Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yaya Mai Tauhidi Zai Zama Maƙiyin Annabi (SAW)?

Babu yadda za a yi mutum mai Imani, mai Tauhidi, mai bin Sunna, amma kuma ka same shi ba ya son Annabi (saw), ba ya girmama shi.

Ba zai taɓa yiwuwa a samu wannan mutumin, mai waɗannan siffofi, amma kuma ya kasance maƙiyin Annabi (saw)!

Kawai inda matsalar take shi ne; -wai- yadda Sufaye suke guluwwi a haƙƙin Annabi (saw), to hakan shi ne son Annabi (saw)!

Idan ba ka yi yadda Sufaye suke so ba, to kai maƙiyin Annabi (saw) ne!

Duk abin da za ka faɗa game da Annabi (saw) sai dai ka faɗa yadda suke so su ji, in ba haka ba duk abin da ka faɗa sai su ce ka yi ɓatanci wa Annabi (saw)!

Alhali suna raya son Annabi (saw) amma sun fi kowa saɓa wa Annabi (saw), saboda sun saɓa Sunnarsa, sun kishiyanci Addinin da ya zo da shi, saboda aikata shirka a ƙabarburan waliyyansu.

Wallahi son Annabin da kake rayawa aikin banza ne idan ba ka da Tauhidi.

Saboda Tauhidi shi ne tushen Addini.

Shi ne manufar halittar dukkan halittu.

Shi ne gaya a Addini da halitta da rayuwa, da wajen Allah gaba ɗaya.

Don haka Sufaye da suke ƙaryar son Annabi (saw), alhali ba su da Tauhidi, suna shirka ma Allah, aikin banza suke yi.

Amma ba zai taɓa yiwuwa a samu mai Tauhidi kuma maƙiyin Annabi (saw) ba. Wannan abu ne "mustahili" .

Amma ana samun masu nuna son Annabi (saw) amma ba su da Tauhidi, suna shirka, don haka son Annabinsu ya zama a banza.

Allah ya mana tsari.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments