Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mijin Da Yake Shan Nonon Matarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam mace ce a duk lokacin da suka sadu da mijinta nonon ta kawai yake sha kuma gashi tana da karamar jinjira wai har ya kan shanye ruwan nonon duka yarinyar bata samun nasha idan har tafiya zai yi yakan so ta tatsi nonon ta bashi ya tafi da shi to wai dan Allah ya wannan alamarin ya ke a musulunci meye kuma matsayin wannan dan Allah ina jiran mafita.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Miji ya tsotsi nonon matarsa yayin da suke gabatar da sunnah wannan addini bai haramta ba. Sai dai kuma bai kamata shi mijin nata ya mayar da nonon tamkar abincinsa ba.

Wannan ya zo da bakon abu wanda zai iya zama cutuwa agareshi ko ga ita matar tasa ko kuma yarinyar da take shayarwa.

Don haka ya kamata ya ji tsoron Allah ya dena ketare iyaka. Mutum ya tsaya inda addininsa ya tsaida shi, kuma ya kyautata Dukkan mu'amalarsa ta auratayya.

Shan nono wanda yake haramta aure shi ne wanda aka yishi alokacin da mutum yake yaro karami bai isa yaye ba. Kuma sai ansha kamar sau biyar (cikakkun sha tare da koshi).

Shari'a ta halasta wa mutum ya ji daɗi da matarsa gwargwadon yadda ya so, amma ba tare da saduwa ta dubura, da kuma lokacin haila da nifasi, da lokacin harama da aikin Umra da Hajji ba, abin da ba wannan ba ya halasta miji ya ji daɗi da shi a jikin matarsa gwargwadon buƙata, kamar sumbanta, da kallo da shafa da makamantansu.

Hatta mutum ya sha nonon matarsa duk yana daga cikin jin daɗi halastacce, ba a hukunta shi da irin hukuncin shayar da ƙaramin yaron da bai cika shekaru biyu ba, domin shayar da babba nono ba ya tasiri wurin haramta abin da shayarwa kan haramta, nau'in shayarwar da ke tasiri shi ne shayarwar da aka yi wa yaron da bai cika shekara biyu ba.

An tambayi malaman Lajnatud Da'ima cewa: Mene ne hukuncin addini game da mutumin da kan ji daɗi da nonon matarsa har ya sha, shin abin da ya yi haramun ne ko halas, shin idan ruwan nonon matar nan ya isa zuwa hanjin mijin nan ta haramta a gare shi sai an raba auren?

Sai suka ba da amsa da cewa: "Ya halasta ga miji ya sha nonon matarsa, haramci ba ya aukuwa saboda isar ruwan nono zuwa hanjinsa". Duba Fataawaal Lajnatid Da'ima 19/351.

Sannan an tambayi Sheikh Ibn Jibreen game da wannan matsalar sai ya ba da amsa da cewa: "Shayar da babba ba ya tasiri, domin shayarwar da ke tasiri shi ne wanda ya kasance an yi sau biyar ko fiye a cikin shekaru biyu kafin yaye, amma shayar da babba ba ya tasiri, saboda haka, in da wani zai sha daga nonon matarsa, to shi fa bai zama ɗanta ba". Duba Fataawa Islamiyya 3/338.

Imamuna MALIK ya ruwaito a cikin Muwaɗɗa daga hadisin Abdullahi ɗan Umar ya kasance yana cewa: "Babu hukuncin shayarwa sai ga wanda aka shayar yana ƙarami, kuma ba hukuncin shayarwa ga babba". Duba Muwaɗɗa 2/603 na Imamu Malik.

Bisa dogaro da waɗannan dalilai babu laifi don mutum ya sha nonon matarsa, sai dai da za a tsotsa ba tare da shan ruwan ba hakan ya fi, amma shan ba laifi ba ne kamar yadda malamai suka bayyana.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa... 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments