Ticker

6/recent/ticker-posts

Banbancin Da'awarmu Ta Salafiyya Da Da'awar Kungiyar Ikhwan

Da'awar Ikhwan: a gyara Siyasa a yi gwagwarmaya a kafa Khilafa da Gomnatin Shari'a.

Da'awar Salafiyya: a gyara Aqidun mutane a tarbiyyantar da Al'umma sai Gomnatin Shari'ar ta kafu, kamar yadda ya faru a Kasar Saudiyya.

Wannan ya sa a kullum Kungiyar Ikhwan aikinta shi ne sukar Gomnatoci da Shugabanninsu da siyasosinsu, da gwagwarmayar kafa Gomnati.

Su kuma 'Yan Salafiyya a kullum babban aikinsu shi ne sukar munanan Aqeedu da yakar bidi'a, da koyar da ingantacciyar Aqeeda da Sunna.

A nan ina magana ne a kan Salafiyya bisa hakikaninta ba wata kungiya mabiya wani malami ba.

Alhali sukar Shugabannin Musulmai da Kungiyar Ikhwan take yi Manhaji ne na Khawarijawa da Rafidha 'Yan Shi'a, ya saba ma tafarkin Salaf, duk da cewa ba lallai ne mai yin hakan ya zama dan Kungiyar Ikhwan ko dan bidi'a ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments