Daga cikin salo da masu inkarin Sunna suke bi wajen inkarin Hadisan Annabi (saw) akwai amfani da wasu sharuda da Malaman Usulul Fiqhi suka gindaya wajen inganta Hadisi, alhali sharudan asalinsu daga gubar Mu'uazilanci ne da "Ilmul Kalam". Wannan ya sa muke da bukatar sanin wadanda suke da hakkin inganta Hadisi ko raunata shi.
Ibnul Muzaffar Al- Sam'aniy ya
ce:
فكما
يرجع في معرفة مذاهب الفقهاء الذين صاروا قدوة في هذه الأمة إلى أهل الفقه، ويرجع في
معرفة اللغة إلى أهل اللغة، ويرجع في معرفة النحو إلى أهل النحو، فكذلك يجب أن يرجع
في معرفة ما كان عليه رسول الله - صلى الله عليه وسلم - وأصحابه إلى أهل النقل والرواية،
لأنهم عنوا بهذا الشأن، واشتغلوا بحفظه والتفحص عنه ونقله، ولولاهم لا ندرس علم النبي
- صلى الله عليه وسلم -، ولم يقف أحد على سنته
وطريقته.
الحجة
في بيان المحجة (2/ 228 - 237) مختصر الصواعق المرسلة (ص: 589)
Kamar yadda ake komawa ga Malaman
Fiqhu wajen sanin Mazhabobin Malaman Fiqhun, wadanda suka zamo jagorori abin
koyi a wannan al'umma, kuma ake komawa ga Malaman Harshen Larabci wajen sanin
Harshen, kuma ake komawa ga Malaman Nahwu wajen sanin Nahwun, to haka YA WAJABA
A KOMA GA MALAMAN HADISI DA RIWAYA WAJEN SANIN ABIN DA MANZON ALLAH (SAW) DA
SAHABBANSA SUKA KASANCE A KAI NA ADDINI, SABODA SU SUKA DAMU DA WANNAN SHA'ANI,
SUKA SHAGALTU DA HADDARSA DA BINCIKE A KANSA DA MARUWAITARSA, BA DON SU BA DA
ILIMIN DA ANNABI (SAW) YA BAR WA AL'UMMA YA BACE, DA BABU WANDA ZAI SAMU
SUNNARSA DA TAFARKINSA".
Haka Shaikhul Islami ya ce:
إذا كان
الإجماع على تصديق الخبر موجبا للقطع به فالاعتبار في ذلك بإجماع أهل العلم بالحديث
كما أن الاعتبار في الإجماع على الأحكام بإجماع أهل العلم بالأمر والنهي والإباحة.
مجموع
الفتاوى (13/ 352)
"Idan yin Ijma'i a kan
gaskata Hadisi zai sa ya fa'idantar da yakini a kansa to Ijma'in Malaman Hadisi
ne abin lura a hakan, kamar yadda ana lura ne da Ijma'in Masana Halal da Haram
(Malaman Fiqhu) wajen Ijma'i a kan hukunce - hukuncen Shari'a na Fiqhu".
Saboda haka babu wanda yake da
hakkin tabbatar da Hadisi ko kore shi, inganta shi ko raunata shi sai Malaman
Hadisi, saboda su ne suka shagaltu da Ilimin Hadisin, suka san yanayin yadda
ake ruwaito shi, suka san halayen maruwaitansa, suka san lokacin da yake
tabbata ko ya zama ba tabbatacce ba.
Don haka ka'idoji da sharuda da
wasu suke gindayawa wajen inganta Hadisi dogaro a kan Malaman Usulul Fiqhi
Mabiya tunanin Mu'utazilanci da "Ilmul Kalam" abin watsarwa ne ba
abin lura ba. Kuma wannan yana nuna; idan mutum ya kutsa cikin fannin Usulul
Fiqhi ba tare da ya samu riga-kafi na Aqidar Ahlus Sunna ba to zai iya
tasirantuwa da Aqidun Mu'utazilanci.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.