Ticker

6/recent/ticker-posts

Saurayina Ya Ki Ya Zo Ya Gabatar Da Kansa Gaban Iyayena

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Barka da wannan lokaci. Dan Allah shawara ce nake nema. Wanda yake So na ne shekararmu ɗaya a tare bai taɓa zuwa gurin magabatana ba kullum na Masa magana sai ya cemin Yana sone saiya kammala aikinsa na gida nagaya Masa bawai maganar aure ba kawai Ni inason magabatana su San da zamansa Amma yaki yaje Wai yafison saiya shirya daga tambaya sai ad'aura aure shi Yana gudun Kar yaje ace Masa ya fito Kuma bai shirya ba nayita son fahimtar dashi baza'a ace haka ba amma yaki yarda harna gaji Masa ido, Abu na biyu yanada kishi Wanda nake ganin ya yi yawa babu damar yakirani ya ji Ina waya bazai tambaye dawa nake wayar ba saidai kawai yad'auki fushi da zuciya yinin ranar bazai kirani ba koda Kuma ya kirani to kawai zai cemin ne inbari harna Kare wayar da nakeyi, yanada saurin fushi sannan koda kirana ya yi nace masa na fita bana gida to ransa zai ɓaci duk yanda ya 6oye Zan gane Dan Allah abani shawara Ina sonsa saidai bana kaunar halayansa sannan ashirye nake Dana hakura dashi indai hakan shi ne ya fi dacewa.

Saurayina Ya Ƙi Ya Zo Ya Gabatar Da Kansa Gaban Iyayena

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis salaam: Toh abun da Shari'ar Musulunci ya Shar'anta wa me neman Aure a gurin Mace shi ne, Idan Namiji ya ga Mace ta yi masa ya ji cewa lallai Yana son ta da Aure, toh Addinin Musulunci ya ce na farko ba zai tare ki akan Hanya ya ce bari ya yi magana da ke ba, zai bi bayan ki ne har zuwa gidan ku ba tare da ya yi miki magana ba.

Idan ya iso gidan ku sai ya tura cikin gidan a kira Mahaifin ki, idan Mahaifin ki ya fito sai su gaisa ya ce ai ya ga wata ne kuma abisa alama wata kila Yar gidan nan ne, sai ya gabatar da sunan sa da inda yake da iyayen sa komai nashi sai ya ce yana son a ba shi izinin yin magana da ke ko neman Auren ki indai ba'a ba wa kowa ba. A lokacin Mahaifin ki zai ce eh ba'a ba wa kowa ba an ba shi izinin Neman ki, ko kuma ya je gobe ya dawo, ko kuma bari ayi miki magana a ji ta Bakin ki kafin a ba shi izini, ko kuma ya je bayan sati 2 ya dawo sai an yi Bincike a kansa.

Waɗannan sune abun da Shari'ar Musulunci ya ce ayi, kuma duk wadda ya San me yake yi abun da yakamata ya fara yi kenan kafin magana da Yarinya, kema idan kin San me kike yi a rayuwar ki ba za ki taɓa yarda kuyi shekara 1 ba tare da ya zo gaban iyayen ki ba, toh shiyasa rashin bin abun da Addinin Musulunci ya ce ayi wallahi shiyasa idan an yi Aure ake samun matsaloli daban daban, ko shekara ba'a yi da yin Auren ku ba ki dawo zaman gaba da mijin ki kullum tashin hankali da Bala'i ba dare ba Rana duk rashin bin abun da Addinin Allah ya ce ne.

Sabida haka Malama gaskiyar magana shi ne duk wadda kika ga cewa shekarun ku daya da shi, bai nema ace yau ya je gaban iyayen ki ya nema izinin yin zance da ke ba, Bai je gaban iyayen ki ya gabatar da kansa sun San da shi ba, bai je gaban iyayen ki da Niyyar neman Auren ki ba, har gobe bai nema ba shi damar rika zuwa zance a gurin ki ba Kuma kullum sai Kun yi waya ko chatting ko Hira. Kin ga wannan kwata-kwata ma bai dace da ya zama Mijin ki ba, domin Abu na farko ke kanki Bai San Darajar ki ba, bai San Ƙimar ki ba, Bai San Mutuncin ki ba, sa'annan bai San Martaban ki da nasabar ki ba. Inda ya San su da ya yi aiki da abun da Addinin ki ya ce kamar yadda nayi bayani a sama.

Sa'annan duk Namijin da ya San waɗannan abubuwan da lissafa miki su a yanzu, kuma lallai ne yana son ki da Aure, toh Wallahi kwana biyu ko sati 1 da fara yin Soyayya da shi a take zai fara neman hanyar da Mahaifin ki zai San lallai wane ne yake son Yar sa, sa'annan duk Ranar da kuke yi waya da shi, dole ne ki ji ya ce miki Yaya Mamar ki? Dole ne ki ji kullum Yana cewa ki gaishe da Mahaifiyar ki, Kai wani lokacin ma zai ce wacce ki ba wa mama waya mu gaisa. Idan Namiji baya son ki da Aure da ki gwada shi da wannan idan kuna waya da shi ki ce ga mamana ku gaisa yau za ki ji ya za a kare zancen. Toh duk wadda ya San waɗancan abubuwan da na lissafa miki kuma yana son ya Aure ki ne har zuciyar sa baya son rabuwa da ke wallahi ba sai kin ce ka zo ka nema izinin iyayena ba.

Amma wadda bai San waɗannan abubuwan ba, toh a kullum tunanin sa irin na waɗanda ba su da Ilmi ne, a kullum lissafin sa shi ne kada ya zo ace sai Aure kawai ko bai shirya ba, alhalin ba kowa bane wadda yake da irin zuciyar sa, wasu iyayen suna ba wa mutum uzuri iya yadda yake so, sa'annan ya ce miki sai ya gama aikin sa, sai ya gama shirye shiryen sa kafin nan zai zo gaban iyayen ki, shekara 1 ace mutum kullum aiki yake yi bai gama ba wanne irin aiki ne? Shekara 1 ace kullum mutum shirye shirye yake yi me yake shiryawa? kin ga wannan a zuciyar sa yana son yin rayuwa da ke sosai, yana son ya Aure ki, amma kuma ke ba ki samu Mijin Aure ba, ko kin Aure shi za ki fuskanci matsalolin da za kiyi nadamar Auren sa.

Sa'annan kin ga bai San Darajar iyayen ki da Mutuncin su ba, domin babu yadda za a yi ace Uba da Uwa sun wahala a kanki tun ba ki San wacece ke a rayuwar ki, ba ki San mene ne Soyayya ba, ba ki San mene ne ake nufi da Aure ba, ta dalilin iyayen ki ne kika San komai a rayuwar ki suka ba ki Tarbiyar da za ki tsaya a gaban sa kiyi magana har ya ji dadi a ransa, shi kansa ya kalle ne da girman ki, amma bai San wanne irin fama ne iyayen ki suka yi kafin Nan kika zama Mace irin wannan ba, kin ga kenan da ace ya San Darajar iyayen ki da Mutuncin su ke kanki ya San Darajar ki kuma zai kare miki su, sa'annan yana girmama iyayen ki yana ganin Ƙimar su, toh Wallahi shi ne zai Rika cewa zai zo gaban iyayen ki ya nema izinin su domin su ba shi damar yin zance da ke, domin su ba shi damar Neman Auren ki, shi ne a kullum zai rika Furta Miki Hakan cewa zai zo, ke kuma wata kila ki ce a'a kada ya zo domin kin San iyayen ki, idan ya zo fa, toh maganar Aure ne kaɗai za a yi, amma duk Namijin da za a ce wai Budurwa ce zata Rika matsa masa cewa don Allah ka zo gidan mu ka Gabatar da kanka a San ka, ka nema izinin Neman Aure na Yana cewa a'a Yana Jin tsoro, toh wannan ba Mijin Aure bane gara kin hakura da shi wallahi.

Mene ne a gurin toh? kawai ya zo da kansa ne, ko da abokan sa ya ce nine wane daman na ga wacce Ina son ta da Aure, a ba ni izinin neman Auren ta idan ba'a yi mata Miji ba, shikenan Mahaifin ki ya ce na ji daɗin zuwan sa, a'a ba'a yi miki ba, Kuma an ba shi damar neman Auren ki, toh sai yayiwa Mahaifin ki bayanin cewa shi a yanzu yana aikin gidan sa ko wani abu daban, amma ayi hakuri a jinkirta masa a ba shi lokaci, idan ya gama komai zai Turo iyayen sa a zo ayi maganar Aure tsakanin ki da shi, dole ne Mahaifin ki ya Saurare sa kuma ya ji uzurin sa.

Amma Kun shekara 1 har gobe bai da Niyyar zuwa gaban iyayen ki, har gobe iyayen ki ba su San waye yake neman ki ba. Kin ga anan Ke kanki ba ki San Yancin Kanki ba, domin bai kamata ki ba wa Namiji damar ya Rika zuwa gurin ki kuna soyayya, amma ace iyayen ki ba su san da shi ba, ke kanki indai hakane toh ba kiyi kyauta ba, balle shi da kike matsa ya zo ya ce a'a tun ba yau ba, kin ga bai San Darajar iyayen ki ba tunda ai ke ba'a Bishiya kike fito ba dolen sa ne ya zo gaban su indai son ki yake yi, amma Yana kawo miki hujjojin sa na iska, toh me zai sa ki ci gaba da kula shi? Kuma Irin su ne idan sun Auri Mace, su dawo ba su ganin Mutuncin iyayen ki, ba su ganin Darajar iyayen ki, ba su dauke su a Bakin komai ba, ke kanki ba ki tsira ba, don haka ko abu ya haɗa ku kina gidan sa, idan kin gayawa iyayen ki domin ayi masa magana ya gyara ko a jikin sa, Zagin ki zai rika yi da tsinewa iyayen ki, ba zai taɓa chanja halin sa ba idan sun yi masa magana sabida bai San Darajar su ba.

Sa'annan ke kanki yanzu kin ce ba ki son Halayyen sa da yake nuna miki, kin ga wannan fa tun a waje ne ga abun da kike ce, toh Ina ga kuma Yau kin zama Matar sa ya mallake ki, sai abun da ya ce miki shin kina tsammanin me zai faru? Yaya rayuwar ki zai zama tunda a waje ma ga shi kin fada da Bakin ki, toh Ina ga kuma zama da kwanciya da komai ya haɗa ki da shi ya zakiyi? Wannan ne ya sa ake cewa ayi Bincike sosai akan wadda za a Aura kafin Mace ta yarda ta Aure shi. Don gudun irin wannan matsalolin.

Yanzu wata kila tun Haduwar ku zuwa Yau shekara ɗayan, ba ki taɓa cewa yau bari kiyi Bincike a kansa Yaya halin sa da Addinin sa yake ba, kawai Soyayyar kaɗai ke kika sani, sai an yi Auren sauran halayyen sa su Kara bayyana, ki dawo ki ce kin tsane shi, mene ne mafita alhali lokaci ya kure miki, kin ga ba kiyi Bincike ba, Amma ga shi har kin gano cewa wasu halayyen sa ba su dakyau ba ki son su, toh idan kuma kin ci gaba da yin Bincike sosai fa me za ki gano? Mata ayi Bincike sosai akan Namiji kafin ki Aure shi, domin wallahi Aure ya wuce tunanin ki, Mazãjen yanzu wasu Fuskar ce kawai, amma zuciyar babu kyau idan kin Aure shi wahala kaɗai za ki Sha, ko shekara 10 zakuyi ana Binciken waye za ki Aura? wallahi gara ayi shekara 10 a gama Binciken komai a kansa kafin a Aurar da ke ga wani, amma idan an yi gaggawar Aurar da ke babu Bincike, toh za ki dawo kina Nadamar Auren sa, abun da yake faruwa da Yan Mata kenan a Yanzu.

Sa'annan kin ce yana da Ƙishi, Abu ne me kyau Namiji ya yi Ƙishin a kanki sosai akwai Hadisan da suke cewa idan Namiji bai da Ƙishi akan Matar sa toh ba zai shiga Aljannah ba, toh amma a yadda kika yi bayanin ki wannan ba Ƙishi bane zargi ne. Domin Namiji me Ƙishi dole ne ana samun sa da yiwa wadda yake so uzuri tare da Jin dalilan ta, kuma dole ne ya tambaye ki da wa Yaye kike waya? Idan kin yi masa bayani shikenan ya yarda da ke 100% ya amince da ke sosai, ba zai sake nuna damuwar sa ko fushin sa ba a kanki ba.

Dole ne a same shi da Yi miki uzuri sosai da Jin dalilan ki idan Abu ya faru, wannan shi ne Miji me Ƙishi kuma wadda yake son ki tsakanin sa da Allah yana tausayawa rayuwar ki, Amma wadda yake da zargi toh wannan Siffar a kullum ita ce a gaban sa bawai Ƙishi bane, idan kin zama Matar sa, Makwabtan ku ma idan kin yi wasa daker zai bar ki kina shiga, suna ko zuwa Biki a dangin ki, shi ma ba zai bar ki ba, zuwa ziyara Zumunci kab wannan sai kin yi Sa'a ki je, duk waɗannan abubuwan sun faru da wasu Matan sun yi mana bayanin halin da suke ciki sun ce sun rasa ya zasuyi, toh kema za ki zo wannan matakin indai ya zama Mijin ki.

Sabida haka shawara yanzu tana gurin ki, domin rayuwar ki ne, kene yakamata ki tsarawa rayuwar ki Abu me kyau daga yanzu har zuwa Mutuwar ki, da yadda za ki kasance a gidan Miji da Yaran ki da Jama'a, sai ki zabawa kanki abokin rayuwa wadda ya San wacece ke, zai iya tausayawa rayuwar ki idan kin shiga wani hali, wadda zai damu da damuwar ki, Wadda yake girmama iyayen ki, da iyayen sa, yake Jin maganar na gaba da shi, wadda ya San Darajar ki, ya San Ƙimar ki, ya San Mutuncin ki, ya San martaban ki, kuma zai iya kare miki su, wadda yake da tsoron Allah a Zuciyar sa, yake da tausayi a zuciyar sa, wadda yake da riko da Addinin Allah, yake da yiwa mutum uzuri a kowane hali ne da sauran su, wannan ya zama Mijin ki za ki ji daɗin rayuwa da shi, Kuma Auren ku har abada in Sha Allah.

Amma irin waɗannan Samarin da kika yi bayanin sa ba su cancanci a ba su Auren Mace ba, don haka sai ki yanke shawara da kanki ba tare da an ce miki ga abun da zakiyi ba, amma ni kam wannan ba Mijin da Mace zata Aura bane, Allah ya tsare ya sa a gane. Dafatan Kin gane ko?

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments