Ticker

6/recent/ticker-posts

Wace Ce Wannan Matar, Mijinta Annabi, Babanta Annabi Danta Annabi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Malam dan ALLAH wata tambaya ce anata tambaya acikin groups shi ne nace bari na tambayeka, wace mata ce wannan?

• Mijinta- Annabi

• Babanta- Annabi

Ɗanta- Annabi

• Yayanta- Annabi

• Ta-raini- Annabi

• Ta-yaye- Annabi

• Ta-haifi- Annabi

Wannan ita ce tambayar malam.

WACE CE WANNAN MATAR, MIJINTA ANNABI, BABANTA ANNABI ƊANTA ANNABI?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaika Assalam warahmatullah wabarahkatuh.

Gaskiyar magana babu wata mata da aka keɓanta da irin wannan a duniya, babu a Alƙur'ani da hadisan Manzon ALLAH {Sallallahu Alaihi Wasallam}.

Haka kuma acikin littattafan Ahlul kitab ma bamuji wata ƙissa irin wannan ba.

Wasu suna tunanin cewa Layyah ce 'ƴar Annabi Yaƙub (A.S) saboda tana da alaƙa da wasu Annabawan ALLAH, amma gaskiyar magana ba ita bace, ita ba ma ta yi zamani da waɗannan Annabawa ba.

Kawai dai wasu mutane ne suke zama suna ƙirƙiro maganganu domin kawo ruɗani acikin mutane, da kuma shaiɗan da yake bawa mutane aiki akan abin da bazai amfanesu ba acikin addininsu da rayuwarsu.

Wani abune wanda saninsa bazaisa mutum ya sami lada ba, kuma rashin saninsa bazaisa mutum ya sami zunubi ba.

Da mutane zasu maida hankali akan sanin hukunce-hukunce da ALLAH ya wajabta musu daya amfanesu a duniyar su da lahirar su, Amma mutane suna ɓata lokacin su akan abin da bazai amfanesu ba aduniya da lahira wannan kuskure ne babba.

Saboda haka wannan mata babu bayananta acikin littafin ALLAH kwata-kwata.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ALLAH shi ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments