Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Tsawaita Sujjadar Karshe A Cikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin tsawaita sujjadar ƙarshe a cikin sallah da wasu mutane su ke yi, shin yin hakan sunna ce yana da asali a addini ko babu?

HUKUNCIN TSAWAITA SUJJADAR ƘARSHE A CIKIN SALLAH

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alalhaƙiƙa wannan wani abu ne da ya yaɗu a tsakanin al'umma idan sun zo sujjadar ƙarshe a sallah sai a ga sun tsawaita ta fiye da sauran sujjadodin da ke cikin sallar, da nufin cewa wai addu'a sukeyi, kuma mafi yawa daga cikin masu yin hakan za ka samu babu wani dalili da suka dogara a kansa, sai dai kawai sun gani a wajen wasu suna yi ne suma suka kwaikwaya, a zatonsu hakan wata falala ce, wanda shi kuma addini anaso ne kafin ka fara abu to ka fara neman sanin hukuncinsa a shari'a, idan kuma daga baya kagane cewa kuskure ne to sai ka dena ka koma kan asalin abin da shi ne yake daidai.

Malamai suka ce ko shakka babu cewa keɓance sujjadar ƙarshe a cikin sallah a tsawaita ta hakan ba sunna ba ne sai dai ma ace ya saɓawa sunna, domin ana buƙatar ayyukan sallah daɗewarsu ta zama daidai wa daida ko kuma ta kasance kusa da daidai, kamar yadda Hadisin (البراء بن عازب) yake cewa:

"كانت صلاة رسول الله () وركوعه وإذا رفع رأسه من الركوع وسجوده وما بين السجدتين قريبا من السواء" (رواه البخاري ومسلم)

MA'ANA: Sallar Mαnzon Aʟʟαн (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta kasance (tsakanin daɗewar da ya ke yi) a ruku'insa da ɗagowa daga ruku'i, da kuma (daɗewar da ya ke yi) a sujjadarsa da (daɗewar da yakeyi) a tsakanin sujjada-2, to (yanayin daɗewar) yana kusa dai dai ne.

Dan haka kenan idan mutum yana sallah ko shi kaɗai ko kuma shi ne liman, to anaso ya kasance yanayin irin daɗewar da ya yi a cikin ruku'in farko haka zeyi a cikin sauran ruku'an sallar.

Haka nan kwatankwacin daɗewar da ya yi a cikin sujjadar farko to irinta akeso ya yi a cikin sauran sujjadodin sallar ko kuma ya zama kusa da dai dai, haka zaman da ke tsakanin sujjadodi-2, wannan shi ne abin da wancan Hadisi ya ke nuna mana, domin a cikin ayyukan sallah Mαnzon Aʟʟαн (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ya tsawaitawa da yawa a wani wajen fiye da na sauran, kamar yadda Hadisai suke nuna cewa Annαвi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana daidaita tsakanin rukunan sallah ne ko kuma ya yi su kusa da juna, dan haka Malamai suka ce babu wani dalili ko hujja da ke nuna cewa a tsawaita sujjadar ƙarshe a sallah.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

 Mυѕтαρнα Uѕмαи

 08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments