Ticker

6/recent/ticker-posts

Taya Murna

Wannan waƙar mai suna “Taya Murna” an tsara ta ne domin taya murna ga Dr. Abu-Ubaida Sani game da kammala karatunsa na digirin digirgir. Da fatan Allah ya sanya wa wannan karatu albarka. Amin.

Abu-Ubaida Sani

TAYA MURNA

Ta

Aminu Sani Uba Ringim (Abu Isah Asshanqedy)

Bismillahir rahmanir rahima

1. Tafiya a sannu a sannu in kai haƙkuri,
Sannan ka yo aiki da gake kana zuwa-

2. Can inda ke da wuyar zuwa a wajen wasu,
Tuni zaka je burinka kai yi cikawa.

3. Ni tawa murnar na saka ta a waƙe ne,
Kui haƙƙuri in nai kure ya 'yan uwa.

4. Haƙkuri da kai yau gashi ya zo muntaha,
Ka kammala yau ga shi ka yi gamawa.

5. Mai son ganin Dakta ya zo to gaka nan,
Ph da  D sunanka za a gamawa.

6. Digirin digirgir ka riga ka zarce nan,
Dirinka cif uku ce ku zam ganewa.

7. Dakta a al'ada a yau sabo fifil,
Tabbas a yau harshemu ya yo ƙaruwa.

8. Allah nake roko ya amfanar damu,
A cikin abinda ya baka mui yo ƙaruwa.

9. Haka nan ya zam kare ka sharrin ɗan Mutum,
Har ma da aljan kar su yo cutarwa.

10. Murna na zo yi ba yabon ka ba gaskiya,
Amma yabonka ina shirin tsarawa.

11. In har na ce zan yo yabonka a nan wurin,
Baiti dubu nan take zan saƙawa.

12. Amma a gaske iya sanin da na yo a yau,
Kan intanet Hausarmu kai yaɗawa.

13. Ka zam gudu a wurinmu mai tamkar dubu,
Aikin da kai Allahu yai sakawa.

14. Kafin na sanka a fuska can kan intanet,
Na gano ka aiki mai yawa ka azawa.

15. Wallahi tun sannan nake kaunarka ni,
Domin kwa ka yi abinda ba'a iyawa.

16. In har kuna son gane aiki ja da yai,
Tafi intanet sunansa kai yi sanyawa.

17. Koko ka je shafi na amsoshi ka ga,
Dubban takardun Hausa yai tarawa.

18. Fata nake Allah ya baka tsayi na rai,
Aikin da kaffara ka yo idawa.

19. Na nufin ka kai Hausarmu kan ƙololowa,
Domin ta bunƙasa a zam nunawa.

20. Ta biyo sahun manya na yaren duniya,
Wannan da kowa ya ji zai ganewa.

21. Waƙen ga ni ne nai shi ɗan almajiri,
Alaramma yaro mai jinin Hausawa.

✍✍
Daga Alƙalamin
Aminu Sani Uba Ringim
Abu Isah Asshanqedy.
Phone: 08162293321
Email: aminusaniuba229@gmail.com
Daren Laraba
08/Rabi'ul II /1447h
30/Satumba/2025.

Post a Comment

0 Comments