Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka San Mulhidai A Saukake

Atheists, Deists and Secularists/ Modernists

Na farko da na biyu duka ba su yarda da samuwar Allah ba. Banbancin da ke tsakaninsu:

Su na farko ba su yarda akwai mahalicci ga Duniya ba. Wadannan su ne "Atheists" (الإلحاد المؤكد).

Na biyu kuma sun yarda akwai abin da ya halicci Duniya (a matsayin shi ne sababin samuwarta), amma ba shi ne Allah da Musulmai suke bauta masa ba. Wadannan su ne "Deists" (الربوبيون).

Na uku kuma su ne 'Yan Boko Akida, su sun yarda akwai Allah, kuma sun yarda shi ne mahaliccin Duniya, amma ba su yarda a ce: shi zai tsara wa mutane rayuwa ba. Don haka ba su yarda a bi Alkur'ani da Hadisi da Shari'ar Muslunci a tsarin rayuwa ba, suna ganin kawai a bar kowa ya bi abin da yake so. Wadannan su ne "Secularists/ Modernists" (العلمانيون/ الحداثيون).

Mulhidan kashi na farko (Atheists) da na kashi na biyu (Deists) duka sun yi tarayya da Mulhidan kashi na uku (Secularists/ Modernists) a cikin Ilhadin (Secularism/ Modernism).

Don haka kowane Atheist da Deist, Secularist/ Modernist ne, amma ba kowane Secularist/ Modernist ne yake Atheist ko Deist ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments