Ticker

6/recent/ticker-posts

Annabi (SAW) A Wajen Sufaye

Wato fa so ake a rena wa Ahlus Sunna hankali, a tilasta su suna kallon Annabi (saw) ta irin yadda Sufaye suke kallonsa. Dole su koma yin magana game da Annabi (saw) irin yadda Sufaye suke yi.

Sai ta yadda Sufaye suke so Ahlus Sunna zai faɗi magana game da Annabi (saw)!

Alhali yana daga cikin manyan abubuwan da suka raba tsakanin Ahlus Sunna da Sufaye akwai guluwwi a haƙƙin Annabi (saw).

Yaya za a zo ana hukunta mu da "muhallin niza'i", abin da a kansa muke saɓani da su?!

Idan mun ce:

- Ba a neman taimakon Annabi (saw),

- Ba a neman agajinsa,

- Ba a tawassuli da shi, ko darajarsa, ko alfarmatsa, ko, ko,, ko,,,

Sai a ce: mun yi "su'ul adabi" wa Annabi (saw)!

Alhali aikata ɗaya daga cikin waɗannan yana warware Addinin da Annabi (saw) ya zo da shi, na Tauhidi; kaɗaita Allah da bauta!

Idan mun ce: Annabi (saw) ya mutu, sai a ce: mun yi "su'ul adabi", alhali har cikin Alƙur'ani an ce Annabi (saw) ya mutu!

Sayyidina Abubakar (ra) ya ce: Annabi (saw) ya mutu!

Sahabbai masu yawa sun ce: Annabi (saw) ya mutu!

Idan mun ce: Annabi (saw) ba shi da siffa kaza, da siffa kaza, saboda dabbobi ma suna da siffar, ko Arna suna da ita, sai a ce: mun yi "su'ul adabi", alhali kore siffar muke yi, saboda ba ta tabbata gare shi ba, kuma ko ta tabbata ba "khususiyyarsa" ba ce!

Ta yaya za a zo ana hukunta Ahlus Sunna da Aƙidar ƴan bidi'a, na guluwwi a haƙƙin Annabi (saw), abin da a kansa Ahlus Sunna suke husuma da su?!

Don haka ba Sufaye ne za su nuna mana yadda za mu yi magana game da Annabi (saw) ba.

Mu mun fi su sanin Annabi (saw)!

Mun fi su sonsa!

Mun fi su girmama shi!

Mu mabiyansa!

Shi ya sa muke riƙo da Sunnarsa, muke aiki da Hadisansa!

Mu a wajenmu, Sufaye ba su san Annabi (saw) ba!

Ba sa binsa!

Ba sa girmama shi!

Suna guluwwi a haƙƙinsa, wanda hakan ya sa suka wayi gari cikin masu yi masa jafa'i!

Suna dai raya sonsa kawai, amma ba soyayyar a ƙasa!

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Ta'addancin Makiya a kan Ibnu Taimiyya

A gaskiya za ka dade ba ka ga zalunci da ta'addanci irin na makiya Ibnu Taimiyya ba.

Ibnu Sayyidin Nas ya yi tarjama wa Ibnu Taimiyya, Ibnu Hajar ya nakalto ta a cikin littafinsa "al-Durar", sai ya ba da labarin cewa:

Ibnu Taimiyya sha-kundum ne a ilimi, don kuwa ya yi fintinkau ga malaman kowane fanni na ilimi, wanda hakan ya sa Malaman zamaninsa suke yi masa hasada, inda ya ce:

((برز في كل فن على أبناء جنسه، ولم تر عين من رآه مثله، ولا رأت عينه مثل نفسه، كان يتكلم في التفسير فيحضر مجلسه الجم الغفير ويردون من بحره العذب النمير يرتعون من ريع فضله في روضة وغدير إلى أن دب إليه من أهل بلده داء الحسد وألب أهل النظر منهم على ما ينتقد عليه من أمور المعتقد...)).

الدرر الكامنة في أعيان المائة الثامنة (1/ 183 - 184)

((Ibnu Taimiyya ya yi fice a kowane fanni na ilimi, har ya tsere wa Malaman zamaninsa. Duk wanda ya taba ganinsa to idonsa bai taba ganin wani mutum kamarsa ba. Kai, hatta shi kansa Ibnu Taimiyyan, idonsa bai taba ganin kamarsa ba. Ya kasance yana yin darasin Tafsirin Alkur'ani, dandazon mutane masu yawan gaske suna halartan majalisin nasa, suna sha daga tekun iliminsa mai dadi mai amfani, suna kiwo a gonar baiwa da Allah ya yi masa na ilimi, a dausayi da kududdufi, har sai da cutar hasada ta silalo ta kulli zukutan Malaman garinsu, sai kuwa Malaman suka tunzura mutane a kansa, A KAN MAS'ALOLIN AKIDA da suke sabani da shi a kansu…)).

To tun daga nan suka kafa masa kahon zuka, sai cutarwa kala-kala, mugunta iri-iri, suka rinka jifansa da ja'iran tuhumomi daban-daban, suna yanke hukunce-hukunce a kansa, wasu suka jefe shi da Bidi'a, wasu suka kafirta shi. Ba don ya saba Alkur'ani ko Sunna ko hanyar Salaf ba, a'a, don ya saba Bidi'o'insu na Sufanci da Ash'ariyyanci.

Ai ba su tsaya a nan ba, sai da suka fara shige da fice wajen sarakuna suna kai kararsa. Suka tunzura 'yan daba a kansa suka cutar da shi. Har aka kama shi aka jefa shi kurkuku, aka daure shi. Malaman nan ba su tsaya a nan ba – da ma su ne Alkalan -, suka yi ta kokarin halasta jininsa da yanke hukuncin kisa a kansa. Amma daga karshe Allah ya maida kaidinsu da makircinsu kansu.

Haka ya yi ta fama tsawon rayuwarsa, daga wannar fitina zuwa waccar. Har karshe wani Alkali daga cikin masu husuma da shi ya daure shi, wanda a cikin kurkukun Allah ya karbi rayuwarsa. Allah ya kara haskaka kabarinsa, ya sa dausayin gidan Aljanna ne.

Wannan shi ne irin ta'addancin da makiya Ibnu Taimiyya suka yi a kansa, suka bidi'antar da shi ba tare da hakki ba, suka kafirta shi ba bisa hujja ba. Amma tun wancan lokacin har zuwa yau, makiyansa suna ta kururuwa, suna sukarsa da cewa; yana kafirta Musulmi, alhali ya fi kowa nisantar kafirta Musulmi, da hani a kan haka ba bisa hujja ba. Shi ya sa ya ce:

 ((أني دائما - ومن جالسني يعلم ذلك مني - أني من أعظم الناس نهيا عن أن ينسب معين إلى تكفير وتفسيق ومعصية، إلا إذا علم أنه قد قامت عليه الحجة الرسالية التي من خالفها كان كافرا تارة وفاسقا أخرى وعاصيا أخرى وإني أقرر أن الله قد غفر لهذه الأمة خطأها: وذلك يعم الخطأ في المسائل الخبرية القولية والمسائل العملية)).

مجموع الفتاوى (3/ 229)

((Lallai ni a kullum - kuma duk wanda ya zauna da ni ya san haka daga gare ni - ina cikin wadanda suka fi kowa hani a kan kafirta Mutum Musulmi ayyananne, ko fasikantar da shi, ko danganta shi ga sabo, sai dai idan hujjar Shari'a ta tsayu a kansa, hujjar da duk wanda ya saba mata to ya zama kafiri, ko fasiki ko mai sabo. Kuma ni ina tabbatar da cewa; Allah ya gafarta ma wannar al'umma kuskurenta, kuma wannan ya shafi kowane irin kuskure, sawa'un a Mas'aloli na Akida ne ko kuma Mas'aloli na Fiqhu ne)).

Kuma da wannan za ka fahimci girman kuskuren masu magudi suna kamanta wasu 'yan gwagwarmayar siyasa da Ibnu Taimiyya, don kawai an daure su a kurkuku, ko don wasu Gomnatoci sun kashe su, alhali Manhajinsu ya yi hanun riga da Manhajin Ibnu Taimiyya, gwagwarmayar da suka yi ba irin Jihadin da Ibnu Taimiyya ya yi ba ne. Babban misali a kan haka shi ne yadda Mabiya Sayyid Qutub suke kamanta shi da Ibnu Taimiyya, alhali shi Ibnu Taimiyya Manhajinsa na Salaf ne, shirka da bidi'o'i ya yaka, kuma ya yaki Manhajin Khawarijawa na kafirta al'ummar Musulmi da tawaye wa shugabanni da ta'addanci a kan al'ummar ta Musulmi. Shi kuma Sayyid Qutub Manhajinsa na Khwarijawa ne, babu abin da ya koyar face kafirta Musulmai da fito-na-fito da shugabannin Musulmai, da fita daga cikin al'ummar.

Saboda haka Makiya Ibnu Taimiyya su suka fi cancanta a kira su masu kafirta Musulmi ba shi ba. Su kuma Mabiya Sayyid Qutub, su dena cakuda karya da gaskiya, Sayyid Qutub bai hada hanya da Ibnu Taimiyya ba, kwata-kwata Manhajinsu ba iri daya ba ne.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments