Ticker

6/recent/ticker-posts

Tahmisin Wakar Sanarwar Birnin Sirti (Hasken Hadin Kan Afirka)

Waɗannan baituka sun kasance tahamisi na Waƙar Sanarwar Birnin Sirti (Hasken Haɗin Kan Afirka).

TAHMISIN WAƘAR SANARWAR BIRNIN SIRTI (HASKEN HAƊIN KAN AFIRKA) 

Rubutawa
Farfesa A.B. Yahya
(09/09/1999) 

***

Tahmisi
Usman Nagado (II)
(06/0CT/2025)

Da sunanka Allah nake tutiya,

Ka sa mini haske cikin zuciya,

Na tsara ƙasidar ƙasar Libiya,

Ina gode Allah Gwani Mai niya,

Da Yas sanya niz zo cikin Libiya.

 

Akwai Larabawa da halin ƙwarai,

Suna san mutane da tarba ƙwarai,

Akwai natsuwa nan da kwanci na rai,

Zamana a Sabha da sihha sarai,

Cikin ƴanuwana lumui lafiya.

 

Madalla da shugaban ƙwarai Gaddafi,

Fa laya a yau ta yi kyawun rufi,

Ga mai son ya san shekarar da na tafi,

Taran tara tis'a ka yo lissafi,

Wa tisuna ga alfu Miladiya.

 

Ina can a Sabha ina shan gara,

In tsoma biyar ga ruwana na gora,

Ina can zamana ina Lakcara,

Ina kay yi Bayero nij ji kira,

Muhammad na Shaibani yac ce tsaya.

 

Na ce mai ina Sabha ai har-ila-yau,

Ka diba garin naku ya yo fayau,

Taho nan ka daina zama sakayau,

Garin Sirti an buɗe ƙofa ga yau,

Ta ƴantar da ƴaƴa na Ifriƙiya.

 

Ka sa ni murna cikin zuciya,

Alla sa dai shi ɗore mu yo moriya,

Muhammad na Shaibani yai magiya,

Mabuɗinta Ƙaid Muammar jiya,

Ka ambato wannan cikin ƙafiya.

 

Don Sha'iri kakke na gaskata,

Ka waƙe Mu'ammar sadaukin fita,

Yaƙi na ƴanci fa ba kunyata,

Yana yin shi gwarzonmu na tabbata,

Sabilinmu bardenmu bai togiya.

 

Ƴanci a yau ya tsayar hasumiya,

A birnin birane na Ifriƙiya,

Tun dai da Gaddafi yai jiniya,

Muna gode Ƙahharu Mai tamaya,

Da Yab ba mu Gaddafi Ifriƙiya.

 

Gaddafi ya yi kira ƴan'uwa,

Kowa ya yafe mu yo affuwa,

Mu ƙara haɗin kai da ma shaƙuwa,

Ku zo ƴan'uwa dum mu yo gaisuwa,

Wurin Ƙa’idi namu mai gaskiya.

 

Mu ƙara hazaƙa mu zamto gaba,

Mu ƴanto ƙasashen Afrika haba,

Burinsa ke nan mu bar rarraba,

Muradinsa Gaddafi ai ci gaba,

Wadata da yanci ga Ifriƙiya.

 

Dukan farfaganda mu tuttunkuɗe,

Mu rege mu tsehe mu yo tankaɗe,

Mu tsaishe muradanmu ko ba daɗe,

Bukatarsa kullum ya zan mun haɗe,

Muna tare jiddun kamar tsintsiya.

 

Haba ɗiyan Afirika mu wawwattsake,

Ya ce zuciyarmu mu dai tsalkake,

Ga yau ga Mu'ammar ƙwarai ya dake,

Mutuncinmu girmammu duy ya fake,

Ga yau babu zulmu bale to tsiya.

 

Mu zauna da juna a lami lumi,

Afirka a yau mun haɗo gangami,

Ba ma raga wa dukan zalumi,

Mu rayu da ƴancinmu ba ƙuƙumi,

Aminci ya wanzu kaza lafiya.

 

Sai mun yi himma fa mun yunƙura,

Mu zauna da ƴancinmu ba takura,

Ga wa za a samo fa wannan dabara,

Muammar tunaninsa shi yag gira,

Muallim jawabinsa ne iggiya.

 

Ina ne zumunta take yaɗuwa,

Ina ad da kishi da san ƙaruwa,

Ina ad da mulkin nagarta kuwa,

Ina ad da rizƙu da son ƴan'uwa,

Ina ne da baiwa ga mai tambaya.

 

 

Ina Ɗanmu'abba ina Zabiya,

Ku shelanta wannan cikin duniya,

Ina nan a Sabha ina tambaya,

Wace ta fa aljanna nan duniya,

Mufakkir ya gano ta Ifriƙiya.

 

Kun ban gari ne fa ko kun tuna,

Idan babu amsa fa kun dangana,

Ku bi ni da sannu ina zayyana,

A can Sirti hasken ga yab bayyana,

Ga yau kuma ya game dun nahiya.

 

Hasken fa ya zarce hasken subahi,

Mun samu ni'ima ƙwarai wallahi,

Alhamdu mui godiya gun Ilahi,

Zama wanga shi ag garin fatahi,

Mahaifar karimi na Ifriƙiya.

 

Haskensa ya game duk duniya,

Ya sa Afirkanmu tai lafiya,

Yau Sirti ta haifi mai gaskiya,

Imamimmu Gaddafi mai anniya,

Cikin Sirti ka ƴanto Ifriƙiya.

 

Ka shelanta ƴanci ga duk duniya,

Ka ce ƴan Afrika mu ɗau aniya,

Mu zo kai ma ƴanci a nan tushiya,

Kiran ga da kay yi ka san mun jiya,

Faɗi naka ne mu ka yi sat ɗaya.

 

Fuskar Afrikanmu ta yi kyan dibi,

Tsarin da kas sa mu yai kyan zubi,

Da ɗaiɗai da ɗaiɗanmu ai bi-da-bi,

Tafarkin da kas sa mu shi za mu bi,

Kana gaba dahir mu kai aliya.

 

A da ayyukanmu suna karkace,

Nasara su watso dukan tarkace,

Ga yau nahiyarmu fa mun taskace,

Ga yau ba mu tsoro bale wai a ce,

Mu zauna da raki kamar mujiya.

 

Sadaukin Afirka ga yau mun biɗai,

Ya watse magabtanmu shi shi kaɗai,

Ƙwarai ba musu ai da ɗaiɗai da ɗai,

Magabtammu mun san su ko can daɗai,

Da kura da shaho da ko mikiya.

 

Ga yau mun fahimce ka mun gaskata,

Muna yin bara'a ga tsarin ɓata,

Ɓarayinmu fuskar su ta jirkita,

Da ɓera da kolon ga sun firgita,

Rashinka ka sanya su yin murɗiya.

 

Gwarzo Mu'ammar fa tun da ya furta,

Mun daina yarda da gayyar macuta,

Yau arziƙinmu ga ku ya haramta,

Ga yau kam ina suke dus sun shata,

Kana tsaye zaki na Ifriƙiya.

 

Muna nan a tare ma'an rai-da-rai,

Hana musu ɓarna su gungun birai,

Gaddafi taso da himmar ƙwarai,

Fatattaki gungun macuta ɓarai,

Hana musu rinto na Ifriƙiya.

 

Mu taso mu kange dukan rawuka,

Da yunwa talauci mu bar basuka,

Mu'ammar fa ka san su domin haka,

Ka kwankwatse kanun dukan karnuka,

Da su ne akan cuci nan nahiya.

 

Suna sa siyasa muna rarraba,

Suna bamu bashi na tsintsar riba,

Su kwashe arziƙi suna ci gaba,

Sunai mana hila da son ci gaba,

Su ja mu su jefa cikin rijiya.

 

Abdalla Bayeronmu ne Farfesa,

Asalinta waƙar ya tsara bisa,

Sharrin Nasara ya yo fallasa,

Muradinsu saishe mu har duƙ ƙasa,

Muna bauta Turai da Shaiɗaniya.

 

Da TAHAMISI Usman Nagado na iso,

Hijira tana ZAMTASHUN na hammaso,

Ar ku ja jiki tun da mun burguso,

Fa kaiconsu bardenmu ai ya iso,

Niƙatau Muammar da ke gaskiya.

Rubutun waka

Post a Comment

0 Comments