] Tijjani: A Jami'ar Bayero dai, an amince a kira "AI" da Ƙirƙirarriyar Basira.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Ko dai "Ƙirƙirarriyar Basira"? Fasaha ai kowacce da ma ƙirƙirarriyar ce.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Tsarin salon tunani da mu'amalar ɗan'adam (basira), su ake ƙoƙarin koya wa kwamfutoci. Ke nan za su kasance tamkar masu "basira" irin ta mutane. Sai dai yayin da "basirar" mutum ta kasance "natural" (duk da different factors do shape it), to ita ta na'ura ta kasance "ƙirƙirarriya". Cikin sauƙi idan aka haɗa waɗannan alƙaluma, za a iya ganin dacewar fassarar, wato "Ƙirƙirarriyar Basira."
[24/10/2025] Tijjani: Haka ne, to wataƙila "Basira" ne.
Amma dai ba na mantawa na halarci wani defence a kan aikin da ya danganci AI kuma manyan malaman Sashe suna wajen.
[24/10/2025] Halima Adamu Mayana: Basirar karya ko Hankalin naura.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Haba dai?
[24/10/2025] Adamu Ago Saleh: To! @Malam Arabi, ka ji fa.
[24/10/2025] Malam Arabi: Wai! Kwamacala!
[24/10/2025] Adamu Yunusa Ibrahim: Ƙirƙirarriyar basira ake cewa a yanzu. Ƙila nan gaba a samar da wata kalma ko kalmomin da suka fi haka dacewa.
[24/10/2025] Dr. A S Wali: AI
[24/10/2025] Adamu Yunusa Ibrahim: Dr. A faɗaɗa mana bayani. Kawai idan aka ce AI shikenan ya wadatar?
[24/10/2025] Dr. A S Wali: Ni ina la'akari da abin da mafi yawan mutane (ba masana nake nufi ba) suka fi fahimta kuma suka fi amfani da shi.
Idan yanzu kana hira a gidan rediyo ko talabijin ko kafar sadarwa ta soshiyal midiya, ka dinga amfani da *ƙirƙirarriyar basira* ba lallai ne mafi yawancin mutane su fahimce ka ba. Idan kuma ka dinga amfani da *AI*, na fi tunanin mafi yawan mutane za su fi fahimtar abin da kake magana a kai.
Hasali ma, su kansu mutanen sun fi amfani da *AI* fiye da *Ƙirƙirarriyar basira*. Za ka iya gwada yin bincike a tsakanin matasa Hausawa masu amfani da AI a wayoyinsu ko kwamfutocinsu domin tabbatar da hasashena ko akasin haka.
Haka kuma, idan har kalmomi irin su *kwamfuta, sim-kad, burauza, talabijin, bidiyo* da sauransu ba a dage wajen cewa sai an fassara su ba tun a shekarun baya da fasahar zamani ba ta yawaita ba, me zai hana ko AI ɗin a yi abin da ake cewa, "adaptation" (kwaskwarima) a maimakon fassarar da ake shan bamban fiye da shurin masaƙi?
[24/10/2025] Adamu Yunusa Ibrahim: Na gamsu da wannan bayanin. Amma ina ganin duk da cewa mutane sun fi amfani ko sun fi fahimtar AI a kan ƙirƙirariyar basira, bai dace kawai a tafi a kan AI din ba. Ya zama a Hausa babu wata kalma sai AI. Domin ko ita kalmar AI ɗin da ake faɗa, taƙaitawa ce a kalmomin Artificial Intelligence. Wannan ya nuna cewa, su masu asalin kalmar suna amfani da ita ne da nufin nuna wani zurfin ilimin ƙirƙira.
A ganina, ko da za a fi fahimtar AI, yana da kyau a Hausa a samu fassarar kalmomin biyu. Kuma kar yadda Dr. Musty ya faɗa, haka ne akwai kalmomin Ingilishi da na Larabci da Hausawa suka aro su daga asalin harshen suka Hankakantar da su, suka zama nasu. Amma idan aka bi diddigi, suna da sunayensu da Hausa. Don haka ina ganin sai an kula sosai wajen yin amfani da ma'ana da zubi da tsarin kalmomin da ake son fassarawa, ko da kuwa za su yi nauyin fahimta.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Lallai ana amfani da AI sosai.
[24/10/2025] Adamu Ago Saleh: Ko don yin tsimiin kalma ma, ai AI tàa zauna!
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Gaskiya ne...
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Sai dai akwai wuraren da ake bukatar fassarar. Misali, a Ingilishin ma akwai context da AI ɗin yake zuwa in full. Kuma a haka ake buƙatar sa a target.
A cikin rubutu ana iya cin karo da:
..... Artifical Intelligence (AI)...
Ke nan fassara zai kasance:
.... Ƙirƙirarriyar Basira (AI)...
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Na jefa wa wannan tunanin kuri'a.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Portion ɗin bai fito a DNT ba. Don haka dole ana buƙatar equivalents na cikakken sunan da kuma alphabetism ɗin.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Wuraren da suka fito a AI kawai, ƙwarai ana iya fassara su da AI.
Ko su akwai certain needs da za su saka dole sai an fassara su. Ko jiya @Surajo Teete ya yi irin wannan aikin.
Source din ya zo da "NYC" amma instructions ya ce dole a fassara shi, kuma in full
[24/10/2025] Adamu Ago Saleh: Da kyau! Shi ya sa na ce, "... *tàa* zauna", ba ~táa~ zauna ba.
[24/10/2025] Rabiu Musa Gambaki: Mun gode
[24/10/2025] www.amshoshi.com: Don haka dole ke nan zai kasance an fassara.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Da AI ne ya zo a gurbin, kuma aka ci karo da irin wannan instructions ɗin, ke nan dole za a fassara shi.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Wani abu kuma shi ne, an yarda Hausantar da kalmomi abu ne mai matuƙar amfani ga harshe. Amma an san da cewa, Hausantarwa yana tafiya tare da mayar da kalmomi 'yan gida - za a riƙa furta su kamar yadda al'adar furucin sautukan Hausa yake.
Idan aka ce 'AI" kuwa, babu Hausantarwa a nan. Hasali ma, sai idan za a koma tsarin Ingilishi ne, "zahirin sautuka daban, amma furucinsu daban". Idan Bahaushe zai rubuta AI, ai zai yi wani abu ne mai kama da haka "E'AY". Shi kuwa "AI' zai furta she ne a matsayin 'ai" (as in "Ai kuwa haka ne").
[24/10/2025] Halima Mansur Kurawa: Na ji daɗi wannan. Ina koya wa yara kalmomin Hausa a wajen rubuta sunaye sai guda ya rubuta AI, (taƙaitaccen sunan mace Aisha). Ko da yake bai san akwai wannan alamar ba ('), amma na fahimci da sake.
[24/10/2025] Malam Arabi: To shin ya Hausawa suke furta BBC da WAEC d.s.ya kuma suke rubuta su?
Wannan zai taimaka mana wajen fahimtar yadda ake hausantar da taƙaitattun kalmomi.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Lallai a Turance ake faɗin su. 👍
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Har su ABU da BUK
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Amma fa waɗannan ana iya cewa sunayen yanka ne (proper names), saɓanin AI da yake common noun.
Sunaye kuwa zunubi ne ma fassara su a mafi yawan ayyukan fassara.
An taɓa soke wata fassara sukutum da aka yi (legal translation) kan sauya spelling na sunan wata mata.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: UBA
First Bank
PalmPay
Duka sunayen yanka ne.
[24/10/2025] Malam Arabi: Ni furucin da rubutun ne nake da ja a kai!
SIM
ATM
FM
Duk waɗannan ma common noun ne.
Abin tambaya a nan shin furicin ya daidai da rubutun?
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Wannan gaskiya ne👍👍
[24/10/2025] www.amsoshi.col: Na yarda.
[24/10/2025] Malam Arabi: Allah Ya sa mu dace baki daya...
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Amin amin malam.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Sai idan ana son kawo wani sabun salon adaptation a Hausa inda za a tilasta wa Hausawa fara amfani da salon Ingilishi na sautukan rubutu daban, rufucinsu daban - Kamar yadda suke fusta "queue" a matsayin "q" ko "psychology" a matsayin "saikoloji" etc.
[24/10/2025] www.amshoshi.com: A taƙaice, a Hausa "what we say, is what we write". "AI" kuma, we are saying a thing and writing another.
[24/10/2025] Adamu Yunusa Ibrahim: Ni yanzu idan na ga an rubuta AI, kafin na gane Artificial Intelligence ake nufi sai na karanta shi a "ai" kafin na fahimci sauran saƙon da ke biye.
[24/10/2025] www.amsoshi.com: Ina goyon bayan amfani da AI, amma ba a kowane bagire hakan yake yiwuwa ba.
[24/10/2025] Adamu Yunusa Ibrahim: Gaskiya ne, ba a ko'ina zai zauna ba.
[24/10/2025] Muhammad Ahmad: Duk da cewa ni ɗalibi ne amma ina ganin kamar fassarar "ƙirƙirarriyar fasaha" zai fi dacewa da AI
[24/10/2025] Malam Arabi: Tsokaci📌📌📌
Muhawara kan Fassarar Kalmar 'AI' 'Artificial Intelligence' ta kasu rukuni-rukuni.
Rukuni na Farko: Dogaro da Tushe (Ƙirƙirarriyar Basira)
Waɗansu masana sun zaɓi fassara 'AI' da 'Ƙirƙirarriyar Basira'. Sun ginu a kan tsohuwar fassara ce da aka yi a baya, inda aka fassara kalmar 'Artificial Language' da 'Ƙirƙirrarren Harshe' a cikin littafin 'Hausa Metalanguage'. Idan aka duba sashin 'M' a littafin, za a tabbatar da wannan fassara.
Rukuni na Biyu: Aro ko Taƙaitawa (AI)
A gefe guda kuma, akwai waɗanda suka gwammace a bar kalmar 'AI' yadda take a matsayin aro (ko kuma suka yi kwaskwarimar dacewa da ita). Sun ɗauki wannan mataki ne domin rage yawan kalmomi da kuma samun taƙaitaccen bayani mai saukin faɗa. (Tsimi)
Rukuni na Uku: (Fasahar AI)
Sai kuma wasu masu ra'ayin da suke haɗa kalmar 'Fasaha' don samun 'Fasahar AI', wanda ya shafi dukkanin tsarin aikinta.
Rukuni na Huɗu:
(Ƙirƙirarriyar Basirar Wucin Gadi) ban san da me suka dogara ba.
[24/10/2025] Abdullahi S Gulbi: Ni na fi aminta da rukuni na uku.
[24/10/2025] Muhammad Lawal Shitu: Allah ya saka da alkairi, ni dai har na hango danginmu kuma na bi na yarda da hujjarsu 👏🏾
[24/10/2025] www.amsoshi.com: 👍👍
[24/10/2025] Umar Bulama Maiturare: Fasahar Zamani.
[24/10/2025] Malam Arabi: Wace fasahar ce ba ta zamani ba?
[24/10/2025] Surajo Teete: Wannan tattaunawa ta yi fa'ida, mun ƙaru sosai. @Malam Arabi da kuma @www.amsoshi.com kowanne ya kawo dalilai amma dai daga ƙarshe an cimma matsaya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.