𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum ya kokari
Malam. Idan mutum ya yi zina lokacin bai yi aure ba, yanzu sai ya ji wa'azi zai
mika kanshi ne a yi masa hukunci bisa shari'ar Musulunci? Ko kuwa yaya zai yi?
Na taɓa tambayar wani Malami sai ya ce wai koda mutum ya tuba Allah ba zai Karɓa ba, kuma lallai sai mutum ya yi wani irin mummunan wari a lahira kamar yadda dukkan mazinata keyi. Kuma ya ce babu ruwan wanke wannan warin sai an dulmiya mutum acikin wutar jahannama. Malam hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi. Ko kuwa in gaya wa mijina?? Don Allah ka taimakeni da fatawa da shawara.
Nagode
NA AIKATA ZINA TUN KAFIN
NAYI AURE, SHIN ALLAH ZAI KARƁI
TUBANA KUWA?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika tabbas zina babban
laifi ne wanda in banda shirka babu laifin da ya fishi girma. Kuma koda mace
tana da aure ko bata dashi, idan ta yi zina tabbas ta saɓawa
Allah, kuma taci amanar kanta, taci amanar iyayenta da danginta, kuma taci
amanar mijin da zai aureta, harma zuriyar da za ta haifa nan gaba. Kuma in har
ta mutu bata tuba ba, Allah yana iya yafe mata, ko kuma ya azabtar da ita da
irin azabar da ya yi tanadinta ga mazinata.
To amma abin da ya fi daidai
da fahimtar Mazhabobin Ahlus Sunnah wal Jama'ah shi ne duk wanda ya tuba daga
zunubi kuma ya yi nadama sannan ya nisanci wannan laifin, to Allah zai gafarta
masa wannan laifin koda kuwa ya yi shekaru masu yawa yana aikatawa.
Allah ya faɗa
acikin Alƙur'ani cewa:
إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰلِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ
"Sai dai waɗanda suka tuba bayan nan (wato bayan sun
aikata laifin) kuma suka kyautata aiki, to hakika allah mai gafara ne mai jin ƙai garesu". (Surah An-Nuur: 5)
Kuma duk girman laifin mutum
in dai ya tuba da gaskiya, to Allah zai karbi tubansa ya gafarta masa kamar
yadda ya umurci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya gaya mana:
قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ
"Ka ce yaku bayina waɗanda suka aikata ɓarna bisa kansu!! kar ku fidda tsammani
daga (samun) rahamar Allah. hakika allah yana yafe dukkan zunubai baki ɗaya na, hakika shi ne mai gafara mai jin
ƙai" (Surah Az-Zumar: 53)
Ba'a shiga tsakanin Allah da
bawansa. Babu wani mai ikon yiwa bawa azaba ko gafara in banda Allah. Kuma idan
Allah yaso ya yafe wa bawansa babu wanda ya isa ya hanashi.
Manzon Allah (sallal Lahu
'alaihi wa aalihi wa sallam) Ya ce "Hakika Allah yana shimfida rahamarsa
da daddare domin karɓar tuban waɗanda
suka aikata zunubbai da rana. Kuma yana shimfida rahamarsa da rana domin waɗanda
suka aikata zunubai cikin dare su tuba. (Bazai gushe yana yin haka ba) har zuwa
sanda rana za ta ɓullo daga mafadarta".
Ya kamata malamai su zama
masu kiran mutane ne zuwa ga Allah, ta hanyar nuna musu hanyoyin samun kusanci
da Shi, ba wai su rika kore bayin Allah ta hanyar tsoratarwar da babu albishir
acikinta ba.
Shi kuwa mai gidanki, kada
ki sanar dashi komai acikin wannan, tunda Allah ya rufa miki asiri ya
suturceki, kada ki yaye suturar da Allah ya lulluba miki. Yin hakan zai janyo
zubewar Ƙimarki da mutuncinki agun mijinki, kuma
bazai Ƙara yarda dake ba.
Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam Ya ce: "KU NISANCI WAƊANNAN
ƘAZANTAR DA ALLAH YA HANA, WANDA KUWA YA
SHAFU DA ITA, (WATO YA AIKATA) TO YA LULLUBU DA SUTURAR NAN TA ALLAH, KUMA YA
TUBA ZUWA GA ALLAH...." Imamul Hakim ne da Malik suka ruwaitoshi.
Al Imamun Nawawiy (rahimahul
Lahu) acikin shahararren littafinsa mai suna RIYADHUS SALIHEEN MIN KALAMI
SAYYIDIL MURSALEEN (Sallallahu alaihi Wasallam} afarkon babin tuba, ya yi wata
magana inda yake cewa: "Malamai sun ce tuba wajibi ce daga dukkan zunubai.
Idan laifin ya kasance tsakanin bawa ne da Allah Ta'ala babu hakkin wani Ɗan Adam aciki, to tana da sharuɗa
guda uku kamar haka:
1. Dena aikata Saɓon
nan take.
2. ya yi nadama bisa abin da
ya aikata ɗin nan.
3. Ya ɗauki
niyyar cewa bazai sake komawa zuwa ga wannan aikin ba, har abada.
Idan aka rasa ɗaya
daga cikin waɗannan sharuɗan,
to tubansa bata inganta ba.
Don haka ki cigaba da gyara
ayyukanki tare da kyautata alƙarki
da Allah. Ki yawaita ayyukan alkhairi waɗanda
zasu goge miki wancan laifukan na baya. Allah Ya ce "HAKIKA KYAWAWA (WATO
AYYUKAN LADA) SUNA TAFIYAR DA MUNANA".
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...'
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.