Ticker

6/recent/ticker-posts

Dole mu Girmama Manzon Allah (SAW) a Kira ga Tauhidi

Ahlus Sunna su ne mabiya Annabi (saw). Su suka yi imani da shi, suke sonsa, suke girmama shi, suke binsa, suke yi masa ɗa'a, suke riƙo da Sunnarsa, suke shagaltuwa da Hadisansa, suke ɗaukar Addini daga gare su, shi ya sa ake danganta su ga Sunnarsa.

Saɓanin ƴan bidi'a, ba sa binsa, ba sa riƙo da Sunnarsa, sai dai raya sonsa, ba tare da karɓa daga gare shi ba.

Saboda haka mabiya Sunnar Annabi (saw) su ne masoya Annabi (saw) na gaskiya, su ne masu girmama shi girmamawa ta gaskiya.

Wannan ya sa hatta wajen kore wa Annabi (saw) haƙƙin Allah dole ne a duba haƙƙin Annabi (saw) na girmamawa da Allah ya wajabta mana. Saboda Annabi (saw) mutum ne mai girman matsayi. Shi ya sa Allah ya yi umurnin a girmama shi:

﴿لِّتُؤۡمِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُۚ وَتُسَبِّحُوهُ بُكۡرَةࣰ وَأَصِیلًا﴾ [الفتح ٩]

Ibnu Jarir ya ce:

"فأما التوقير: فهو التعظيم والإجلال والتفخيم".

تفسير الطبري (٢٢/ ٢٠٨)

Allah ya koyar da mu yi masa ladabi da girmama shi, a cikin Ayoyi biyar ɗin farko na Suratu al-Hujrat; daga ciki, ya hana ɗaga murya a wurinsa:

﴿یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ لَا تَرۡفَعُوۤا۟ أَصۡوَ ٰتَكُمۡ فَوۡقَ صَوۡتِ ٱلنَّبِیِّ وَلَا تَجۡهَرُوا۟ لَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ كَجَهۡرِ بَعۡضِكُمۡ لِبَعۡضٍ أَن تَحۡبَطَ أَعۡمَـٰلُكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ﴾ [الحجرات ٢]

Ya haɗa umurni da yin Imani da shi tare da imani da Allah:

﴿یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤا۟ ءَامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ﴾ [النساء ١٣٦]

Ya haɗa yi masa ɗa'a tare da ɗa'a ma Allah:

﴿یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤا۟ أَطِیعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَوَلَّوۡا۟ عَنۡهُ وَأَنتُمۡ تَسۡمَعُونَ﴾ [الأنفال ٢٠]

A wani wajen ya ce:

﴿مَّن یُطِعِ ٱلرَّسُولَ فَقَدۡ أَطَاعَ ٱللَّهَۖ ﴾ [النساء ٨٠]

Ya haɗa sonsa tare da son Allah:

﴿ أَحَبَّ إِلَیۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَجِهَادࣲ فِی سَبِیلِهِۦ فَتَرَبَّصُوا۟ حَتَّىٰ یَأۡتِیَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا یَهۡدِی ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَـٰسِقِینَ﴾ [التوبة ٢٤]

Saboda haka kuskure ne a samu Ahlus Sunna suna sakaci wurin girmama Annabi (saw), saboda girman matsayinsa, da yadda suke girmama Sunnarsa.

Yana da kyau mu koma ga Salaf mu ga yadda suke girmama Annabi (saw).

- Urwatu bn Mas'ud ya ce: Na je wurin sarakuna, na je wurin Qaisar da Kisra da Najashiy, amma Wallahi ban taɓa ganin wani Sarki da mutanensa suke girmama shi kamar yadda Sahabban Annabi Muhammad (saw) suke girmama shi ba...

Idan yana magana za su yi kasa da sautinsu. Ba sa iya ƙura masa ido saboda girmamawa.

- Sahabbai idan suna zaune a gaban Annabi (saw) suna nitsuwa matuƙa, kai ka ce tsuntsaye ne a kawunansu.

- Idan suna zaune a gaban Annabi (saw) ba sa ɗaga kai gare shi, saboda girmamawa.

Don haka idan ka bibiyi Manhajin Salaf wajen girmama Annabi (saw) za ka fahimcin kuskuren da wasu suke yi, na rashin ladabi wa Annabi (saw) da sunan kare Tauhidi.

Shaikhul Islami daga cikin abin da ya faɗa, na abin da Alƙali Iyadh ya naƙalto daga Malik a kan matsayin Annabi (saw), a "Ashafa":

"...أَنَّ حُرْمَةَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَعْدَ مَوْتِهِ وَتَوْقِيرَهُ وَتَعْظِيمَهُ لَازِمٌ؛ كَمَا كَانَ حَالَ حَيَاتِه. وكَذَلِكَ عِنْدَ ذِكْرِهِ، وَذِكْر حَدِيثِهِ وَسُنَّتِهِ وَسَمَاعِ اسْمِهِ".

الفتاوى (١/ ٢٢٦)

"...Lallai kare alfarmar Annabi (saw) bayan wafatinsa, da daraja shi, da girmama shi dole ne, kamar yadda lamarin yake a halin rayuwarsa. Haka nan dole a girmama shi wajen ambatonsa, da ambaton Hadisinsa da Sunnarsa, da jin sunansa".

Sai ya kawo misalai daga Salaf:

- Ayyub al-Sukhtayaniy, idan an ambaci Annabi (saw) kuka yake yi, saboda girmama Annabi (saw) da kwarjinin da yake yi masa.

- Haka Ibnu al-Munkadir.

- Haka Amir bn Abdullah bn Zubair.

- Haka Safwan bn Sulaim.

- Malik, idan an ambaci Annabi (saw) sunkiyar da kai yake, fiskarsa ta canza.

- Haka Ja'afaru al-Sadiq.

- Haka Ibnul Qasim.

- Al-Zuhriy, idan aka ambaci Annabi (saw), yana kaɗuwa sosai.

Haka Shaikhul Islami ya nakalto daga Alƙali Iyadh, daga Malik.

Saboda haka, abin da wasu suke yi, da sunan Tauhidi, ko raddi ga Sufaye, suna haɗa sunan Annabi (saw) da sunayen wasu shehunai, suna siffanta su da sunaye na kaskantarwa, ko salon magana wacce babu girmama Annabi (saw) a ciki, wannan abu ne da ya saɓa girmama shi (saw), ko da kuwa da sunan Tauhidi aka yi. Saboda Allah ya hana yi wa Annabi (saw) magana kamar yadda za mu yi ma waninsa:

﴿لَّا تَجۡعَلُوا۟ دُعَاۤءَ ٱلرَّسُولِ بَیۡنَكُمۡ كَدُعَاۤءِ بَعۡضِكُم بَعۡضࣰاۚ﴾ [النور ٦٣]

Saboda haka duk Tauhidin da babu girmama Annabi (saw) a haɗe da shi to ba ingantaccen Tauhidi ba ne.

Don haka a maganar Tauhidi dole a duba girmama Manzon Allah (saw).

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments