Saleh Arzai ya ce:
Annabi (saw) yana da karama, daga
cikin karamominsa, da kaciya aka haife shi.
Garba Triumph ya ce:
A'a Malam Arzai, wannan ba ya cikin karamomin Annabi (saw).
Saleh Arzai ya ce:
Ku fa yan Izala Wahabiyawa maƙiya
Annabi ne. Ba ku so ku ji an ambaci darajojin Annabi (saw).
Garba Triumph ya ce:
Haba Malam Arzai, me ya sa kuke
saurin kafirta Musulmi ne?!
Cewa mu maƙiya Annabi ne, ai kafirta
mu ka yi!
Saleh Arzai ya ce:
To ai ba ku so a faɗi wata daraja ta shugaba
(saw).
Garba Triumph ya ce:
Ba ba mu son a faɗi wata daraja ta Annabi
(saw) ba ne, muna matuƙar son mu ji an faɗi
darajoji da karamomi na Annabi (saw).
Saleh Arzai ya ce:
To me ya sa ka musa abin da na faɗa?
Garba Triumph ya ce:
Yawwa Malam Saleh, to ka yi
tambaya mai kyau.
Abin da ya sa na yi maka musu shi
ne; saboda bai tabbata an haifi Annabi (saw) da kaciya ba.
Saleh Arzai ya ce:
Ta yaya za ka ce: bai tabbata ba?
Garba Triumph ya ce:
Saboda riwayoyin ba su inganta a
wajen Malaman Hadisi ba.
Saleh Arzai ya ce:
To ai mu Sufaye muna karɓan Hadisai masu rauni.
Garba Triumph ya ce:
Ai kuwa ba a tabbatar wa Annabi
(saw) wata daraja ko karama sai da Hadisi ingantacce.
Kuma bayan haka, miye ma abin
birgewa a cikin hakan, alhali kafirai ma ana haifansu a haka?!
Saleh Arzai ya ce:
To ka ji irin ƙiyayyar
taku ko?
Ka faɗa min, wane kafiri ne aka haife shi da kaciya?
Garba Triumph ya ce:
An ruwaito; Qaisar Sarkin Rum shi
ma da kaciya aka haife shi.
Saleh Arzai ya ce:
To ai ba matsala, tun da duka an
ruwaito.
Garba Triumph ya ce:
A'a, akwai matsala, ba za a
danganta hakan ga Annabi (saw) ba.
Saboda bai inganta cewa; an haife
shi da kaciya ba,
kuma saboda ana samun hakan a
cikin sauran mutane, hatta waɗanda
ba Musulmai ba.
Saleh Arzai ya ce:
Ku dai Wahabiyawa haka kuke, ba
ku so ku ji mun kawo darajar Annabi (saw) sai kun kore.
Garba Triumph ya ce:
A'a, ba haka ba ne, mu kawai so
muke a taƙaita
a kan abin da ya inganta na darajojinsa da karamominsa.
Saleh Arzai ya ce:
Yanzu maganar kwalli ma ba ku
yarda ba ko?
Garba Triumph ya ce:
Kwalli kamar yaya?
Saleh Arzai ya ce:
Ba ka san da kwalli a idonsa aka
haife shi ba?
Garba Triumph ya ce:
To wannan ma dai kamar na baya
ne. Tun da bai tabbata ba, to bai halasta a danganta shi ga Annabi (saw) ba.
Saleh Arzai ya ce:
Au, shi ma haka za ka fada?
Garba Triumph ya ce:
Eh mana, haka zan faɗa. To miye kamala a cikin
hakan, bayan bai tabbata ba, kuma hatta cikin dabbobi akwai waɗanda haka yake a
halittarsu?
Ai bai kamata mu danganta abu wa
Annabi (saw) ba, sai abin da kamala ne, ba naƙasa a ciki, kuma idan ya inganta.
Kuma ba a yabonsa sai da
khususiyyarsa, abubuwan da shi kaɗai
yake da su.
Saleh Arzai ya ce:
A maganar kaciya ka ce Arna ma
ana haifuwarsu da haka.
A na kwalli kuma ka ce akwai a
cikin dabbobi ma.
Me ya sa za haɗa Annabi (saw) da waɗannan?
Garba Triumph ya ce:
A'a, ni ba haɗa su da Annabi (saw) nake
yi ba, raba su nake yi.
Hasali na kawo maka ne don ka san
cewa: abin da kake jingina wa Annabi (saw) duka bai dace ka jingina su gare shi
ba, don cikin masu siffofin har akwai Arna, da ma dabbobi, don haka ba tsantsar
kamala ba ce, wacce za a siffanta Annabi (saw) da ita.
Saleh Arzai ya ce:
To amma me ya sa za ka ambaci
sunan Annabi (saw), kuma sai ka ambaci Arne, da kuma dabba?
Garba Triumph ya ce:
Ai hakan ba laifi ba ne, tun da
kore sifar Arne da dabban nake yi daga Annabi (saw).
Kuma manyan Malamai magabata ma
suna yin hakan, saboda babu matsala. Ka duba littafin Imam Ibnul Qayyim, mai
suna "Tuhfatu al-Maudud", da littafin al-Waɗwaɗ,
mai suna "Mabahiju al-Fikr", za ka ga kowannensu ya kawo sunan Arne,
cikin waɗanda aka
haifa da kaciya.
Shi Ibnul Qayyim yana kore wa
Annabi (saw) ne.
Amma shi kuma al-Waɗwaɗ tabbatarwa yake yi, amma sai da ya ambaci
Qaisar Sarkin Rum, kafin ya ambaci Annabi (saw).
Don haka ni abin da na yi irin na
Ibnu Qayyim ne, ina kore wa Annabi (saw) ne, ba alaƙanta shi nake yi da Arnen
ba.
Saleh Arzai ya ce:
To na fahimce ka.
A gaskiya a da na ɗauka ƙiyayya
ce ta sa kuke kore wa Annabi darajoji da muke faɗa,
ashe dai kuna da hujjojinku.
Garba Triumph ya ce:
Ai ku ne ba ku fahimce mu ba,
amma ta yaya za a ce mu maƙiya Annabi (saw) ne, alhali mu a kullum burinmu mu yi koyi da
shi, mu yi Addini kamar yadda ya zo da shi, mu zama mu ne mabiyansa?!
Saleh Arzai ya ce:
Allah ya shiryar da mu gaba ɗaya.
Garba Triumph ya ce:
Ameen Malam Saleh.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.