𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Don Allaah, ina da tambaya: Wai mecece riya? Wane abu ne idan mutum ya yi shi ya zama riya? Don Allaah, ina neman ƙarin bayani.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam
warahmatullahi Wabarkatuh
Kalmar riya asalinta
balarabiya ce, watau daga harshen Larabci ne Hausawa suka samo ta, kuma
ma’anarta a wurin malaman Aƙida
da Tauhidi ita ce: Yin wani aikin ibada na-Allaah, kamar Kalmar Shahada ko
Sallah ko Zakkah ko Azumi ko Hajji ko Sadaka ko Tilawa ko Zikiri ko Kyautatawa
ga iyaye da marayu da talakawa da maƙwabta
da sauransu, amma ba don Allaah ba, sai domin kawai mutane su gani su yabe shi!
Wannan mummunan zunubi ne daga cikin manyan Kaba’irai da aka ba shi matsayin Shirka Ƙarama, in ji malamai. A ƙarshen Suratul Kahf Allaah Ta’aala ya
ce:
فَمَنْ كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا
Duk wanda yake ƙaunar haɗuwa
da Ubangijinsa to sai ya aikata ayyuka na-gari, kuma kar ya haɗa
kowa a cikin ibadar Ubangijinsa.
Sannan Al-Imaam Al-Haakim ya
riwaito Hadisin da Al-Haafiz Az-Zahabiy ya dace da shi wurin sahhaha shi a bisa
Sharaɗin
Al-Bukhaariy da Muslim daga Sahabi Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa:
Wani mutum ya faɗa wa Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: Ni, ina tsayawa a wani irin matsayin da ina
neman Fuskar Allaah, a lokaci guda kuma ina neman mutane su ga irin wannan
matsayin. Amma sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai ba shi
wata amsa ba sai da wannan ayar ta sauka.
Abin da ya wajaba dai ga
mumini shi ne: Duk lokacin da ya tashi yin wani aiki sai ya tsarkake niyyah tun
daga zuciyarsa saboda Allaah shi kaɗai
kawai. Haka Ubangiji Ta’aala ya yi umurni:
وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ
Kuma ba a umurce su da komai
ba sai dai su bauta wa Allaah, suna masu tsarkake addinin gare shi.
Aiki kuwa ba ya zama na-gari
(Amalun Saalih) in ji Malamai, sai ya cika waɗansu
muhimman sharuɗɗa guda biyu:
1. Ya zama an tsarkake
zuciya a wurin yin sa, watau a yi shi ne tsantsa saboda Allaah shi kaɗai.
Wannan shi ne: Ikhlaas, wanda yake kawar da shirka.
2. Ya zama an bi koyarwa da
karantarwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a wurin yin aikin
sau-da-ƙafa. Wannan ne kuma shi ke kawar da bidi’a.
Wannan irin ɗabi’a
ta yin riya a cikin ayyukan ibada siffar munafuƙai
ne waɗanda
ba su yi imani na-gaskiya da Allaah da Ranar Lahira ba, kamar yadda Allaah ya
yi bayaninsu a cikin Suratul Maa’uun. Sannan kuma a cikin Suratun Nisaa’i ya
siffata su da cewa:
وَإِذَا قَامُوا إِلَى الصَّلَاةِ قَامُوا كُسَالَى يُرَاءُونَ النَّاسَ وَلَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ إِلَّا قَلِيلاً
Kuma idan suka tashi zuwa ga
sallah sai su tashi cikin kasala, suna yin riya ga mutane, kuma ba sa tuna
Allaah sai ɗan kaɗan.
A ƙarshe dai a wurin ƙarin bayani da fayya ce komai da komai
da kuma bayar da hukunci, sai malamai suka karkasa ayyukan da riya take shiga
cikinsu gida-gida, kamar haka:
1. Idan ya zama abin da ya
zaburar da mutum ga yin aikin tun farko don ya nuna wa mutane ne, ba don neman
Fuskar Allaah Maɗaukakin Sarki ba, to wannan
aikin ya zama shirka kai-tsaye kuma aikin ɓatacce
ne.
2. Idan kuma da farko mutum
ya mike domin yin ibadar saboda Allaah ne amma kuma daga baya sai riya ta shige
shi, to idan ibadar farkonta ba a haɗe ya
ke da ƙarshenta ba, to sashen farko na ibadar
Sahihiya ce, sashen ƙarshe
kuma da riyar ta shige shi ne ya lalace.
3. Idan kuwa farkon ibadar
da ma a haɗe ya ke da ƙarshenta, to idan mutumin ya natsu da
riyar kuma bai yi tsayin daka wurin kore ta daga zuciyarsa da gwargwadon ikonsa
ba, to dukkan aikin ya ɓaci!
4. Idan kuwa zuciyarsa ƙyamar riyar ta ke, ba ta natsu da ita
ba, har ma ƙoƙarin kore ta daga zuciyarsa ya ke, to a
nan ba za a ce aikinsa ya ɓaci ba in Shã Allãh.
5. Haka kuma idan tunanin
riyar ya faɗo masa ne a bayan ya kammala aikin
ibadar, a nan ma dai malamai sun tabbatar cewa aikinsa yana nan daram, bai ɓaci
ba.
Haka babban malami As-Shaikh
Muhammad Bn Saalih Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) ya fayya ce waɗannan
abubuwa tare da misalai a cikin littafinsa: *Al-Ƙaulul
Mufeed.* Allaah ya saka masa da alkhairi.
Ban da wannan, akwai kuma
wani aikin da malaman Tauhidi suka nuna cewa in bai yi daidai da riyar ba, to
kuwa ba za ta fi shi muni ba, shi ne: Mutum ya tashi ya yi aikin ibada da
tsarki zuciya saboda Allaah kuma a bisa koyarwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam), sai dai kuma a cikin zuciyarsa ya yi wannan ne ba da manufar
yin bauta ga Allaah Ta’aala wadda yake fatar samun lada a wurinsa ba, sai dai
kawai domin Allaah Mabuwayin Sarki ya ba shi wata buƙatarsa a cikin rayuwar duniya!
Allaah ya kiyaye, ya taimake
mu, kuma ya sa mu fi ƙarfin
zuciyarmu da shaiɗanunmu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.