Ticker

6/recent/ticker-posts

Sabani Tsakanin Ahlus Sunna Da 'Yan Bidi'a

Sabani tsakanin Ahlus Sunna da 'Yan Bidi'a; Sufayensu da Ash'arawansu da Khawarijawansu da Rafidhawansu, ba sabani ne wanda yake da halasci ba, wanda ijtihadi zai iya shiga cikinsa, a'a, sabani ne na Manhaji, tsakanin Manhajoji guda biyu masu kishiyantar juna, wanda yake hukunta daya yana kan gaskiya, daya kuma yana kan bata.

- Manhajin Ahlus Sunna ya ginu ne a kan Bin Wahayin da Allah ya saukar wa Manzonsa (saw) na Alkur'ani da Sunna, bisa fahimtar Sahabbai da sauran magabatan al'umma.

- A lokacin da Manhajin Sufaye ya ginu a kan Kashfi, da gabatar da shi a kan Wahayi.

- Manhajin Asha'ira ya ginu a kan Hankali, da gabatar da shi a kan Wahayi.

- Manhajin Khawarijawa ya ginu a kan bataccen Addini ta hanyar Bin Alkur'ani ba bisa fahimtar Salaf da Manyan Malaman Al'umma da aka musu shaida ba.

- Manhajin Rafidha ya ginu a kan tatsuniyoyi daga Limamansu, da gabatar da su a kan Wahayi.

A bisa hakika duk Manhajin da ba shi da alaka ta kai tsaye da abin da Manzon Allah (saw) ya bar Sahabbansa a kansa to batacce ne, kuma bata ne.

Saboda haka masu kokarin yin sako-sako da sabanin da ke tsakanin Ahlus Sunna da Sufaye, ya kamata su koma su san Manhajin na Ahlus Sunna, kuma su san Manhajin Sufayen, kafin su fara yin magana.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments