Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Yana Kallon Hotunan Batsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mallam mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. Babban abun bakin ciki shi ne shi da kansa yake tambayesu su aiko masa dashi. idan yagani sai kaji ya ce ya yi missing ɗinsu kuma dasuna kusa da sai ya yi making love dasu, duk lokacin da na buɗe wayansa zan ga ire-iren wannan pictures a wayarshi. Wani ma za ka ga mace da namiji suna sex ni kuma narasa ta inda zan masa magana saboda zai ce ina masa bincike awaya. kuma za mu yi faɗa da shi, kullun hankalina atashe yake bana samun isashshen barci. Idan na tuna halin da mijina yake ciki, malam tambayata anan ya halatta na riƙa daukan nawa hoton tsirara ina tura masa a waya ko zai rage kallon na matan banza ko kuwa? ina neman shawara da addu'arka Mal. wassalam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Hakika abin da mijinki yake aikatawa, ko kaɗan bai dace ba. ya kauce ma hanyar Allah. Kuma ya afka cikin manyan-manyan alkaba'ir.

Shi dai kallo izuwa ga matar da ba taka ba, haramun ne koda ba tsirara take ba. Shi kuwa kallon tsaraici, Allah (Swt) ya la'anci masu yi, kuma ya la'anci masu nuna tsaraicin nasu da gangan don akalla.

Mijinki yana nuna miki Ƙarara cewa Shi mazinaci ne kenan. Saboda haka shawarar da zan baki anan it a ce: Ki bi abun ahankali. kar ki sanya gaggawa ko husuma acikin sha'anin. in ba haka zai iya rikicewa.

Ki samu mijinki kiyi masa wa'azi cikin murya mai sanyi. Ki gaya masa cewa Allah (swt) ya umurci muminai maza su rintse idanuwansu, su kiyaye al'aurarsu daga zina da dangoginta. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam acikin wani hadisi yana cewa: "SHI KALLO, KIBIYA NE MAI TSANANIN GUBA DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS. DUK WANDA YA BAR KALLON DON TSORON ALLAH, TO ZAI SAMU (ƘARUWAR) IMANI WANDA ZAI RIKA JIN ZAƘINSA AZUCIYA".

Kiyi masa wa'azi sosai ki tsoratar dashi game da mummunan Sakamakon da zai riska idan bai tuba ba. Ki gaya masa ya ji tsoron ranar tashin Alƙiyamah, ranar da Allah zai sanya gabobin jikinsa su rika magana suna bada shaida akan laifuffukan da ya aikata.

Idan yaki jin wa'azin naki, to babu laifi ki haɗa shi da wani mai hankali daga cikin abokansa domin ya yi masa nasiha. In sha Allahu zai ji kuma zai yarda.

Kar ki ɗauki irin mummunar hanyar da wadancan matan suka bi. Domin kuwa idan kika zuba masa Hotunanki Tsirara acikin wayarsa, zata yiwu watarana wani daga cikin abokansa ko 'yan'uwansa ya ɗauki wayar kuma ya leka ciki ya ganki tsirara. kinga wannan bai yi daidai ba.

Babban abin da mijinki yake buƙata daga gareki shi ne ladabi, biyayya, da nasiha agareshi cewa ya ji tsoron gamuwarsa da Ubangijinsa.

Ki matsa ma mijinki ya rika halartar jam'in sallolinsa a masallaci, kuma ya rika karanta Alƙur'ani ayawancin lokutansa.

Ki sanyashi cikin addu'o'inki ako yaushe. Kuma muma muna yi miki fatan Allah ya shiryi mijinki ya cire masa son zina. ya cika masa zuciyarsa da tsoron Allah.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments