Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhimmancin Ladabi Da Kyawawan Dabi'u Ga Masu Dangantuwa Ga Ilmi Da Ustanzanci

Malamai suna kasa Addinin Muslunci zuwa ga ginshikai guda uku; Aqida, da Ibada da kuma Kyawawan dabi'u da halaye. Don haka duka wadannan tushe guda uku abin nema ne a wajen bawa ya sansu ya yi aiki da su a aikace, ba a nazarce kawai ba.

Wannan shi yake nuna mana girman kuskuren wasu daga cikin masu dangantuwa zuwa ga neman ilmi da ustazanci masu sakaci da bangaren halaye da kyawawan dabi'u wajen mu'amala da mutane, saboda shi aiki da ilimin a aikace shi ne gaya mafi girma kuma mafi muhimmanci.

Siffantuwa da ladabi da kyawawan dabi'u wajen mu'amala, da nesantar munanan halaye na rena mutane da hasada da "hiqdu" (kulle mutum a zuciya), da nuna gaba da kiyayya, da girman kai yana daga cikin cikamako na ginshikan Aqidar Sunna kamar yadda Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya bayyana a cikin "Al- Wasidiyya", ya ce:

ويدعون إلى مكارم الأخلاق ومحاسن الأعمال ويعتقدون معنى قوله: " {أكمل المؤمنين إيمانا أحسنهم خلقا} . ويندبون إلى أن تصل من قطعك، وتعطي من حرمك، وتعفو عمن ظلمك؛ ويأمرون ببر الوالدين، وصلة الأرحام وحسن الجوار والإحسان إلى اليتامى والمساكين وابن السبيل والرفق بالمملوك؛ وينهون عن الفخر والخيلاء والبغي والاستطالة على الخلق بحق أو بغير حق؛ ويأمرون بمعالي الأخلاق وينهون عن سفسافها

"Ahlus Sunna suna kira ga kyawawan halaye da kyawawan aiyuka, kuma suna kudurta ma'anar fadin Annabi (saw):

"Mafi cikan imani daga cikin muminai shi ne wanda ya fi su kyawawan halaye"…

Har inda ya ce:

"Suna hani ga alfahari da girman kai da zalunci da karan tsaye wa mutane da gaskiya ko babu gaskiya, kuma suna umurni da madaukakan halaye suna hani ga makaskantan halaye (munanan dabi'u na mungun hali)".

Duba Fatawa 3/ 158 – 159.

Duk da muhimmancin kyawawan halaye da dabi'u, da kasancewarsu suna daga cikin rassan imani wadanda imani na wajibi ba ya cika sai da su, amma sai ka samu wasu masu dangatuwa ga ustanzanci da neman ilimi suna siffantuwa da munanan halaye, har ana iya siffantasu da girman kai da rena mutane, da karan tsaye wa mutane, a hade da hasada ga wadanda Allah ya yi musu wata falala fiye da tasu.

Abdullahi bnul Mubarak da Laith bn Sa'ad sun ce ma daliban hadisi:

 «أنتم إلى قليل من الأدب أحوج إلى كثير من العلم»

"Ku kun fi bukatar koyon ladabi dan kadan, fiye da bukatuwarku zuwa ga ilimi mai yawa".

Duba Mu'ujamu Ibnil Maqri'i (269), Tarikhu Dimashq 32/ 445, Al- Jami'u li Akhlaqir Rawiy 1/ 405, Sharafu Ashabil Hadis (122).

Wani daga cikin malaman Arabiyya da Adabi Abdullah Al- Badalayusiy ya ce:

إنك تجد في العامة الذين لم ينظروا في شيء من الأدب من هو حسن اللقاء، جميل المعاملة، حلو الشمائل، مكرم لجليسه، وتجد في ذوي الأدب من أفنى دهره في القراءة والنظر، وهو مع ذلك قبيح اللقاء سيء المعاملة، جافي الشمائل، غليظ الطبع.

"Za ka samu daga cikin gama garin mutane wadanda ba su yi nazari a wani abu na Adabi ba, wanda yake mai kyakkyawar cudanya da mutane, mai kyakkyawar mu'amala, mai kyawawan dabi'u, mai karrama abokin zamansa, haka kuma zaka samu masanin Adabi, wanda ya karar da rayuwarsa a cikin karance – karance da nazari amma duk da haka mai mummunar cudanya da mutane ne, mai mummunar mu'amala, mai kaushin hali, mai tsaurin dabi'a".

Duba Mu'ujamul Udaba'i 4/ 1529.

Saboda haka yana daga cikin wajiban Addini a kan dukkan musulmai, musamman masu dangantuwa ga neman ilimi da ustazanci su siffantu da kyawawan halaye da dabi'u, su nisanci miyagun halaye da mummunar mu'amala.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments