Kowace kungiya tana da Usul, wato manyan ginshikan da aka gina ta a kansu, haka kuma tana da alamomi da siffofi na mabiyanta (السمات).
Misali ginshikan Khawarijanci su
ne:
- Kafirta Musulmai da abin da bai
kai kafirci ba, bisa shubuhar "Hakimiyya".
- Da kuma halasta jinanen
Musulmai, da daukar makami a kansu.
Kowane daya daga cikin wadannan
guda biyu suna tabbatar wa mutum Khawarijanci. Shi ya sa duk wanda yake da
Akidar kafirta Musulmai, bisa shubuhar "Hakimiyya", ko da bai taba
kashe kowa ba, kuma ko da yana zaune cikin gari tare da sauran al'umma, to shi
Bakhawarije ne zaunanne, wanda ya zauna bai yi hijira ya yi kaura ya bar garin
da suke kira garin kafirci ba. Sawa'un yana kira ga Akidar tasa ko a'a. Irin
wadannan su ake kira Khawarijawa zaunannu (الخوارج
القعدة). Dole sai ya zama suna dauke da Akidar Khawarijanci, na
ginshikan nan guda biyu da suka gabata.
Kuma Khawarijawa suna da Siffofi
masu yawa (السمات), wasu lazimai ne da
su, ba sa rabuwa da su, wasu kuma ba lazimai ba ne. Daga cikin siffofinsu
lazimai akwai rashin fahimtar Addini (jahilci), da wautar tunani, da guluwwi a
ibada, a Sallah da Azumi da karatun Alkur'ani, kamar yadda Annabi (saw) ya yi bayaninsu.
Haka daga cikin Siffofinsu
wadanda ba lazimai ba akwai: askin malu, wato aske kai tal-tal. Kamar yadda
Annabi (saw) ya ce:
«يخرج
ناس من قبل المشرق، ويقرءون القرآن لا يجاوز تراقيهم، يمرقون من الدين كما يمرق السهم
من الرمية، ثم لا يعودون فيه حتى يعود السهم إلى فوقه»، قيل ما سيماهم؟ قال: «سيماهم
التحليق - أو قال -: التسبيد»
صحيح
البخاري (9/ 162)
((Wasu mutane za su fito ta
bangaren gabashi, suna karanta Alkur'ani amma ba ya wuce makoshinsu (ya isa
zukatansu), suna fita daga Addini kamar yadda mashi yake fita daga abin da aka
harba, sa'annan ba sa dawowa gare shi, har sai mashin ya dawo samansa, (wurin
da ake daure zare). Sai aka ce: miye alamarsu?
Sai ya ce: "Alamarsu ita ce
aske kai, ko cewa ya yi: malu)).
Ka ga wannan Hadisi yana nuni ne
ga sifar Khawarijawan farko, don haka a yau ba za ka ce dole sai ka ga masu
malu kafin su zama Khawarijawa ba.
Don haka yana daga cikin Guluwwi
jingina mutum ga Khawarijanci don kawai an ga wata alama tasu a tare da shi.
Shi ya sa hatta Munafurci ma, mutum ba ya zama cikakken Munafuki har sai ya
hada alamomin da Annabi (saw) ya fada a cikin Hadisi:
«أربع
من كن فيه كان منافقا خالصا، ومن كانت فيه خلة منهن كانت فيه خلة من نفاق حتى يدعها:
إذا حدث كذب، وإذا عاهد غدر، وإذا وعد أخلف، وإذا خاصم فجر»
صحيح
البخاري (1/ 16)، صحيح مسلم (1/ 78)
((Wasu siffofi hudu duk wanda
suka kasance tare da shi to ya kasance tataccen Munafuki, wanda yake da sifa
daya daga cikinsu to ya kasance yana da sifa ta munafurci har sai ya barta:
idan ya yi magana ya yi karya. Idan ya kulla yarjejeniya sai ya yi ha'inci.
Idan ya yi alkawari ya karya. Idan ya yi husuma sai ya yi fajirci)).
Wannan ya nuna ashe sashe na
siffofin Sunayen Shari'a masu hukunci ba sa sa mutum ya zama tataccen mai
wannan sunan, kamar sunan kafiri, munafuki, bakhawarije, dan bidi'a da
sauransu.
Wannan ya sa don kawai mutum ya
yi inkari wa shugaba a kan Mimbari ko ya caccake shi, ya soke shi, alhali
shugaban ba ya wajen, kuma shi mutumin ba ya dauke da wadancan ginshikan guda
biyu to bai zama Bakhawarije ba, duk da kasancewar hakan alama ce ta Khawarijawa.
Khawarijawa aka sani da tara jama'a suna sukar shugaba, da sunan inkarin
munkari, alhali shugaban ba ya wajen.
Wannan ya sa duk masu kafa hujja
da riwayoyi daga Salaf a kan inkari wa shugaba a fili cikin hujjojin ba mu ga
wanda wani cikin Salaf ya hau kan mimbari yana inkari wa shugaba ba, ko ya tara
mutane yana inkari wa shugabanni. Shaikh Ibnu Uthaimeen ya ce:
((كلامنا
على الإنكار على الحاكم مثل أن يقوم الإنسان -مثلا- في المسجد ويقول: الدولة ظلمت الدولة
فعلت، فيتكلم في نفس الحكام، وهناك فرق بين أن يكون الأمير أو الحاكم الذي تريد أن
تتكلم عليه بين يديك وبين أن يكون غائبا؛ لأن جميع الإنكارات الواردة عن السلف إنكارات
حاصلة بين يدي الأمير أو الحاكم)).
لقاء
الباب المفتوح (62/ 13، بترقيم الشاملة آليا)
A nan sai Ibnu Uthaimeen ya nuna
cewa; don Gomnati ta yi wasu Munkarai, ba dadai ba ne mutum ya tashi cikin
Masallaci yana inkari, alhali shugaban ba ya wajen. Sai ya tabbatar da wata
ka'ida kamar haka:
((Dukkan inkarori ga shugaba
wadanda aka ruwaito daga Salaf inkari ne da suka faru a gaban gomnan ko
shugaban kasan)).
Don haka ba za ka hau mimbari a
garinku kana inkari wa shugaban kasa ko gomna, alhali ba sa wajen, sa'annan ka
zo kana raya cewa: -wai- ai Salaf sun yi inkari wa shugaba a fili. A'a, ba mu
san haka daga Salaf ba. Irin wannan inkarin aiki ne na Khawarijawa.
Abin nufi shi ne fadakarwa a kan
wadannan mas'aloli da suka rikice wa mutane, tsakanin masu guluwwi suna
Khawarijantar da Malamai Ahlus Sunna da wani aiki ba ginshikai na Khawarijancin
ba, da kuma masu kafa hujja da inkarin Salaf don halasta inkari wa shugaba a
kan mimbari, alhali shugaban ba ya wajen.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.