Ticker

6/recent/ticker-posts

Fura Da Damu - Wakar Taya Murna Ga Dr. Abu-Ubaida Sani

Wannan waƙa an tsara ta ne domin taya murna ga Dr. Abu-Ubaida Sani game da kammala karatunsa na digirin digirgir. Da fatan Allah ya sanya wa wannan karatu albarka. Amin.

Abu-Ubaida Sani PhD - 2

FURA DA DAMU (Waƙar Taya Murna Ga Dr. Abu-Ubaida Sani)

Ta

USMAN NAGADO (II)

Na yi ma murna -Ubaidu,
Rabbi Allah ne ya bamu.

Yanzu an maishe ka Dakta,
Ga fura sauranka damu.

Kas siɗe ƙwaryarka tastas,
Kar ka yo wasa a kamu.

Mun yi murna mun yi murna,
Kai fa yaya ne a gunmu.

Yanzu ka koma fa koko,
Ka wuce layin su kamu.

Dan da mun yo tambayoyi,
Sai fa Amsoshi ka bamu.

Rumbunan ilimi ka tara,
Dan ka kore ƙishirwarmu.

Himma dai ɗan Muhamman,
Sani yau ga jinjinarmu.

Kai fari sauranka maimai,
Kai Muhim sauran Ahammu.

Kai ta ƙwazo ba musu sai,
Ka haƙe dukkan biramu.

Saƙon murna a waƙe,
Ni na miƙo gun gwaninmu.

Karɓi Dakta Abu-Ubaida,
Ƴar mitsil nai kar ka damu.

Sha'iri ne ni wa ismi,
Usman Nagado gulamu.

Rabbana Allah ya kama,
Dakta ga addu'armu.

Biyu rak ga watan Oktoba,
Tu da Faif (25) Miladiyarmu.

Baitukan waƙar ka ƙirga,
Ai Sabintin (17) za ka samu.

FA'ILATUN FA'ILATUN,
Rabbi Allah ne ya ba mu.

 ©USMAN NAGADO (II)
 2/Oktoba/2025.
 4:30pm

Post a Comment

0 Comments