Ticker

6/recent/ticker-posts

Son Manzon Allah (SAW)

Babu Musulmi da ya isa ya ce ba ya son Annabi Muhammadu Manzon Allah (saw), saboda son Annabi (saw) ita ce alamar da ta banbance tsakanin kafiri da Musulmi. Shi ya sa hatta Munafukai ba su isa su ce ba sa son Annabi (saw) a fili ba. Don haka a zahiri kowane Musulmi yana son Annabi (saw).

Kuma dole ne mutum ya gabatar da son Annabi (saw) a kan son kowa da komai, ya gabatar da sonsa a kan son kansa, da son 'ya'yansa, da son matansa, da son danginsa, da 'yan'uwansa, da son dukiyarsa da kasuwancinsa, da komai na abin so cikin halitta.

Kuma son Annabi (saw) ba ya cika sai da yi masa da'a. Shi ya sa da aka tambayi wani cikin magabata game da soyayya sai ya ce: Ita ce dacewa da wanda ake so a kowane hali.

Alamar gabatar da son Annabi (saw) a kan son sauran halitta shi ne idan an samu cin karo tsakanin da'a wa Annabi (saw) a cikin umurninsa, da kuma umurnin waninsa wanda ya saba umurnin Annabi (saw), to idan mutum ya gabatar da da'a wa Annabi (saw) da bin umurninsa a kan umurnin wancan to wannan dalili ne da yake nuna ingancin sonsa ga Annabi (saw) da kuma gabatar da soyayyar tasa a kan komai. To amma idan kuma ya gabatar da da'a ma wancan a kan da'a wa Annabi (saw) to wannan sonsa ga Annabi (saw) bai cika ba, kuma imaninsa ma bai cika ba.

To ta yaya ake samun son Annabi (saw)?

Son Annabi (saw) yana samuwa ne da saninsa, da sanin kamalarsa, da sanin siffofinsa, da sanin girman abin da ya zo da shi daga wajen Allah.

Son Annabi (saw) yana da darajoji guda biyu:

1- Soyayya ta Farilla ta Wajibi:

Ita ce wacce take hukunta yi masa da'a, da bin umurninsa na wajibi, da hanuwa daga haninsa a kan abubuwan haramun, da kuma yarda da hakan. Kuma kar ya ji wani kaikayi a ransa game da abin da Annabi (saw) ya zo da shi, kawai ya mika wuya matukar mikawa.

2- Soyayya ta Sunna:

Ita ce soyayyar da take hukunta koyi da Annabi (saw) a cikin halayensa da dabi'unsa da ladubansa na zahiri, na koyi da shi a rayuwarsa, da kyakkywar mu'amalarsa da mutane, da zamantakewarsa da iyalansa da 'yan'uwansa, da koyi da shi a halayensa na gudun Duniya da kwadayin Lahira, da koyi da shi a kyautarsa, da fifita bukatun mutane a kan bukatarsa, da hakurinsa, da yafiyarsa, da rangwamensa, da tsantseninsa da tawalu'unsa. Da koyi da shi a halayensa na badini, na jin tsoronsa ga Allah, da sonsa ga Allah, da son haduwa da shi, da yarda da kaddararsa, da rataya zuciya ga Allah, da gaskiyar ta'allakuwa da shi, da dogaro gare shi, da tawakkali gare shi, da ambatonsa a zuciya da baki da gabobi.

A dunkule: Halayen Annabi (saw) su ne Alkur'ani, yana binsa yana aiki da shi, yana yarda da yardarsa, yana ki da kinsa.

Don haka mutum mafi kamalar son Annabi (saw) shi ne wanda ya hakikance wajen koyi da shi, da binsa da gaskata shi a magana da aiki da hali da yanayi, wadannan su ne Siddikai a cikin al'ummarsa, shugabansu shi ne Abubakar (ra), su ne ma'abota daraja mafi daukaka a cikin Aljanna bayan Annabawa.

Saboda haka duk wanda zai raya yana son Annabi (saw), amma sai aka samu yana saba wa Annabi (saw), ba ya bin Sunnarsa, yana aikata Bidi'a, ba ya aiki da Shari'arsa da abin da ya zo da shi daga wajen Allah, ba ya aiki da Alkur'ani wanda shi ne halin Manzon Allah, to lallai shi makaryaci ne a cikin ikirarin soyayyar Annabi (saw) da yake yi. Saboda masoyi na gaskiya ba ya saba wa abin sonsa. Don haka son Annabi (saw) na hakika shi ne bin umurninsa, da nisantar haninsa, da riko da Sunnarsa, da nisantar kowace Bidi'a, sawa'un ta Akida ce ko ta aiki. Saboda abu ne sananne a dabi'a duk masoyi to mabiyi ne ga masoyinsa mai bin umurninsa ne. Wani ya ce:

(قالت وقد سألت عن حال عاشقها *** بالله صفه ولا تنقص ولا تزد)

(فقلت لو كان رهن الموت من ظمأ *** وقلت قف عن ورود الماء لم يرد)

Saboda haka duk mai raya son Annabi (saw) alhali ba ya bin Sunnarsa, yana kan Bidi'a, yana saba Shari'a da umurnin Manzon Allah (saw) to ba cikakken Masoyin Annabi (saw) ba ne. Cikakken Masoyin Annabi (saw) ba ya Bidi'a, ba ya saba Shari'ar da Annabi (saw) ya zo da ita.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments