Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Gano Cewa Da Kudin Haram Ne Mijina Yake Ciyar Da Mu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mijin da matar shi ta gano cewa da kuɗaɗen sata ne yake ciyar da ita, mene ne matsayinta a wurin Ubangiji?

NA GANO CEWA DA KUƊIN HARAM NE MIJINA YAKE CIYAR DA MU

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abu ne sananne a cikin dokokin shari’a cewa, haram ne musulmi ya ciyar da kansa da haram, haka ma haram ne ya ciyar da duk wanda haƙƙin ciyar da shi ya ke rataye a wuyansa da haram. Domin hatsarin da ke tattare da hakan tun daga nan duniya, kafin zuwa makoma Lahira.

A cikin hadisi Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) wanda Al-Imaam Muslim ya fitar da shi a cikin sahihin littafinsa (2393):

ثُمَّ ذَكَرَ الرَّجُلَ يُطِيلُ السَّفَرَ أَشْعَثَ أَغْبَرَ، يَمُدُّ يَدَيْهِ إِلَى السَّمَاءِ، يَا رَبِّ، يَا رَبِّ، وَمَطْعَمُهُ حَرَامٌ، وَمَشْرَبُهُ حَرَامٌ، وَمَلْبَسُهُ حَرَامٌ، وَغُذِيَ بِالْحَرَامِ

Sai kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ambaci wani mutum wanda ya yi doguwar tafiya, mai yamutsattsen gashin kai mai cike da ƙura, yana miƙe hannuwansa zuwa sama, yana addua da cewa: Ya Ubangijina! Ya Ubangijina! Amma kuma ya kasance abincin sa haram ne, abin shan sa ma haram ne, tufafinsa ma haram ne, sannan kuma da haram aka rene shi Shi ne Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

فَأَنَّى يُسْتَجَابُ لِذَلِكَ؟

To, ta yaya za a amsa masa?

Wannan dalili ne mai ƙarfi kuma a fili ƙarara kan cewa: Cin haram yana daga cikin abubuwan da suke hana amsar addua a nan duniya, ko da kuwa mutum yaro ne wanda ba shi da kansa ne ya samo haram ɗin ya ci ba! Musamman idan shi kuma a bayan ya girma sai ya ɗora daga inda mai ciyar da shi ɗin ya tsaya.

A Lahira kuma akwai alƙawarin shiga wuta ga mai cin haram, saboda riwayar da ta ce:

«إِنَّهُ لَا يَرْبُو لَحْمٌ نَبَتَ مِنْ سُحْتٍ، إِلَّا كَانَتِ النَّارُ أَوْلَى بِهِ»

Babu wata tsokar naman da za ta ginu daga haram, face Wuta ce ta cancance shi. (At-Tirmiziy: 614, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi).

Allaah Ta’aala ya kiyaye.

Daga ƙarshe muna bayar da shawarar cewa: Wajibi ne irin wannan mijin ki yi masa nasiha a cikin hikima da kyakkyawan waazi, domin ya tuba ga Allaah, ya mayar wa da waɗanda ya zalunta haƙƙoƙinsu, ko ya nemo yafiyarsu kafin rasuwarsu ko rasuwarsa. Kuma lallai ya bar wannan sanaar da yake yi, ya sauya wacce ta fi ta alheri, gare shi da iyalinsa a duniya da makoma lahira.

Allaah ya datar da mu ga aikata ayyukan na-gari.

Wal Laahu A’lam

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

+2348021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments