Ticker

6/recent/ticker-posts

Tattaunawa A Kan Rabon Gado Da Tsarinsa A Al'adar Hausawa Kafin Zuwan Addinin Muslunci

A ranar 30/10/2025 a zauren Whatsapp na www.amsoshi.com wani malami ya yi tambaya game da rabon gado da tsarinsa a al'adar Hausawa kafin zuwan addinin muslunci. Malamai, dalibai da masana sun tofa albarkacin bakinsu game da lamarin, wanda daga karshe aka kundance shi domin tarihi da ilimantarwa.

Malami A Aji

30/10/2025, Dr A S Wali

Assalam alaikum, 

*Shin kafin zuwan musulunci, Bahaushe yana rabon gado?*

*Idan yana yi, yaya tsarin rabon gadon yake?*

Don Allah manyan malamai su taimaka.

30/10/2025, Manirusidi64@...:

Duk da kasancewar addinin Musulunci ya zo da tsarin rabon gado la'akari da nassoshin Alqur'ani da sunnah, Amma har yanzu akwai nason rabon gado na gargajiya a cikin al'ummar Hausawa. Alal misali mata ba su gadon ƙasa kamar gidaje da filaye. Haka kuma rabon gadon har yanzu akwai fin ƙarfi a ciki manya suke taushe na ƙasa.
Don Allah lalle tabbas. Wannan yake nuna wataƙila a gargajiyance mata ba su da gadon duk abinda ya shafi ƙasa. Haka kuma wanda ya fi ƙarfi a cikin maza shi ne zai fi kaso mai yawa.

30/10/2025, Dr A S Wali:

Idan na fahimce ka, kana son cewa:

(1) kafin zuwa Musulunci mata ba sa gado a al'ummar Hausawa,

(2) wanda ya fi ƙarfi shi ke gadon abin da mamaci ya bari?

30/10/2025, Manirusidi64@...:

Har zuwa yanzu a cikin alummar mu akwai nason wannan al'adar ba a cika ba mata gadon gida ko gona ko duk abinda ya shafi ƙasa ba. Ka ga ke nan wannan yana da alaƙa da gargajiyar Bahaushe tun gabanin samuwar addini

30/10/2025, Jikan Hinnaye:

Duk wannan ga alama yakan faru ne idan ba a tuntubi Alƙali ko malami ba, kuma watakila zai fi aukuwa a ƙauyuka inda karantarwar Musulunci ba ta yi ƙarfi ba.
Zan so in ji hujjar abin da aka faɗa.

30/10/2025, Dr A S Wali:

Malaman al'ada... a taimaka muna da amsar wannan tambaya. Idan babu amsa, ya kamata mu shiga bincike.

30/10/2025, Abu Isah UDUC...:

@⁨~manirusidi64@gmail.com⁩ 

Bayanin da kai yana kan hanya amma a lura da kyau

Batu akan rabon gado abu ne da yake da rikici kwarai da gaske, Wanda hakan ya sa a wasu wuraren kusan an haramtawa wani malami rabon gado a gida dole ne a Dangana da hukuma, don alƙali yai aiki don gudun matsalolin da ka iya bijirowa daga baya, wannan abu ne sannan ne.

A babin rabon gado a Muslunci akwai abinda ake cewa *Tamlika* wato yadda yawancin ake a kotu shi ne za a fara da maida dukkan abinda mamaki ya bari wanda ya kai ai masa ƙima da ta Kudu zuwa kudu, Misali ya. bar Gida da mota, da gona. To maimaikon a raba gidan da gonar wanda suna iya rabuwa ta hanyar iyaka, saɓanin mota baya rabuwa, to a nan sai ai masu ƙima ta kuɗi, wato motar ai ma ta kuɗi gidan ai masa kuɗi haka ma motar, sai a hade kudinsu wuri guda, daga bisani sai a ɗauka tamkar mamacin kuɗi ya bari, daga nan sai a mallakawa kowa wani ɓangare na dukiyar imma gida ko mota ko gona, gwargwadon kasonsa na kuɗi, idan ya yi daidai da kason Shikenan. In Kuma ya gaza sai ya yi ciko, in kuna bai kai ba sai ai masa ciko wannan shi ake cewa *Tamlika*

30/10/2025, Jikan Hinnaye:

Ma sha Allahu

30/10/2025, Abu Isah UDUC...:

Tau abinda ke faruwa a yayin wannan Tamlikar shi ne, mu kaddara cikin magadan akwai *mata* akwai *'ya* akwai kuma *Ɗa* abinda mamaci ya bari kuma akwai gona akwai mota da kuma kuɗaɗe.

A zamanin da muke ciki inda rikici yai yawa, alƙali yakan bada dama ga magada su sasanta kansu Dangane da *Tamlika* wato wane yana son kaza wance tana son kaza don haka idan Alƙali ya zo *Tamlika* zai yi masu gwargwadon abinda suka amince, irin wannan ba mamaki da ba a kutu akai ba daga baya wani ya dawo ya ce bai yarda ba ya fasa, amma da yake a kotu ne idan Alƙali ya yanke bayan aminciwarsu to shikenan ta zauna. Kenan a nan ba tauye haƙƙi ba ne, a a ba mamaki a matsayinsa Na namiji zai yi noma ya taimaki kansa tare da su baki ɗaya

Yawanci wannan yanayi yakan faru ne yayin da ake da hadin kai a cikin gida wato babu 'Yan Ubanci domin kuwa a irin wannan yanayi na zaman doya da manja zai wahala a samu daidaito.

To a nan nefe zaka ga ba mamaki abinda *Ɗa* zai samu ba mamaki bai kai a bashi Gona ba, amma da yake sun sassanta kasu sai a bashi da nufin zai yi ciko. Kenan a nan ba tauye haƙƙi ba ne, a a ba mamaki a matsayinsa Na namiji zai yi noma ya taimaki kansa tare da su baki ɗaya. A yayin da wannan sassanci ya faskara kuwa dalilin 'yan Ubanci ko wani dalili daban, to Alƙali shi ke da wuƙa da nama, shi zai yaken kuma ba me cewa dan me.

To a yayin da Alƙali ke kan aiki nan ma ba mamaki a bisa abinda ya bayyana a gare shi Namijin ya fi buƙatar Gona fiye da mace don haka sai ya bashi koda kuwa kasonsa bai kai nan shi da nufin zai yi ciko.

Don haka mu lura da kyau bukatar gona gida mota, da makamantansu sun fi karkata ne ga 'ya 'ya maza, don haka ake mallaka masu su fiye da mata, ba wai don a tauye haƙƙinsu ba. wanda hakan takan faru a bisa zaɓinsu ko zaɓin Alƙali, kamar yadda mukai bayani.

30/10/2025, Manirusidi64@...:

Masha Allah Dr. Muna godiya sosai. Tambaya a nan ya tsarin yake a kasar Hausa kafin zuwan Musulunci?

30/10/2025, Dr A S Wali:

Wannan ita ce ainihin tambayata.

30/10/2025, Abu Isah UDUC...:

Na yi wannan bayani ne domin kuwa har yanzu akwai wanda ke ganin irin haka a matsayin tauye haƙƙin mata da ake a Muslunci wanda hakan kuskura ne.

Allah ne ma fi sani


30/10/2025, Jikan Hinnaye:

Haka ne. Ba a ko sauya abin da Musulunci ya shata, kuma ba za a samu abin da ya kai shi ba. Abin da ya dace gare mu shi ne mu ƙarfafa ilmantar da jama'armu. Komawa ga gargajiya jahilci ne.

30/10/2025, Abu Isah UDUC...:

Wannan haka yake sir, Allah ya datar damu 🤲

Post a Comment

0 Comments