Ticker

6/recent/ticker-posts

Shagala Da Yawan Tunanin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mace ce tana son aure sosai to kuma lokacin auren bai zoba seya zamana kowani lokaci tunanin ta na aurene ko mijin da zata aura kuma malam har a cikin sallah tana shagala da wannan tunanin tana son abata shawarar da zata rage wannan tunanin takuma dena yinsa a cikin sallah Allah yasaka da alkhairi🙏🙏🙏

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh Shawarar da zan ba ta Shi ne ta Ci gaba da yin Addu'a Sa'annan ta Sanya Niyyar yin Aure a Ranta, Sa'annan duk abun da Allah ya Jinkirtawa Bawan sa, toh ki Sani Cewa Wannan Abun Yana Zama Alkhairi ne ga Bawa. yin gaggawar Aure a wannan zamanin Kuskure ne sosai ga Mace domin halin wasu Mazan yanzu sai Allah kawai, ayi Auren ki wata 2 kaɗai Amma a sati 1 ko 2 ki gane cewa kin yi Kuskuren Auren wannan Mijin kin ga ai akwai matsala gara jinkirin.

Don Haka ta ci gaba da yin Addu'a kullum sannan ta Rika Sanya Addu'oin a Cikin ibadar ta, Allah ya kawo Mata Miji Nagari Mai Addini, Amma ta rage Yawan Tunanin Haka idan har tana cikin yin ibadar Allah ne, toh ta Cire komai a Cikin Ranta ta Kusanto da Imanin ta da Dukkan Hankalin ta zuwa gurin ibadar ta, kada ta Rika tuna Komai Sai tuna Allah da Makomar ta.

Matukar tana tuna Haka Sa'annan tana yawaita yin Addu'oin domin Allah ya kawo mata Mijin Auren, toh In Sha Allah Mijin ta Yana Nan tafe zata gan shi.

Duk yadda ta kai ga Son yin Auren idan Lokacin yin Auren ta Bai Yi ba, toh Mijin nata wato Wadda zai Aure ta ba zai taɓa zuwa ba, Amma matukar Lokacin ta ya yi toh In Sha Allah zatayi Auren ta, Kuma Jinkirin da Allah ya yi mata Babu Auren zai Zama Alkhairi ne gare ta. Dafatan kin gane Koh?

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments