Ticker

6/recent/ticker-posts

Asalin Salafiyya Lakabi Ne Na Manhajin Ahlus Sunnati Wal Jama'a A Addini

Asalin Salafiyya lakabi ne na Manhajin Ahlus Sunnati wal Jama'a a Addini; wato a babin Aqeeda da Fiqhu da Mu'amala da halaye, wato dai Addini a dunkulensa.

Babban abin da ya banbata Manhajin Ahlus Sunna da kishiyoyinsa shi ne babin Aqeeda; wato babin daukar Addini daga Alkur'ani da Sunna da Ijma'in Salaf, da kuma imani da Allah (a Rubibiyya, Uluhiyya da Asma'u was Sifaat) da imani da Mala'ikunsa da Littatafansa da Manzanninsa da imani da Ranar Karshe, da imani da Kaddara na alheri da na sharri.

Da kuma babin mas'alolin imani da matakan muminai a cikinsa da hukunci wa mutane a kansa, da babin matsayin Sahabbai da Ahlul Baiti da kuma babin da'a ma shugabannin Musulmai.

Amma a babin Fiqhu galibi sabanin da ke tsakanin Mazhabobi hudu na Sunna sabani ne mai sauki, saboda dalilan Fiqhu suna da yawa, kuma Ijtihadi yana shiga cikinsu. Sai dai masu ta'assubancin Mazhaba, masu tsananta gaba da Hadisi da jefa shi a bola, wadannan kam ana tsorace musu halaka, da fita daga da'irar Ahlus Sunna, saboda Hadisi shi ne tushen Sunna kamar yadda kowa ya sani.

To amma a zamanin yau, sakamakon bullar kungiyoyi da sunan da'awa ko harka da jihadi, ya zama cewa; babban abin da yake banbance Salafiyya Manhajin Ahlus Sunna daga waninsa shi ne: Babin da'a ma shugabanni da Manhajin mu'amala da su.

Abin da Manhajin Ahlus Sunna ya ginu a kai a wannan babi shi ne yin da'a wa shugaba Musulmi a kan kyakkyawa, ko da kuwa azzalumi ne ja'iri, ko da kuwa juyin mulki ya yi ya kwaci mulkin. Da yin hakuri a kan zaluncinsa, da yi masa Nasiha a kebance, da yi masa addu'ar alheri da shiriya. Da nisantar duk abin da zai bude kofar tunzura jama'a ga yi masa bore da tawaye. Ba don komai ba, sai don tabbatar da wanzuwar zaman lafiyar al'umma da kare jinanenta da dukiyoyinta da alfurman matan al'ummar.

Dalilai a kan wannan Manhaji kuwa, dalilai ne daga Alkur'ani da Sunna da Ijma'i, hadi da dalilai na hankali da nazari da kiyasi da hangen nesa da waqi'i. Saboda kowa ya ga makomar al'umma da sakamakon bore da aka yi ta yi a tsawon Tarihi, da wanda aka yi ta tayarwa a kasahen Larabawa da sunan (الربيع العربي), wanda bangarorin siyasa na 'yan adawa da kungiyoyin Addini na siyasa - kamar Kungiyar Ikhwan da magoya bayanta - suka haifar na fitina da hasarar rayuka. Su ba su samu mulkin ba, kuma sun yi sanadin shekar da jinane da raba mutane da matsugunansu.

Saboda haka, a yau, babban abin da yake banbance Salafiyya, wato Manhajin Ahlus Sunna mabiya Salaf daga Manhajoji na 'Yan Bidi'a da kungiyoyin harka, musamman kungiyar Ikhwan shi ne Babin Mu'amala da shugabannin Musulmai, bayan wadancan ginshikai na Manhajin na Ahlus Sunna da suka gabata.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments