Da a ce Musulmai za su yi riko da Tafarkin Sunna, kuma su lura da Tarihi ya zama musu madubi kuma abin wa'azi, da ba su afka cikin fitintinun da suke gudana a tsakaninsu ba. Saboda Manzon Allah (saw) ya yi hani a kan jayayya wa masu mulki a kan mulkinsu, don a tsare jinane da dukiya da mata da mutunci da rabuwar kai da raunin al'umma.
Haka Tarihi ya nuna mana cewa;
jayayya wa masu mulki a kan mulkin nasu ba ya haifar da da mai ido. Tarihi ya
ba mu labarin natija na fitintinun da suka yi ta faruwa a Daulolin Muslunci na
asarar rayuka da raunin al'umma. Sa'annan a yau mun ga abin da ya faru a wannan
zamani a Misra da abin da yake faruwa a Syria da Libya da Yemen.
Iyakacin abin da zai faru shi ne
masu neman mulkin su yi galaba, daga baya a zo a hanbare su daga kan Mulkin.
Sai masu galaban da wadanda aka yi galaba a kan nasu su wayi gari cikin
mummunan karshe a Duniya da Lahira.
Shaikhul Islami ya ce:
حال المقتتلين
من المسلمين في الفتن الواقعة بينهم فلا تكون عاقبتهما إلا عاقبة سوء الغالب والمغلوب
فإنه لم يحصل له دنيا ولا آخرة كما قال الشعبي: "أصابتنا فتنة لم نكن فيها بررة
أتقياء ولا فجرة أشقياء". وأما الغالب فإنه يحصل له حظ عاجل ثم ينتقم منه في الآخرة
وقد يعجل الله له الانتقام في الدنيا كما جرى لعامة الغالبين في الفتن فإنهم أصيبوا
في الدنيا كالغالبين في الحرة وفتنة أبي مسلم الخراساني ونحو ذلك.
مجموع
الفتاوى (14/ 127)
"Halin masu fada da juna
daga cikin Musulmai a fitinu da suke faruwa a tsakaninsu, karshen wanda ya yi
galaba da wanda aka yi galaba a kansa shi ne mummunan karshe. Saboda ba zai ci
ribar Duniyar ba, haka Lahirar ma. Kamar yadda Al- Sha'abiy ya ce:
(Fitina ta same mu, ba mu kasance
masu da'a ma Allah masu Taqwa a cikinta ba, kuma ba mu kasance fajirai shakiyai
ba).
Amma wanda ya yi galaba to zai
samu rabo a nan Duniya sai kuma Allah ya kama shi a Lahira, kuma ta yiwu Allah
ya gaggauta masa kamu tun a nan Duniya kamar yadda hakan ya faru ga mafi yawan
wadanda suka yi galaba a cikin fitinu, saboda an kashe su tun a nan Duniya,
kamar yadda ya faru da wadanda suka yi galaba a Harra (fitinar Madina a zamanin
Yazeed) da fitinar Abu Muslim Al- Khurasaniy da makamancin haka".
* Ma'anar maganar Imamu Al-
Sha'abiy ita ce; sun shiga fitinar Ibnul Ash'ath ce bisa kyakkyawar niyya don
kawar da zalunci, amma ba su bi hanyar Sunna ba. Ya fadi maganar ce a gaban
Hajjaj bn Yusuf Al- Thaqafiy.
* Abu Muslim Al- Khurasaniy wanda
ya jagoranci da'awar kafa Daular Abbasiyya da sunan Ahlul Baiti, ya kashe
mutane masu yawa, har ya yi galaba aka kafa Daula, amma daga karshe Khalifa Abu
Ja'afar Al- Mansur ya kashe shi.
* Saboda haka, wadannan
kungiyoyin harka masu manufar Siyasa da kuke gani, kamar Kungiyar Ikhwan,
kungiyoyi ne na fitina, fitina mai halaka al'umma, mai gusar da karfinta, don
haka ku yi hankali da su.
* Sai su tsokano fitina a yi musu
kisan gilla, sai kuma su zo suna kuka suna nuna an zalunce su, don su ja
hankulan mutane zuwa ga kungiyar tasu, alhali abin da suka yi abin zargi ne a
Shari'a, saboda saba Sunnar Annabi (SAW).
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.